16
*NANNY...!*
_(Mai Reno..)_
*NA*
*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR (Janafty)*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*BABI NA GOMA SHA SHIDDA*
"""Tahir Ya Fito Cikin Fitanshi na Zuwa Office yana Sanye Cikin American Suit Dinsa,Black and White ya matse Wuyansa da Tie yana Dauke da Brifcase Dinsa Lokacin daya Sauko Kasan Falo Ya Iske Basma da Laila da Bassam da Mudu suna zaune Bisa Dinining Suna Breafsat Suna ganinshi Kowanne ya Washe baki Suna Fadin"Daddy gud Mrning...?
Karisowa yayi yana Fadin"Mrning my Childreen How was Ur Nite.."Suka amsa da Fine Kan Basma da Laila ya Dafa kafin yace"Laila da Mudan Hutunku ya kare Fa Tun last Week ko .? Kai Suka gyadamai alamar Hakane Numfashi ya Sauke kafin yace"Ok Bari na Dawo Kila ko Zuwa Gobe Ko Jibi Saturday Sai mu maida ku gida ko..? Kallon Junansu Sukayi kafin Suce"Toh Daddy.."Suka Fada Suna Dariya Jin Harda Bassam zasu Rakasu gida.
Teburin yabi da Kallo kafin yace"Ina iya da Mufeeda Bazasu karya bane..'Basma ce tace"Bamu sani ba Daddy ammh iya Ta Dibarma Mufeeda Ta kaimata Daki Tundaga nan Data Fito sai Ta Koma Dakinta Bamusan Abunda Ya Faru ba.."Basma Taa Fada Tana kallon Tahir din Kafin ya samu Zarafin Mgana Bassam ya karbe da Cewa"Eh mana Daddy Gidan Duk ba Dadi Mufeeda bata Fitowa yanzu Iya ma kamar Akwai Abunda ke Damunta yau Duk kamar ba Ita ba.."Yafada cike da Kewa Irin Abun bayamai Dadi.
Shuru Tahir yayi kafin ya saki Ajiyar Zuciya yace"Ikon Allah Meyafaru ne..? Basma tace"Bamu sani ba Daddy Kila Ita da Momy ne kafin Tatafi.."Da kallo yabi Basma Baki bude kafin Yace"Tatafi..? Faridar bata nan ne..? Ina taje..? Ya jero musu Tambaya Lokaci Daya.
Basma ta Zakuda kafada kafin Tace"Bamu sani ba Daddy Tadai Tafi Har iya ta mata mgana Ta kusa Zaginta.."Ido ya zaro yana kallonta ganin Haka yasa ta Shiga maidamai Abunda ya Faru,Jinjina kai ya Hau yana Jin Wani Bakinciki na Ratsashi,Wato Duk Bayan Rusamai Rayuwa da Farida Tayi bai Isheta ba sai Tabi gari Ta gama Tonamai Asiri ko..? Domin yana da Tabbatacin Bata je Kano Domin bada Safenan ya samu Wayar Umma,bayan Sun gaisa Ta kara bashi hakuri game da Farida Tare da Fatan zasu zauna Su Rungumi kaddaransu kuma yanzu bads Dadewa ba Suka kara Mgana Da Abba duk da Mganar Business ne ammh da Farida Taje kano Jiya Dayaji lbri,Shi ba Wannan bama Damuwarshi naga Goggo Abu Domin Innaro da Ashe Sun Kirashi Awaya Suna Sanar Dashi ya Kokarta yazo Domin Baba Hakimi yayi mugun Fushi da goggo Abu baya Shiga Dakinta kuma yahanata Shigowa Turakarsa kuma Baya Shiga Sabgarta Tayi kuka Tanuna Nadamarta Ammh Baba Hakimi yayi Burus Da Ita Innaro ma Data Nemi Shiga Mganar Hakimi yaja mata Kunni da Kakkausan Muryan Kan in Ta sake ta Kara Shiga Mganar Itama zai Jingine ta Gefe Kamar yadda ya Jingine Goggo Abu..
Jin Haka yasanya Goggo Abu Ta Rikice sai Zazzabi da Ciwon kai Kafin kace kwabo ta Kwanta Ciwo koda Likita yazo Dubata sai Iske Jininta yayi bala"in Hawa nan Dai ya Dubata ya bata Mgunguna,ammh Duk da Haka Baba Hakimi bai Sakin ma Ra"ayinshi ba Koda ma akayi Haka ko Shashen Goggon Abu bai leka Ba gefe Daya kuma Inna Fulera na gida kwance ba lafiya Tun bayan Dawowarsu Hakimi ne Dayaji Lbri yasa Innaro da Ashe Suka Tafi Suka Dubata itama nan Suka Isketa jiiki yayi Zafi Maman lantana ke Kula da Ita Koda Suka zo suka Fada Hakimi bai Bata Lokaci ba ya Saka Aka kaita Asibitin garin Danbatta,Itama dai Damuwar ne ya Rafketa Hawan Jininta ya Tashi Gado Aka bata sai da ta Kwana Daya da Wuni kana aka sallameta Saboda Haka gabadaya Hankalinshi ba"a Kwance yake ba yana Jin Damuwarsa na Saka Ahali Dadama Damuwa gashi ya Lalatama Mufeeda Rayuwa da Farincikinta Gabadaya Saboda Shi bata da Sakewa kamar baya.
Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Umh..Bari nayi mgana da Iya Tukunnah.."Yafada yana Sauke kanshi kasa Cike da bakinciki mai yawa yakama Hanyar Dakin Iya kenan Basma tace"Daddy..." Ya waigo yana kallonta cikin Dankwabe kai da Marairaicewa Tace"Ka fara Shiga Wajen Mufeeda First Daddy..."Tafada Tana Hada Hannuwanta alaman Roko..
Tsam yayi yana kallonta Cike da Mamaki kafin yace"Alright..."Juyawa yayi zuwa Dakin Mufeeda ammah Kuma Acikin gangar Jikinsa babu karfin Gwiwa Turo kofar yayi Ya Shiga da Siririyar sallama bata Jishi ba Tana Zaune Dirshan Akan gado Naila na kan Cinyarta Kanta ba Dankwali sai Kitson Shikon Dake kanta Wata doguwar Rigar Roba ce ke Jikinta Kirar Bhrain,Kofin Shayi ne Ahannunta Tana Sha gefenta kuma Farantin Silba ne Cike da Kwai da Dankwalin Turawa Wanda Iya ta Kawomata Naila ce ke mika hannu Tana yafiton kofin Shayin Cikin Sanyin muryanta tace"Nailata zaki Sha Shayi ne.."Kamar tasani ko Ta daga kai Dariya Tayi Har Fararen Hokoranta Suka bayyana Kofin takafa mata abaki Tana bata kadan Kadan Tana Sha,Gefe Daya kuma tana gutsurin kwan Tana bata Tana Fadin"Zan Cigaba da baki Abincin aboye Nailata bana so kiyi Rama.."Itako Naila batamin Jinta malulan kwanta Take Cike da Jin Dadi.
Tahir Dake Tsaye bakin Kofa ya saki baki da Hanci yana Kallonsu Gefe Daya Wani Tsausayin Mufeeda ke kara Tasiri Acikin Ranshi ga Naila Wacce in ya kalleta sai yaga ko Hakkinta Allah ya kama Farida dashi bazata Taba Jin Dadin Duniya ba,Ganin Basuji Shigowarsu ba ya Sanya yayi gyaran Murya da Sauri Mufeeda Ta Dago Daga bama Nailan kwai abaki ganin Tahir Tsaye sai ya kara Rikita ta Rude,Ta Riko Naila Lokaci Daya Tana Kokarin Ijiye Kofin Shayi bisa Side Drower sai bai zauna Dakyau ba Da Hanzari Tahir ya Isa Wajen ya Rike Kofin Lokaci Daya yana Dauke Farantin kwan Tsurama Mufeeda ido Cikin Cikin Sanyinsa yace"Shiii..Is ok..Relax.."
Ya Fada yana Daidaita Natsuwarsa yana kuma kara gyara zaman Brifcase dinsa Dake Hannunsa,Cikin Kunya da Wani Nauyi Mufeeda ta sadda kai Tana Fadin"Ina..ina kwana Daddy..."
Bai amsa ba sai da ya Ijiye Brifcase dinsa gefen gadon Mufeeda ya mika Hannu ya Dauki Naila Wacce Tunda ya Shigo Take mikomai Hannu kafin ya amsa yana Fadin"Lafiya lau kin Tashi lafiya..? Ya fada cikin Kunya kadan Domin bayason ma yana kallon Kwayan Idanuwanta.
Itama Kunyar Takeji Shiyasa Bata Dago ba tace"Lafiya lau.."Shuru ya biyo bayan Mganar Mufeeda,Wacce kanta ke Kasa Duk kunya Ta gama kamata na Halin da Tahir ya Isketa Wata Zuciya tace"Me zaki boye Abunda Yagama Dake.."Dam Take taji Hawaye Sun Cikamata ido Shi kuma cikin Nazarinta ya Furta"Ya Jikin ki..? Kina jin Wani Ciwo Acikin jikinki..?
Shuru Tayi kafin ta girgiza mai Batayi mgana Illah Hawayen Data Rikewa ne Suka zubomata,Tsam yayi yana kallonta tana Share Kwallah cikin Tsausayawa ya Durkusa kan Gwiwoyinsa yana Rike da Naila yace"Don Allah kiyi Hakuri mufeeda kiyafemin laifin Dana aikata agareki Hakika na zama azzalumi Kuma naci Amana,Ina Jin kunyar kaina Mufeeda.."Yafada Cikin Rawan Murya.
Dagowa Tayi ganinshi Durkushe agabatan Yasa Tace Da Sauri."A"ah Daddy Meye Haka..? Don Allah katashi Ni Tun Daren da Abunda ya Faru Zuciyata ta yafemaka bayan ta tabbatar bazaka Taba aikata Haka da gangan ba.."Tafada kai Tsaye Tana Dauke Hawayenta Mikewa yayi Jikinsa Asanyaye kafin yace"Nagode Mufeeda,Ki sanar da Iya duk sanda Kikaji Wani Chanji Ajikin ki kinji ko .? Cikin Ladabi Ta Daga kai Da cewa"Toh Daddy.."Dan Mirmishi yayi kafin yace"Gud gal..Kuma kiyimin Alfarma zaki saki Jiki kamar baya,Kinga su Basma basajin Dadin ganinki Haka.."Kanta na Kasa Ta Dago da Niyyar mgana Suka Hada ido yadda idanuwansa ke Narkar da Zuciyarta yasa Tayi Saurin Sadda kai Tana Fadin"Insha Allahu Daddy.."
Mganarta Tamai Dadi Cikin Farinciki ya Furta.."Allah yayi miki albarka,ga Diyarki zan Fita aiki kada na Mkara.."Yafada yana mika mata Naila Wajen saka Hannuwanta ta karba Hannuwansu Suka Hadu Waje Daya Wanda Dukkansu sai da Sukaji Wani Shock Atare,Mufeeda Tayi Saurin Jan Hannunta Tana barin Jiki Shi kuma yayi Saurin Doramata Naila kan Cinyarta,Lokaci Daya yana Daukan Brifcase dinsa ya Fice Daga Dakin da Sauri da Kallo Mufeeda ta bishi Zuciyarta na Bugawa batasan Dalili ba Tun Zuwanta gida nan Indai zata ga Daddy Toh Zuciyarta Ta hau buguwa kenan da Sauri Sauri kamar Wacce Tayi Gudun Tsere..
Yana Fitowa yaci karo da Iya Dauke da Ghana must go Cike da Kaya Su basma na Tambayata ina Zata,taci ko Lullubinta Cikin Mamaki ya Karisa Kusa Dasu sai Dai Sukaji Muryanshi yana Fadin"Iya lafiya kuwa..? Ina zaki da Wannan kayan..?
Jin Muryansa yasa Iya Ta Durkushe Kasa Tana Fadin"Alhaji kayi Hakuri da Abunda zan Fadamaka,Na yanke Shawaran zan bar aiki agidan nan bawai Dom kun Saba min ba ko kuma kuna min Wani abu A"ah sai domin Tsira da Mutumcina.."Cikin Wani Haushi Tahir ya Furta.."Kan Issues din Farida ne ko..? Yafada Cikin bacin Rai bai bama iya Zarafin mgana ba yace"Tunda Muke Zaune Dake Acikin Gidan nan Iya na Taba Saba Miki..? Iya ta Girgiza kai Tana Sharan Kwallah Ya cigaba da Fadin"Su basma fa..? Nan ma ta girgiza kai ya kada kai yana Fadin"Toh Tunda babu Daya iya babu Inda zakije matukar Ni Tahir Mansur Danbatta ina Raye,Koda Farida Take Takama Ta Dalilinta Kikazo Gidan nan bata da Ikon Koranki Saboda Nima karkashin Ikona Take,saboda Haka mganar Gaskiya babu Inda zakije kina Tare damu Mudin Rai.."Yafada kai Tsaye kafin yace"Basma,Laila ku kama Jakar iya ku maida mata Ciki ni na Fita sai na Dawo .'Yafada kai Tsaye yana Wucewa Cike da Haushin Farida ji yake kamar ya yanke Duka alakan Dake Tsakaninsu Wata Zuciya tace"Not Now Tahir..Juz leave her to pay Wht She Didt For u.
Iyya bata da yadda Ta Iya Su Basma Suka ja jakarta Zuwa Cikin Dakinta Suna Murna Harda Su bassam Ihunsu ya Fito da Mufeeda Ita da Naila Tana Tambayan Lafiya nan Basma Ke Sanar Da Ita Itama Murnan Tayi Jin Tahir ya Hana Tafiya Tana ji Acikin Ranta In iya Tatafi ai Ta kara Shiga bala"i Fitowar Mufeeda yasa gidan ya kara Dadi Tun Tana Dari Dari dasu Basma Har Ta sake ganin basu kyamaceta ba sai ma Kafa kafa Da Sukeyi Da Ita Hakama iya Motsi kadan Sai Sunje meke Damunta Ita Tsausayi Su basma Ke bata ganinsu yara ammh Susan Matsalolin Rayuwa Da yawa.
******
*DANBATTA*
Ranar Asabar Tun Safe Tahir Da Basma,bassam da laila da Muda Garzali ya Debesu Zuwa Danbatta bayan Tahir ya cika Muda da laila da Sabbin kaya da Kayaan kwalama,gefe Daya kuma an Cika Booth da kayan Abinci Aka bar Mufeeda Da Iya agida da Naila, Wacce da zasu Tafi idanuwanta Suka Cika da Kwallah ganin Haka sai Tahir yace in zata Ta Shirya Harda Iya Su Tafi Gabadaya ammh Sai Mufeeda Tace bazata jeba Ta Shige Daki da Gudu Tana Dannen Kukanta Domin Tana Tunanin Da zarar Taje Danbatta Nunata Za"ayi Tayi na Cewa Tayi Cikin Shege kuma Inna Fulera yanzu batazatayi murna da Zuwanta ba Shiyasa Tace bazata Je ba Ta koma Daki Tana Kuka Abun ya Taba Ran Tahir Har Suka Isa Danbatta kanzil bai ce ba Gabadaya Rayuwarsa batamai Dadi Daya Tuna da Abunda ya Aikata ma Mufeeda sai yaji Duk ya Tsani kanshi.
Baba Hakimi na Waje da Jama"arsa Motar su Tahir Ta Tsaya Tunda Hakimi yaga Tahir yazo Aranshi yace mganar Zainabu ne,Shiyasa Ko Fuskar bai Sakarmai ba bayan Yaran Sungama gaisheshi Suka Shiga Cikin Gida Shi kuma ya Tsaya Waje Suna gaisawa da Jama"a Kafin ya karisa gaban Hakimi ya zauna yana Tankwashe kafa,Yau din yana Sanye ne Cikin Wani yadi kalan Sararin Samaniya Da Hulansa Zannar Bukar kallon Farko zakamai ka Fahimci yayi Rama Sosai sai Dogon Hanci Kai Tsaye ya mika ma Hakimi Hannu yana Fadin"Barka da Safiya Ranka ya Dade..".
Musabaha Sukayi kafin Hakimi yace"Yauwa sannunku da Zuwa..,lafiya nagangu Duka gidan Kuna Tafe da Safe Ina Ita Faridan..?Sunkuyar Dakai yayi kafin yace"Lafiya lau Baba Hakimi Dama na Dawo Dasu Muda ne Hutunsu ya kare Shine Muka Taho Tare dasu Basma.."Gyada kai Hakimi yayi kafin yace"Masha Allah..Allah sa akbarka ya Wajen Ita Mufeedan ince dai ba Wata mtsala.."Kai yagyada mai kafin yace"A"ah Babu Wata Mtala,Sai dai Dama Dalilin Zuwan nawa kai nake son gani Ranka ya Dade..".
Kai Tsaye Baba Hakimi ya kalleshi kafin yayi mirmishin Takaichi yace"Dama na sani Tunda na Ganka nasan kazo kan Mganar Sakaryar Uwarku ce,Uhmm.."Yafada yana Kallon Gefe Dayake babu Kowa saman Tabarman Tunda Tahir ya kariso Aka Watse aka barsu Su Zanta,Gaban Tahir ya Fadi ya Dago Yana kallon Baba Hakimi Cike da Firgici Domin Tunda yake da iyayensa bai Taba jin makamacin Wannan mganar yana Shirin Bude baki yayi Mgana Baba Hakimi ya Dakatar Dashi bayan ya Dagamai Hannu yace Cikin kakkausan Murya"Tashi ka Shiga Ciki zan Shigo yanzu Tunda kaima ka zama Sakarai mata na Walagigi Dakai baka iya Katabus.."Kunya Ta kama Tahir ya Sosa keya kafin ya mike yana Fadin"Ashigo lafiya..'"Ko kallonsa Baba Hakimi baiyi ba Domin Shima Haushinsa yakeji yadda ya biyema Shirmen Mata baizo ya Sanar Dashi Mtsalanshi ba,Da kallo ya bishi har ya Shige Gidan Idanuwansa Suka kada kamar yayi ma Tahir Kwallah Shikenan gareshi kwara Daya Tal kamar Dubu ammh Abu Tayi Sanadiyar Jefa Rayuwarsa Cikin Garari Bazai kyale ba Dole ne ya Nuna mata Kuskuranta Iskancin banza Wautar Wofi Zumunci me?na Cuta da Rashin gaskiya,Haka Hakimi keta Fada Shikadai Acikin Ranshi.
Tahir Sashen Innaro yafara Zuwa Sai ya Tarar Bata Ciki Tana Shashen Goggo Abu kai Tsaye ya Nufi Shashen Goggo Jikinsa Duk ba Dadi na Abunda ke Faruwa Tsakanin iyayen nashi Ta Dalilinshi,Da sallama ya Shiga yana Kokarin Tube Takalmin kafanshi Ashe Dake Zaune Gefen Goggo Abu Dake Kwance Kan Cafet Ta Tada kanta da Filo Ta mike Tana mai Sannu da Zuwa sai Innaro Dake gefenta ,su Basma Kuwa nadaga Gefe Sun Jeru kamar masu karban gafara,
Karisowa yayi yana Amsa ma Ashe Cikin Kulawa gefe Daya kuma yana kallon Goggo Abu Dake Kwance Duk Ta Rame kamaer ba Ita,yana Kokarin zama Kusa da Ita Innaro Tace"Sannu Attahiru..? Dago da kansa yayi yana kallon Innaro Cikin Kunya Domin Kunyar Kanshi yake da Abunda ya aikata Hatta Ashe bai iya Hada Ido da Ita ba,Kansa ya Sadda kasa bayan ya saka Hannu ya Rike Hannun Goggo yana kallonta Tana Kallonshi Itama Idanuwanta Suna Taruwa da kwallah.
Innaro Tace"Karka damu Attahiru kadai jin Wani Iri mu iyayenka ne Munfi kowa saninka Mu bar Haka amatsayin Gaddara mu Fuskanci gaba,Domin Hakimi yayi Fushi Sosai kan Goggo Wlh har yau bai Tako Falon nan ba Balle yazo ya Dubata Nayi mgana abanxa Daga Karshema yace In ban Cire baki na ba sai ya sabamin.."Tafada Kamar Tayi Kuka,Dago da kansa yayi kafin yayi mgana goggo Ta Fara Kokarin Tashi Da Sauri Ya Saka Hannu yana Taimaka mata Ita kuma Ashe ta saka mata Filo Abayanta ta Jingina Suna Jeramata Sannu Atare
Kai goggo Abu Ta gyada Tana Share Hanci Tafara Mgana"Attihiru Don Allah ka Yafemin Na cutar da Rayuwarka na Zama Sanadiyar Fadawarka Wani,Hali Wlh bansan Abun ya Wuce Misali ba Na zata Farida mai Jin mgana ne,Gashi Ta sakani Cikin Fitina nayi Sanadiyar da D'ana yayi Zina yayi ma Wacce ke kallonsa matayin Uba Ciki..Kaico na Ni Abu gashi Babanku na Fushi Dani Ina zan Saka Raina naji Dadi.."
Tafada Tana Kuka Sosai,Tahir yayi Shuru yana kallon Goggo Zuciyarsa na Gudu Bayansa ya Waiwaya da Niyyar yama Su Basma mgana su basu Waje sai yaga wayam Sun Dade da Ficewa Tun Sadda Innaro Ta Fara mgana,maida Hankalinsa Yayi kan Goggo Abu kafin ya Saka Hannu ya Riko Hannunta Cikin Tsausayawa yana Fadin"Bakomai Goggo Don Allah kidaina bama Kanki laifi,Nima ina da Laifi Tunda na bari Tuntuni Farida Tafi karfina ban Isa na gayamata Taji ba,Abunda ya Faru Tsakanina da Mufeeda goggo bamu Isa mu Tsallakeshi ba Domin Rubutattace ne Daga Rabbil Izzati,Kidaina damun kanki kinga Jininki ya Hau,ki,Daina damuwa Indai Mganar Baba Hakimi ne Abunda ya Kawoni Kenan zan mai mgana Kuma Insha Allahu zai ji mganata Kinji.."Yafada yana Kallonta LokaCi Daya yana Sanya Hannu yana Share mata Hawaye,Hannunsa ta Riko Tana kallonsa kafin tace"Nagode Attahiru Allah yayi Maka albarka.Allah ya Kare Gaban ka da Bayanka ya Raya maka Zuru"a,.."Da Ameen yake amsawa Su Innaro na Tayashi.
Cikin Alhini goggo Abu Tace"Ina Mufeedan? Fatan dai bawata mtsala..? Itama Inna Fuleran Sai da Ta Kwanta Asibiti.."Tahir yace"Lafiyanta kalau goggo ba Wata Mtsala sai Abunda ba"a Rasa ba,Eh Ashe ta sanar dani kafin na Wuce zan Shiga na Dubata kuma na Nemi Izinin Hakimi kan ya bari na Tafi da Inna Fuleran Kaduna Kila Dukkansu In Suna ganin Juna Hankalinsu ya Kwanta."
"Kul..karka Fara Ban Amince ba Kuma Ban lamunta ba.."Sukaji Muryan Hakimi Daga Bakin Falon yana Shigowa Gabadayansu Suka Mike Banda Goggo Dake Zaune Tana kallonshi Cikin Fada Baba Hakimi yace"Ka Barta anan,Kawai ka kyaleta zata Warware Damuwa ce Kuma Ta zama Dole Domin barin Fulera garin nan Zargi zai Hau kan Mutane Har Daganan lbrin ya Shigo Gari Abunda bana Fata kenan.."jinjina kai Tahir yayi kafin yace"Hakane Ranka ya Dade An bar mganar.."
Gyada kai yayi kafin yace"Yauwa...Kuskure ne ya Riga yafaru ba Yarda zamuyi,Tunda ka Hadu da Shashashar Uwa Mara Lissafi Tayi Dalilin bata Rayuwar Mutane Dama Ciki harda D'anta kan Dalilinta Mara Tushe ballatana Makama.."Yafada yana Hararan Goggo Abu Data Sadda kai Tana Sharan Kwallah.
Tahir da Ashe Suka kalli Juna Cikin Rauni Tahir zai yi Mgana Kenan Innaro Ta Rigashi Da Fadin"Haba Ranka ya Dade sai Hakuri,Tunda Abunda Ake Gudun ya Riga ya Faru..."Ke Salamatu Rufemin baki.."Hakimi ya Katseta Cikin Fada Da Fushi.
Shuru Tayi Tana Kallonshi Cikin Nunata Da Yatsa yace"Kul Ki kama bakinki Kan Wannan mganar in ba So kike na Saba Mii ba,kina Wata mganar Banza Inda Tun Lokacin da D'anta yazo mata Bukatarsa Ta Saurareshi Haka Zata Faru..? Nace Haka zata Faru..? Yafada Cikin Tsawa kafin ya Cigaba Da Fadin"Dalilin Rashin Sauraranshi Shi ya Jawo komai,Banta ba Jin inda kaki naka kaso bare ba Zumunci Iskanci ko na Cuta Tunda Ita Faridar batasan Ciwon kanta ba Su kuma Iyayenta Sun saka mata ido toh mu sai mu bar Rayuwarmu Da'nmu Ta lalace ..? Ammh Saboda Sakarci,Kina babba Ki Haifi kamar Attahiru,Da Aisha ammh baki da Wayau ko kadan,Zumuncin Dakike Mgana Ba Dalilina Kikasan Ibrahim din da Aliyan ba..? Haka Kurum Saboda baki Daukeni Da Daraja ba, Kika Dakatar Dashi Wai kada ya sanar Dani Sai da Abu ya Kwabe Kana kizo kina Kuka kina Nadama Lokacin bata da Amfani.."Yafada yana Nuna goggo Da Yatsa Cikin Fada.
Ashe da Tahir dai ba Baki Domin yau kam An kure Baba Hakimi ba Kasafai Yake Fada ba Sai an Kureshi,Hakurinshi Tahir ya Kwaso yana Saba Babban Rigansa yace"Ke ni bari ma Kiji Haushinki nakeje Wlh kamar na Makeki Abu,Shiyasa na Kyaleki ki Girbi Abunda Kika aikata Kin Cucu kanki ne Domin Ita Farida ba Ita kika batama Rayuwa ba Marainiyar Allah kika saka Cikin Gararin Rayuwa kuma sai Allah ya Sakamata akanki Domin Duka Laifin na Attahiru ya Rataya a Wuyanki ne Zainabu.."
Yafada Lokaci Daya ya Juya yana kokarin Ficewa Daga Falon Goggo Abu ko Banda Kuka Babu Abunda Takeyi Innaro na Tsaye Ba bakin mgana Tahir ne ya Bi bayan Hakimi yana Fadin"Baba...Ka Tsa..."Kai Saurareni nan Attahiru.."
Hakimi ya Katseshi bayan ya Waigo Sagale Tahir yayi yana Kallon Hakimi Wanda yakallesa Shima yana Fadin"Bari kaji na Fada maka zaka batama kanka Lokaci ne Indai Akan Mganar Abu ne,Gwara Tun Wuri kazo ka Wuce Sabgar ka zaifi maka in kuma ka Dameni Wlh Allah Harda kai zan Hada na ci Muku Zarafi Domin kaima ina Cike dakai yadda ka zauna mata na Kwallo da Rayuwarka kajima na Fada maka.."ke Aisha...?
Yafada yana kallonta da Sauri Tace"Na"am Baba.."
"Fitio Maza Ki Tarkata ya"yanki ki Wuce gida kaima ka Tarkata naka ka koma bakin Aikinta Ku barta Ta Shiga Nadamarta Ita kadai.."Yafada yana Ficewa Daga Falon.
Gabadayansu Jikinsu yayi Sanyi bamai Kwakwaran Motsi sai Kukan Goggo Abu Dake Tashi Kasa kasa.
Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.
*Janafty*
*Aisha alto*