Halimatus’sadiya (sakayya)

8

by @102565813543784586917

____Da dare ya koma gidan su halimatu su kayi fira minti 15, cikin minti 15 kowannan su ya fadi biography da ga nan kuma ta mashi sallama dan in har ta na tare da shi tamkar ana ingiza ta, ga kwarjinin da yake mata shiyasa ba ma ta son ta dadai.


Ta na komawa ciki wurin randa ta wuce ta zuba ruwa a buta tayi alwalla sannan ta dawo wurin tabarmar da kubura suke ta kabbara sallah.


Bayan ta sallamai autan su mai shekara 9 huzaifah, ya ce "Halima kalla wannan mutumin yaba ni." Ya ida maganar yana nuna mata 500.


Ta dubai shi ta dubi umman su dake jan charbi ta ce "Umma ya bashi 500 ya amsa kuma ki ka yi shiru."


Yayarta, iya ga mariganya matar MalanYakubu, nusaiba ta ce "Halima 500 kadai ce. "


Halima ta ce "Duk da haka, kai huzaifah daga yau in ya kara ba ka kudi kar ka amsa har ma da ku."


Umma dai jan charbi ta ke ba ta ce masu komi ba.


Saifullahi shima d'a ga malan Yakubu, matashi da shi ya shigo tare da yin sallama. Suka amsa. Ya jawo kujera ya zauna. Huzaifah ya nuna mashi kudin da Asim ya bashi. Saifullahi ya ce ka mashi godiya 


Huzaifah ya ce "Eh na mashi."


Halimatu ta ce "Ka aje ta duk ranar da ya dawo ka maida mai ita."


Fara'ar dake fuskar huzaifah ta washe. Saifullahi ya ce "A'a halima ay ba a haka ba a maida hannun kyauta."


Halima ta ce "Saifullahi ba kasan halin masu kudin nan ba gwara muyi kaffa dasu, baka damu da abin hannu su ba sun wulakanta ka ina ga ka nuna kana so."


Umma da ke cire hijabin jikin ta ta ce "Toh shi yaro ina Ruwan shi, kyauta ce ya ma shi. Sannan shi yaron nan yanda mahaifin ku ke ce min bai da matsal kamili ne nitsatse. '


Saifullahi ya ce "Ko shi ne wanda jiya ya sami baba a shago?


Umma ta ce "Eh shi ne."

Saifullahi ya ce "Gaskiya yana da nistuwa."


Halima ta ce "Ku baku san halin yan gidan su ba ne, ni da na ke tare da su ni na san su, mahaifin sa kwtakwata baya son talakka bayan son ya ra bi tallaka balle ya hada zuri'a da talaka. 


Umma ta ce "Halima naiman aybanta shi ki ke yi."


Ta ce "Umma ba haka ba ne mi zai sa in aybanta shi."


Umma ta ce "Toh shi ke nan a kullun ina maku fatan mazaje na gari, yanda ya'unwan ku su ka yi aure suka zauna haka kuma za a aure ku, Allah zaba abin da ya fi al khairi kuma mazan Allah ya baku mataye na gari.


Saifullahi kadai ya amsa da Amin a bayyane halimatu da nusaiba a sirrance.


A bangren gidan Alhaji Inuwa, Asif na parlourn Umma da shi da kannen sa mata Aysha da Jannat sai yayar su Safna wadda da ga ita sai su Asif. 


Kallo suke amma Umma da Asif suna fira. Cikin firar ta su ta tambaye shi "Mi ke damun dan uwanka dan na san ba zai boye ma ba?


Murmishi yayi ya tuna maganar su ta dazu ya ce "Umma ni na isa ay in yana cikin wata damuwa ki ce first."


Umma ta ce "Zaku hadai min kai yanda ku ka sa ba to ku kuka sani."


Safna dake amfani da wayar ta ta dago kanta ta ce "Umma in da sabo ya ci a ce kin saba da hade kan su da suke yi."


Asif ya ce "Au ke ma zaki goyi bayan umma."


Safna ta ce "Of course."


Asim da buba suka yi sallama suka shigo.


Asif ya ce "Yauwa Asim gawar da ka zo Umma da safna sun ti sani gaba wai muna hadai kai."


Suka amsa sallamar. Asim kuma yayi murmishin sa wanda fuskarsa ba ta rabuwa da kyakyawan murmishin sa mai kara masa kyau. Ya zauna.


Buba kuma yace "Daman Asim da Asif ne sun saba hadai mana kai su nuna wariyal launin fata." Ya ida yanza zaune.


Safna ta ce "Thank you buba. Kadai ji Asif.


Asim ya ce "Mu wani hadai kan da muke yi ku ne dai ke mana haka."


Bubu ya ce "A dai yi shiru."


Umma ta ce "Aikuwa dan ko duka mutannen gidan nan za a tambaya amsar daya za su fada."


Kowannan su ya yi dariya. Haka suka cigaba da firar ta su har dare ya ja suka yi wa umman ta su sallama suka wuce part din su daman hamza kullun yana part din su suna PS in ya fito abinci ne da sallah dan wani lokacin daukar abincin ya ke ya koma part din su.


Washe gari, bayan ya tashi daga kasuwa ya dawo gida yayi wanka ya wuce gidan su halimatu. Cikin sa’a yau ma ya hadu da Huzaifah ya dawo daga masallaci shi da abokan sa. 


Asim dake tsaye wurin kofar gidan, Huzaifah ya nufo sa da gudu ya karaso. Ya rintsuna ya gaishe shi.


Asim ya amsa tare da ce mashi ya shiga ya kira yayar shi.


Huzaifah ya ce "Halima fada za ta min dan jiya ma sai da ta min wai dan na amsa kudinka."


Murmishi yayi ya ce, "Toh daga na baka kyauta sai fada."


Huzaifah ya ce "Ay saifullahi ne  ya ce kar na maida ma ba a maida kyauta ba za ka ji dadi ba."


Asim yace "Kwarai ma, da ka maido min da ba zan ji dadi ba."


Sallama a ka mashi ya mika hannun suka yi musabaha. Asim dai bai san waye ba.


Matashin mai suna Haidar, sa'an halimatu a shekaru, d'an mariganyiwa matar malan yakubu ya ce wa huzaifah ya wuce gida. 


Huzaifah ya ce wa Asim sai anjima na godai. Asim ya dan daga mai hannu.

Hadair ya ce gashi ban san ko kai waye ba ko zan iya sanin ka." He asked politely.


Asim yace "Sunana Asim Inuwa, na hadu da kanwar ka Halimatu, ta kwanta min kuma ina son ta, sanan mahaifin ku ya yarje min."


Haidar ya ce "Ohh kai ne saurayin na ta, ba shakka naji Baba suna Magana amma miyasa ka zabi kanwata a kaf matar kano? Bayan matsayin ku ba daya ba.?


Slight smile ya mashi kafin yace "Ka manta zuciya bata da k'ashi, ita zuciya ba Ruwan ta da waye kai ko kuma waye ni, abinda ta sani ta so mai ita sannan dukan mu ay musulmai ne.


Ya sauke kafudu kafin ya ce "Toh ka san ku masu kudi mu talakka nai dole mu yi takatsantsan ba za mu kai kan mu ba in da Allah bai kai mu ba. In har ta ce ba ta son ka sai dai kayi hakuri ka kama hanyar ka.


Asim yace "In sha Allah hakan ba zai faru ba."


Haidar bai bashi amsa ba zai wuce Asim ya ce "Dan Allah ka mata Magana ta fito." 


Ba tare da ya juyo ba ya ce "Toh" ya shige ciki.


Zaune ya gan ta bisa sallaya ta na wudri. Ya ce "Halima Asim ya ke da suna ki je yana jiran ki."


Halima ta dan bata rai tare da cewa "Ni fah bana so alakar mu tayi zurfi, bana son tashin hankali na tabbata iyayen sa basu san yana juwa nan ba musanmn mahaifin sa."


Haidar ya ce "Ki dai je in muga suna neman wulkanta mu sai ki rabu da shi dan kosuna da kudi ba za su samu damar wulakanta mu ba."


Umma ta mata nuni da ta tashi ta je. Ta mike ta sa takalmi ta fita. Ta na isa ta mashi sallama. Ya amsa. Ta gaishe shi ya amsa, shi kuma yatambayi su Umma.


Shiru na dan wani lokaci kafin ya ambaci sunan ta. Ta amsa shi ba tare da ta dago ta kalle shi ba. 


Ya ce "Kamar ki na jin shakkar yi min Magana dan Allah feel free ask what in your mind, kin ji."


Ta na kallon gefe sa dan ta ki bari su hada ido ta ce "Miyasa ni? Duk yawan matan kano, masu kudi, masu Mulki, masu sarauta, farare kyawawa. Miyasa sai ni yar talakka wanda bai da gata sai Allah, talakkar ma yar aiki a gidan kawun ka, Dan allah ka yi hakuri ba na so na rasa aiki na dan tabass in dan suka gano haka za su kore ni. Kayi hakuri ka rabu da ni ka nemi dai dai da ajin ka ba ni bah."


Ya sauke ajiyar zuci kafin ya ce "Halimatu, ko daya ban damu daga cikin abin da ki ka lissafa, ina son ki da Allah ina son ki da aure, ina son ki ki zama uwa ga ya'ya na domin na yaba da tarbiyar ki, nutsuwar ki, kamin kan ki da kuma kunya. Mi zai sa na so kyan fuska bayan zuciyar baka ce. Damar ki kawai na ke bukata, na maki alkwarin ba za ki rasa aikin ki ba sai ma dai ki dawo matsayi daya da su. Dan Allah ki amince za ki aure ni."


Shiru ta yi kafin ta tambaye shi "Ka san mine aure?


Ya ce "Eh to aure ibada ne, sai a primary mun san marriage is a union of husband and wife."


Ta ce "Naba ka aiki ka je ka san komi gamaida aure sai ka dawo."

Idanuwa ya dan zaro kafin ya ce "Ina zan san su.


Ta ce "Ko ina."

Ya ce "Toh zan je in naimo su a duk inda suke kamar yanda na nemo ki." Ya ida yana murmishi.


Ta ce "Na godai sai da safe." Zata wuce ya ce "Minti daya."


Ta dagata tare da juyowa.

Ya ce "Ina so na baki sako ko zaki iya biyo ni."


Ta dubai shi suna hada ido da shi tayi sauri ta janye idanunta.


Ya ce "Wlh ba cutar da ke zanyi ba" Ta ce "Ba sai ka rantse ba."


Ya mata godiya ya wuce ta bishi a baya. 

Yana tambayar ta sai dai ta amsa shi d uhmm hmm, mm, har su ka karaso wurin mota ya budai ya dauko leda ya rufe sannan ya mika ma ta. 


Ta mashi alamar tambaya yace "Waya ce dan zan yi tafiya gobe ko jibi I can't miss your melodious voice."


Ta ce "Kayi hakuri ba a bani izinin amsar abu daga hannun saurayi ba."


Daga haka ta juya ko da ya ambaci sunan ta ba ta tsaya ba ya koma mota ya wuce shagon malan Yakubu. 


Ya na isa ya fito daga motar shi ya rufe ya karasa shgon na shi da ke daya da ga cikin shagunan kan layin. Ya shiga ciki tare dayin sallama a hankali. Mutane dake shagon suka amsa har da malan Yakubu.


Malan Yakubu ya ce wa saifullhi ya cigaba da attending customers din. 

Ya fito daga shagon Asim ya bi shi a baya. Suka karasa wurin motar shi.


Asim ya mika mashi hannun suka yi musabaha daga nan ya rintsuna ya gaishe shi.


Malan Yakubu ya amsa tare da tambayar shi yan gidan su.


Asim ya amsa shi suna nan lfy.

Malan Yakubu ya ce Masha Allah. 


Asim ya mika mashi leda tare da ce wa "Abba daga wurin Halimatu nake ta ki amsa ta ce sai ka bata izini shi ne na ce bari in zo in kara tambayar izini."


Malan Yakubu ya amsa ledar yana murmishi cike da dadin ganin yanda iyayar ta shi ta ke bashi girmamawa. Ya ce"Tabbass ba sa amsan abin saurayi har sai an masu izinin haka amma kar ka damu zan mata mgn"


Asim ya rintsena ya na godai ma sa.

Malna Yakubu ya ce "Ba damuwa."


Asim ya sa hannun sa cikin aljihun wandon sa ya jaro kudi ya mika wa malan Yakubu.


Malan Yakubu ya dan bata rai tare da ce wa "A’a yaro zamu bata in dai kace haka zaka din ga min, daman jiya ka ba yaro karami 500 ina laifin 100 zuwa 200 in kyautar ce."


Asim yayi murmishi ya na ce wa "Baba kyauta ce."


Malan Yakubu ya ce "A’a ba a saban ta wa yaro da kudi, 500 ta mashi yawa duka na wa yake, in dai ka na so mu shedai toh ba Ruwan ka da ba mu kudi, naka kawai ku sasan ta in ta amince toh in bata amince ba sai dai mu ba ka hakuri dan ba zamu mata auren dole ba."


Asim yace "Toh baba in sha Allah za ma ta amince."


Malan Yakubu ya amsa da "Allah ya yarda."


Asim ya ce "Amin Baba ni zan wuce sai da safe." Ya ida yana mai rintsina mashi.


Malan Yakubu ya ce "Allah kai mu." Ya juya ya budai motar ya shiga ya rufe ya tada motar ya wuce ya bar Malan Yakubu yana yabawa da kyawun halin shi ya sabanta da yanda halima ke fadi mashi halin yan’gidan, yanda suke keymar talakka suke wulkan ta shi amma shi ya zo da kan shi yana neman alfarma wurin sa kuma yana bashi cikaken girmamawa. Tabbass ya kwanta mashi arai.