Chapter 28
A zaune Sooraj yake a parlour yana aiki a system ɗin shi,Layla na gefen shi a zaune.
Wayar shi ta fara ringing ya kalla yaga sunan Ummah na yawo a kan sceen ɗin.
Ƙin ɗagawa ya yi saboda baya son ya yi magana da ita Layla na wurin.
Ganin ya ƙi ɗagawa yasa ta kalli screen ɗin don ganin wake kiran shi.
Ganin sunan Ummah a jiki ya sa haka nan ta ji gabanta ya faɗi.
Kallon shi ta yi ta ce "Ummah ce fa ke kiran ka meyasa ba zaka ɗauka ba?" Ta faɗa don ta ji me zai ce.
Ƙoƙari ya yi kar yanayin fuskarshi ya canja ya ce " eh na gani maganar da zamuyi da ita ne mai ɗan tsayi, shiyasa na bari na gama aiki sai na kira ta, tana son zan yi mata visa ne zata je umrah."
Jin abinda ya faɗa ya sa ta yi murmushi har tana hamdala a cikin ranta ta ce " ya kamata dama ta koma ai last year bata je ba."
Murmushi ya yi ganin ta yadda da abinda ya faɗa mata ya cigaba da aikin da yake yi.
Ita ma wayarta ta cigaba da dannawa ganin ya cigaba da aiki bai ƙara magana ba.
Rikicewa gaba ɗaya Zannur ya yi ya ma rasa abinda ya kamata ya yi.
Bamɗaki ya shiga ya ɗebo ruwa ya shafa mashi a fuska amma a banza ko motsi bai yi ba.
Wani tunanin ne ya zo kan shi sai kawai ya ɗauki makullin mota ya fita.
Motar HAYDAR dake gidan mamy ya ɗakko ya kawo ta bakin ƙofar part ɗin su, fitowa ya yi ya koma ciki ya ɗakko HAYDAR da ƙyar ya shigar da shi cikin motar.
Babu wanda ya lura da lokacin da Zannur ya saka shi a cikin mota sai kawai ya yi reverse yana yin wani mahaukacin horn.
Hatta mamy dake ɗakinta sai da ta tsorata da irin horn ɗin da taji ta leƙo amma lokacin har Zannur ya fita da motar daga gidan.
Duk tunaninta HAYDAR ne, da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga neman layin shi.
Ta kira na farko bai ɗaga ba ta kira na biyu, har sai da tayi mashi kira uku sannan ta haƙura ta koma kiran layin Zannur don ta san ba zai barshi ya fita shi kaɗai ba.
Shima kira uku ta yi mashi bai ɗaga.
Wayar da take ta kira ya barta a ɗakin HAYDAR ɗayar ce a cikin aljihunshi.
Kai kawo ta fara yi a cikin ɗakin saboda a yadda suka fita kuma suka ƙi ɗaga waya ta san tabbas akwai abinda ke faruwa.
Jiddarh ce ta shigo cikin ɗakin ita ma a ruɗe ta ce " mamy kin ji yadda su yaya suka fita anya lafiya kuwa?"
Mamy da ke ta kai kawo ta ce " nima abinda nake ta tunani kenan."
" Ga abinda ya faru ɗazu nasan halin ALIYU da baƙar zuciya da kafiya kamar kafuran farko."
Jiddarh da ta yi tsaye itama ta ce " kuma wallahi mamy har ɗazu da naje ɗakin su ranshi a ɓace yake don ko kallo na ma bai yi ba."
Hankalin mamy ya ƙara tashi da taji abinda Jiddarh ta faɗa ta ƙara ɗaukar waya tana ƙara kiran su.
Amma still dai basu ɗauka ba.
Addu'a mamy ta yi akan Allah ya tsare su ya kuma kare su a duk inda suke.
Jiddarh ta ce " Ameen."
Zannur da ya fita daga gidan bai tsaya ko ina ba sai nearest hospital dake kusa da su.
Yana zuwa aka karɓi HAYDAR aka wuce da shi A&E.
Manyan likitoci ne suka rufa a kanshi suna bashi taimakon gaggawa, amma duk da haka gangar jikinshi ta ƙi yin aiki zuciyar shi ce kaɗai ke aiki.
Sun ɓata awanni suna aiki a kanshi amma jikin shi kwata kwata baya responding da treatment ɗin da suke bashi.
Ana ta abu ɗaya har ƙarfe ɗaya na dare.
Ƙarfe daya da minti ashirin likitocin suka fara fitowa daga emergency, Zannur da ke ta kai kawo a ƙofar shiga emergency ɗin ya miƙe tsaye yana tambayar su yanda ake ciki.
Cewa ya yi ya biyo shi office ɗin shi.
Bayan sun zauna ya fara mashi bayani " mun yi iya ƙoƙarin da za muyi amma zuciyarshi ce kaɗai ke fafutukar rayuwa amma jikin shi kwata kwata baya karɓar treatment ɗin da muke bashi."
" Sannan ita ma zuciyar ta shi akwai matsala a tattare da ita."
" Zamu bari mu gani daga gobe zuwa jibi idan bai farka ba gaskiya akwai possibility ɗin zai iya faɗawa coma."
Faɗuwa ya ji gabanshi ya yi, da ƙyar ya iya buɗe baki ya ce " amma doctor babu wani abu da za'a iya yi masa?"
Girgiza kai doctor ɗin ya yi ya ce " duk wani abu da ya kamata a ce mun yi masa mun yi amma gaba ɗaya baya ƙarɓar treatment ɗin."
" Yanzu abinda za muyi shine mu jira na ɗan lokaci mu gani."
Jinjina kai kawai Zannur ya yi ya ce " thank you."
Sannan ya fito daga office ɗin, sai a lokacin ya tuna babu wanda ya faɗawa halin da ake ciki, kuma yana da tabbacin a yadda ya fita daga gidan mamy na can hankalinta ya ƙi kwanciya tana ta zullumi.
Aljihunshi ya shafa sai ya ji waya ɗaya ce a jikin shi.
Zarota ya yi ya ga ita ma ɗin a flight mode take, cirewa ya yi ya fara dailling number mamy.
Ringing ɗin farko ta ɗaga,ta ce " Usman kuna lafiya?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " mamy dama HAYDAR ba shi da lafiya."
" Ɗazu ma da na fita daga gidan a birkice shine ya suma,kuma har yanzu bai farfaɗo ba."
" doctors ɗin sun yi iya ƙoƙarin su amma har yanzu bai dawo cikin hayyacinsa ba."
Mamy da ke ta sauraron sa ta ce " a wani asibiti kuke gani nan zuwa."
Kallon agogo Zannur ya yi ya ga ƙarfe ɗaya da rabi sai ya girgiza kanshi ya ce " ki bari ko zuwa gobe da asuba mamy yanzu dare ya yi."
Lokaci ita ma ta kalla kuma tasan yana can sai kawai ta ce " shikenan, Allah ya kaimu goben."
Ya ce " ameen." Suka yi sallama.
Bayan Sooraj ya gama aikin da yake yi ya ce ma Layla bari ya fita ya siyo masu abinci.
Wayarshi ya ɗauka ya fita.
Bayan ya siyo abincin ya tsaya a gefen hanya ya kira number ummah.
Bayan ta ɗaga suka gaisa ummah ta ce " amma ka san lokaci kaɗan na ba ka gashi har an ci kwana huɗu a ciki, ba ka ƙara cewa komai ba a kan maganar da muka yi."
" Na faɗa maka gaba ɗaya auren nan bana son ya wuce sati uku zuwa huɗu."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " ki yi haƙuri ba wai na manta bane,kawai ina buƙatar a ƙara bani time ne."
Tsaki ta yi ta ce " babu lokacin da zan ƙara maka, kuma yanzu na kira ka ne na faɗa maka na yi ma iyayenka magana akan zasu je wurin iyayen Shaheedarh a nema maka aurenta."
" Zaka tura man kuɗin da za'a haɗa mata lefe, ita kuma matarka idan kuɗi zaka bata ko kuma ita ma akwatina zaka haɗa mata ni ba ruwa wannan tsakaninku ne."
" Ni gobe zan koma gida, ina me umartarka ka rinƙa zuwa gidan Saleemarh kuna hira da Shaheedarh saboda ku ƙara samun shaƙuwa a tsakaninku."
Babu yadda ya iya haka ya amsa mata da toh.
Mamy na idar da sallar asuba ta ɗauki makullin mota ta fito ta shiga ɗakin Jiddarh ta tarar ta idar da sallah tana azkhar.
Gaishe da ita Jiddarh ta yi ta amsa sannan ta ce " da safe ki haɗa breakfast sai ki saka driver ya kawo ki asibitin."
" Toh." Jiddarh ta ce sannan mamy ta fita daga ɗakinta ta shiga wanda Safiyyah ke ciki.
Tana shiga ta sameta itama a kan sallaya tana addu'a.
Tana ganin shigowar mamy ta sunkuyar da kanta ta ce " ina kwana mamy."
" Lafiya ƙalau." Mamy ta bata amsa.
" Dama shigowa na yi na ga ko kin tashi sallah, tunda kin tashi ma shikenan ni zan fita ALIYU ne bashi da lafiya yana asibiti."
Ƙara sunkuyar da kanta ta yi saboda tana da tabbacin saboda ita ya kwanta ciwo.
" A dawo lafiya, Allah ya bashi lafiya." Safiyyah ta faɗa cikin wata karyayyiyar murya.
Ta ce " ameen."
Gari da duhu ta ƙarasa asibitin, wayar Zannur ta kira yazo ya tafi da ita.
Bayan ta zauna ya gaishe da ita ta amsa,sannan ta tambaye shi ya jikin HAYDAR.
Ya ce mata har yanzu dai bai farka ba.
Kallon shi ta yi, shi kuma ya sauke kanshi ƙasa.
Shiru suka yi na ɗan wani lokaci sai Zannur ya ce " mamy ashe an saka ranar bikin Jay?" Ya faɗa da sigar tambaya.
Jinjina kai mamy ta yi ta ce " jiya aka saka bikin ai."
" Allah ya sanya alkhairi." Ya faɗa sannan ya ƙara cewa " mamy waye zata aura?"
Kallonshi ta yi sai kuma ta faɗa mashi wanda zata aura.
Murmushi ya yi ya ce " ai na ma sanshi."
" Akwai wani lokaci da ya bawa HAYDAR wani contract na ginin gida, ni na yi handling komai da aka yi."
" Muna gaisawa wani lokacin."
Jinjina kai mamy ta yi ta ce " hakan na da kyai ai."