6
Har dai su ka tafi bai sake sa ta a ido ba.
Da dare zai kwanta ya din ga sake sake yarinyar da ya ganin ce ko ba ita ba idan itace hakan na nufin ya kamu da son yar aikin gidan kawun sa that can’t be possible kamar shi yayi soyaya da yar aiki.
Haka dai ya cigaba da sake sake har yayi bacci. Washe gari ya shiga harkokin sa duk da kasan zuciyar sa halimatu na nan sai dai yana kokarin hana zuciyar sa abinda ta ke so.
Amma ita zuciya ba Ruwan ta da kyau ko kuma wayewa, arziki ko talauci. Tin da ya koma gida ya kasa samun nitsuwa da ya tuno da ita yake jin fisga a jinkin sa. Duk son sa da barin tunanin ta ya kasa har dai ya yanken hukunci yi mata Magana.
Ya zo gidan kawu mala a kan ya zo wurin su Mohsin sai dai hankalin sa na kan halimatu ina zai ganta.
Har dai yagama gaisawa da mutanen gidan bai ganta ba sai da ya fito ya tambayi masu gadin gidan suka ce mashi ay aikin jeka ka dawo ta ke yi.
Washe gari ya dawo gidan tin da safe sai dai bakin sa kofar gidan ko fitowa daga mota bai yi ba yana jiran zuwan ta.
Ta na nufowa gidan da sauri ya fito daga motar ya sha gaban ta wanda hakan ya firgita ta.
Kanta ta sunkuya ta rintsuna ta gaishe shi. Dan ita ba ta gane shi ba bata san shi ne wanda ya tsaida ta ba.
Ya amsa tare da ce mata ta biyo shi mota ta amshi sako. Bata musaba ta bi shi a baya.
Ya na isa motar ya tsaya tare da rungumai hannun sa bisa kirjin sa. Ya jingina da motar ya zuba mata ido.
Abinda ya fara birge sa kunyar ta da tin da ta karaso kan ta a saddai ya ke. Jin bai ce komi ba ta ce "Yallabai ina sakon yake?
Asim ya dawo cikin hankalin sa ya tambaye ta sunan ta.
Ta amsa shi batare da ta dago ta kalle shi ba.
Ya ce "Nice name HALIMATUS SADIYAH, Kina da waya?
Ta girgiza mashi kai.
Ya ce "Ikon Allah as big you are, okay ban address din gidan ku."
Da mamaki ta tambaya "Miyasa ka ke son ganin gidan mu?
Ya ce "Ina so in taimaka ma ku."
Tayi murmishi ta ce "Mun godai kwarai."
Ya ce "Fadi ina jin ki."
Ta ce "Muna nan a sharada phase 1 unguwan dan wasai.
Ya ce "Toh gidan wa zance?
Ta ce "Gidan malan Yakubu."
Ya ce "Thank you."
Ya budai mota ita kuma ta juya ta nufi hanyar gate. Ya wuce. Jin sa ya ke cikin farin ciki mara misultuwa domin tin da ya ke bai taba soyyayba, wani irn yanayi mai dadi da bai mitultuwa kuma ya rasa gane dalilin haka.
Bayan kwana biyu da dare bayan sallah isha ya je gidan su da dare.
Yayi parkin motar a layin gidan sannan ya fito ya tambayi wani karamin matashi gidan alhaji Yakubu ya mashi kwatance ya mashi godiya sannan ya karasa ciki a kafa dan mota ba ta shiga ciki.
Ya zo kofar gidan ya aika wani yaro da ya shiga ya ce a na sallama da Halimatu.
Yaro ya shiga cikin gidan.Ya fadi sakon sa. Halimatu da ke zaune bisa tabarma ita da su aseey kowa na lissafa cinikin sa na yau.
Ta ce wa yaron ya je ya tambayi waye ke salma da ita. yaron ya fita ya isar da sakon.
Yayi murmishi ya ce "Ka ce wani bawan Allah ne dan Allah kar ta ki fitowa."
Yaron ya koma ya shiga ciki ya isar da sakon ta ce "Ka ce ma shi bai da niyar ganin ta tinda ba zai fadi kowaye ba."
Mahafiyar ta ta ce "A'a yaro je ka ce ga ta nan."
Yaron ya koma ya isar da sakon Asim ya bashi tukuici ya godai masa ya wuce abin sa.
A ciki kubra tace "Halimatu nace ma ki ki dai na haka wata rana sai kin kori mijin da zaki aura ke shi ke nan ba za a zo gidan ku neman ki ba."
Ta ce "Umma mazan ne yan banza ne yan iska ne shiyasa na ke jin tsoran su na fi so ko ma waye ya tarbi baba kafin ni."
Ta ce "Eh haka ne amma yanzu ki tashi ki fita."
Ta nuke bata son fita kubra ta kara da;
Maza tashi ki je. Halimatu ta mike tare da jan hijab din ta saman igiya ta sa ta fito waje.
Kasan cewa unguwar ba wuta wurin da duhu sai hasken farin wata.
Ta na fito wa ta ce "Wa yeke nai ma na."
Asim ya mata salama sannan ya amsa ni ne Asim.
Hankalinta bai kawonmata Asim Inuwa ne ta ce "Ban gane ba wani Asim?
Ya ce "Kin gane bana, okay Asim na gidan uncle Inuwa."
Zaro ido tayi da mamakin ganin sa ta ce "Yallabai Asim mi ya kawo ka gidan mu?
Ya ce "Taimako na zo nema."
Bata fahimci mi ya ce ba ta ce "Ban gane ba wani taimako za mu ma ay sai dai kai ka taiamake mu."
Ya yi karamin murmishi ya ce "Halimatu..."
Ya furzar da lumfashi kafin ya cigaba. "Zaki iya tina wanda ya tsaida ki wata biyar da suka wuce yana neman gidan ku ki ka ce mashi ya naima?
Ta shiga tunani sai dai ita ta manta ta ce "Gaskiya na manta."
Ya ce "A layin gidan kawu maala. Har ya sha gaban ki?
Wani dum zuciyarta tayi ta na fari da ido. Ta ce "Yallabai Asim kai ne ka tsayar da ni??
Ya ce "Kwarai ma kuwa shiyasa na yi tattaki na zo nan domin neman taimako wurin ki na san kin san wani taimako na zo nema amma bari na fayya ce maki.
Halimatu tin ranar da na sa ki a ido na na ji kin kwanta min kuma ina son ki, dan Allah kar ki ki amincewa da tayin soyayya ta.
Tayi shiru ta na nazarin maganr sa, Asim ne ke cewa yana son ta ko kuma mafalki ta ke.
Jin tayi shiru ya ce "Halimatu ba ki ce komi ba?
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ni bani ke da iko da kai na ba ka tambayi mahaifi na."
Ta na fadin haka ta juya zata koma da sauri ya ce "But zuciyar ki ce."
Ta dagata ta ce "Eh zuciya ta ce amma zabi da hukuncin mahaifina ta ke bi."
Ta wuce ciki ta bar shi a tsaye yana jinjina maganarta tabbass ta samu tarbiya mai kyau. Hakan ya kara sa mashi son ta musanman yanda ta ke da kamin kai, kuma tabbass ya samu uwa tagari ga yayan sa.
Bai bar unguwar ba har sai da ya samu malan Yakubu ya nemi izin wurin sa ya yarje mai, ya so ya koma wurin ta ganin dare yayi ya koma gida.
Malan Yakubu da ya dawo gida har sun yi shinfida a waje sun yi Shirin baaci ya ambaci sunnan ta.
Ta na cikin net din sauro kwance a katifa ta amsa shi.
Ya ce "Ashe dazu bako ki kayi."
Haliamatu tayi shiru ba tare da ta ce mashi uh fan ba
Kubra ta ce "Na manta ma in ce ma ka dazu wani ya aiko a na kiran ta sai dai kasan halin ta da korar samari."
Halimatu ta ce "Umma ba fah korar su fa nake yi ba nace maki samarin yanzu sai mutun yana takatsantsan."
Malan Yakubu ya ce "Gaskiya ne Halima shi dai wannan yaron ya zo ya samai ni yace yana son ki kuma yana son ki da aure kuma na amince mashi.
Cike da rudani ta kalli baban ta ta kalli umma sannan ta mai da kallon ta ga mahaifin ta ta ce "Baba ka ba dani, baba ka san wa ye shi, Baba ni ba tsarar shi ba ce, baba ina ni ina shi."
Kubra ta ce "Ku dagata ku fayyace min kun sa ni a duhu.
Malan yakubu yace "Yaron da ya zo dazu ba kowa bane face d'a ga yayan Alhaji mala inda ta ke aiki.'
Kubra ta budai baki kafin ta ce "Dan uwan alhaji mala ka ce??
Malan gaskiyar ta ne ina mu ina masu kudi wanda ahalin su suna daya daga cikin manya-manya kano."
Malan yakubu ya ce "Shi ya zo ya ce ya na son ta ay ba wani abu ba ne daman nace mashi ya zo su sasanta in ya miki sai ayi aure amma ki fara duba fallar auren sa."
A bangaren Asim tin da baban halimatu ya yarje mai zuciyar sa take cike da farin ciki, yana jin daddadan yanayi wanda bai taba jin sa tamkar wanda aka yi wa albishir da gidan aljannah.
Da ya koma gida, kafin ya wuce part din su na samari, ya na zuwa wurin umma su yi sallama. A yau da ya shiga ita kanta ta san dan ta na farinciki ta tambaye shi miyafaru fuskar sa dauke da annasuhuwa.
Murmishi yayi tare da tunano maganr malan Yakubu ya zauna yace "Umma ki taya ni da addu’a Allah ya bani nasara."
Umma ta tambaye shi nasara a mi?
Nan ma murmishi yayi 32 out kafin yace "Umma in ta samu za ki ji, dan Allah Umma ki tayani da addu'a
Umma ta ce "To Allah biya ma bukatunka kuma addu'a kullun cikin yi maku a ke, ina dan uwan naka?
Ya mike tare da cewa ban san in da ya shige ba.
Umma ta ce "Kila ya je zance gwara kai ma ka fito da ta ka a hada a ma ku aure lokaci daya.
Murmishi yayi ya fita dan shi bai ki a yanzu ma a daura mashi aure da halimatu sai dai ya san he has to face some chanllages musanman wurin mahaifin sa bai san yanda zai tare shi da yana san auren halimatu mai aikin gidan kannen sa.
Part din su ya wuce, wanda ke gefen farkon gidan, a ciki akwai daki biyu sai parlour. Daki daya na samarin uwar gida sai dayan dakin na su Asim wato ya’yan amaryar alhaji inuwa, su hudu a daki Asim da Asif, sai buba, sai kuma hamza, a dayan dakin kuma akwai Abdullahi, ahmad, Ayan, sauran mazan ta biyu sun yi aure hashim, da yazeed.
Ahmad, hamza da abokan su biyu ya iske suna biga PS a parlourn. Ya karaso suka yi musabaha da abokan biyu sannan ya wuce dakin su, yayi taking shower, change to pyjamas, then bounced on soft bedress. Ya lumshe idanunshi yana murmishin da bai ma san yana yin sa ba dan ya bace a tunanin halimatu.
Ba jimawa Asif da bubu suka shigo dakin. Asim bai ma san da shigowar su ba dan guguwar soyayya ta dibe sa.
Buba daga gadon sa ya hango smilling din Asim ya tabo Asif ya mashi nuni da ya kalli Asim.
Asif ya kalli Asim da ke gefen sa kwance saman cikin sa kan sa bisa pillow yana murmishi.
Buba ya mashi nuni a kan mi ya samai shi. Asif ya mashi nuni da hannun oho. Sannan ya ambaci sunan dan uwansa.
Asim bai ji sa ba har sai da Asif ya bubbugi bayan sa. Asim ya tashi zaune yana ce wa "ta ce Auren ta.."sai kuma ya dawo hayyacin sa ya dafe goshin sa.
Daga buba har Asif suka kalli juna sannan Asif ya dubi dan uwansa da ya dafe goshin sa, za ayi ya cewa yana jin kunyar maganar da yayi ba tare da ya kula ba.
Cikin wasa Asif ya ce "Ya dai asim ta sa mu ne have you fall in love??
Ya dago kai zai bashi amsa Hamza ya shigo, ya ce, don’t disturbed me i' m fatigued I want to sleep.
Zai kwanta Asif ya reko shi yana cewa "Kai ka fada mana who is the luckies to have you as a husband, ohh Allah Asim da soyayya.
Suka fashe da dariya Asim ya janye hannunsa da ga wurin Asif rai bace ya ce da alla kar ku damai ni. Ya ja tsaki ya kwanta.
Buba ya tabe baki tare da cewa kwatata ba a gane mashi ya ce bai soyayya shi ba dan wahala ba ne yanzu kuma mafalki yayi ko daydreaming??
Asif ya ce "Kyale shi in tayi tsami za mu ji shi da kan sa zai fadi mana.
Hamza da shi ma yayi Shirin bacci ya karaso wurin gadon su shi da buba yace toh mu ma bari mu kira sahiba kafin mu kama gobe.
Asif da buba suka yi dariya Asif ya ce "Ji min yaro what do you know about love."
Buba ya ce "Bari kawai bai gama gina rayuwar sa ba amma har ya fara soyayya."
Hamza ya ce " It is better to start early."
Asif ya ce "Hey ka bari ayi wuf da mu kafin ka, kai da go university ba ka fara ba."
Hamza ya ce "Aure nufi ne na Allah kila ma dukan ku in riga ku yin sa.
Buba ya yi tsaki ka fin ya ce "Haba malan ya da irin wannan addua’r, kai yaro ba abin da ka sa ni."
Hamza ya ce "Gaskiyar ke nan shi ba a sa mashi lokaci sai dai in lokacin yayi za ka ga an yi.
Asif ya ce "Whatever fatan mu mataye na gari."
Suka amsa mashi da amin. Buba ya mike ya koma parlour asif kuma ya shiga yayi wanka ya shirya ya kwanta a gefen dan uwansa dake hararo rayuwarsa ta nan gaba da halimatu.
Wa shegari da safe bayan kowa ya tafi hidimar gaban sa. Asif ya shigo dakin ya iske Asim na shiryawa ya karaso ciki ya zauna saman gado ya ce "Asim wai lafiya tsakanin jiya da yau sai farin ciki ka ke ka fadi min nima in taya ka."
Asim na combing kan sa a gaban mirrow ba tare da ya joyo ya kalle shi ba ya ce "Aure zan yi."
Dariya ta kubcewa Asif duk da daurewar da Asim yayi sai da Asif yai dariya kafin ya tambaya "Wa ce ce mai sa’ar nan da har zata sa dan'uwana sunbatu da dare?
Asim ya zauna a gefen gadon sun buba suna facing juna da Asif sai dai kan shi a saddai ya ce "Asif ban san miyasa yarinyar nan ke kokarin zautar da ni, every minute every second i'm thinking of her, na kasa concentrating a kan komi. Lokaci daya tana neman zauta ni.
Asif mamaki yake ba shi wai Asim ne da kalaman nan ya ce "Ikon Allah wace ce wannan yarinyar?