Chapter 4
by @oumfatayat
*FARAUTAR MUTUNCI*
Marubutu:
Na’ima Sulaiman Daƙayyawa ( Oum Fatayat)
Page:4
Yasan duk duniyar nan ba wacce za ta masa haka sai Hajjo. Durƙusawa ya yi har ƙasa yana gaida ta, tare da tambayar Allah yasa dai lafiya.
“Ikon Allah, yanzu Mamuda dan ba ni na haife ka ba, shine don na zo gidan ka za ka na tambayata ko lafiya, to ka sani wallahi ko tsine maka nayi sai tsinuwa ta bi ka, ehe”.
“Ki yi haƙuri Hajjo wallahi ba haka nake nufi ba, gani nayi yanzu shaɗaya na dare, amma ni da nake so ki zo ma Hajjajo kuma…..”.
“Rufe min baki, ina makirar matar taka da ta rabaka da kowa, tom yau dai agidan nan zan kwana sai dai in mutuwa za tayi ta mutu”.
Hayaniyar da suke yi ne, yasa Nuri ta fito da sauri, ciɓis sai ta ga Hajjo da ɗan ƙullin bakkonta a kai, kamar wacce ta yi maita aka korota, saura kaɗan dariya ta kufcewa Nuri, saboda ita abu kaɗan ne yake bata dariya.
Daƙyar ta maje ta sunkuyar da kanta ƙasa,ta matso salo, salo kamar ka ce mata keret ta gudu.
“Ina wuni”.
“ Lafiya, almura, munafuka, dole zan amsa saboda kinsan manyan malamai sunce amsa gaisuwa ma lada ne, tom ba zan bari ki samu ladan ke kaɗai ba”.
Ba ta sake furta komaiba ta juya ta koma, don tasan in za ta shekara anan a tsaye baza ta saurare ta ba.
“Ina za ki je? Owo, bari na za kiyi bayan kinsan yinwa na ke ji, kuma wallahi da zan samu tuwon dawa da kin gama min komai Nuriyya”.
Cak ta tsaya, hanyar kicin ta nufa ko juyowa bata yiba, da sauri da sauri ta haɗa ma Hajjo a bunda za ta ci don wallahi bacci take ji, abunda baza ta mata ƙorafi ba ta kawo mata, gashashiyar kaza mai ɗan romo-romo sai lemon kwali da bread.
Zama tayo dirshen tana cin kayanta, hannu baka hannu ƙwarya, ganin hankalinta na kan abinci ya sa Nuri ta shi siƙaf za ta shige ɗaki, kururuwar da Hajjo ta fara yi ne yasa ta juyowa, shi kuwa Mahmud ya daɗe da zama akan kujera ya zuba tagumi yana kallon mariƙiyarta sa.
Da sauri shima ya ƙaraso kusa da ita yana tambayar mainene ya faru? Ashe romon Kazarne ya fallatsar mata a ido, nan fa ba sarki sai Allah ba su suka samu kan Hajjon ba har sai uku saura da bacci ya kwashe ta, tunda dai shi ba ɗan gidan su bane.
Ashe ana tsaron iya in ji ‘yar mayya, don haka siƙaf suka bar Hajjo a kwance reran a falo sukuwa suka nufi ɓangaran Mahmud abinsu.
Basu suka farka ba sai misalin ƙarfe goma da rabi na safe, saboda rashin samun baccin da basuyi jiya ba, da sauri Nuri ta diro daga kan gado ganin yadda lokaci ya ja, batare da ta tashi Mahmud ba ta fito, kai tsaye falon da suka bar Hajjo ta nufa, tun daga hanya take jin iskar gidan nata ta canja da irin wani hamami kamar mushe, a haka dai ta ƙaraso tana buɗe falon ta sake jin wani ɗoyi ya bugo hancinta bus.
Da mamaki take kallon Hajjo ganinta cikin zawo faca-faca, da sauri ta yi baya a guje don ita duk duniya ba abun da ta tsana irin ɗoyi, amai kawai ta ke kwararawa kamar an buɗe famfo. Hajjo kuwa sai dariya take tilliƙawa don ta san tsiyar da ta shukawa Nurin dama tasan haka za ta kasance.
Kukan da Hajjo take kwalawa ne yasa Mahmud fitowa a guje, abun da idon sa ya gane masa ne ya sashi ya tsaya cak, ko ina na falon zawo ne tayi faca-faca da shi kai hatta da kan kujeru duk tabi ta goggoga musu kashin.
“Hajjo lafiaya mai ya same ki na ganki a haka?” Da jin muryar Mahmud,Hajjon ta riƙe ciki, ta sake damalmala jikita acikin kashin tana faɗin……
بقلم أم فتيات 👧👧👧✍🏼……