Halimatus’sadiya (sakayya)

5

by @102565813543784586917

____Direct event center yayi da su.

Suka fito ya dubi Qawwma ya Ambaci sunan ta.

Sai ta dan saki fuskar ta.

Siyama ta ce "Abi I think pack za mu, ko eatry??


Ya ce "No dinner mu ka xo."

Ta bata rai dan ta hango fadila iyar Aunty zulaih ta ce "Ni dai ba zan je ba ta buda mota ta shiga za ta rufe ya rike kofar, kamar yanda ya shawo kan Qawwma haka ita ma siyam duk da ta fi Qawwma taurine kai.  


Ya mika wa Ammi gate pass din ta Qawwmma kuma ankon ta shine gate pass. Ya dau ki Fatima, dayan hannun ya rike hannun siyama sai kuma a gefen sa in da ya dau Fatima Qawwma ta tsaya sai kuma Ammi daga gefan siyama suka shiga ciki. 


Empty table suka zauan su duka.  Siyama tin da ta zauna ta ke game da wayar Abi dan ko kadan ba ma ta so idon ta ya ga wani har ma ta mashi Magana. 


Qawwma itama amfani ta ke da wayar ta sai in wani ya zo gaishe da Abi sannan zata dago ta gasihe shi. Daga karshe Asif shima ya dawo wurin shi da family din shi hakan ya sa siyama sake wa ita da farhina.  


Kasan ce wa Abi na wurin ba wanda ya fadiwa Ammi maganar banza sai ma jan ta a jiki da suke yi na yaudara,  daman sun saba haka, in Abi bai wurin su taso ta gaba in kuma ya na nan su nuna mata so.


Suna yin hoto shi da amrya da beloved family din sa suka koma gida dan Fatima har tayi bacci.


Washe gari ranar daurin aure da wuri Abi ya fita kasan cewa daurin auren na safe ne karfe 10am.  


Su kuma sai  wurin 3 suka je dan har sai da suka dawo daga thafiz  sannan su ka tafi gidan bikin. Ammi ta samu wuri tayi parkin motar ta sannan ta fito ita da Qawmma. Bayan ta fito ta budai masu kofa fatima ta sauko siyama ta  zauna fuskar ta a daure ba ta da niyar fitowa.


Ammi ta ce siyama ki fito mu tafi. Siyama tayi shiru. Ammi ta kara mata mgn nan ma tayi shiru. Hakan ya bata wa ammi rai. Ta dauke ta ta fitar da ita daga motar ta sa luck a motar suka wuce suka bar siyama a wurin sai hura hanci take.


Da isar su suka shiga ciki tin da ga falfajiya ta fara gaishe da mutane wasu su amsa wasu su yi banza wasu ko kallo ba za ta sa mu ba. Haka ma a parlour suka gaishe da mutane da ke ciki sai ta wuce dakin Aunty Zulaiha, da shigar ta ta gaishe da su haka ma wasu sun amsa wasu ko kallo bata samu ba. Hakan ya karawa qawwma rai.


Ko da tayi Allah san ya alkairi ba wanda ya tanka ta, ta kama kanta ta fita ita da ya’an ta suka koma in da su Mummy suke, ita da matar uncle bubu da uncle hamza. Daman su ka dai ne mazan dakin su Abi.


Siyama dake waje jin ki ne da motar Ammi. Aunty lubna, husna da kursum suka samai ta a wurin. Husna ta ce "Siyama miyasa ki ke waje? 


Lubna ta rike hannun ta ta ce zo mu shiga.


Siyama ta girgiza mata kai.

Lubna ta ce waya duke ki fada min waya taba ki. 


Mahir ya karaso kusa da su shi da abokan sa biyu ya tambaye su miyafaru.


Husna ta ce "Mun dawo daga rakiya mu ka ganta nan jinki ne kuma ta ki mgn."


Mahir yayi murmishi ya ce 'Siyama kin batawa ammi rai ko. Shi ke nan mu je ciki na bata hkr.


Nan ma ta mashi shiru ba ta ce masu komi ba ta ci ze taki tafiya ta ki magana.


Kursum dake cikin jerin wanda ba su san su ta yi tsaki ta ce "Da alla ku kyale ta sai wani bin ta a hankali ku ke ta na maku bakin hali irin na uwarta.


Mahir ya juyo ya kalli kursum bai ji dadin mgnr ba sai dai bai iya ce mata komi ba sbd ta girme su.


Tayi tsaki ta koma ciki. Dakar lubna da mahir suka samu ta shigo ciki. Lubna ta kai ta inda su Ammi ta ke ta tambaye ta mi a ka wa Siyama.


Ammi ta ce "Sheganta ganta ta fi karfin kanta."


Lubna tayi karamar dariya ta ce ay ta dai na...


A takaice sai bayan magariba suka koma har da su Mummy. 


(FLASH BACK)


ASIM INUWA CHALAWA

Asim Inuwa, d'a ne ga Alhaji Inuwa, wanda su ne yan majalisar kano, suke da ikon yanke hukuncin da ya shafi politic din kano. Mahaifiyar shi yar'ce ga formal sarkin Borno kanwa ga present sarki.


Asim yanada twins brother Asif wanda suke kama kamar ma har ta baci dan ba kowa ke gane su ba sai mahaifiyar su musanman da suke yara hatta uban su bai gane su sai da suka ta sa suna shekara shida kasan cewa Asim shi ne hassan bai jin Magana kiriniyar shi tafi karfin kan sa, suna kutsin wasa ya yi tintubai ya fadi kan sa ya bige da bench na ajin su, ya ji ciwo a gefen goshi wanda ya sa a ka masa stiches, mafarin ke nan  aka fara banbance su Asim na da dinki a gfen goshi Asif kuma  bai da shi, malaman makaranta sun ji dadin haka dan biyun nan suna sa masu ciwon kai basa iya gane takamaimai mai laifi amma yanzu za su iya gane wanda yayi laifi. 


Sune na hudu a wurin mahifiyar su a haihuwa, na 10 a wurin Alhaji Inuwa. 

Asim ya kammala degree din sa a Uganda inda suka karancin digital enterpreneauship.


Bayan sun gama, dama ka idar Alhaji Inuwa in yaro ya gama degree ya na bashi jari. Ya basu jari suka fara business. Asim ya budai shagon provision shi kuma Asif kitchen untensil. 


Bayan shekara uku da fara kasuwancin su ya ba kowa offer shi dan a aje ta ke sai dai ba zaka fara aikin gwanati ba har sai kayi kasuwanci na shekara uku haka Alhaji inuwa yake tafiyar da tsarin gidan sa. 


Kasuwan cin sa ya bunkasa ya kai da ya budai company na drinks da gana ya budai na waffer da bisciut. Wanda a yanzu next target din shi zai budai confectionaries(company na sweet da chocolate)


Masha Allah kasuwar Asim ta habaka daga shago ya mai da ta karamar mall, yayi rejecting offer mahaifin sa dan shi ya fi son kasuwancin sa sama da aiki, sai dai aka ba immediate kanna sa Abubakra(bubu) duk da akwai mace tsaknin su sai dai ita iyar uwar gidan ce kuma shi alhaji Inuwa yayan shi mata ya fi son su da lecturing. Shi kuma Asif ya hada biyu da aiki da kasuwanci duk da sai dai ya sa yara a shagon sbd  aikin gwamnatin da ya ke.


Alhaji Asim mutun ne mai son gayu da nuna wayewa ko kadan bai jin kyashin kashe ko nawa  a kan yayan sa da matar sa. Mutune mai son ya'ya wanda ko kadan bai son ganin bacin ransu akan su zai iya komai Hakan ya sa dangin sa suke kin yaran musanman Ammi a ganin su ita ke kitsa mashi komi ita ke mulkan sa. Suka jefata an kan ta mallake masu dan uwa da bai basu kulawa. 


Halimatu Wada 

wato Ammi mata ga alhaji Asim, Uwa ga Qawwama, Siyama da Fatima. Halimatu cikakkiyar yar kano ce. Mahaifin ta ya rasu tana yar shekar 2, ya mutu ya bar mahifiyar ta da ya'ya 5. Mahifiyra ta Khadija Kubra ta sake aure bayan mutuwar mahaifin ta sai dai auren baiyu ba sbd mijin da ta aura ya nuna bai son ya’yan ta sai dai ta kai su gidan su ko gidan yanyun ta ba dai gidan shi ba. 


A lokacin halimatu na shekara biyar ita kuma Kubra ba uwa garaita ba balle ta kai Halimatu wurin ta ba mahaifi gare ta ba kuma sauran yayan ta maza ne da suke da mata dama ta na da yar'uwa mace sai ta kai ta wurin ta. Sauran mazan uku suna wurin dangin marigayi sai kuma mace Hannatu wadda ta ke wurin ta. Sulaiman sabon mijin na ta ya tuberai akan shi ba  zai dau agola gidan sa, hakan ya sa Kubra ta naimi saki. Ya sake ta. 


Da dan kudin gadon ta ta nai ma masu gida ita da yan’yanta biyu mata ta cigaba da kulawa da su tana fadi tashi har Allah ya hada ta da Malan Yakubu, ya aure ta ya cigaba da kulawa da ita da ya’yanta biyu ita kuma ta hada da ya’yan shi bakwai mata hudu maza uku wadda mahaifiyar su ta rasu. Yara biyu ta Haifa tare da shi mace da namiji.


Malan Yakubu shima dan kasuwa ne mai biga na biga chan sai dai har ya tsufa kasuwar shi bata yi karfi ba. Kafin wannan lokacin suna fiskan tar HAALIN RAYUWA iri iri sai dai duk da haka yana kokarin wurin ganin yaran sa sun yi karatu musanman matan. Idan matan suka gama secondry ya na aurar da su in sun samu miji in ba su samu ba haka zai jajirce su fara NCE ko diploma kar dai su zauna hakan nan mazan kuma suna bin sa kasuwa duk da ya saba wasu ya kai su makaranta wasu kuma ya bar su a kasuwa.


Asim ya hadu da Halimatu a kan hanya zai je gidan kannen baban sa Alhaji maala. Har yayi gaba ya dawo ya sha mota gaban ta kasancewa ba babban titi ne ba bisa lungu gidan ya ke.


Ta kauce daga wurin motar shi kuma da sauri ya fito tare da yi mata sallama jin yayi salma ta amsa shi ba tare da ta juyo ta kalli wake mata sallama. Ya ce tambaya na ke.


Ta ce "Allah sa na sani."

Ya ce "Kin ma sani."

Ta ce "Toh ina ji."

Ya ce "Number wayar ki na ke roko."

Ta ce "Ban da waya."


Da mamaki ya maimaita sai kuma ya xe"Toh dan Allah address din gidan ku fah."


Ta ce "Ka nema da kan ka." Zata wuce ya kara shan gaban ta ya ce "Dan Allah ina zan nemai shi a garin kano."


Ta ce "Wannna kuma damuwar ka ce, bai da ce in tsaya da wani sauriya ba a kan hanya dan haka sai anjima." Ta wuce ta gefen sa ya juya yana kallon ta yana jiran ya ga gidan da zata shiga sai bai gani ba har ta fita titi. Ya na so ya bi ta sai dai kuma saqon Alhaji ba yanda ya iya ya shiga mota ya wuce gidan kawu mala.


Daga ranar Asim yake zuba ido ko Allah zai sa ya kara ganin Halimatu ko kuma ya san gidan su dan ta kwanta mashi a rai musanman kamin kanta. Haka ya cigaba da baza ido har ya fidda rai ya cigaba da harkokin sa. 


Bayan wasu watanni sun zo gidan kawu mala suna shashen Mummy ta biyu ga Alhaji mala. Halimatu tayi sallama.


Idon sa na kan wayar sa ya dai ji muryar sound familiar sai dai bai dago kan sa ba. Ta karaso kusa da Asif ta aje masu lemu da ruwa a tsakaknin su zata mike kamar an ce mashi ya dago kan sa yana dagowa idon sa suka fada kan fuskar Halimatu. Kara budai idon sa yayi da kyau dan tabbatar wa itace sai dai ita kuma ta na tashi ta fice ya bi ta da kallo. Ya na mamakin mi ta zo yi a gidan kawunsa, ko kuma gizo ta ke mashi. 


Mummy ta katse shi daga tinanin sa. "Kai Asim tunanin mi kake yi kai da ba mata ba balle yara."


Murmishi yayi kafin ya ce "Mummy ashe kina da mai aiki na dauka su Yasmin ke aikace aikacen gidan nan."


Asif ya ce "Ji wata Magana kai yanzu sai a ce ma su ke aikin gidan sai ka yarda."


Ya ce "Ahh minene a ciki daman mata da aiki a ka sansu."


Mummy ta ce "Halimatu ta dadai a nan kowa dai da portion din sa su ma su Yasmin suna da aikin su."


Asif ya ce "Ashe namesake din umma ce."


Asim ya ce "Gaskiya kam gwara su iya kar sai sun je gidaja-janzu a samun mtsl."


Mummy ta ce "Ashe dai ka ganai.." 


fira su ke amma Asim hankalin sa na kan Halimatu so ya ke ya tabbatar wa kan sa wadda ya ganin ce a kan hanya ko kuma wata daban.


Halimatus'sadiya(sakayya)

Meenamajeed🥀


Don't forget to vote, comment & share.


Thank you🙏