NANNY(MAI RENO)

15

by @jamilaumarjanafty

*NANNY...!*
  _ (Mai Reno..)_

*Na*

*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR (Janafty)*

M.A JUMARE FOOD AND SPICES
Pure and Natural hygienic tasty.

Muna da garin Ɗanwake da yaji mai kyau dakan hannu, akwai kuka, tsamiya, garin tamba, kuɓewa da daddawa.
Muna aikawa da kayanmu a ko'ina
Anguwan Ma'aji new millennium city kaduna
Phone number ***

*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*

    *BABI NA GOMA SHA BIYAR*

Har kan Gadonta ya Zaunar da ita,Dagowa Tayi Tana kallonsa Da Jajayen Idanuwanta Tana Zubar da kwallah Cikin Siririyar Muryanta ta Furta"Kayi hakuri Daddy..."Tsam ya Tsaya yana kallonta gefe Daya na Zuciyarsa Tsausayinta na Ratsashi,Basma Dake gefe Tsaye ya kallah kafin yace"Ku kula da Ita sai na Dawo..'

Yafada Haka kafin ya kai ya Fice Daga Dakin da Sassarfa,basma Dake Tsaye ta Kariso Kusa da Ita Tana lallashinta Tahir yana Fita yaci karo da Iya Tsayawa yayi yana Fadin"Iya don Allah ki kula da Mufeeda..."Iya Ta gyada kai Tana Fadin"Insha Allahu Alhaji.."

   Sama ya haye Cikin Dakinsa ya Shiga Daga ganin yadda yake Komai Cikin Hanzari zaka Fahinci yana Cikin bacin Rai,Cikin Sauri ya Dauki Duka Fayels din ya Fito Garzali Dake Waje yana Jiransa ya Shiga Mota Suka koma Campany Wanda Tunda ya Dawo Ishaq ya lura kamar Ranshi abace yake ba Haka ya Fita ba bai mai mgana ba Sai da Suka Dawo Masallaci Sun Shigo Office Din Tahir din 

Kan Wata Kujera Dake Cikin Office din Ishaq ya zauna yana Fadin"Kai inaga fa zan Koma gida cikina yana ta Kiran Ciroma.."Tahir Dake zaune kan Kujeran gaban Tuburansa Ya Dago yana Fadin"Allah Sarki kuda Kukayi Dace kenan Mu ko Mun koma muda banza Duk Daya While sai ka Dawo ni kila sai la"asar in zan Koma gida na Biya na Siya Fura ."

Ishaq ya gyara zama yana Fadin"Tahir meya Faru ne..? Dazu Bayan kaje gida Dauko Wadanan Fayels din ka Dawo Ranka bace.."Ajiyar Zuciyar Tahir ya Sauke kafin ya Mike yana Fadin"Nida Farida ce Wato Ishaq Farida Muguwar Yar Rainin Hankali ce Ayadda nakeji yanzu kamar na kamata nayi ta Duka Gabadaya na Doramata kaso mai girma na Abunda ya Faru Domin Data Kiyaye Hakokina na aure da Duka Haka bata Faru ba.."Yafada yana Saka Duka Hannuwansa Ciki  Aljihun Wandonsa.

Ishaq yace"Me kuma ta Sakeyi..? Tahir ya waigo yana Fadin"Zuwa nayi na tarar da Ita zata kori Mufeeda Daga gidan.."Ido Ishaq ya zaro yana Fadin"Kabari don Allah...? Tahir ya kariso Kusa da Ishaq ya zauna yana Fadin"Wlh Allah ina gayamaka tana Kuka Wai Tana Fadin Ta Cuceta Ishaq can u juz imaging Wai Farida na Kuka saboda ni Tahir na Ma Mufeeda ciki.."Ishaq ya saki Dariya ahankali yace"Dama tana Sonka Tsabar Iskanci ne ke Cinta nayi Takaichin Abunda ya Faru Tahir Duk da bawa bai isa ya Gujema kaddaransa ammh Ta wani Fanni naji Dadi ko banza Lokaci yayi da Farida zata girbi Abunda ta Shuka.."

Tahir ya kuramai ido yana kallonsa kafin yace"Kamar yafa..? Bangane ba..? Tashi Ishaq yayi kafin ya Sakala Duka Hannuwansa Akirjinsa kafin ya Fuskanci Tahir yana Fadin"Eh mana Ai ada Tana ganin baka da Wani amfani Awajenta,Tana ganin ka Daga Ita sai kai yanzu kuwa Dole zata Shiga damuwa Domin Tana Sonka auren Soyayyah Kukayi bana Kiyayyah ba So Dole Farida tayi kuka Kishinka Take Tahir.."Shuru Tahir yayi kafin ya Jinjina kai yace"Hakane..,? Toh ai Ta makara Sai dai komai yagama lalacewa.."Ishaq yace"Shine ake Jiyemata Tun Farko Kada tayi Nadamar Dole Wacce bata da Wani Amfani.."

Mikewa Tahir yayi kafin yace"Wannan ya Rage nata Ishaq Abunda na sani Shine Matukar Farida tace zata matsama Mufeeda Wlh Itama zata Shiga mtsala na Fadamata in batason ganin Mufeedan agidan zata iya komawa gidansu ban Hanata ba ."Ishaq yace"Ina bayanka Wlh gwara ka Nuna mata Kuskuranta Tun yanzu.."

Tahir yace"Uhm,Kabari kawai Ishaq Zata ga ainihin kalata Wlh.."Ishaq yace"Asaussauta mata Alhaji Abarta taji Da Daya..Yafada yana yar Dariya Shima Tahir Dariyan yayi kafin yace"Yau da Safe Goggo Ta Kirani Tana Kuka Tana Fadamin Tunda Suka Dawo Baba Hakimi baya kulata nadai lallasheta nace Tabari Ranar sati zan Shigo D'anbatan,Duk da ina jin kunya Ishaq sai nake ganin kamar kowa yasan Abunda na aikata.."

Kusa dashi Ishaq yazo Lokaci Daya yana Dafa kafadarsa Cikin Sigan lallashi yace"Daga goggo Har Farida nasan Haka zata Faru dasu kayi Hakuri zasu Daidaita ammh kaima kasan Dole Baba Hakimi yayi Fushi mganar Kunya kuma Don Allah ka saki Jikinka ba Wanda zai san Wannan Mganar bayan mu da muka sani kuma ko Ansani Bafa laifinka bane Kaddara ne kuma Bawa bai isa ya kaucemata ba.."Ajiyar Zuciya Tahir ya Sauke kafin yave"Hakane Nagode Sosai Ishaq Da bansamu Amini kamar ka ba Dabansan Wani Hali zan Shiga ba.."Mirmishi Ishaq yayi kafin yace"Nima Haka da Ban Hadu da Amini kamar ka da na Tafka Asara.."Atare Suka saka Dariya kafin Ishaq yace"Allah ya Sauki Mufeeda Lafiya,Ammh sai nake ganin kamar yarinyar tayi kankanta da Haihuwa fa.."Wani kallo Tahir yayi mai kafin yace"Nima fa ina Mamaki kaduba kagani yarinyarnan kamar kara ammh Ta iya Daukeni Tsaf.."Ishaq ya Buga Kafadarsa yana Fadin"Bugu Daya ko Mallam Kasaka Kwallo Araga.."Ture Hannunshi Tahir yayi yana Fadin"kaifa Dan Iska ne Zahra ta bata ka.."

Ishaq na Dariya yana Fadin"Yan Iska dai Mallam kadinga saka Mun jaye.."Shuru Tahir yayi kafin yace"Wani Hanzari ba Gudu ba,ya Zan yi da Mufeeda bayan Ta Haihu..? Ishaq yayi Shuru Shima yana Wani Tunani kafin yace"Mubar Wannan Mganar Fatarmu dai Allah ya Sauketa lafiya Insha Allahu bazai gagaraba."gyada kai Tahir yayi kafin Ishaq yace"Bari na Kira Zahra ta saka Direba ya kawoma Abincin nan kawai sai muci ko..?

Tahir na Shafa Cikinsa yace"Daka Agaza kuwa Domin nafara ganin Hazo hazo.."Dariya Ishaq ya saka kafin ya fice yana Laluban Zahra ta Waya Shiko Tahir komawa yayi yazauna  yana Auna Mganar Yadda zai yi da Mufeeda bayan Ta Haihu..? Wata Zuciyar tace In ta yaye Abunda Ta Haifa sai ka mata Aure ka bata jari..,Toh wazai Aureta bayan Ta Haihu..? Babu Wanda ya chanchanta ya Aureta sai kai Tahir.."Wata Zuciya ta karantamai da Sauri yace"A"a Bazai Yuyu ba Naso kaina Dayawa bayan na lalata mata Rayuwa kuma na Tursasamata zama dani Tana karamar yarinya bazan yi Haka ba.."Yafada Afili Cikin Karayar Zuciya Lokaci Daya Tsausayin Mufeeda na Ratsashi Runtse Ido yayi Yana Tunanin Wani kariya zai Bata saboda Farida Domin yadda ya Zuciya da Farida indai Tace zata Takura Ma Mufeeda Zasu samu babban Mtsala.

****
  
Farida Kuwa Tunda Ta Shiga Daki Tafada Bisa gado Tana Gunjin kuka kamar Zatayi Hauka Gabadaya ta Birkice Haka take Buga kanta bisa katifa Tana Kuka Hannuwanta Dafe da kanta bayan Ta Barbaja Gashin kanta Ya Watse kamar Wata Kamun Hauka Cikin Ranta da Zuciyarta kamar Ta Buga Saboda Kunci Da bakinciki.

Duk bayan Kowacce Dakika sai kalaman Tahir Sun Fado mata arai Wani Jiri take gani Idanuwanta Sun kode Saboda Kuka Tana ji acikinta Ranta Tahir ya gama da Ita Tuni Shedan yamata Zugan dama Duk karya ne plan ne Tahir ya Shirya dama Sun Dade Suna Cin Amanarta Shida Mufeeda munafukar Allah,Ji Takeyi ayanzu Duk Duniya bata da wata makiyiya kamar Mufeeda Tanajin bazata iya Rayuwa acikin gidan Nan Tana kallon Mufeeda da Cikin Tahir ba Watarana Bakinciki zasu Sa Zuciyarta ta buga Ta Fadi ta Mutu .

Cikin Hanzari ta Mike Daga kan Gadon Wajen Jerin Akwatunanta Karamin Ciki Ta Dauko Ta Budeshi Bisa gado kafin Ta Bude Wardrope dinta Tana Debo kayanta tana Sakawa Gefe Daya kuma Tanayi Tana Share Kwallah,Sai da Cikata kafin ta maidata ta Rufe Tana kuka Ta Dauki Wani Hijabin Data Cire Wanda Ke Jikinta Duk gayun Farida Yau batama Tuna da Wani Abu ba Waishi Wanka balle Kwalliya,ta dauko Akwatin kenan Wata Zuciya tace"Farida ina zaki..? Kawai Taji bakinta ya Furta Kano lokaci Daya kuma kalaman Abbanta ya Fado mata Kuka Takara sakawa Kafin Ta koma Bakin gado ta Zauna Tana Faman Sharan Kwallah Cikin Ranta Tana Tunanin bayan Kano bata inda zataje kuma,Danbatta..? Kai ina..? Bazai Yuyu ba Ko Naje chan Duk Daya ne Goyon bayan Dansu zasu yi Toh ina yakamata Naje..? Kai Tsaye Wata Zuciyar Tace"gidan Bilkisu..."

Tuna Haka yasa Ta saki Mirmishin Karfin Hali kafin Ta mike Har Ta kusa Ficewa Ta Tuna Da Wayarta tazo Ta Dauka Ta Fice Cikin kunar Rai Take Saukowa Daga Stairs tana Bin Dakin Mufeeda Dawani kallo har ta kariso Tsakiyar Falon kenan Sai ga Laila da Basma Sun Fito Daga Kichen Laila na goye da Naila Ita kuma Basma na Dauke da Wani Jug ahanunta Da alama Lunching Suke Shiryawa bayan su Kuma Iya ne Dauke da Wasu Manyan Food Flaks kallo Daya Farida Tayi musu Ta Dauke kai bata kara kallonsu ba Ta Nufi Hanyar Ficewa...

Cike da Mamaki Basma ke Fadin"Mommy ina zaki..? Afusace Farida ta Waigo Tana Watsama Basma Harara kafin Tace"Inda Ubanki Tahir ya aikeni zani Don Kakarki Goggo Abu.."tafada Idanuwanta Sun kada Sunji Jajir Daga Basma Har laila balle iya baki Suka Rike Suna salati acikin Ransu Iya ce Tayi Saurin Cewa"Subhanallah...Haba Hajiya Wannan zagin bai kama..."Dallah Malama ki Rufan baki Tsohuwar Munafuka.."Farida ta katse Iya Tana Fadin Haka ..

Ido kawai iya ta sakamata batare Datace komai ba,Baya Farida ta Dawo Tana Nuna Iya da Yatsa Kafin tace"Nasan Duk Abunda Tahir da Mufeeda Suka Taru Suka aikata kina sane ammh Dayake ke Tsohuwar Munafukace Shine kika munafunceni ko .? Toh kema kinsan Da sani Karshen Aikin ki yazo Acikin gidan,Zan Tafi na barma Tahir gidan Tunda Dama Burinku kenan Daga ke Har Mufeedan In Kinji ko kuma In kun Burgeni ku Maye masa Gurbina da Mufeeda kodon Taimakon Shegun ya"yan dazasuyi Ta Haifa.."Tafada Tana Watsama Iyan Wani kallo Lokaci Daya da Mufeeda Wacce Taji Mganar Faridan Ta Fito tana Tsaye Kofar Dakinta tana Kuka..

Wani Mirmishin Kuka Farida Tayi kafin ta Dauki Akwatunta ta Fice da Sauri Su Iya Suka Marata baya,Basma ce tafara Juyawa Zuwa Saman Dining ta iJiye Abunda Ke Hannunta da Gudu Ta Nufi Hanyar Dakinta tana Kuka Laila ta marata Baya Cike da Tsausayi Iya Kuwa Jikinta Asanyaye ta Karisa Jera Kololin Abincin Bisa Dining kafin Ta Waigo Tana kallon Mufeeda Cikin Kulawa tace"Kidaina yawan Kuka Mufeeda bashi da Alheri..Kiyi Hakuri Daman Dole zaki Fuskanci Haka Allah ya baki Ikon Karban Kaddaranki Hannun Bibbiyu.."Daga Haka Ta Shige Kichen Tana Shara Kwallah Aranta Tana Ji ko Farida bata Koreta ba ita da kanta zata Tafi Tunda Gidan ya Rikice komai Babu Dadi,Dama Babu Abunda Ta Nema Rasa na Rayuwa Domin Danta ya samu Aiki Ta Dalilin Tahir Kawai Karamcinene da Mutumcin shi yasa Take Zaune Dasu Haryanzu Ammh Lokaci Yayi da zata koma gida...

******

_Anguwan SARKI_

Bilkisu Kawar Farida ce Wacce Sukayi Mkranta Tundaga Secondry Har Zuwa Buk,Course Daya Suka karanta kuma Suka zo Sukayi Aure A kaduna sai dai Ita Bilkisu Ta Riga Farida Aure da Wajen Shekara Daya da Rabi,Tana Cikin Wadanda Suke Zuga Farida acikin Kawayensu Duk da ko Ita ba Haka take Tafiyar da Gidanta ba Ko yar Aiki bata Dashi sai Wata Tsohuwa mai Zuwa tana mata Wanke Wanke da Wanki Shima Sai Mijinta ya Fita tazo Tagama aikinta ta tafi ya"yanta Hudu yanzu Haka kuma bata Tsaida Haihuwa ba Ammh Tana Daga Cikin Wanda Suka Zuga Farida kan Ta Tsaida Haihuwa Hakannan Dama Duk Inda ka zama Sakarai sai Ana nuna maka Hanyar da zaka sake bi ka kara Sakarcewa.

Farida da Motar Ta Fita Zuwa Gidan Bilkisu Tana Driving Tana Kuka Lokacin Data Shigo Babban Falon Gidan Bilkisu Tana Zaune kan Kujera Tana Waya da kaninta Wanda zai yi Aure Sai ga Farida ta Shigo Tana kuka Abun yabata Tsoro da Hanzari ta yanke Kiran Ta Mike Tana Fadin"Fari Mezan gani Haka..? Mutuwa Akayi..? Farida bata samu zarafin mgana ba Illa Zubewa datayi jikin Bilkisu Ta saki kukan Datake yinshi Acikin Zuciya 

Riketa Bilkisu Tayi Cikin Tashin Hankali Take Fadin"Na Shiga Uku Fari wai meya Faru..? Basma ce Ta Rasu ko Shi kanshi Tahir din ne Wani Abu ya sameshi Kaina ya Kulle Don Allah ki gayamin Abunda Ke Faruwa...? Farida Ta Dago Daga Jikin Bilkisu Tana Fadin"Billy Tahir ya Cuceni...Tahir ya gama Dani Billy Shida Mufeeda Sunci Amanata..."Take Fada Hawayenta Suna Kwararowa 

Bilkisu Tace"Tahir da Mufeeda Kuwa Me Sukayi Kuma...? Tafada Cike da Mamaki,Kan Kujera Farida Ta Fada Tana Dafe kai kafin Tace,"Billy..." Bilkisu tace"Na'am...Farida.." Farida Ta Runtse Ido kafin Tace"Ciki Tahir yayi ma Mufeeda Mai Renon Naila.."Wani Zabura Bilkisu Tayi baya sai gata zaune gaban Farida Duka Hannuwanta akai kafin Tace"Kibari don Allah Farida..! Wani Tahir din Wai Abbansu Basma kikeso kice yayima yarinya Dakuka Daukota Daga Kauyensu Ciki...? Tafada Duka Idanuwanta Awaje.

Idanuwan Farida na Runtse Hawaye Suka kara Kwaranyomata kafin ta Gyada kai Cikin Kuka tace"Kwarai Da Gaske..."Nan ta Shiga labartamata Abunda ya Faru Tundaga Farko Har Karshe Ai sai Bilkisu Ta Mike Tana Fadin"Kutumar Uba..Lalle Tahir Mugun dan Wasa ne Wato Fyade yayimata baya Cikin Hayyacinsa Kajimin Matsiyacin Mara Mutumci da Kima Wato Shine Iyayensa Suka Taru Suka Marama Dansu baya Saboda Tacewa Ke kuma gaki banza Sakarya sai ki zauna  Araini Cikin Shege agabanki ko..? Farida na Share Hanci Tace"Abunda ke sakani Kuka kenan Billy Bansan Iya Adadin Tarayyar da Tahir yayi da Mufeeda Ba Bilkisu ammh Duk da An batamin ba Wanda yaga laifinshi sai ma laifina ake gani Daga Karshe Cemin yayi Mufeeda bazata bar Gidan ba Sai dai ni in nagaji na kara gaba."

Billy tace"Jar Uba..!Lalle Tahir Mugun Dan Iska ne,Haka yace...? Tafada Tana Girgixa Jiki batai Tunanin Magidanci kamar Tahir Tana Surfamai Zagi,Farida ta gyada kai kafin tace"Shine Dalilin Dayasa na Taho Tunda Umma da Abba ya mallakesu ko na Koma Bazasu Taba Saurarana ba Kirufamin Asiri ki barni na zauna Awajenki Har Tahir yagane Kuskuransa.."

Bikisu Tayi Shuru Cikin Nazari Farida Ta kalleta Tana Share Kwalla tace"Ko da kwai Mtsala ne..? Ajiyar Zuciya Bilkisu ta Sauke kafin Tace"Ba mtsala in ma Dashi Abban Su Walida ne,ammh komai ke zanyi mgana Dashi in ya Shigo Tashi na rakaki Dakin da zaki Sauka bazan bari ki koma gidan Tahir ba Domin  Cuta kam an Cuceki Wlh Cikin Shege Acikin gidanki don Wulakanci ma Mafi kaskanci Mai Renon Yarku Gaskiya Tahir ya bata Wayonsa Kuma girmansa ya Zube Acikin Idanuwata.."Tafada Tana Daukan Akwatin Farida Tatashi Suka nufi Wani Korido Suna Tafe Billy na Tsinema Tahir Wanda Har Azuciyar Farida Tana Jin Zafi ammh bata da yarda zatayi Tunda Ita ta Tona ma kanta Asiri.

Daki ne Mai Dauke Da gado da Wardrope sai Madubi da Tiolet ba laifi ko"ina Tsab Tsab nan Bilkisu Ta Fita ta barta Zuwa Kichen Ta Zubomata abinci Domin Duka yaran nata Suna Islamiya Fargaban Bilkisu Daya Megidanta Wanda yake da Zafi Sosai In Har yaga Farida tadawo Gidan sai yaji Dalili Kuma Akwai sanayyah Sosai Tsakaninshi Da Farida Har da Shi kanshi Tahir din Ita kuma bataso ma Tahir yasan Farida na gidanta sai yagama Wahalan Nemanta tukunna Hardai ta Zuboma Farida Abinci bata samu Mafita ba Tana ta Dai Tufka tana Warwara Tsoro ya cika Ranta Saboda Tasan Abban Walida bai da Wasa.

****

Tahir kuwa bai da lbrin Farida bata gidan Domin Bai Dawo Daga Office ba sai bayan Isha"i Suna Zauna Suna Duba sakon Wasu Sabbin Samfur din Motoci Cikin Laptop din Tahir din Shida Ishaq basu ma gama ba Suka Rabu Akan Tahir zai karisa Komai kafin gobe koda ya Dawo ya Biya ya Siyo Furanshi yana Shigowa,kafin ya Shiga Dakinsa ya Fara Biyawa Dakin Su basma ya Tarar dasu suna kallon Cartoon Oyoyo Sukayimai ya Rumgumesu yana Tambayansu ko Sunci Abinci Tsaraban Furan Daya Siyo ya basu kulli Daya kafin yayi musu Saida Safe Daganan ya Shiga Wajen Su bassam ya samesu Shida Muda Suna buga Game,nan Suma Suka Tashi Suna mai oyoyo Shafa kansu yayi yana Tambayansu lafiyansu Suma Furan Guda Daya ya basu kafin Daganan ya Fito yaja musu kofa,Dakin Mufeeda ya kallah har zai Wuce sai kuma ya kasa Cikin Sanyin Jiki yanufi Dakin Nata yana Tura Kofar yaganta Kwance Kundundune chan Tsakiyar gado Cikin bargo Tana barci Bai Shigo ba Daga Kofar Dakin ya Tsuramata ido yana kallon Karamar Fuskarta Cike da Tsausayi Wani Abu na Tasomai Daga Kasan Zuciyarsa Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya koma Da baya ya jamata Kofar.

Yana Shirin barin Falon ne yaji Muryan Iya na Gaisheshi Da Sauri ya Waigo yana amsawa Cikin Sanyin Murya Iya tace"Alhaji Naila na Wajena Saboda ganin yanayin Mufeedam.."Gyada kai kafin yace"Bakomai kin kyauta.."Har ya Juya ta Sake Fadin"Amh Alhaji dama Ina son mgana dakai in ba Damuwa.."Cikin mamaki Tahir ya Waigo kafin yace"Mgana kuma...? Toh Shikenan iya Kibari da Safe kafin na Fita Ki Tunamin yanzu Dare yayi.."Jinjina kai Tayi kafin Tace"Shikenan Allah ya Tashe mu lafiya.."Da Ameen Ta amsa Har ta Juya zata Tafi ya Kirata ta Waigo ya mikamata Fura guda Daya karba Tayi tana mai Godiya Daganan ya mata sai da Safe ya Haura sama ko kallon Dakin Farida baiyi ba.

Sai da yagama Duka al"adansa na Kwanciya kafin ya Dauko Laptop dinsa  ya Dora Bisa Gado ya Haye Tsakiyar gadon ya Cigaba da aikinsa Lokaci bayan Lokaci yana Kurban Furar Daya Tsiyaya Cikin karamin Kofin glass bai kwanta ba sai Wajen 1pm kana ya Kashe komai ya koma ya Kwanta bayan yayi Addu"ar barci.


Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.

*Janafty*
A.ALTO*