BABI NA SHA BIYAR
by @maidambu41
KARFE DUKKA KARFE NE...!!!
{Zanen ƙaddarar Falilah}
BABI NA SHA BIYAR
🌸 Assalamu Alaikum Yan'uwa Mata.
Kowace mace tana son ta ga kitchen ɗinta cikin tsari da kyau, tare da kayan zamani masu inganci. Amma abin da kan hana mutane shi ne tara kuɗin saye lokaci guda.
Shin tara kuɗin saye ne ke miki wahala?
Ko kuma idan kin tara sai wasu buƙatu su sa ki kashe su?
Ki kwantar da hankalinki, domin MA KITCHEN ta zo da mafita.
Mun buɗe Adashen Kayan Kitchen domin ki mallaki kayan da kike buri cikin sauƙi, ba tare da wahalar tara kuɗi lokaci guda ba.
✨ Abubuwan da za ki samu:
✅ Kayan kitchen na zamani masu inganci.
✅ Farashi mai sauƙi.
✅ Adashe mai sauƙi da kwanciyar hankali.
✅ Ana kai kaya zuwa duk inda kike.
✅ Biyan kuɗi a hankali cikin sauƙi.
Za a fara nan ba da jimawa ba, In shaa Allah.
📞 WhatsApp/Call: ***
📲 Shiga WhatsApp Group ɗinmu domin samun cikakken bayani da fara rajista:
***
🌹 Arha ta fi bashi, adashe kuma ta fi bashi kwanciyar hankali. Ki yi rajista tun da wuri, ki mallaki kitchen ɗin mafarkinki cikin sauƙi.
MA KITCHEN – Muna tare da ke har ki cika kitchen ɗinki da kayan da kike buri. 💚
Page din na Group din MIJIN Mariah ne da fıtıklar Hikayar Mai_Dambu
“Ya Nafi’u ka je gida ka huta ai muna nan da ita.” Kallon Aunty Sadiya yayi na wani lokaci, kafin ya ce mata. “Baku bukatar kome?” Girgiza kai tayi tana kallon Hajja Mama da take gyarawa Falilah kwancinya. “Hajja!” “Ai shi ba Yaro bane, idan har zai iya rike yar shekaru talatin da wani Abu har yau ai ba sai na gaya mishi abinda ya dacewa kanshi ba” shafa kai yayi yana murmushi. “Shi Kenan Hajja sai da safenku Allah ya bata lafiya.” Ya juya tare da barın dakin, bin sa da Ido Hajja Mama tayı tana fadin. “Zurfin cikinka ya ishe ka.” Darıya Aunty Sadiya tayı tana fadin. “Hajja Mama ai bai yarda da kanshi bane gani yake kamar tafi karfinsa ne fa!”
“Gidanku nace, a ina kika ji mace ta fi karfin namiji? Shi dai halinsa ne boye abu a ransa.” Murmushi suka yi baki daya, tun kafin ya isa gıda ya kira Jamal ya gaya musu ta sauka lafiya an samu Ahmad da Aisha, suka yi ta godiya.
****
Lokacin da na farka, dakin ya cika da yan uwana. Anan nake jin labarin Hajiyarsu Ahmadi tana hanya, goge min jiki aka yi na sauya kaya, sannan naci abinci kadan, ina kallon yaran da aka miko min su na basu Nono, sai nayi ta Jin wani abu a raina ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, kuka nake sosai ina Jin wani irin kewar Ahmadi yana kara çıka kin raina, da taimakon Nurse Ruth na bawa Yaran nono bayan sun gama nima kamar zasu kwace.
Wurin karfe hudu dakin ya kara cika, a bakin Aunty Sadiyah take gaya min Ya Nafi’u’ ya koma Lagos, sai da idanuna ya cika da kwalla. “Shine ya tafi bamu yi sallama ba?” Na tambayi Hajja Mama, share ni tayı Aunty Sadiya ta ce min. “Daddynki ya tafi wani aiki ne, ko ya dawo
Ya tare anan ne?” Juya idanuna nayi ina me jin ba dadi a tafiyarshi. A hiran Hajja Mama na tsinci wasu maganar da na kasa gane su, ya zauna har sai da aka min aiki ya tafi.
Lagos
Ya isa bayan laasar, Kasancewar go slow da aka samu a Lagos bai isa gidan da wuri ba, koda ya isa abinci ya ci ya don tun a airport yayi sallah, Shigowa Maman Hanifa tayı tana taimaka mishi da kayan da zai saka, “Ya lilyn take?” “Alhamdulillahi a same Ahmad da Fatimah.” “Masha Allah! Allah ya raya ita kuma ya bata lafiyar shayarwa, “Amin Ya Allah!” Ya furta yana kallon yadda take kome jikinta a mace, “Me ya faru?” Kallonshi tayı tana murmushin yake.
“Me ya faru?” Ya kuma tambayarta, “kawai na san yanzu hankalinka zai koma kan Kanwarka ne.” Rike hannunta yayi suka zauna ya ce mata. “Me yasa kike kawo mana haka ne?”
“Muhammad kana son Falilah na sani kaima kasan na sani me yasa sai mun bawa kan mu wahala ne? Gara min Falilah sau dubu akan ka dauko min wata, at least ita zata zauna da ni a matsayin da take kallona, ka auri Falilah hankalina zai kwanta ma gaji da ganinka kana fama da haka.” Rike hannunta yayi ya ce mata. “Ya isa haka Falilah kanwata ce kuma yar da na rike, ba zata yarda ta zauna da ni ba ki barshi mu tafi a haka a matsayina na wanda take kira Uba.”
Rike hannunshi tayi yayi tare da cewa, “idan har ke ki yarda da ni, duniya ba zata yarda ni nake kashe mata aure don na same ta ba, kawai kaddarata ce haka amma ni ban taba kashe mata aure ba, idan na Auri Falilah girma da zumuncin da yake lullube duniya zata bude abar kome a inda yake Allah ya bata lafiya.”
Tasan yadda yake kuntata amma yadda ya ce ya barshi sai ya zabi shiru, amma tana fita a dakin da Hanny suka yi waya. Yarinyar ta bawa uwarta goyan bayan tayı dük abinda ya dace, idan har suka bashi damar zama da Falilah for the eternity haka zai kara mata mutuncin da daraja a cikin gidan Ya Man. Haka kuwa suka tsayar da maganar tare da Fatan Allah ya basu saa.
***
Falilah
Yadda nake samun kulawa dağa dangina har da Ahmadi abin sai da ya bani tsoro, Ahmadi ya bude min nasara ya tafi ya barni. hajiyarshi tazo ranar da muka çıka sati biyu a gadon asibiti. Ai kuwa ta tsaya a kaina sai da nace mata. “Hajiya ki je gida ki huta kema baki da lafiya ai”
Murmushi tana shafa kan Ahmadi wnada suka bükaci a boye suna shi nace aa bar mishi Ahmadinsa. Domin nima ina son Ahmadin ina jin dadin kiran sunan, Macen kuma aka barta da Batul, haka muka kwashe sati a asibitin sannan aka sallame ni, amma ina ganin rawan kai a wurin Doctor Muawiya, amma naki bashi wani fuskar ba zan iya da damuwa ba,
Sai da na cika sati biyu aka yi walima tun aka jibi walimar Maman Hanny tazo ana gobe kuma Hanny tazo gidan ya cika sosai. Saboda wannan shine farkon da zaa yi hidima na a cikin gidanmu, ana gobe walimar aka tattaro hakkina da ma Yarana yan uwan Ahmad Lamido suka kawo min, a ranar nayi kuka domin muna dawowa hajiya ta koma yola, ranar naji kamar kome ya tafi min har abada, Ahmadina yafi ya barni da katon rami a zuciyata!
Ranar kuwa an gayyato Babban Malam da tazo tayı mana nasiha da tarbiya a muslunci, a lokacin da ake Maganar tarbiyya sai nake ganin kamar ban da wannan kwarin gwiwar da zan kalli kaina as Mother, haka aka tashi Umaima kanwar Ahmad da Jaliyah sai matan Jamal da Babangida, a wurin walimar suka hadu da Abidah sai kunya tayi ta kamata.
Sai da muka nutsu suke gaya min ai ga Abunda ya faru zuwansa Umara, suka hadu da Abidah shine take basu labarina, a gaban Hajiya da Mariah dalilin da yasa na kasa samun zaman lafiya kenan da Uwar mijina da kishiyata, Matar dan uwana çıkı daya ban san me na tare mata ba wallahi, amma ba kome ma yafe mata, a yanzu haka kamar mujiyq take balle kuma wani Abu ya faru,
Hamidah da take gefena tana shirya kaya, Hanif ya shigo ya ce mata,”Didih ki zo inji Ya Man!” Darıya tayı tana fadin, “To na rantse bazan baka kwandalata ba ai ni Daddy ya bawa kudin ba kai ba, ba Ya Man ba ko malunmalun ne ba zan baka ko sisi ba tunda ka zama ashana ana baka kudi zaka ne kana bajinta a wurin Yara me kasayawa Babyns din Mammy?”
Turo baki yayı ya ce min “Mommy ni babba ne da zan iya saya musu abu na kawo? Mammy kice ta bani idan na sayi abu zan basu wallahi su ci ai dük namu ne?” Aunty Zahra da ta shigo ta ce mishi. “Hanif waye ya gaya maka ana bawa jarirai
Abu?”
“Mammyn kaduna to ki ce ta bani kudina mana, shi Kenan sai ta rike ta hana ni?” Janyo jakata nayi na zaro mishi Dari Dari guda biyar na bashi, ya kalli kudin ya ce min. “Gaskiya ba zan karba kudina hamsin hamsin ne shi zata bani.” Kafin
Nayi magana ta zo ta dangware goshinsa ta bashi kudin. “Allah ya isa min muguwa, kawai ba zan yafe miki ba, meye iskanci kawai.” Ya fita da gudu, wani irin nauyi naji ya tsaya min, kallonta nayi na ga jikinta yana rawa Allah yasa dağa ni sai Aunty Zahra na ce mata. “Har yanzu kina kan rashin jin ne?” Hawaye ne ya zubo mata ta ce min. “Wallahi ban yi kome ba, na rantse da Allah Mammy bana kome!” Hamidah Yarinyar ce karama, da bana son zunubina su shafe ta……….