TURƁAYA

Unfinished Ties

by @zeeyluv

🔥TURƁAYA🔥


Story

and 

written


By


Zainab Bint Abdulrahman 


(Zeeyluv💞



*** 


*From the most precious Association*


YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION 

(YOTA)


YOTA KO DA KUƊINKA SAI DA RABONKA💃🏻💃🏻💃🏻




Page................6


Ko waigowa bai yi ba balle ta saka ran zai amsa ta. Ya na fita kai tsaye wajen motar shi ya nufa. Faɗawa cikin ya yi ya zauna ya na dafe kanshi. Maganar Ummie ne ya dinga dawo mishi kunne ɗayan bayan ɗayan su na maimaita kansu kamar yanzu Ummie ke mishi maganar. Tuna abin da ya yi Ummie ya yi ya ce "Ya Allah me ya hau kaina ne yau da har Ummie za ta dinga magana ina maida mata" Sauke ajiyar zuciya ya yi haɗe fice daga cikin motar ya nufa cikin gidan.


"Ummie me ya sa ba za ki fahimta ba Ya Asad ya na da gaskiya, da kin hana shi zuwa inda muke. Ummie ina ƙarama sosai lokacin da ya bar mu wanda ba ma zan iya tantance kamannin shi ba a lokacin, amma duk da haka na tuna lokacin da ke da Ya Asad ku ke yin aiki tuƙuru domin ku ganni cikin farin ciki da walwala. 


Abie ya ba wa sauran ƴanƴanshi duk kayan more rayuwa da farin ciki amma ya manta damu a rayuwar shi. Lokacin da Ya Asad ke ɗauka ta a kafaɗa ya kai ni makaranta, su kuma su Hamra da Nudrat a motoci masu tsada ake kawo su. Duk da arziƙin Allah ya ba shi bai taɓa waiwayar mu don ya sauke nauyin mu da rataya a kanshi ba, tsawon shekarun nan bai taɓa zuwa ya ganmu ba sai yanzu da mu ka zama mutanen abin alfahari, Ummie don me ya sa za ki bashi damar zuwa nan yanzu?" 


"Farhat! Ya isa haka" cewar Asad da ya shigo cikin parlourn. Sannan ya juya zuwa ga Ummie ya ce "Ummie na zo na baki haƙuri ne a karan farko na ƙi bin umurnin ki, i'm sorry Ummie, kin san wannan ba ɗabi'ar ɗanki bane saboda ba tarbiyyar da kika ba shi ba kenan kawai na kasa controlling ɗin fushi na ne a kan shi. Idan ki na son na haɗu da shi ba damuwa in sha Allah zan yi yanda ki ke so" Da sauri Ummie da Farhat su ka ɗaga kai su na kallon shi cikin mamakin furucin shi. Ya ƙara da cewa "Sannan Farhat ma za ta kasance a wajen" Farhat na jin haka ta yi ɗakinta cikin kuka. 


"Ummie rashin haɗuwa ta da shi ya na nufin kasawa, sannan wacce ta tarbiyyantar da ni ita ce abin tambaya. Ke kika koyar da ni kan cewa duk lokacin da mu ke da baƙi mu yi iya yinmu wajen kyautata musu, na san ki na tabbaci a kan ɗanki ba zai taɓa kunyatar da ke ba a idon bare ba" Ya na kai wa nan ya sa kai ya fice.....


************************************


POV: ABIE/AMMIE


"Kiranta ka sake yi a waya yanzu Lateef? Duk da abin da ka jawo mana jiya na cin mutuncin a wajen ɗanta. Bangane wannan abin ba. Ɗan ƙaramin rauni Asad ya ji amma yanzu ka na neman hanyar da za ka samu keɓantuwa da ita ta dalilin wannan"


"Abie ya ce Arwa! Arwa don Allah ki saurare ni yanzu in ya so daga baya duk abin da kika ce na yi zan yi na miki alƙawari" Zama ta yi ta na hawaye. Abie ya cigaba da faɗin "Zan faɗa miki wannan maganar ne saboda na fitar da ke daga zargi da kokonton da kike ciki kullum. Ki yarda da ni bana son na yi wani abu a bayan idonki Arwa, sannan ki tuna zan je can ne don na ga Asad ba wai don na ga Leen ba"


"Ki saurare ni yanzu. Misali a ce ina tare da su ne ba tare da ke ba. Saurin girgiza kai Ammie ta yi. Abie ya ce misali fa na ce miki, ki ƙaddara hakan a matsayin misali to sai wani abu ya samu ɗanki Afeef, ba za ki so na zo inda ya ke ba domin na ga lafiyar jikin shi ba? Ba jira amsarta ba ya ci gaba, to ta ya aka yi Asad ya ji raunin nan za ki duba. Afeef aka kawo wa harin nan sai Asad ya kare shi a matsayin shi na babban yayanshi, to yanzu da Afeef aka samu fa? Arwa ɗanmu Afeef fa! Da ya za mu yi? 


Arwa na san na banzatar da ƴaƴan nan tsawon lokaci ba tare da na damu na bibiye lamurar su ba amma wannan karon abin daban ya ke. Asad ya bada rayuwar shi don ya cece rayuwar Afeef ɗanmu. Ya sauke nauyin shi a matsayin shi na babban wa, nima yanzu ya kamata na sauke na wa nauyin a matsayina na uba. Arwa ina son na gansu a karo na ƙarshe idan da dama amma ba zan taɓa zuwa ba idan ba ki bani damar yin hakan ba" 


Cikin kuka ta ce "Indai wannan shine na ƙarshe ka tafi ba zan hanaka ba" Ta na gama faɗin haka ta tashi ta fita wani sabon kuka na taho mata. Ita har ga Allah ba komai ya sa ta ke nesanta shi da ƴanƴan shi na wajen Leen ba sai dai ta na tsoron tsohuwar soyayyar shi da ita ya farfaɗo ne saboda ta san yanda ya ke son Leen ɗin matuƙa kuma ta san a komai Leen ɗin ta fita shiyasa ta ke tsoron mijinta ya saɓuce mata saboda itama ta na sonshi shine farin cikin rayuwarta.


****************************


Washe gari


POV: HAYAT 


Tun safe ta ke farin ciki yau saboda Uncle ya ce su shirya gaba ɗayan za su je shopping daga nan su zagaye gari. Kasancewar ta akwai shegen son yawo ya saka komai cikin ɓacin ran da ta ke ciki da ta ji maganar zuwa yawo za ta ware ta yi ta walwalarta, don ga dukkan alamu ma har ta manta abin da ta aikata jiya da su ka fita da Uncle ɗin. 


Ta riga kowa gama shiri hakan ya sa ta zo ta tasa Aunt Laylah a gaba da mitar ba ta shiri cikin sauri za ta ɓata musu lokaci. Haka su ka yi tsiyar su su ka gama yanda kasan saƙon juna saboda yanda Hayat ta mayar da Aunt ɗin babbar ƙawarta ba ta taɓa yin ƙawa ba a rayuwarta tsawon shekaru Aunt Laylah ce ƙawarta, aminiyarta sannan kuma uwa a gare ta.


Ɗaya daga cikin manyan wajen shaƙatawa da ake ji da shi a garin Cairo su ka nufa bayan sun gama shopping. Su na tafiya su na hirar su gwanin ban sha'awa cikin wasa da dariya. Hayat da ta samu abin dariya ai kuwa ta zage sai dariyar ta ta ke yi hankali kwance daidai su na ƙarasowa mazaunin su. 


Aunt Laylah ce ta lura da irin yanda mazan wajen ke ta bin Hayat da kallo hakan ya sa ta zungure ta ta na faɗin "Hayat wani irin dariya haka ko kin manta a waje kike? Haka ya kamata a ce mace na dariya cikin jama'a? Yanzu ki duba yanda mutane ke binki da kallo"


Hayat ta dafe kai ta na faɗin "Oh gosh! What is wrong Aunt? Idan mutane na kallo so ki ke yi na dinga dariya haka? Ahn hn?" Dariya Uncle ya fashe da shi ya dungure mata ya na faɗin "Hayat you won't kill me laugher" Hayat ta ce "No Uncle like serious ko da a hakan na yi dariya definitely dole sai mutane sun kalle saboda shi mutum ba'a iya mishi, so shiyasa is better idan za ka yi abu kawai ka yi shi kanka tsaye ba tare da shakkar abin da za su faɗa ba idan ba haka ba wata rana sai sun kaika wuta"


Dungurin ta Aunt ta yi ta ce "Parrot caacaacaa! Ɗaya na faɗi amma ke sai kin faɗi ɗari i wonder idan bakinki ba yi miki zafi ne idan ki na wannan shegen surutun na ki na fama" 


Daga bayan su su ka ji an kwashe da dariya hade faɗin "Wow amazing lady" Da sauri Aunt Laylah ta juyo zuwa inda ta ji sautin maganar ya fito. Wasu matasa ne su uku wanda da gani kasan ba sa jin magana irin mayun matar nan ne. 


Hayat ta kalle Aunt Laylah da Uncle ta gefen ido za ta yi magana Aunt ta yi saurin dafe mata hannu ta na girgiza mata kai alamar kar ta tanka musu. Amma ina a banza don ba ta barin ta kwana.


Murmushi ta yi ta na miƙewa Uncle zai yi magana ta ɗaga mishi ta na girgiza kai alamar ya bar ta kar ya ce komai. To sanin halin na ta da idan ta yi niyyar yin abu to da wuya ta hanu hakan ya sa ya ƙyaleta. Tattaki ta yi zuwa table ɗinsu da su ke zaune. 


Ganin haka ya sa su ka sha jinin jikinsu don Hayat kam ba dai ƙwarjini ba. Ganin sun ɗan razana da miƙewarta ya sa ta ƙara saita kanta cikin murmushin ta na ko yaushe da bai bari fuskarta ta ce "Hey! I'm Hayat! Hayat Taufeeq" ta yi maganar ta na miƙa musu hannu alamar su gaisa. Girgiza kai su ka yi su na zazzare ido cikin i'ina ɗaya ya ce "I'm Laziz" Ɗayan wanda shine ogansu ya ce "I'm Muzai Badani"


Ta ce "Wow Mr. Badani nice to meet you" Cikin yaƙe su ma du ka haɗa baki wajen faɗin "Nice to meet you too" Hayat ta ce "Yauwa tun da mun zama abokai yanzu za ku yi min wata alfarma ɗaya ina son ku kula min da Auntyna da Uncle ɗina kafin na je na yi wani aiki na dawo" Cikin sauri su ka ce "Em em dama makaranta zamu tafi yanzu kuma mun yi latti" Ta ce "Fine to a tafi makaranta lafiya" Ta yi maganar ta na musu waving hannu alamar bye. 


Juyawa ta yi zuwa wajen su Aunt Laylah ta ce "Aunt ni na tafi ganin waje see you soon"

Dariya Uncle ya kwashe fa shi ganin yanda cikin sauƙi ta yi maganin ƴan iskan ba tare da tashin hankali ba. A ranshi ya na jaddada kwanya da basira irin na Hayat ɗin. Aunt Laylah ta ce "Amjad wannan ba abin dariya bane yanzu ya zamu yi da ita da wannan halin na ta? Sannan a haka ne har ka amince mata ta zauna a Cairo ita kaɗai, is not possible to leave her alone here in Cairo" Waitress ɗin da ta zo wajen ɗauke da menu ne a hannunta ta katse musu zance daga haka ba wanda ya sake cewa komai.....


Tafiyar ta ta ke yi cikin kwanciyar hankali da annushuwa ta na tafe ta na ɗaukar duk abin da ta ga ya burgeta a hoto. Haka ta cigaba da ganin abubuwa daban daban ma su kyau da ban sha'awa musamman abubuwan tarihi. Asad da ya karyo kwana a motar shi da gudu ya yi sauri taka burki ji kake ƙiiiiiiiiiiiiiiii! Tuni Hayat ta kai ƙasa saboda gefen motar da ya bugeta wanda hakan har sai da ya yi sanadiyar ɓarin da ya yiwa wani mai siyar da kayayyakin flowers a kan barrow. 


Da sauri ya fito a motar ya nufa inda ta ke yashe a ƙasa ta juya mishi baya. Cikin kulawa ya ce "Are you okay?" A fusace ta juyo ta na faɗin "Oh my goodness what's wrong with yo....." Sauran maganar ya maƙale mata a baki sakamakon wanda idonta ya yi tozali da shi. 


Kallon kallo su ka shiga yi a tsakaninsu kowanne ya na tuna farkon shekarun thaɗuwarsu wanda the same incident ne ya haɗa su. Ita fara katse shirun na su da faɗin "You! Are seriously following me all around?" Bai kulata ba ya miƙe tsaye abin shi ya saka hannu a aljihun wandon shi ya ciro kuɗi ya na miƙa wa mai siyar da kayan flowers ɗin ya ce "Karɓi wannan na san an jawo maka asara da yawa"


Hannu mutumin ya sa ya karɓa hannun shi na rawa ganin ninkin kuɗin kayan shi da aka ninka mishi. Daga haka ya juya zai nufa wajen motar shi cikin azama Hayat ta sha gaban shi ta ce "Wato ga mahaukaciya na magana dole ka yi banza da ni. Jama'a ku kira min ƴan sanda don Allah wannan mutumin mai laifi ne karo na biyu kenan ya na ƙoƙarin kashe ni, gashi yanzu ya sake yinƙurin yin haka" 


Asad ya ce "Listen to me" ya yi maganar yana ɗan matsowa kusa da ita. Hayat ta ce "Don't dare come closer to me, stay away from me or else" ta ciro pepper spray ɗin ta da ke cikin jaka ta na nuna shi da shi. Ta ci gaba da faɗin "Na san irinku sosai, daga ni ma kai abin zargi ne. Kawai ka ga mace sai ka fara ƙoƙarin bin ta duk inda ta je. Do you know what? Thanks to this pepper spray, wannan kaɗai ya isa na yi maganinka da shi ta hanyar da za ka daina bibiyata duk inda na je"


Asad ya ce "Ai ba ki buƙatar pepper spray wajen kare kanki wannan zazzaƙar muryar ma kaɗai ya isa" Hayat ta ce "My goodness what's with you? What do you think of me huh? Ina maka magana ka na neman ka banzatar da ni koff koff koff" Tari ya sarƙe ta ba tare da ta ƙarasa maganar ta ba. Asad ya yi saurin miƙa mata ruwa cikin rashin lura da wanda ya bata ruwan ta amsa har za ta kai baki cak ta tsaya ta daga kai haɗe da dungurar mishi da ruwan shi a hannu ta ce "Ko da mutuwa zan yi ba zan taɓa amsar ruwa a wajen mutum irinka ba" 


Juyawa ya yi zai bar wajen ba tare da ya sake ce mata komai ba ta kalle mutane wajen ta ce "Yanzu ba za ku ce mishi komai ba wanda ya damu bayan kun san shi ya jawo hatsarin?" Ɗaya daga cikin dattijon da ke wajen ya ce "Hakane ta na da gaskiya yaro kana gudu sosai a hanya" Cikin ƙufula Asad ya ce "Ya kamata na isa gida yanzu saboda ahalina su na jira na" Dattijon da ya zama interpreter a tsakaninsu ya juya zuwa ga Hayat ya ce "Ya ce Ahalin shi na jiran shi ne a gida shiyasa"


Hayat ta ce ba shi kaɗai ya ke da ahalin da ke jiran shi ba ai saboda ya kamata ku dakatar da wannan rainin hankalin na shi" Dattijon ya sake juyawa zuwa ga Asad ya ce "Ta fika gaskiya" Cikin fusata Asad ya ce "Look it was my mistake, i apologized, zan iya tafiya yanzu? Ina bukatar tafiya" Dattijon ya sake juyawa zuwa ga Hayat cikin kwantar da kai ya ce "He needs to go"


Hayat ta ce "But, by the way why are you interfering? Zan iya kwatar wa kaina ƴanci ba tare da taimakon ko wannenku ba saboda haka na gode sosai" Ta yi maganar ta na haɗe hannu waje ɗaya alamar godiya sannan ta yi tattaki zuwa gaban Asad da ya rasa ma me zai yi mata ya huce takaicin shi.


"And by the way you why are following me like that? Shin haka kowa ya ke yi a nan kasar?" Ta ƙarasa maganar cikin tsiwa. Asad ya matso dab da ita ya ce na san daga ƙasar turai kika fito zan iya faɗin haka daga yanayinki, but originally you are... "Stay away from me" Ta katse shi ta hanyar pointing ɗin shi da pepper spray ɗin da ke hannunta tun ɗazu ta ƙara faɗin "I told you not to come close to me mister. Or do you want me to" Ta yi maganar danna abin feshin spray ɗin kusa da fusakan shi amma ga mamakinta abin yaƙi fesuwa. Da mamaki ta sake danna abin ta na faɗin "Oh my goodness what's wrong with it" amma still yaƙi yi, juyo da shi fuskarta ta yi ta na sake gwadawa cikin rashi sa'a kuwa sai a idonta.


Ihu ta fara ta na faɗin "Please help. water. Someone please give me water. Somebody help me please" Ruwan da ta ce ko za ta mutu ba za ta taɓa karɓar ruwan a wajen mutum irin shi bane shi ya sake miko mata. Cikin sauri ta amsa ta na faɗin ''Open please" Buɗewa ya yi ya shiga zuba mata a hannu ta na watsawa a idon har yaji ya fita. 


Ɗago kan da za ta yi kawai taga shi ya ba ta ruwan cikin masifa ta ce "Don me ya sa za ka bani ruwanka bayan na faɗa maka ko mutuwa zan yi ban zan karɓa ruwa a wajenka ba, Shin ba ka gane abin da na ke faɗa ne?" Ta na cikin masifar ya sake miƙa mata raguwar ruwan gorar ta karɓe ba ta san ta karɓe ba sai masifanta kawai ta ke zubawa. Asad ya ce "Incredible foolish" Daga haka ya juya ya nufa motar shi ba tare da ya sake kallon ko inda take ba. Itama juyawar ta yi sai a lokacin ta lura da ruwan da ke hannunta ta juyo a fusace za ta sake tada wani bambamin sai dai ta makaro don tuni har ya fige motar shi ya yi gaba. Ta ce "Bloody Stupid"


********************************


Tun safe Ammie ta shiga kitchen ta na ƙoƙarin yin abin da zai faranta wa Abie rai, don a zuciyar ta ƙuduri cewa za ta yi duk yanda za ta yi ta faranta mishi rai yau ɗaya tun da har ya mata alƙawari cewa daga yau inda ya je ga Asad ba zai sake waiwayar su ba wannan shine na ƙarshe. Hakan ya sa itama zage ta na haɗawa Asad lafiyayyen koshari (wani abincin gargajiya ne a Cairo). Mom ta shigo kitchen da mamaki ta tsaya ta ke kallonta saboda ta san ba koshari bane a timetable ɗin su na yau ba. Kasa daurewa ta yi ta ce "Arwa wannan kosharin fa me za'a yi da shi?" 


Cikin fara'a Ammie ta ce "Oh Tante ban faɗa miki ba ko, na yi magana da Lateef ya yi min alƙawari ba zai sake waiwayar Leen ba" Mom ta washe baki ta na faɗin "Yauwa Arwa kin yi abin da ya dace" Ammie ta ce "Amma ya ce min ya na son ya je ya duba jikin Asad a ƙaro na ƙarshe da ba zai sake neman su ba, amma idan har na amince da hakan idan kuma ban amince ba zai je ba. Ni kuma na ce mishi ya je na amince tun da ya yi alƙawarin wannan shine na ƙarshe shiyasa na ke shirya mishi abin da zai kai wa Asad ɗin kar ya je empty handed" 


Take annurin fuskar Mom ya dishashe daga fara'ar da ta ke yi. Ta ce "Yanzu idan na yi magana ki ce na fiye magana da yawa" Cikin takaicin Ammien da rasa abin da za ta ce mata ne yasa kawai ta fice ta bar mata kitchen ɗin. Ammie ta ce "Ya Allah Tante me kuma ya faru?" Ko kallon inda ta ke Mom ba ta sa ke yi ba ta saka kai ta fice zuciyarta a harsale. 


Ammie ta ce "Ko me yake damun matar nan ne oho, matar kamar mai aljanu yanzu yanzu ka ganta daidai yanzu yanzu kuma ka ga ta sauya" Ba ta damu ba ta juya abincin a cikin ɗan madaidaicin flask mai kyau ta fito da shi a hannu ta nufa ɗaki wajen Abie.........


Ko da Mom ta bar kitchen ɗin ba ta tsaya ko ina ba sai bedroom ɗinta. Safa da Marwa ta shige a ɗakin ta na surutu ita kaɗai, can ta ce "Kai ba zai yiwu ba dole na san abin yi da zai hana Lateef zuwa can gidan. Har abada babu Leen babu Lateef inda dai ina numfashi a duniyar nan saboda komawar Lateef da Leen tare ya na nufin tonar asirin da muka binne shi ne shekaru ashirin da su ka ce wuce. 


Leen mace ce mai masifar wayo da basira da babu wanda zai taɓa juya ta yanda ya ke so saɓanin Arwa da sai abin da na shirya mata ta ke bi ba tare da ta san amfani na ke yi da ita ba" Nauyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta na furta "To yanzu meye abin yi?" Ta yi wa kanta tambayar.


"Kiswar" Amsar da zuciyarta ya ba ta kenan. Wani shu'umin murmushi ta yi ta ce "Tabbas Kiswar ita ce kaɗai mafita ta a yanzu musamman yanda Arwa ta ke son ta ga anyi auren ƴarta Hamra ba za ta bari wannan damar ya ƙubce musu ba idan damar ta zo, saboda haka wannan shine kaɗai hanyar da za ta bi ta dakatar da Lateef daga zuwa wancan gidan" Cikin hanzarin ta ɗauko wayarta ta na lalubo numbar Kiswar ɗin..........


*****************************


Daga bangaren Ummie kuwa tun da ta tashi yau ta ke jin ta cikin wani irin farin ciki na musamman, irin farin cikin da ta manta rabon da ta yi irin shi a rayuwarta , farin ciki ne irin wacce duk wata mace ke tsintar kanta a ciki lokacin da mijin ya yi tafi zai dawo zuwa gareta. Tun da gari ya waye ta shiga kici-kici a kitchen ta girka wannan ta girka wancan. Duk wani nau'in abinci da ta san Abie na so sai da ta girka shi. 


Bayan ta gama ta zo gaban wardrobe ɗin sai faman zaɓen kayan da za ta saka ta ke yi, ta saka wancan ta cire ta sake saka wani ta cire haka ta dinga har ba ta san adadin lokutan da hakan ya ɗauke ta ba. Idonta ne ya saukar mata a kan wani baƙar Abaya mai kyaun gaske nan ta ke ta tuna da rayuwarta na baya tare da Abie lokacin da ya taɓa siyo mata wani koren Abaya bayan ta saka ya kalle ta cikin so da ƙauna ya ce "Leen ki na kyau cikin baƙin kaya a duk lokacin da na ganki cikin irin wannan shigar sai na ji dama na dauwama cikin kallonki har abada ba tare da na ƙyafta ba ko da na second ɗaya ne kuwa" 


Hawayen da ya gangaro mata a bisa kuncinta ta yi saurin sharewa tuna rayuwarsu na baya ita da Lateef da su ka yi cikin tsananin so da ƙaunar junan su a zaman auren su tamƙar ba za su taɓa rabuwa ba ya kan sa ta ji ba ta jin zafin abin da Lateef ya yi mata soyayya har ta sake saka ran wata rana za su sake kasancewa cikin wannan rayuwar domin har yanzu ta na jin numfashi auren wanda hakan ke nuni da cewa bai mutu ba gaba ɗaya......


Baƙar abayar ta ɗauka ta ajiye a saman gadonta kafin ta shiga wanka. Ta daɗe ta na dirjen jikinta a bathroom ɗin kamar wanda ta shekara ba wanka tsabar yanda ta ɗauki lokaci a ciki. Duk wannan abin da ta ke yi Farhat na ankare da duk wani motsinta wanda hakan ba ƙaramin sake tunzura ta ya yi ba ganin yanda Ummien na su ke rawar jikin ganin mutumin da ya watsar da su tsawon shekarun nan. 


Wanda dududu a lokacin ko shekaru 4 ba ta cika ba a duniya ya saka ƙafa ya watsar ba tare da tunani ko lissafin halin da za su shiga ba wai amma shine Mahaifiyarsu ke wannan rawar jikin a kanshi. A zuciyar ta na ayyana irin girman soyayyar da ta ke mishi......


*******************************


Cikin sauri Abie ya fito sanye da shiga ta alfarma da ya ɓoye asalin shekarun shi wanda idan ka ganshi da Afeef ba za ka ce shi ya haife shi ba balle kuma Asad wanda shine babban ɗan shi. Duk wanda ya kalle fuska Abie a ranar sai ya tabbatar cewa ya na cikin farin ciki na musamman wanda hakan ya kasa ɓoyuwa. Ƙris ya rage su ci karo da Afeef. Saurin ja da baya Afeef ya yi ya na faɗin 


"Afwan Ya Abie" Ya yi maganar ya na ta bin Abien da kallo cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa shima a fuskarsa ganin wai yau Abien ne da kanshi zai taka ƙafarsa a cikin gidan yayan shi Asad. Cikin tsokanar da ba ya rabu da shi ya ce "Kai Abie irin wannan kyau haka kamar sabon ango ko dai Ammie za ka je ka yi wa kishiya ne" Ya ƙarasa ya na murmushin da ya bayyana dimple ɗin sa. 


Raƙwashi Abie ya kai mishi a kai ya yi saurin dafe wajen ya na "Ouch! Abie da zafi fa" Ya yi maganar cikin shagwaɓa. Abie ya ce "Ai dama zafin na ke son ka jk tun da ka mai da ni kakan ka" Dariya Afeef ɗin ya yi ya na karɓar flask ɗin da ke hannun Abien su ka jera gwanin ban sha'awa ya na faɗin "Yo Abie tun da ban taso na samu kakana a raye ba, ba sai kai na ja kamar kakan ba tun da shi Uncle kullum fuskar shi a ɗaure ya ke ba ya ko fara'a balle shi a samu a yi wasa da sh....." 


Maganar ce ta maƙale mishi a baki dai-dai lokacin da su ka iso parking slot na gidan sakamakon waɗanda ya gani. Gaban shi ne ya faɗi a shiga kallon kallo tsakanin shi da Abie da waɗanda ya gani ɗin an rasa mai bakin magana cikin shi da Abie..............


#Hayat

#Asad

#Abie

#Ummie

#Mom

#Rikici

#Team-ecoth-of-yota

#Autar-yota.......✍🏻