10
Daga wurin malan Yakubu gida ya wuce direct, yayi parkin motar sa shi kuma Asif yana rufe ta shi. Ya jira dan uwannan sa ya rufe ta sa motar sannan suka karasa ciki. a kan hanyar su Asif ya ce "Ka san Abba na neman mu."
Asim ya ce "No, fatan lfy?
Asif ya ce "Ban sa ni ba mu je mu ji mai zai ce da mu. Suka karasa suka yi sallama suka shigo parlourn.
Alhaji inuwa fara’a dauke a fuskar sa ya ce "Tagwaye na sun karaso."
Suka karaso suka rintsana suka gaishe shi.
Alhaji inuwa ya amsa tare da basu izinin su zauna. suka samu wuri suka zauna dan duka family din a ka hadu ban da matanyen da suka yi aure sai dai mazan, hashim da yazeed.
Alhaji Inuwa yayi gyaran murya yana mai gyara zaman sa na qasaita ya ce, Daman ku mu ke jira.
Ina so kowannan ku ya fadi min financial state of his capital zan fara da kai karamin su Hamza ina sauraran ka, ya ka ke tafiyar da kasuwan cin ka.
Hamza shi ne autan gidan, shi yanzu yagama secondry, Alhaji inuwa yana neman masa admission a Canada. Kafin ya tafi Alhaji Inuwa ya bashi jarin 50k. Ya fadi masa daga shi sai Ahmad har zuwa Baban su Yazeed.
Ba karamin dadi Alhaji inuwa yaji ganin yanda kasuwan cin yaran nan sa ke habaka musanmaman na Asim da kuma autan sa Hamza wanda yake jin dadin shi ne karamin su amma da dukkan alamu ya fisu iya tafiyar da harkar kasuwanci. Haka ma iyayen na su mata.
Daga nan ya ce "In Allah ya kaimu gobe za azo neman auran kanwar ku Sadiya."
Dukan wurin suka amsa da Masha Allah, Allah sa alkhairi.
Alhaji inuwa ya kalli tagwayen na sa sannan ya ce "Saura ku, har yanzu shiru ba wani motsi.
Murmishi Asim yayi kafin ya ce "Abba in lokacin yayi zamu yi."
Asif ya ce "Abba a dai kara bamu lokaci."
Alhaji inuwa ya ce "Ku dai ku ka sani tin da ba ajin cikin ku, Halimatu ko kin sa ni? wato umman su.
Ta ce "Ni na isa in sani su ka dai suke kidin su suna rawar su."
Alhaji Inuwa ya ce "Kun dai ji."
Jannant ta ce "Abba daman jiya muka gama Magana akan suna hadai kan su."
Alhaji inuwa ya ce "Ay ko wa ya sani."
Duka parlourn ya dauka da dariya. Sannan Abba yace "Ay ga dan uwan su chan shima da yake tagwayen ne yayi shiru bai ce ko mi ba, sai ka tsufa ba ka yi aure ba ga yar uwar ka ta kusan aje biyu.
Ayan shima tagwaye ne na Hajiya Shafa, sai dai su sun saba mace da namiji Ayan da Ayana.
Ayan yayi shiru dan wannan auren da a kayi wa yar'uwar shi da ya na da ikon raba shi da yara ba auren, haushin ta ma ya ke ji da ta tsaya har ta haihu da mashayin mijin na ta.
Alhaji Inuwa ya cigaba da cewa "In sha Allah za a sa bikin wata 7 kafin nan ina so da kai Abdullahi da Asim da Asif duk ku fito da matayen aure a hadai gaba ki daya shiyasa tin farko na tamabayi financial state din capital din ku dan in ji in za ku iya rike gida, bayan haka kowannan ku na aikin gwamnati ban da Asim dan haka ku hanzarta ku fito da matayen aure kafin nan da wata 2.
Asim a yanzu ya samu mata sai dai yana shakar tinkaren mahaifin sa da maganar Halimatu.
Alhaji Inuwa yace dare na yi sai kowa ya je ya kwanta.
Suka mike kowannen su yayi wa alhaji Inuwa sai da safe suka fita. Mazan suka yi part din su haka ma matan.
Suna shiga Ayan ya zauna ransa bace.
Asim ya zauna kusa da shi, Hamza ya wuce daki sauran kuma suka zauna a nan parlour.
Asim ya tambaye shi Ayan mike damun ka ba ka da walwala?
Ayan ya kara daure fuska tamkar Asim ne ya masa laifi. Asim yayi karamar dariya ya ce "Ayan Ka fada mana perherps we can help you."
Asif ya ce "Eh mana ba wai ka zauna ka na boye damuwar ka ba."
A hassale ya dago tare da cewa kun san damuwata, shike nan yaran nan ba su da wani right din kan su, dole sai mai kudi, shike nan dan kana da kudi sai ka ce ya’yan sai masu kudi ay wannan ba rayuwa ba ce, zalunci ne.
Asif ya sauke ajiyar zuciya dan lamarin Abban na su ba karamin damun su ya ke ba. In su maza ne za su iya jurewa za su iya mulkan gidan su matan fah??
Kwatakwata bai ta ba duba ingancin auren sai dai profit din da zai samu.
Asif ya ce "Ayan you should be used to this, ba sau daya ba sau biyu ba."
Buba ya ce "Kana nufin sadiya ma zai hada ta da wani??
Ayan ya ce "Eh mana baka gan shi ba a haife ma ya haife ta wannan wata irin rayuwa ce."
Buba ya ce "Gaskiya abin da Abba ya ke bai kyautawa yana shiga hakkin su sannan duk kudin da zaka yi Gadara da su rana daya Allah zai iya amshe ma su.
Ayan ya ce "Nawa aka yi.
Asif ya ce "Ba sai an je da nisa ba mijin maman Khalil(iya ta farko gaba ki daya a wurin Alhaji Inuwa Khadija) in kun tuna lokacin da aka yi bikin wani irin banar kudi ba ayi ba a bikin, ana ta taya ta murna amma yanzu milis ake ji ya riga da yagama cin tainuwar sa saukin ta da ilimin ta da kudin ta, ita ke kulawa da su."
Asim shiru yayi yana sauranran su dan hankalin sa rabi na wurin su rabi na wurin Halimatu.
Ayan da zuciyar sa ke tafarfasa da bakin cikin halin mahaifin su ya ce "Wlh da da hali da zan iya raba auren Ayana da isma’il da tuni da na raba su ina dalilin masifar nan."
Buba ya ce "Abi a sannu in ka ra ba su dan ta fah ga kuma ta na dauke da wani cikin hakuri za muyi a taya ta da addua'."
Ayan ya ce "Shi ke nan sai mu zuba ido ya ta zaluntar ta, dan kawai yana da kudi uban san na da power, ba dole masu irin halin su su cigaba da cutar mata ba, abin takaici har ta kai da yana dukan ta sai tayi Magana aba ta hakuri wannan ba rayuwa ba ce."
Da mamaki Asif ya maimaita "Duka!
sannan ya kara da "ita kuma sai tayi tsaye ya duke ta."
Ayan ya ce "Kyale doluwar haushi ma ta bani dazu da ta kirani ta na kuka can you imagine ya sa belt ya daki mai ciki wannan wani irn lusarin miji ne."
Sai yanzu Abdullahi ya sa baki ya ce "Da ta haihu wlh sai an raba auren, ya gama shaye shayen sa ya huce kan ta wlh bai isa ba, wanna wani irin azzalumin mutunne mara imani da tsohon cikin sa ya sa belt ya duke ta."
Ayyan ya jadda mashi kai dan duk cikin su ya fi su jin zafin haka. Ya kara da;
"Ta wani saki jiki da shi ta wani haihu har ta na ne man na biyu." Ya ja kuntun tsaki.
Asim da sai da Ayan ya maganar duka ya maido hankalin sa wurin su yace "Kar ka ga laifin ta dan ta haihuwa da shi yanzu dai mu san yanda za ayi in ta haihu ta dawo gida ko kuma ta maka shi kotu."
Asif ya ce "Best solution, dan in mu ka sa ido a cigaba da bagidajancin da tin shekarun baya a ka dai na shi."
Haka kowannane su ya kwana da takai cin mijin ayana musanman Hajiya Shafa da dama ba san auren ta ke ba an yi shi ne dan an nuna mata fin karfi wurin iya sai dai a kullun fatan ta Allah ba iyayar ta cin jarabawa da wannan jarabawa ce wurin ubangaji, ba ta inda bai jaraba bawan sa, wurin ya’yan wurin miji wurin iyaye har ma wurin makwabta.
Bayan takaicin mijin Ayana, ga kuma aurren da za asa wa sadiya da abokin shi wanda a haife ya haifi sadiyar sai dai shi ya sha banban da mijin Ayana dan shi ya na da nitsuwa da dattakunta.
A bangaeren su Halimatu malan Yakubu da ya dawo daga shago, ya gama cin abinci ya kira halimatu.
Halimatu dake cikin daki kasancewa ranar suna da wuta, tana cikin daki ita da Nusaiba suna fira. Ta amsa shi ta mike ta fito ta zauna a kofar dakin.
Ya ce "Dawo nan ki zauna ki dai na zaman kofa musanmman da dare." Ya mata muni da bisa tabarmar da yake zaune.
Ta tashi ta koma kusa da shi ta zauna sannan ya mika mata leda.
Ta amsa ba tare da ta tambayi mine ne ba.
Malna Yakubu ya ce "Dazu yaron nan ya kawo min sakon ki ya ce kin ki amsa shi ne ya zo neman izini."
Umma ta kama baki kafin ta ce "Oh ni kubura na rasa gane kan gadon yarinyar nan anya ba ki da aljannu, arziki na biki ki na gujewa.
Halimatu ta turo baki. Malan Yakubu ya ce"Ba wani aljannu Y'ata qlau ta ke kuma hakan da ta ke ye shi ne daidai ba kowani namiji ba zai zo ya taya su da arha sai ka ce baki auras ba.
Umma ta ce "Ay malan Halimatu lamaarin ta sai addu’a. "
Halima budai mu ga irin wayar?
baki ture ta budai ledar ta fiddo kwalin infinx ta fiddo ta daga cikin kwalin, Ifinix smart 7, baka sai sheki take. Halimatu ta juya ta gaba da baya ta tabe baki. Malan Yakubu da Umma baki ya ki rufuwa.
Umma ta ce "Masha Allah Halimatu wannnan babar waya, Alhamudullilah Allah."
Nusaiba da ke daki ta fito jin muryar Umma ta na godiya. Ta na fitowa ta ci karo da wayar da ke hannun halimatu. Ta karaso wurin ta ta na tambayar wayar wacece?
Umma ta ce "Wayar Halima ce."
Malan yakubu ya ce "Miko min in shafa ta."
Halima ta mika mashi malan Yakubu ya amsa wayar da hannu biyu yana ce wa "Masha Allah Allah sa alkhari halima, gaskiya yaron nan mutumin arziki ne."
Halimatu ta ce "Abba duk salon yaudara ce walh masu kudin na ba imanai ya ishe su ba."
Umma ta kwabe ta "Rufe min baki."
Maln Yakubu ya ce "Uhm uhm in ba mutumin kwarai ba ne na sa ana bincike ke kuma dabi'un sa tabbass masu kyau ne sai dai a maganar aure yana da kyau a fadada bincike.'
Halima ta ce "Abba ni fa ba soyayaa muke yi ba balle a kai da maganar aure shi fa kawai taimakon mu yake ba wani abu."
Malan Yakubu ya ce "In da taimakon mu kadai zai yi mi zai sa shi zuwa neman aure ki?
Umma ta ce "Fada mata, nima ban wayar in shafa."
Nusaiba ta ce "Nima Umma in kin shafa bani nima in shafa shafa shafa.
Halimatu ta mike ta wuce daki tare da ce masu sai da safe.
Haidar da saifullahi da suka shigo suma suka yi kicibis da wayar Halimatu duk da cikin ya'yan akwai masu shaf shafa sai dai basu taba siyan sabuwar touch da kudin su ba sai dai second wata ma ta ji duniya shiyasa suke farin ciki sosai da ganin wayar Halima.
Wayar dake hannun Haidar wada sai da zuwan sa ya kunna daman shi ya san kangadon waya ya na duba ta ya ce "Umma wanna fah ba karamar waya ce fah."
Umma ta ce "Allah ko Hadair.
Haidair ya ce "Wannan zata kai 70 in ma bata fi ba."
Dukan su suka saki baki. Umma ta ce "Kai haba!
Haidar ya ce "Wlh Umma, kuma har layi ya sa a wayar har ma da kati bari muga.. kut katin dubu daya."
Nusaiba ta dafe kirjin ta ta na cewa "Dubu daya! Naira daya daya har dubu daya."
Ya ce "Wlh."
Saifullahi ya ce "Gaskiya mutumin na yana da mutunci."
Haidar ya ce "Muma yana da kyauta duk da ba wani jima ba muna fira va amma da duk alamu bai da mtsl."
Malan Yakubu ya ce "Ni ma dai haka na ke gani amma ay har yanzu ana min bincike ba mu sa ni ba haka kawai zan dau yarinya in bashi ba, da haka na ke yi da sauran ya’ana da sun sha wahala a gidajen auren su amma yanzu kaji shiru suna zaune lafiya kasancewa kowannen jajirtar ce ce ne kuma na gari ina fatan shima ya kasance haka.
Suka amsa da Amin.
Umma ta kira Halimatu, Halimatu tayi shiru har Umma ta gaji da kiran ta.
Malan Yakubu ya ce ta kyale ta, tayi bacci gobe da safe sai ta mashi godiya.