GUMBAR DUTSE

G_D - 21

by @khadeejacandy

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 2️⃣1️⃣

JAWAD POV.

"Garin ya?"

"Wai yar aikinta ce ta kona shi, amman dai da sauki, an ba shi magani yanzu ma suka wuce gida"

"Okay"

Ya amsa ta ipod din dake kunnensa sannan ya ya aje karafen dake hannunsa na motsa jiki, ya juya ya fice daga dakin gumi duk ya gama jikashi. Yana shiga dakinsa cire tufafi ne kawai ya zame masa dole ya shiga bathroom yayi wanka ya fito yana goge kansa da tawul ya nufi sashen da tufafinsa suke ya dauko riga da wando ya saka ya fito ya fesa turaren da ya zame masa wajibi sannan ya dauki keys dinsa ya fice daga dakin.

Da sassafar ya sauka kasa duk wani abun da ya shafi yan'uwansa baya wasa da shi, musamman yaran Adda Sa'adatu da suke sonsa shi na yake son su.

Cikin yan mintuna ya isa bakin gate din gidan sai aka kara bude masa ya shiga ciki yayi parking a daidai gurin motar da Adda ta fita da ita yanzu, ya fita ya zagaya ya isa bakin kofar falon ya tura ya shiga. Set din farko na cushion din da suke falon ya samu Alhaji Sufiyan ya rufr Batula da fada, ta inda ya ke shiga ba ta nan yake fita ba.

"Baki da hankali ne ke? Yaro karami kamar wannan zaki sakar matsa ruwan zafi? Wallahi da yau wani abu ya same shi da sai na daure ki, ko da yake ba laifin ki ba ne, laifin Sa'adatu ne, saboda me zaki dauki yarinya aiki bayan an fada miki kurma ce?"

Adda Sa'adatu ta fara kokarin kare kanta.

"Wallahi bata fada min ba, sai bayan ta tafi sannan ita yarinyar ta nuna min ita Kurma ce bata magana, kuma already na fada a gaban jalila cewar zan kirata ta zo ta dauke ta, dan ni ba zan iya zama da ita ba, ashe rabon ta yi min aika aika, daman ni na fada musu babu ruwana da maraicinta idan ta yi min ba daidai ba zan hukuntata, kuma ko yanzu sai na hukuntata"

Kuka sosai Batula take marar sauti majina ta gama bata mata hanci, ga kanta ta bororo saboda faduwar da ta yi a dazun, ga tsoron fadan da suke mata, ga fargaba hukuncin da za su mata na abun da bata aikata shi da son rai ba. Jawad ya mikawa Alhaji Sufiyan hannu suka gaisa sannan ya zauna ya wasa da hannun Hakima da tun da ya shigo ta kama hannunsa ta rike..

"Garin ta watsa masa ruwan zafin"

"Daga cewa ta musu wanka, ina tunanin aikin ne bata so, shiyasa ta yi haka, ni daman ko baki kona min ɗa ba maidaki zan yi can inda kika fito"

Batula ta girgiza kai ta hade hannayenta tana rokonsu.

"Kar yarinyar nan ta kwana gidan nan ki kira wanda ta kawo ta, ta zo ta tafi da ita"

Alhaji Sufiyan ya fada sannan ya mike tsaye ya fice daga falon, Alhaji Sufiyan irin mazan nan ne da basa daukar wasa akan yaransu, ko da kuwa mahaifiyar ce ta taba su, ba kyalewa yake ba balle kuma bare.

"Ariz ya fada maka ko? Shi na kira ai ya zo ya zo ya same mu a asibitin yayi mana komai, yace ma abun da sauki be kona shi sosai ba, zafin ruwan ne dai ya buge shi, ya ba mu magani da za a shafa masa tun can kuma ya shafa masa wani ya ba shi wani ya sha"

Ya daga mata kai.

"Ina Hakim din yake?"

"Yayi bachin Wahala, azzaluma yar iskar yar kauye, aka lullubo sheri aka kawo min har da yar murya wani wai marauniya ce ba uwa ba uba saboda na tausayawa ashe ni zata saka a wahala"

Ta karasa tana watsawa Batula harara. Jawad ya kalli inda Batula take zaune tana ta kuka, ya mike tsaye ya nufi dakin yaran, a hankali ya tura kofar dakin ya shiga ya karasa gurin gadon yaron ya duba shi, jikinsa yayi ja alamar fatarsa ta hadu da bakon abu, but ba sole ba, yadda suke ta daga hankali sai yayi zaton ko yaron ma ya sale ne.

"Muna daki muka ji yayi ihu, muka leka Janna ta kira Ammy, Hakim yana ta kuka sosai, ita ma ta fadi da Momy ta zo zata daketa har ta yi ta yi.. Ta jimu a nan"

Hakima ta nuna goshinta, tana fada masa abun da ya faru.

"Bata ma mana aikin komai ba Uncle ko da za mu wanke baki mu muka zuba komai muka wanke, ita tana tsaye, sai kallon... Sai kallon bandakin take... Kuma Anty Jalila ta nuna mata yadda ake amfani da komai amman bata yi ba ta kona shi"

Ta kara masa cikin zancenta na yara, ya riko hannunta suka fito, ya dawo falon ya zauna sai a lokacin Adda Sa'adatu ta dan waye.

"Kila ma bachi kake aka tashe ka ko?"

"Ina da motsa jiki"

Ya amsa yana tsaye alamar tafiya.

"An kusa gama abun karyawa ka bari ka karya a nan sannan ka tafi, daman ni bana son cin abincin Hajiya Yelwa da kake"

Ya dan tabe baki, sannan ya zauna sai a lokacin ya tuna da ya bar wayarsa a gida.

"An kusa gamawa, na san ai baka son jira, shiyasa duk matar da zan nema maka sai na fada mata waye kai"

Ta fada tana murmushi.

"Miyasa kike nema min mata masu arha?"

"Excuse me... Ina mata masu arha suke?"

Ta tambaya with confused, sannan ta kalli Janna da Hakima.

"Janna kuje ciki ku shirya lokacin makaranta har ya wuce"

"Ammy yau saboda abun da ya faru, ba zamu je makaranta ba"

Ta dan yi jimmm.

"Okay, amman kuje dakinku zan yi magana da Uncle"

"Okay"

Suka sake masa hannu sannan suka nufi hanyar dakinsu.

"Ina nema maka mata masu arha kamar ya? Duk yarinyar da zan nema maka fa sai mai ilmi dai wanda ta kai, yadda kake tunanin kamar zan dauko maka cheap girl na kawo ba haka ba ne"

"Ba kudi nake magana ba, Aji zan fi daraja mace idan ya kasance sai da na wahala sannan ya same ta, if they are not cheap miyasa za su yarda su zo nan mu ga juna mu gaisa? Why not ni naje gidan iyayensu na same su?"

"Zamani ne ya zo da haka Jawad, yanzu ba irin da ba ne, wata yarinyar ma ta fika capacity amman dan ta zo ku gaisa ba wani abu ba ne"

Yayi murmushin gefen baki.

"Har gobe mata masu aji suna da aji, i don't want cheap girls"

A take yanayin fuskarta ya canja.

"Akwai wadannan din ma, next time kai zaka je nemansu, but kamin nan? Shim ka fadawa Hajja Yelwa cewar ina nema maka mata ne? Shiyasa ta zuba maka wani sabon karatun?"

Ya kalleta irin kallon dake nuna ransa ya bace da kalamanta.

"Ke zuciyarki bata da komai sai zargi? Idan kika tsani mutum ba zaki taba ganin alherinsa ba? Miyasa kike tunanin wani na iya chusa min abun da bana ra'ayi? Yaro ne ni karami da Hajiya zata zaunar da ni ta faada min abun da ya kamata da wanda be kamata ba?"

"Ta riga ta mallake ku, duk abun da ta fada ko da kuskure ne a daidai kuke ganinsa"

Yayi murmushin gefen baki, shi kam ya rasa gane kan yar'uwa da take yawan fadar Hajja Yelwa ta mallake shi, wani lokacin har da Ariz take hadawa. Ta watsa masa harara irin ta yaya da kane ta san baya ganin laifin matar baban tasa komai aka yi.

"Hajiya an gama an zubawa kowa, ga na ku nan a dinning"

"Okay, amman kar a bawa yarinyar nan na kira uwar rikonta ta zo ta dauke ta"

Jawad ya kalleta.

"Karki shiga hakkinta"

"Ni baka ga yadda ta hora min yaro ba?"

Jawad ya kalli mai aikin.

"Ina yarinyar take? Kirata"

Ta juya.

"Tohm, gana nan kusa da kofa"

Babu jimawa matar ta dawo Batula na bayanta ido a kumbure ta tsaya daga can kusa da kofar ta risina kasa.

"Shiga dakin yaran nan ki samo abun rubutu"

Matar ta nufi hanyar da zata sadata da dakin yara, ta dauko takarda da pen ta fito da saurinta ta kawowa Jawad, sai ya nuna Batula matar ta karasa ta bawa Batula.

"Wacan Jahila daga kauye fa aka kawota, komai bata iya ba"

Adda Sa'adatu ta fada cike da takaici. Be bi ta kan Adda ba ya kalli Batula. Ta daga idonta daga can inda take zaune ta kalleshi a karo na biyu, bayan kallon da ta yi masa a dazun da ya shigo, a nan din ma sai fuskarsa ta yi mata yanayi da wanda ta taba gani, amman bata tuna a ina ba. Bata bukatar yayi izini ko tambaya ta fahimci manufarsa dan haka ta girgiza masa kai, be ce mata komai ba ya kalli littafin da aka bata ya sake kallonta alamar ta rubuta, ta maida kanta kasa ta rike pen din.

"Ba da gangan na jika shi ba, wannan matar ita ta nuna yadda zan yi kuma haka na yi sai ruwan zafi suka biyo ta hude huden sama, amman da gangan na jika shi ba Wallahi, dan Allah ka bata hakuri, ba zan sake ba, dan Allah ta yi hakuri, Umma Hindu ta ce idan na yi wani laifin aka dawo mata da ni sai na lahira ya fini jindadi, dan Allah ka ba su hakuri Wallahi ba da gangan na aikata ba, nasan baka san ni ba, amman ba zan maka karya ba, dan Allah ka yardar da ni"

Tana rubutun hawayenta na sauka a jikin littafi, sannan ta mikawa Matar dake tsaye kanta, ita kuma ta kawo ma Jawad, ya karba ya karanta ya mikawa Adda Sa'adatu dake dan mamaki abun da Batula ta rubuta a littafin domin bata yi tunanin ta iya rubutu ba. Sai da ta gama karantawa ta ja tsaki.

"Ko kasheki zata yi sai na maidaki, na bar ki nan gaba ki tayar min da gobara? Kuma kina jin Abbansu ai yace a koreki, duk wani marairaicewa da zaki yi ni ba tausayinki zan gani ba"

"Ya aka kawo miki ita?"

Jawad ya tambaya. Sai ta labarta masa yadda komai ya faru, daman tun a dazun yake mamakin jin cewar bata da iyaye, domin ya a inda ya ganta kuma a yadda ya fahimta kamar tana da gata, how comes ta kare a nan? Rashin wadatarta zuci ne ko kuma ne? Sai dai a zancen Adda ya ji tana ta nanata babu ruwanta da maraicin Batula. Da hannu yayi mata alama da ta fice sai ta kara fashewa da kuka ta tashi ta fita matar data dauko littafin ta dauka ta maida a inda ta dauko sannan ita ma ta fita.

Ya mike tsaye

"Zan yi breakfast a gida, Batula zan tafi da ita since you don't like her"

"Bata fa magana"

"Perfect"

Kawai ya fada ya nufi kofar fita falon, Adda ta bishi da kallo zuciyar na raya mata ita nan da kwana biyu zai dawo da ita abu ne mai wahala su jitu. Yana fitowa Batula ta mike tsaye da sauri kanta a kasa.

"Biyo ni muje"

Ya fada sannan ya sauka entrance din ya nufi motarsa, ya matsa key din motar.

"Ina kayanki?"

Ta girgiza masa kai, ya fahimci me take nufi da akwai kayan ai zata nuna inda suke ne, ko inda zata dauko. Alama yayi mata da ta shiga mota, ta girgiza masa kai, ba zata shiga ba, ya dubeta da kyau ta sake mata alama da ta shiga mota, sai ta matsa baya tana girgiza masa mai, tsoro take idan ya dauke ta bata san inda zai kaita ba, kuma bata san manufarsa ta yin haka ba, garinsu zai maidata ko kuma gurin police zai kaita ko wani gurin daban.

Da key din hannunsa yayi amfani ya nuna goshinsa, daidai inda ta samu rauni a goshinta, abunka da mai fahimtar yaren kurame nan da nan zuciyarta ta raya mata asibiti zai kaita. Ta dan matsa kadan ta taka ta isa gurin motar, shi ya fara shiga sannan ya bude mata daga can ciki, ta shiga da dan tsoro ta zauna, yanayin yadda ya rufe gambun be rufu ba, dole sai da ya fita ya zagaya ya bude ya sake rufewa sannan ya zagayo ya shiga motar yaja.

Be dauko dan ta ba shi tausayi ba, be kuma daukota dan kar a maida ita gida ba, ya dauko ta ne saboda yana bukatar wanda zata kula masa da kakarsa da kuma bangarensu, bugu da kari kuma ya san bata magana zamanta a gidan zai masa dadi saboda baya son yawan magana baya son hayani. Batula na rakube a motar tana kallon hanya gabanta na zillo har suka iso gidan da ya ninka wanda suka fito a girma, kuma wannan gidan sama ne.

Bangaren Hajiya Yelwa yayi farkin ya fita ya zagaya ya bude mata ta fito duk a tunaninta asibiti ya kawo ta, har tana mamakin girman asibitin da kyaunta, yana yin gaba ta bi bayansa suna ta tafiya har suka shiga falon Hajiya Yelwa da kamshin turaren yar Fillo ke tashi, a nan ta fahimci ba asibiti ya kawota ba, domin yanayin falon da mutanen cikinsa ba su yi kama da mutanen asibiti ba, daga can inda ta fito har zuwa nan din bata san a inda take ba.

"Yanzu na aika bangarenku, yara sunce ba su ganka falo ba, dakinka kuma ba su shiga ba suna tsoro, na kira wayarka har na gaji ba a daga ba"

Cikin far'a da farincikin ganinsa Hajja Yalwa take maganar.

"Naje ganin Hakim ne, ya ji ciwo"

Ta ɗaki kirji cike da nuna alhini.

"Subhanallahi, garin ya da fatan dai da sauki ko?"

"Da sauki"

"Tohm Alhamdulillah, bari na kirata"

Ta juya.

"Hajja"

Kiran Jawad ya saka ta juyo.

"Na samo wanda za ta rika kula da Gwaggo da bangarenmu"

Yana bata hakkinta ne a matsayinta na matar gida kuma matar ubansa, if not ba zai ma fada mata ba, sai dai ta gani. Hajja Yelwa da sai a lokacin idonta ya kai kan Batula ta washe hakora.

"Maa Shaa Allah, daga can gidan ka zo ta ita? Lalle marhabun yarinya sannu da zuwa, muma ai muna neman mai kama mana wasu abubuwa, Gaskiya Daughter ta kyauta da ta samo maka yar aiki, haka ake son yar'uwa mai damuwa da ɗan uwanta, zan sanar da mahaifinka shi ma zai yi murna"

Yadda take maganar da far'a sai ka dauka har zuciyata ne, alhalin kuma haka be mata dadi ba sam, a ganinta Sa'adatu ta samo mai daukar mata rahoto ne dai ta fake da yar aiki.

"Ga abincinka, Allah yasa dai ba a can ka yi breakfast ba"

Ya kalli Teburin yana jin yau ba zai iya karyawa a gurin ba.

"Zan karya a can, Husaina ta kawo min"

"Tohm, ɗana yanzu kuwa"

Ya juya ya fice, Batula ta bi bayansa tana sharar kwalla, yana jin alamar ana binsa amman be waiga ba kuma be ce mata komai ba har ya isa bangaren na su ya shiga cikin falon, ita kuma ta tsaya daga bakin kofa kamar wanda bata yarda da mutane ba.

Ya juyo ya kalleta.

"Daga yau aikinki ya dawo nan, idan kina bukatar wani abu ki fada min"

Ya haura sama ya barta a bakin kofar cikin rashin makama.