GUMBAR DUTSE

G_D - 22

by @khadeejacandy

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 2️⃣2️⃣

Da ya shiga ciki wanka ya sake ya saka short da jallabiyar da yayarsa ta siya gurin Khadeeja Candy, ya dauki turare ya fesa sannan ya dauki wayarsa ya fito sanye da talkaminsa na bedroom ya sauko kasa.

"Ina ta magana yarinya shiru bata amsa ba, sai sama take nunawa, ko bara ta zo ko wani take nema ban sani ba"

Jawad da hannunsa daya yake aljihu ya dauke idonta daga kallon Gwaggo ya kalli Batula dake tsaye can kusa da kofa.

"Sabuwar mai aiki ce, ita zata rika kula da nan"

Ya fada yana cigaba da kallon Batula wacce ta marairaice kamar zata yi kuka.

"Ah aiko ka kyauta, daman ina son wanda zata rika taimaka mana gurin wasu abubuwa, tun da ita Hajja Yelwa ba barin yaranta take su yi wani abun ba"

Gwaggo ta fada ciki da murna da jindadi.

"Ke kuwa yarinya ai sai ki min bayani, amman kin yi shiru kamar kurma, miye sunanki?"

Har Jawad ya dauke domin baya son dogon zance, sai kuma ya zai yi tun da bata magana ita kuma gwaggo bata iya karatu ba balle idan ma an rubuta mata ta karanta, ya juyo

"Tana jin duk abun da zaki fada, amman bata iya magana, sai dai ta rubuta ko ta nuna, sunanta BATUL"

Yana maganar hankalinsa yana kan waya, sai ka rantse ba da Gwaggo yake ba, amman da yake kakarsa ta san halin kayanta sai fahimci fada mata yake, cike da tausayawa ta kalli Batula.

"Allah sarki, Allah mai iko, kowa da jarabawarsa sannu kin ji yarinya, zo ki zauna"

Batula ta shigo cikin katon falon tana tafiya a hankali ta karaso kusa da Gwaggo ta zauna a kasa.

"Aa tashi haba zauna a kan kujera mana, ai duk daya muke sai wanda ya fi wani tsoron Allah, zauna a kujera"

Batula ta dago a hankali ta kalli saitin inda Jawad yake tsaye sai ta tarar shi ma kallonta yake, umarninsa take jira domin shi ya kawo ta gidan, bayan ya dauko ta a gidan matar da take ganin kamar halin su daya, saboda kamaninsu ma daya, duk kuwa da kasancewa bata san alakarsu ba. Indai dan ya ce ta zauna ne, sai dai ta shekara a gurin, da ido yayi amfani ya kalli kujera sai ta fahimci nufinsa. Ta tashi cike da natsuwa ta zauna akan kujerar mai laushi, hakan ya bata damar ganin katon falon da yayi kyau ya wadatu da set din kujeru kala daya da curtain ga tv shi ma irin na Adda Sa'adatu, ga rufin POP tsakiyar wani Turkish carpet ne aka shimfida, ta dayan gefen falon kuma glass ne mai girma aka malala wanda ke bawa mutum damar hango wani yalwatacen rame cike da ruwa dake can dayan bangaren na gidan swimming pool ne mai kyau, ga kujeru an jera kusa da shi, ta dawo ta duban ta cikin falon, idonta ya sauka kan wani staircase mai matukar kyau, ta nan kam gidan ya shan banban da na Adda Sa'adatu, domin ita nata gidan ba gidan sama ba ne, wannan kuma gidan sama ne da wasu dakunan suke sama, abun ku da yar kauye, haka ta bi ko'ina tana kallo kamar zata zubar da yawu.

"Allah sarki gata kyakkyawarta amman ba baki"

Maganar Gwaggo mai cike da tausayawa ta saka Batula maida idonta kasa, can kuma ta daga ta waiga bayanta, ta hango Jawad zaune a wasu kujerun da aka jera da katon teburi yana ta cin abincinsa a dinning din idonsa na kan wayarsa.

"Kin ci abinci?"

Gwaggo ta tambaya, sai ta maida kanta kasa kunya ba zata barta tace aa kar ace ta zo da yunwa.

"Maina"

Ya dago kyakkyawa idanuwansa ya kalli Gwaggo.

"Ka ce Hajiya ta aiko mata da abinci"

Ya maida idonsa kan wayar kawai ba tare da ya ce komai ba, ya fara typing, babu jimawa sai ga Hassana da plate mai dauk da kwai da biredi dayan hannunta kuma da cup din tea.

"Ga abincin da Ya Jawad yace a kawo"

Ta aje abincin tana kallon Batula da mamakin yadda take zaune a cushion din falon. Batula ta mike tsaye ta dauki abincin zata fita waje ta ci.

"Ina zaki?"

Ta juyo ta kalli Gwaggo ta aje cup din sannan ta nuna kofa.

"Aa ba sai kin fita ba, haba duk fadin falon nan ace sai kin fita waje? Bari na baki guri idan baki son cin abinci a gabana ne, baiwar Allah"

Gwaggo ta rika walking stick dinta ta mike tsaye, tausayin Batula take sosai domin ta yi mata kalar tausayi ga shi kuma bata magana. Gwaggo ta shige dakinta dake kasa ta bar Batula ita kadai a falon sai Jawad dake dinning da be ko kula da inda take tsaye ba. Zama ta yi a gurin tana jin sanyi a ranta, da alama wannan gidan zai dara wacan domin wannan tsohuwar bata nuna mata kyama kamar Adda ba.

Tun da ta kai soyayyen kwan a baki ta lumshe dadin ya kai mata har cikin kai, rabon da ta ji kwai har ta manta, ta kurbi ruwan shayin sai ta ji kamar ta tashi ta yi rawa saboda farinciki da dadi, sai da ta fara cinye biredi da tea sannan ta cigaba da cin wainar kwan a hankali dan kar ta yi saurin cinyewa dadin ya kare, bata natsu ba sai da ta saka halshe ta lashe plate din tana kallon wani katon abu dake tsaye har guda hudu a kowane bangare na dakin, tana mamakin miye shi a gidan Adda ma ta ganshi yana ta fitar da sanyi.

Da ta gama sai ta mike tsaye ta kalli saitin inda Jawad yake zaune rike da cup din da plate, so take ya fada mata inda zata aje, kar ta aje inda za ayi mata fada. Da hannu yayi mata alama da ta zo, sai ta taka ta isa gaban dinning din ta tsaya, bata jira yace mata ta aje ba sai kawai ta dora a dinning din ta juya.

"Ke..."

Ya kirata with soft voice. Ta juyo be ce mata komai ba, ya cigaba da cin abincin, shiru shiru ba ce komai ba, sai ta yi tunanin wata kila bata fahimta daidai ba ne, ba ita ya kira ba, maybe be ma kirata ba domin bata ga alamar hakan ba. Ta juya zata tafiya.

"Ke..!”

Wannan karon da salon dake nuna taya zan kiraki ki juya, a karo na biyu ta juyo fuska kamar zata yi kuka ta na lankwafar da kai ta marairaice. Kallonta kawai yayi ya dauke kai ya zari tissue ya goge bakinsa, sannan ya kara wayarsa kunne.

"Zo"

Ya sauke wayar, ta maida kanta kasa tana wasa da tsiraran yatsun hannunta. Hassana ce ta sake shigowa da saurinta.

"Ya ga ni"

"Ki fada mata aikinta"

Ya fada ba tare da ya kalli daya daga cikinsu ba, Hassana ta kalli Batula.

"Kin ga falon nan kullum zaki share ki goge, ki saka turare, kitchen ki wanke duk kayan da aka bata kullum, sama nan akwai dakina zaki hau ki goge share ko'ina ki goge, ki saka turare, nan kasa ma akwai dakuna ki goge su ki gyara, kuma dakin Gwaggo ma ana sharewa a gyara, bandaki kowane ki gyara, can kitchen ne, can dakuna ne da bandaki a ciki, sama ma dakuna ne sai office din Ya shi kam ki bi a hankali, akwai kuma dakin da yake zane zanensa shi ma ki kula"

Batula ta yi shiru tana jin aikin kamar yayi mata yawa, domin gidan yana da girma sosai.

"Kin gane ko?"

Ta daga kai. Hassana ta kalli Jawad sai yayi mata alama da ta tafi da hannu, sai da ta fice sannan ya mike tsaye yana fadin.

"Abun da baki gane ba, ki tambaya karki je ki yi shirme, idan aka yi ba daidai ba ki gyara ko ki yi magana, duk abun da kika ga ya dace ki aikata ba sai kin jira izini ba"

Ita dai bata ko dago ba balle ta kalleshi, amman tana jin duk abun da yake fada kuma ta gane, sai dai hawa saman ne ba zata yi ba, domin bata taba hawa gidan sama ba, kuma ba zata fara da wannan ba. Sai da ya bar gurin sannan ta matsa kusa da dinning din ta kwashe kayan dake kai ta nufi inda aka ce mata kitchen ne ta shiga, bata same kamar na Adda ba, domin wannan da alama ba a cika amfani da shi sosai ba. Ta zuba kayan a cikin sink ta dawo ta kwashe sauran, ta cire hijab dinta ta daure a kugunta, ta iya kunna ruwa tun da ta gwada a gidan Adda Sa'adatu, sai dai bata sani ba wannan din ma yana da ruwan zafi ko akasin haka, sai da ta gwada tara cup ta tara ruwan ta saka yatsansa ta ji babu zafi. Ta ga soso ta dauka omo ne bata gani ba, tana cikin dubawa sai ga Gwaggo ta shigo da murmushinta.

"Kin gan shi can, anan mai muke amfani da shi"

Batula ta taba gorar da ta yi zaton mai girki ne a ciki ashe man wanke wanke ne. Gwaggo ta karasa ta nuna mata inda zata jera idan ta wanke, wadanda za a wanke a bangare Hajja Yalwa kuma ta nuna mata.

"Ki saki jikinki da kyau, duk abun da baki gane ba ki yi nunu, wanda ya kawo ki ne dai sai kin yi hakuri da shi, amman idan kika saba yana da dadin zama"

Batula ta daga mata kai, tana jera kayan da ta wanke, da ta gama ta dauki wadanda Gwaggo ta nuna mata ta nufi bangare Hajja Yelwa da su, ga mamakinta sai ta tararda Jawad din a can tsaye suna maganar da matar da bata san ya matsayin ta yake a gurinsa ba.

"Kin ga can, kitchen ne ki aje kayan a can, Allah sarki ashe bata magana"

Batula ta nufi inda aka nuna mata ta aje kayan ta fito, domin Gwaggo ta fada mata idan ta kai ta dawo bangarensu ne gurin zamanta ba bangaren Hajiya Yelwa ba.

Da ta dawo bata tararda kowa ba, sai ta nufi gaban tv ta kure shi kar ta zauna a kasan domin ya fi mata dadi, kuma ta fi sakewa ta kalli Tv da kyau. Hankalinta ya tafi gurin tv gaba daya har bata san Jawad ya shigo ba sai da Gwaggo ta yi magana.

"A ina ne garinsu?"

Batula ta juyo. Ya dan yi shiru yana nazari shi ya manta sunan garin ma.

"Gurin jikarki na daukota, na manta garinsu"

Yana fadar hakan ya haura sama, be jima ba ya sauko da littafi full book da pen ya mikawa Batula, ta karba da hannu biyu ta rubuta sunan garinsu ta ba shi.

"Robau, amman yanzu tana zama a sabau"

Ya karantawa Gwaggo ba dan ransa ya so ba, sai dan dole tun da babu mai karanta mata, gashi shi kuma duk wani abu da zai saka shi magana ba son shi yake ba.

"Allah sarki, iyayenki ya can ne ko wane unguwa a garin? Na san garin sosai"

"Mai garin garin ne babanta kamar..."

Ta girgiza kai idonta kasakasa tana kallonsa, ta mika masa hannu ya bata littafinta ta sake rubutu ta mika masa domin ko kadan a yanzu bata son a hadata alaka da mutumen shi ya fara rusa farincikinta.

"Iyayen duka biyun sun rasu, ba Mai Garin ne Babana ba, shi mijin mai rikona ne"

Ya karantawa Gwaggo kamar an masa dole, sai kuma ya kalli Batula, kamar dai ya tuna Adda ta fada masa marainiyace.

"Allahu Akbar baiwar Allah, sannu sannu Allah ya musu rahama ya raya ki, rayuwa kenan Allah sarki"

Gwaggo na maganar tana kallon Batula kamar zata zubar mata da kwalla tsabar tausayi.

"Ita uwar rikon ce ta kawo ki nan?"

Gwaggo ta sake tambaya, Batula ta mikawa Jawad hannu, a zuwan ya bata littafin ta rubuta amsa, dauke kai yayi fuska ba yabo ba fallasa, ya juya rike da littafin ya haura stairs he can't do this anymore, ba zai iya tsayawa a tsakanin Kakarsa da Batula yana fassara abun da aka rubuta ba, shi ma ai maganar wahalar da shi take.

"Haka yake, amman zaki saba da shi yana da dadin zama"

Batula dai tana ta kallonsa har ya haura, sannan ta juya ta cigaba da kallon Tvn.

HAJJA YELWA.

@10:05pm.

"Ranka ya dade, ka rika samu kana hutawa, rai ba ba'ayi shi dan wahala ba kadai ba, ace tun abincin safe baka saka komai a cikinka ba sai yanzu, haba yallabai"

Daddy yayi Murmushi yana tauna naman dake bakinsa.

"Haka muke ta yi, sannu a hankali ai zamu bari"

Ya matsar da plate din, ta dauko ruwa ta mika masa ya karba ya sha.

"Ka samu kankwanta da wuri ka huta, duk dai akwai maganar da nake son mu yi amman dai sai da safe idan ka huta"

Daddy ya dauki toothpick ya saka a baki yana cire naman daya lake masa.

"Aa ai kin san ni ba a min wannan, dan haka fadi maganarki yanzu nan ba sai anjima ba"

"Na so ka huta, bana son dare ya kara baka yi bachi ba, a gidan ka ya kamata ka samu hutu ai"

"Zan kwanta ai amman sai zuwa anjima, akwai wayar da nake son yi ba, amman dai yanzu fadi matsalarki family first"

Hajja Yelwa ta yi murmushi, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya yanayin fuskarta na sauyawa.

"Ban sani ba ko har yanzu ban kai a idon yaran nan ba ne a matsayin uwa, ko kuma ba ni da darajar da su ko kai za a fada min idan za a gudar da wani abu, kamar abun da aka yi a yau, Yallabai shin ba ni da darajar da idan ana bukatar mai aiki a gidan a fada min na nemo, ko kuma a fada min za a kawo, sai dai na ji ga an Daughter ta aiko da ita?"

Daddy ya mata kallon rashin fahimta, sai ta marairaice.

"Na ji Ɗana yana neman mai aiki namiji, amman mace aka kawo, kuma na yi tunanin zai min magana na nemone, ko kuma ya barta bangare na amman duk ba ayi haka ba"

"Ni ban fahimce inda kika dosa ba"

Ta gyara zama.

"Mai aikin da aka kawo mana"

"Mai aiki aka kawo?"

Daddy ya tambaya, sai ta dan zaro ido.

"Karka ce min ba da saninka aka kawota ba, tun da na san ɗana da kai yake shawara idan zai yi komai, kuma gidanka ne ai ko kara za a shigo da shi dole ka sani"

"Wannan kwana, kwanan ba zai min ba, ki fito ki fada min komai, ni babu wanda ya fada min zai kawo kowa"

Hajja Yelwa taja numfashi ta sauke.

"Mu bar maganar nan, kawai Alhaji kar na yi laifi, ni daman shawara ce na zo da ita, a matsayi na uwa, kuma ina ganin kamar hakan ya dace, amman tun da har baka sani ba ba zan ma yi maganar ba, dan ina son yarana ni bana son bacin ransu, kuma kai ma idan ban kwantar maka da hankali ai ba zan daga maka ba"

Daddy yayi murmushi mai sauti.

"Miye abun daga hankali a kawo mai aiki? Idan akwai wani ki fada min kawai Hajiya"

"Babu, amman akwai abun da be dace ba kuma ba zan yarda da hakan ba a matsayina na uwa, ba zan so yarinyar nan ta zauna bangaren nan ba, kuma...."

Sai kuma ta yi shiru, ta tattaro damuwa da alamar dake nuna kulawa ta yafa...