Chapter 5
by @oumfatayat
*FARAUTAR MUTUNCI*
Marubuciya:
Na’ima Sulaiman Daƙayyawa (Oum Fatayat)
Page:5
Ta sake damalma jikinta a cikin kashin tana faɗin “ Wayyo ciki na, o ni Hajjo wannan yarinya ta jamin salalan tsiya”.
Da gudu ya yo kanta, hankalinsa duk a tashe ɓolon aman da Nuri take ne yasa shi ƙara juyawa, ihu Hajjo ta sake ƙwalawa tana burburwa a dole dai ya bar Nurin ya taho wajen Hajjon.
Nuri kuwa aman ya gama galabaita ta, gaba ɗaya jikinta babu ƙwari, ga warin zawon Hajjo ya dameta da yawa, Mahmud kuwa da ya ga babu yadda zai yi da Hajjo ga kuma yasan Nuri ba tason wari, don abun kamar hallitar tane, sai kawai ya yi tunanin kirawo maƙociyarsu Madam Karima, don ta taimaka masa.
Madam Karima mutuniyar kirkice, ta maida Nuri tamkar yar da ta haifa, babbar maca ce tana da yara harda auraru, kuma ma’aikaciyar lafiya ce a Asibitin Gwamnati na nan jihar Kaduna.
Tana shigowa taga yadda Hajjo take yi ta san shirya abunta tayi, inda Nuri ke kwance ta nufa, nan ta bata taimakon gaggawa ta kuma taimaka mata ta, ta kaita ɓangaran Mahmud, kana ta dawo ga Hajjo.
Matsowa ta yi kusa da ita, ta zaro wata zarbaɗeɗiyar Allura daga cikin First Ed’s Box,tana ƙoƙarin tsikarawa Hajjo,sai dai da mamaki Hajjon zunbur ta miƙe, tana faɗin “Ita fa ba a mata Allura”.
Ganin yadda Madam Karima ta haɗe rai ne yasa adole ta tsaya, haka aka mata Allurar jikinta yana karkarwa.
Madam Karima ta ƙara da cewa, za amata ita kullum sau uku, har tsawon kwana huɗu, kafin kace me Hajjo ta ware, amma Madam Karima tace sam bata san zance ba dole sai anyi, Hajjo da taji batun Allura, kafin Mahmud ya ankara har ta fara gyara waje nan da nan ta shiga ban ɗaki ta wanke jikinta ta kuma wanke kayan da ta ɓata.
Hatta da wajen da damalmala shima, sai da ta gyara shi, wai don duk Madam Karima tace tunda ta warke ba sai an cigaba da alluran ba, amma fur Madam Karima ta ƙeƙashe ƙasa tace ai ƙa’idar alluran kenan.
Duk da Hajjo ta yi kusan rabin aiki, sai da Madam Karima ta sake gyarawa Nuri falonta duk wani kayan sa ƙamshi da tatabbatar zai sa falon ya dawo hayyacinsa, sai da Madam Karima ta yi amfani da shi, kafin kace kwabo ƙamshi ya karaɗe ko ina.
Hankalin Hajjo ya gama tashi, domin tabbas idan har ta sake bari aka mata wannan allura, wada za kaji kamar an ɗana mata garwashin wuta tsabar zafi, ina sam ba zai yuba, gara ta haɗa inata inata ta tafi. Madam Karima na tafiya taje ta dawo, Hajjo ta yi wuf ta fice daga gidan don ko Mahmud ɗin bata yi masallama ba.
Bayan Madam Karima ta dawo ne, take tambayar Mahmud inda Hajjon ta shiga, nan suka nemeta ko ina bata nan, hankalin Mahmud ya dugunzuma ya tashi, nan ya fita ko Allah yasa ya ganta, cincirindon mutane ya gani a bakin titi, tambayar wani ya yi mai ake a can, shine yake shaida masa wata tsohuwa ce mota ta buge ta ta…
بقلم أم فتيات 👧👧👧 ✍🏼…..