17
Chapter 17
Nazli bata gama fita daga mamakin Abla ba Araf ma ya tura kujera ya sauko cikin harɗe hannaye a ƙirji ya ce. "ni kuma pancake na ke so." Shiru Nazli ta yi kasaƙe tana ganin tsantsan taɓara. "Uhhem, what's going on here?" gaba ɗayan su suka ɗaga kai dan ganin Wanda ya yi maganar. "Aunty Fari?" Abla ta ƙira sunan ta ruga da gudu ta rugumu ta. "Good morning Aunty." "Morning princess, wa ya taɓa min favorite niece dina?" Fari ta tambaya daidai tana ƙarasa saukowa daga matattakalar beni suka doshi dining da Abla da ke riƙe da hannunta gam ta ƙi sakinta, ta jawa Abla kujera ta zauna kana ta ja ta kusa da ita ta zauna, ta kalli Araf da har yanzu ke tsaye bai motsa ba sai zunbure–zunburen baki yake irin na shagwaɓaɓun yarinya nan ta ce. "Boy wa ya taɓa min kai da wannan safiyar?" Ba tsoro ko shakka ya cire yatsa ya nuna Nazli da har yanzu mamaki bai gama ƙare a wajenta ba, tana ganin ikon Allah yadda gabaki ɗayan su sun manta da wanzuwar ta a wajen, sai a lokacin Farida wato Fari ta kalli Nazli cikin yamutsa fuska ta ce. "me kika masu daga zuwan ki har kin fara ɓata masu rai." Kan Nazli ta samu zarafin ɓude baki ta kare kanta carab Abla ta katse ta ta hanyar faɗin. "Look Aunty, mun ce mata mu noodles da pancake mu ke so but she's forcing us to eat what she cook." Abla ta faɗa hakan cikin zunɓura baki, baki buɗe Nazli ke kallon yarinya ƙarama da ita amma ta iya sheƙa wannan zunzurtun karya har haka.
Rashin sanin da me za ta kare kanta ne ya sa saɗaf saɗaf ta bar palon, dan bata kuma san me za ta ce ba. Ƙiri–ƙiri a gaban idonta suka lalaɓa mata sharri irin haka, wucewarta kitchen ta yi domin haɗa masu abin da suke da buƙata kar shi ma ya zame mata matsala dan ta lura gaba ɗaya yan gidan ba mutunci ne da su ba daga manyan su har yaransu.
Tausar kanta ta soma tana bawa kanta haƙurin za ta juri komai da za su mata har zuwa lokacin da Allah zai masanya mata aikin da ya fi wannan, amma zuwa nan za ta kau da kai daga duk abin da za ta gani ko ta ji, kamar yadda Ammie ta mata nasiha kafin fara aikin. Wannan kaɗan kenan daga cikin aiki a ƙarƙashin wani, sai dai ta ɗaure damarar fuskantar ko wani ƙalubale da za ta fuskanta wannan kuma kaɗan ne compared to abin da ta fuskanta a baya dan haka shima sha come and pass.
{}{}{}{}{}
Tana gama haɗa noodle da pancakes ta ɗaura a a babban tire kanta tsaye ta nufi dining, sai dai me za ta gani? Samu ta yi suna cin doyar da kwan da suke ce basu so, tsaye ta yi da abincin da ke hannunta ta ma rasa me za ta ce a wannan gaɓar, ta girgiza kai kawai tare da ɗaura masu kan dining ta juya da nufin komawa palo Fari ta tsaida ita hanyar faɗin.
"Idan kin gama akwai gyaran ɗaki na da wanke toilet da za ki yi, ki tabbatar kin yi abin da na sa ki kafin na dawo." Ta juya ga yaran ta ce. "Baby's ni zan tafi school, me kuke son na kawo muku." A tare suka haɗa baki wajen faɗin. "Chocolate." "Okay then sai na dawo bye." Ta ɗaga masu hannu kana ta juya ta fita cikin sarsarfa tana duba agogon tsintsiyar hannunta ta fita, ta bar Nazli da baki buɗe tana ƙoƙarin haɗa komai wuri ɗaya, ta so gaya mata wankin toilet ba aikin ta bane girki kaɗai ta zo yi amma ko kan ta farga Fari har ta bar palon sai ƙarar mota da suka jiyo alamun fitan ta.
Ajiyar zuciya ta sauke cikin danne abun da take ji ta nufi dining da suka yi kaca–kaca da shi, ko noodles ɗin ma da suka sa ta dafa basu taɓa ba ta na nan a yadda ta kawo ta, gwara pancake din Araf ya ɗan tsakura kaɗan shima ya barshi. Ta
kalli inda suka koma palo suna wasa da ipad na su, ta girgiza kai kawai ta tuna da yarintar ta.
Sai dai ita duk gatan da ta samu a wurin iyayenta bai sa ta sangartu har haka ba, domin Yummah(Ishiraƙa) bata ɗaga mata ƙafa sosai ta ke tsaye a kanta, idonta kuma na ga dukkan motsin ta. Dalilin da ya sa ma suke yawan samun saɓani tsakaninta da Daddy kenan kan shagwaɓata da ya ke dayawa, a cewarta ba'a nunawa yaro so dayawan da har ya sa idonka rufewa ka kasa gane dai dai ko akasin hakan ba, dole a nuna masu kuskuren su idan suka yi ba daidai ba domin gyara goben su. A lokacin idan Yummah na mata irin haka sai ta ji ai duk duniya bata da maƙiya kamar ta gaba ɗaya ta bi ta tsangometa ko me ta yi sai ta mata faɗa, bata manta ranar da Yummah ta zane ta wayar charger har sai da ta fidda mata shati a jiki dan kawai Shehu mai Gadin su a wacan lokacin ya yi mata faɗan kan wasa da ruwa ta murguɗa masa baki tare da ƙunƙuni. A ranar kuwa Yummah ta ga fushin Daddy da bata taɓa gani ba dan ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba, wai dan me za ta saka wayar charger ta zane ta me ya sa ba za ta mata magana da baki cikin lallɓawa ba, wannan na cikin manyan saɓanen da Daddy da Yummah suke samu a kanta dan a cewar Daddy shi bai yarda a saka hannu a doki yaro ba abin da magana da baki bai yi maganin sa ba to dukaa ba zai magance sa ba sai ma ƙara lalata abu maimakon a samu abun da a ke so sai kuma a koma ruwa.
A wancan lokacin ita daɗi abun ke mata idan ta ji Daddy na yi wa mahaifiyyarta irin wannan faɗan kamar yadda ta saka ta a gaba da faɗa, abu kaɗan ta ƙira sunan ta a kaushashe. Gaba ɗaya ta bi ta saka mata ido dayawa komai ta yi bata yi dai dai ba Shi ya sa ma ta fi shaƙuwa da Mommy don komai ta kawo mata tana goyon bayan ta ba kamar Yummah ba. Sai yanzu take gane ashe gata Yummah take nuna mata, wasu hawaye masu zafi ne ta ji sun zubo mata, ta sa hannu ta da ta goge.
======
Bayan gama tattara wajen ta gyara sai ta maida sauran abincin da ke cikin cooler ta juya cikin madaidaitan wormers ta maida dining dan Hajiya Binta na iya saukowa a ko wani lokacin don yin break, kana ta koma palo. Ta samu yaran na nan har yanzu suna buga games a ipad na su hankali kwance, ita ma ta samu waje kan kujera ta zauna tare da maida hankalin ta bisa tv da ke buɗe ta soma kallo.
Araf ne ya ɗago ya mata kallo ɗaya ya sauke kansa kan game ɗinsa, Sai dai lokaci zuwa lokaci Nazli kan ɗaga kai ta kalle matattakalar benin dan ganin saukowar Hajiya amma shiru kamar an aika bawa garin su, sai ya zamana ma kamar bata cikin gidan. Tunanin haka ya sa ta kasa haƙuri ta ce. "Ban ga Maman ku ba ko har yanzu tana bacci ban ga ta fito ba." "She's gone out." Cewar Abla idon ta na kan ipad ɗinta. "Ohhh! Okay." Iya abin da Nazli ta ce kenan ta cigaba da kallonta tana tunanin ina kuma ta fita da safen nan, amma da ta tuna wannan fa bai shafe ta ba ya sa ta ɗaga kafaɗa irin oho ɗin nan."
Araf ne ya tashi ya nufi fridge ya buɗe ya ɗauki ruwa, ƙoƙarin buɗe murfin bottle water ya ke amma ya kasa. Lura da abin da ya ke ya sa Nazli miƙa masa hannu da ya bata ta buɗe masa, ba musu kuwa ya miƙa mata ta buɗe ta basa. "Thank you." "You're welcome." Cikin son jansa a jiki ta ce. "Ya sunan ka. "Araf." Murmushin nan na ta sakar masa cikin kaɗa kai ta nuna Abla. "And she?" "Abla." Ya bata amsa. "Ma sha Allah, kuna da sunaye masu daɗi Araf." Ha hankali ya furta. "Thank you." "You're welcome." Ta cigaba. "And how old are you?" "Seven?" "Ka ce you're a big boy." Da haka ta soma jansa da hira tana tambayar wani aji ya ke a makaranta, tun yana amsa mata ciki–ciki har ya soma sakewa yana magana.
"za ka iya nuna mini ɗakin Auntyn ku na share mata?" "Yes." Daga haka ya yi gaba ita kuma ta mara masa baya, har ɗakin Fari ya kaita kana ya juya ya koma palo ya barta tana ƙare ma ɗakin da a ka gama harƙitsa da kaya ta ko ina kamar ɗakin mahaukata.
Da kayan da ke baje kan gado ta fara, masu datti ta haɗa su gefe guda marasa dattin kuma ta naɗe ta maida cikin wardrobe. Sai da ta gama gyara ɗakin tsaf kana ta koma bandakin shima ta masa wanki ba na wasa ba nan da nan ko ina ya shiga hayacinsa. Koda ta gama ta sauka bata ga Abla da Araf ba sai ta yi tunanin ko sun wuce ɗakin su, ta kama palon da tattare ganin yadda suka yi watsi da pillow case.
Har yamma Hajiya Binta bata dawo ba, sai dai bayan dawowar Fari ta bada umarnin abin da za'a dafa na dare wanda sai da ta tsaya yi, koda ta gama haɗa komai ta jera masu a dining kana ta soma haraman tafiya gida.
A na ƙiraye–ƙirayen sallar magrib ta shiga gida, ta samu Ammie na tsakar baranda ta gama alwalla kenan za ta tada sallah. "Ammie ina wuni na same ki lafiya?" "Lafiya Nazli sai yanzu zuwan?" "Ehh wallahi Ammie Hajiyar ce bata nan na yi zaman jiran ta ban dawo ba kar na yi gaban kai na abu ya zo bai yi daɗi ba, kuma ta bar yaran a gida bani da waya ma bare na ƙira ta." "Ai shi kenan, ni zama har almuro nan ne bana so dukkan inda ƙarfe biyar ta yi ya zamana kina gida. Ba girman ƴa mace bane a ganta a waje a wannan lokacin." "In sha Allah Ammie hakan ba za ta sake faruwa ba." "Ta dawon ne da kika zo yanzu?" "A'a." Ta girgiza kai.
"Amma akwai ƙanwarta dake tare da su, dama ɗazun ita ma ta fita sai da ta dawo na samu damar zuwa." Daga nan ba wanda ya yi magana a cikin su, ta ɗauke buta ta shiga kama ruwa da ɗauro alwala Ammie kuma ta kabbara sallah.