Chapter 27
Bayan Jay ta koma ɗakinta ta ƙara ƙanƙame Ayaanah ta cigaba da kukan da take yi, ita ma Ayaanah ganin Jay na kuka ita ta fashe da kukan.
Tana cewa " mummy ki yi haƙuri ki dena kuka tana goge mata hawayen dake zuba a kan fuskarta.
Munarh da dawowarta kenan daga wurin mijinta ta tarar da su a haka.
Saurin ƙarasowa inda suke ta yi ta ce " Jay meke faruwa kika sa Ayaanah a gaba kina kuka tana kuka babu me bawa wani haƙuri?"
Shiru ta yi bata ce mata komai ba ta cigaba da kukan ta.
Ayaanah da ita ma take kukan ta ce " aunty ki cewa mummy ta dena kuka."
Murmushi Munarh ta yi ta ce " zata dena kinji kanta ne yake yi mata ciwo."
Murmushi ta yi ta ce " nima ina kuka idan kaina yana ciwo."
Hannunta Munarh ta kamu ta ce " yawwa yanzu mu ƙyale mummy ta yi bacci, maza kije wurin hajiya mama tana can tana ta nemanki zata baki chocolate ."
Tsalle ta yi ta ce " dagaske?"
Gyaɗa mata kai Munarh ta yi alamun tabbatarwa.
Da gudu ta fita tana ta dariya.
Bayan Ayaanah ta fita Munarh ta zauna a gefen Jay ta ce " menene ya sa kika saka yarinya a gaba kina kuka tana kuka?"
Sai a lokacin Jay ta ɗaga kanta ta kalli Munarh ta ce " meyasa ba zanyi kuka ba Munarh."
" Ashe duk tsawon lokacin nan da na ɗauka tare da Ayaanah ina jin ƙaunarta a raina ashe ita ɗin jini na ce."
Ta faɗa tana ƙara fashewa da wani kukan.
Da mugun mamaki Munarh ta miƙe tsaye tana faɗin " bangane me kike shirin faɗa ba.?"
Hawayenta Jay ta goge ta ce " Ayaanah ʼyar da Jasrah ta haifa ce kafin ta rasu."
" Kin ƙara ɗaure man kai Jay, how is this even possible?"
Jinjina kai Jay ta yi ta ce " i am serious about what i said."
Zama ta yi a gefen Jay tana maimaita innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Labarin duk abinda mamy ta faɗa musu ta bawa Munarh.
Shiru Munarh ta yi na wasu ʼyan sakanni sai kuma ta ce " tun ranar farko da na fara ganin Ayaanah na ji a raina tabbas akwai wata alaƙa me ƙarfi da ke tsakaninku."
" Because you share so many things in common and ba zai taɓa yiwuwa ba a ce coincidence ne."
Jinjina kai Jay ta yi ta ce " nima lokacin da na fara ganinta abubuwa da yawa suka rinƙa yi man yawo,amma ban taɓa tunanin cewa yarinyar da Jasrah ta haifa ba ce."
Shiru mom ta yi wasu abubuwan da suka faru a baya suna ƙara making sense a cikin kanta.
Mamy ganin ta yi shiru tana tunani sai ta ce " tunanin me kike yi Bilkisu?"
" Sai yanzu abubuwa da yawa suke warware kansu nake fahimta."
" Ranar da Jay ta fara zuwa gidan nan da tare da Ayaanah har suma na yi saboda firgici."
" Na yi duk irin tunanin da ya kamata na yi amma ban ga ta inda nake da alaƙa yarinyar ba."
" Lokacin da aka haife ta da ALIYU take kama shiyasa ban taɓa kawo komai a raina ba."
" Ashe yarinyar margayiya ce."
" Allah sarki Jasrah Allah ya jiƙanki ya gafarta maki."
Mamy ta ce " Ameen."
" Wasu abubuwan da yawa idan Ayaanah ta yi ina ganin yarintar Jay ne,shiyasa na kan shiga cikin ruɗani."
" Duk da kuma nasan ba zai taɓa yiwuwa a ce Jay ta haihu a waje ba ban sani ba."
Mamy da ke sauraronta ta ce " jini kenan, sai daga baya ne kamanninta suka rikeɗe suka koma na Jay."
Bayan mamy ta yi sallar maghriba ta ce ma mom " bari na koma gida na bar Jiddarh da Safiiyah a gida."
Jinjina kai mom ta yi ta ce " muje na raka ki mota."
Bayan mom ta raka mamy ta dawo ta ɗauki wayarta ta kira wata me gyaran jikin amarya da ta sani a sokoto.
Bayan sun gaisa ta ce " tana son ganinta nan da kwana biyu,bayan ta amsa zata zo, mom tace ta tura mata da account number sai ta saka mata kuɗin mota."
Meemarh ce zaune a parlour tana ta sauraren yadda Billy ke faɗin kirkin ʼyan gidan su Jay.
Ita dai murmushi kawai take yi tana jinta,bayan ta gama bata labarin ta ce " i would like to meet them one day."
" Yes meemarh they are actually nice people."
Suna cikin hira sai ga Faruq ya shigo parlour.
Zama ya yi a gefen kujerar da meemarh take ya gaishe da ita Billy ma ta gaishe da shi.
Bayan sun gama gaisawa meemarh ta ce " Faruq ya ake ciki?"
" Ka samu wani bayani ne da zai taimaka mana."
Girgiza kai ya yi ya ce " meemarh ban samu komai ba har yanzu, kinga binciken kawai muke yi kai tsaye babu wani abu da zai ɗora mu a kan hanya."
" Something like sunan local government ko kuma sunan anguwan ku."
" Amma duk da haka akwai wani mutum da ya haɗa ni da wani private investigator,ya ce na bashi kwana biyar."
Jinjina kai ta yi ta ce " toh shikenan Allah ya kaimu."
Ya ce " ameeen."
Bayan mamy ta dawo ta shiga ɗakin da aka bama Safiyyah.
A zaune ta same ta kan dadduma da ƙur'ani a gabanta tana karatu.
Fitowa ta yi ba tare da ta ce mata komai ba ta wuce ɗakin Jiddarh.
A zaune ta same ta tana gyaran kayanta dake cikin drawer.
Tana ganinta ta ce " mamy har kin dawo?"
" Sannu da dawowa."
Yawwa ta ce sannan ta zauna a gefen gado ta ce " su ALIYU fita suka yi?"
" Gaskiya suna ɗakinsu don tunda kika fita babu wanda ya ƙara fita daga gidan nan."
Jinjina kai mamy ta yi ta ce " na ɗauka sun fita ne don na san baƙar zuciya irin ta ALIYU."
Dariya Jiddarh ta yi ta ce " wai mamy wadda ta zo da aunty Jay ranar nan wacece ita?"
Dariya mamy ta yi ta ce " dama ba zaki gane ta ba, maƙotan su mom ne tun suna maiduguri."
" Sai da kika ambaci sunan Jay ma na tuna, yau aka saka ranar bikinta fa."
Da murna ta aje kayan da take linkewa ta ƙara matsowa kusa da mamy ta ce " ki ce muna da ebo shoki,yaushe aka saka?"
" Sati biyu aka sa." Mamy ta bata amsa.
Miƙewa ta yi tsaye sai kuma ta koma ta zauna ta ce " kai ni ban ma san wa zan faɗawa ba ya taya ni murna."
Ita dai mamy kallonta kawai take tana murmushi can kuma ta miƙe ta ce " na manta ma ashe su yaya suna nan."
Mamy da take ta sauraronta ta ce " kin san dai yau ran ALIYU a ɓace yake karma kije mashi da shirme, babu ruwa na idan ya bige ki."
Turo baki ta yi gaba ta ce " ni dama ba shi zan faɗawa ba ai,yaya Zannur zan faɗawa."
" Yawwa mamy gobe zanje gidan mom gaskiya kin san mune manyan ƙannen amarya kuma manyan ƙawaye."
" Kinga ya kamata muje ayi duk wani shirin da za'a yi damu."
Ita dai mamy bata ƙara ce mata komai ba.
Fitowa ta yi ta tafi ɗakin su.
Ɗakin Zannur ta fara yin knocking ta ji shiru, ta ƙara yi ta ji shiru.
Tura ƙofar ta yi tana leƙa ciki, ganin babu kowa yasa ta koma wurin ƙofar ɗakin HAYDAR ta yi knocking.
Bayan ʼyan sakanni kaɗan sai gashi an buɗe.
Zannur ne ya buɗe,ganin ita ce yasa ya matsa gefe yana murmushi ya ce " daga ganin wannan fuskar ta ki gulma kika kawo."
Dariya ta yi tana shigowa ta ce " kai yaya kuma ni shikenan kullum a kawo gulma zan ƙare."
Shima dariya ya yi ya ce " ai nasan hali ne."
HAYDAR dake zaune a gefen gado yana dannan wayarshi, ya yi kamar bai san akwai wata halitta ba bayan shi a ɗakin, kuma yana jin duk abinda suke faɗa.
Stool ɗin jikin madubi ta janyo ta zauna ta ce " ka san me yaya?"
Ya ce " a'a ."
" yau ina cikin farin ciki ne, kuma na rasa wanda zan faɗawa, ka san bani da ƙawaye shiyasa na zo na faɗa maka muyi murnar tare."
Kallonta Zannur ya yi ya ce " toh ina jinki Tanin mamy."
Gyara zama ta yi ta ce " yaya yau fa aka saka ranar auren aunty Jay."
Danna wayar kawai yake yi amma gaba ɗaya hankalinshi yana wurin Jiddarh da take faɗawa Zannur an saka ranar auren Jay.
Tun bayan da yaji abinda Jiddarh ta faɗa zuciyar shi ke wani irin bugu da ba na lafiya bane.
Fatttt fatttt fatttt haka zuciyar shi take ta bugawa.
So yake ya ƙaryata abinda kunnuwanshi suka ji amma zuciyarshi ta kasa bashi wannan damar.
" Yaya kuma sati biyu aka saka fa." Jiddarh ta ƙara faɗa.
Wani tari ne ya sarƙe shi kuma yana fitowa ne tunda ƙarƙashin ƙirjinshi.
Tunda Zannur ya ga haka ya ce " Jiddarh maza ki je ɗaki zamu cigaba da magana kinga HAYDAR ya ƙware."
Jinjina kai ta yi ta ce " sannu yaya sannan ta fita daga ɗakin.
Inda yake ya ƙarasa kafin yaje har ya sakko daga kan gadon saboda yadda tarin ya yi ƙarfi.
Sannu yake ta jera mashi sannan ya miƙa hannu ya ɗago shi.
Abinda ya gani ne ya firgita shi har yana ƙoƙarin tillar da shi.
" HAY...HAYDAR amon jini fa kake yi."
" HAYDAR don Allah kar...karka yi ma kanka illa."
HAYDAR,HAYDAR,HAYDAR yaka Zannur ke ta kiran sunan shi amma inaaa jikinshi ya saki gaba ɗaya.