NANNY(MAI RENO)

17

by @jamilaumarjanafty

*NANNY...!*
   _(Mai Reno..)_

*NA*

*AISHA ALTO💞
*JAMILA UMAR (Janafty)*


*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*


      *BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

Riƙe ƙugu Tahir yayi yana Sauke Ajiyar Zuciya, gefe Ɗaya kuma Zuciyarsa na Gudu Sosai Saboda Damuwa, Ashe ce Dake gefe Ta ƙarasa Kusa da Goggo Abu Ta Zauna Kusa da Ita Kafin Tace "Goggo..."

Ta faɗa Tana kallonta Innaro Dake Tsaye Ta Ɗora Hannu Bisa Haɓa Tana Faɗin "Wai Hakimi meke Damunshi ne..?Tunda nake Dashi ban taɓa ganin yayi irin Wannan Fushin ba.." Tahir ya waigo ya Fara Taku Zuwa Kusa da Goggo Yana Faɗin "Ranshi yana ɓace...Dole a saurara mai Har ya Sauko Da kanshi.."

Ya faɗa yana Zama gefen Ashe, Dayan Hannun ya kama yana Faɗin "Goggo Don Allah Kiyi Haƙuri kibar kukan nan Haka nan Nayi miki alƙawarin Komai zai Daidaita Insha Allahu..." Ya faɗa yana Kallonta Goggo Ta Murmusa Tana kallon Tahir da Ashe kafin tace "Bakomai...Allah yayi muku albarka Ku Tashi ku Tafi kubi Umarnin Mahaifinku.." Ta faɗa Tana ƙoƙarin Ɓoye Hawayen Da Suka Taru acikin ƙwayan Idanuwanta.

Innaro ta saki Numfashi Tana Faɗin "Shine kawai magana Don Rashin Tafiyar Naku ma Matsala ne, ku Tashi ku Tafi Insha Allah komai zai zo da Sauƙi, maganar Mufeeda kuma Iya ta Dinga Kula da Ita Saboda yarinya ce..ko Goggo ya kika gani..?" Hannunta Ta zare cikin na Tahir kafin ta saka Hannun ta Share Ƙwallarta Tana Faɗin "Eh Hakan ma yayi Innaro, Allah ya Sauketa lafiya kabiya ka gaida Fuleran karka manta.."

Gyaɗa kai yayi kafin yace "Insha Allahu.." Har ya Miƙe Innaro Tace "Ya ita Faridan...? Ina Fatan ba Wata matsala...?" Jinjina kai Yayi kafin yace "Eh Innaro ba Wata Matsala..."

Sauke Numfashi Tayi kafin tace "Masha Allah...Ko jiya naji Mahaifinta suna Waya da Hakimi kan mganar ne, Allah Ubangiji ya kawo mana Komai Da Sauƙi..."..

Gaba ɗaya Suka amsa da Ameen Kafin Ashe da Tahir suyima su Goggo Sallama Suka Fice Suka barta Tana Share Ƙwallah Fita Sukayi Inda yabama Garzali Umarnin ya Shiga da kayan Abinci Zuwa Cikin Gidan Hakimi, A ƙasa Suka Taka Shida Ashe Har Zuwa Gidan Inna Fulera, Wanda Suna Tafe Tahir na Faɗama Ashe Abunda ya Faru da Wanda yake Faruwa yana gaya mata kamar ya Zubar mata Da Hawaye, Cikin Tausayin Ɗan'uwanta Take Lallashinsa Take bashi Shawaran karya Damu, kuma ya ƙyale Farida Duk inda Zataje Zata Dawo ne bayan Duniya ta koya mata Hankali ya yarda Da Shawaran Ashe Duk da A lokacin Farida bata da wani Fari Acikin Zuciyarsa.

A haka suka isa Gidan Inna Fulera, Ashe ce Ta fara shiga Suka Gaisa da Inna Fulera da Maman Lantana kafin tace musu Tahir zai Shigo Cikin Sauri Maman Lantana ta gyara Tabarma Tahir ya Shigo ganin Maman Lantana ne Awajen yasaka Daga Ashe Har Tahir ba Wanda ya Tada maganar Illah Sunkuyar da kai Da Tahir Yayi kunyar kansa na Ƙara kamashi ganin yadda Inna Fulera ta Rame Lokaci bayan Lokaci Tana Share Ƙwallah...

Basu Wani Daɗe ba Tahir ya Miƙe zai Tafi bayan ya bama Ashe 30k yace Tabama Inna Fulera, Ashe na Bata taƙi karɓa Sai Ta Fashe da Kuka Lokaci Ɗaya Ta Ɗago ido Tana kallon Tahir bayan ta Ɗago Daga Kwancen Datake Maman Lantana Tana gyara Mata Filon Kanta Saboda Taji Daɗin Zaman Sosai.

Cikin Muryan Ciwo da Kuka Inna Fulera tace "Alhaji....."Ta faɗa Muryanta na Sarƙewa, cikin Sanyin Jiki Tahir ya Tsaya cak kafin ya Waigo Zuciyarsa na Tsinkewa Sosai Cikin Muryan Sanyi da Roƙo tace "Bana Buƙatar Kuɗinka Alhaji Abu Ɗaya Nake da Buƙata Awajenka.." jikinsa na Rawa ya Dawo ya Duƙe agaban Inna Fulera yana Faɗin "Ki Faɗi Abunda Kike Buƙata komai kike Buƙata matuƙar na Mallakeshi zan baki Shi Inna.." Ya faɗa Cikin Karaya..

Muskutawa Tayi kafin tace "Ba komai nake Bukata ba Illah ka Riƙe min Mufeeda Tsakani ga Allah...Ka zama gatanta..!kaji ƙanta..! Ka jibanci lamarinta...! Ka zama garkuwa a gareta Alhaji Domin Duk Duniya Mufeeda bata da Wani gata bayan kai..Don Allah kar ka barta tayi kukan maraici In kamin Wannan Abun Ka gamamin komai kuma Bana Buƙatar Wani kuɗi ko Kawan Duniya Farin cikin Mufeeda kaɗai Shine Burina Alhaji.." Ta faɗa Tana Rushewa da Kuka, Maman Lantana Dake gefe kanta ya Ɗaure amma bata kawo komai ba sai ta barshi a ƙila zafin Ciwo ne ke Damun Inna Fuleran.

Ƙuri Tahir yama Inna Fulera da Ido kafin ya maida kallonshi kan Ashe Wacce Idanuwanta Suka Cika da Ƙwallan Tausayin Inna Fulera Iska mai Zafi ya Furzar kafin yace "Girman alƙawari Inna Ba Abu bane mai Sauƙi, Amma Duk Da Haka Nayi miki Alƙawarin zama Gatan Mufeeda, Nayi miki alkawarin bazan bari Mufeeda Ta ƙara kukan Wani Abu ba...Sai na zama Silan Murmushinta anan gaba.." Ya faɗi Haka Idanuwansa Sun kawo Ruwa kafin ya miƙe da Sauri ya Fice Saboda Yadda Inna Fulera Ke kuka Tana Godiya sai yaga Kamar Bazata Tashi ba, Lokaci Ɗaya kuma Kunyar Abunda ya aikata ke Dawo mai Har Ashe ta Fito yana Tsaye yana Maida Hawayen Idanuwanshi Haka Suka Jero Har Zuwa gidan Hakimi ba Wanda ya ƙara magana, bai koma Cikin gidan ba Ashe ya umarta data cema su Basma Su Fito Tare Suka Fito Dasu Laila sama sama yayi ma Hakimi sallama suka Shiga mota Har da Ashe Har gidanta Suka kaita Kafin su Sauketa ita dasu Muda da Tsarabansu 20k yabama Muda da Laila ita kuma Ashe ya kara mata 10k ta ƙara Da Wanda ya bama Inna Fulera Taƙi karɓa Haka Motarsu Ta Ɗaga Ashe Ita da 'ya'yanta Suna Daga maSu Hannu Har Suka ɓace ma ganinsu.

Sai yamma Suka Shigo Kaduna Tahir na Sauri Ko Gida bai Shiga ba Garzali ya Juya Dashi kamfani ya samu Kiran gaggawa bai Dawo ba sai Dare Lokacin kowa yayi barci iya kaɗai ya Tarar Farke, Mufeeda Ita da Naila Sun Daɗe da yin barci gaisawa sukayi sama sama, kafin ya Haura Zuwa Ɗakinsa Ransa Duk babu Daɗi ko yayi Wani Motsi sai ya Tuna da Alƙawarin Inna Fulera wanda Maganar da Suka gama Tattaunawa da Ishaq kenan kafin Su Rabu gaba daya Abubuwa sun mai yawa yanzu Farida bata gabanshi Matsala Goggo ce Sai Tausayin Mufeeda Daya ƙi barinshi Su sukafi Zama Cikin Ranshi Suka Hanashi Sukuni.

****

Farida kuwa Tana gidan Bilkisu Wajen Kwananta Uku amma basu ci karo da Mijin Bilkisu ba mai Suna Aliyu Saboda Tun Safe yake Fita kuma sai Dare yake Dawowa, Sai ya Fita Farida ke Fitowa Haka Kuma kafin ya Dawo Bilkisu zata san yadda Tayi Ta Hillaceta ta koma Ɗaki Abunda ke bama Farida Mamaki yadda Bilkisu ke Rawan Jiki da Abban su Walida in ya Dawo Haka zata Tsala Wanka, Taci Gayu Tana Kwakwarsa, In ko Ta mata sallama bata ƙara sakata a ido sai Washegari bayan ya Fita, Amma kuma Tana Daga Cikin masu bata Shawara ko Acikin group ɗinsu na makaranta Kan Mace ta Daina sakarma Namiji amma Ita gashi Bata Iya Haɗa komai da Mijinta.

Wani Abunda baima Farida Daɗi ba Shine yadda Bilkisu Ta Dinga yaɗa Abunda ya Faru Wajen Sauran Ƙawayensu Waɗanda basu san Meke Faruwa ba Haka Suka Haɗu agroup ɗinsu na Classic Ladies Sukayi Ta Tsinema Tahir Aciki Harda masu bata Shawaran Takaishi ƙara Kotu, yaƙe kawai Farida Keyi amma Bata jin Daɗin yadda Billy ta Fallasasu A duniya ba Ko ba komai Tana Son Tahir Kuma Har gobe yana Matsayin Uban 'ya'yanta ne, Kuma Mijinta.

Ɓangaren su Umma kuwa basu san Abunda ke Faruwa ba Don Daga Faridan Har Tahir ɗin ba Wanda basa Waya Dashi amma ba Wanda yace ga wani Abu, Ita Farida Tsoron Su Umma ne Domin Tasan Ranta sai ya ɓaci Balle Abba dayayi Fushi da Ita don Musamman ya Kirata ya Zageta Tas, Balle kuma tace Ta Baro Gidan Tahir ai kila sai Abba ya Kusa Tsine mata, Shiko Tahir Faridan ne Kwata Kwata bata gabanshi Baya Fatan ya ƙara Buɗan baki ya Faɗi Wani Abu Daya Danganceta ya Ratayeta Gefe ne Domin Ahalin Da yake Ciki yafin Jin Tsananta da Haushinta Fiye da Kanshi Shiyasa Ko Umma ta tambayeshi Suna Zaune lafiya yake cema ta ba wata matsala Domin Kaucema Duk Abunda zai Dawo Da Farida Yamafi Jin Daɗi da bata nan Ko ba komai bayasan Abunda zai Dinga Takura Mufeeda.

  Sai Ranar Data Kwana A cikin Gidan Kana Suka Ci karo da Abban su Walida, Ranar bai Fita ba Kwata kwata yana gida, Lokacin Daya ga Farida yayi Mamaki sosai nan yake Tambayanta Yaushe tazo..? Sai tace mai ta kwana biyu ma..Ido ya Zaro yana kallon Billy Wacce Tayi Fiƙi Fiƙi da Ido Zuciyarta na Tsananta Bugu Wani kallo yabi Farida Dashi bai dai yi magana ba Amma Acikin Ranshi yana Tunanin Wani Shirme kenan Mace da Gidan Mijinta Kuma Tazo Gidanshi Ta tare, Ina bazai Ɗauki Wannan Iskancin ba.

Bai mata magana ba sai da Suka Shiga Cikin Bedroom Ɗinsu kana ya Tsareta da Ido yana Faɗin "Da wani Dalili Farida Tazo nan gidan Harta kwana uku ban sani ba..? Ke dama wani Manufa Matar Da take da Mijinta..?"

Ya faɗa yana Hararanta Sanin Halinta na Shanshanci Shi bai Sake mata ba Shiyasa Duk yadda Billy taso tayi Iskanci bata samu Dama ba, Cikin Rawan Murya tace "Dama..Dama..Umh..." Tsawa Ya Daka mata yana Faɗin "Dama Menene..? Baki zaki Buɗe kiman magana Yadda zan Fahimceki kinsan bana son Raini ko....?"

 Kai ta gyaɗa kafin tace "Matsala suka samu da Abban su Basma..." Kallonta yayi A ɗage kafin yace "Matsala..?" Ya maimata da Sigan Tambaya kai Ta gyaɗa mai alamar Hakane, Cikin Dariyan karki Raina min Wayau yace "Kuma Shikenan Don Sun samu Saɓani ita da Tahir sai kuma akace tazo gidan Aurenki ta tare ko..? Ke gaki Uwarta ko kuma Mai bata Shawaran karta koma gidan Mijinta ta cigaba da zama agidan naki Mijin..?" Ya faɗa yana kallonta Cikin ɓacin Rai..

 Jikin Billy na Rawa Ta Riƙo Hannunshi Tana Faɗin "Don Allah ka Tsaya ka Saurare Abban Walida Wallahi Tahir ya chanchanci Farida Data barshi Amanarta fa yaci Shida yarinyar Datake mata Renon Naila.." Ta faɗa Lokaci Ɗaya Tana Zaunar Dashi gefe Ɗaya Kafin ta Fara Rattaba mai yadda Akayi Billy Saboda Sharri Harda ƙari kamar Agabanta Akayi 

 Haba Aliyu ya riƙe Kafin yace "Ke Bilkisu bana son Ƙarya fa..? Shi Tahir ɗin..? Haba Don Allah ya za'ayi mutum mai Daraja ya aikata Haka, Tahir fa Yana da Kima Sosai a idanuwan Waɗanda Suka sansa.." Ya faɗa yana Tantama Rantsuwa Billy Ta fara Jera mai, Domin ya yarda Da Ita, Bai yarda ba Miƙewa yayi yana Faɗin muje naga Faridan, Jiki na Rawa Tamai Jagora Zuwa Ɗakin data Sauke Farida, Cikin Tsare gida yake Tambayanta gaskiyan lamarin Cikin Kuka Farida ke labarta mai Hadda Hukuncin da Iyayenshi Da nata Suka bashi goyon Baya.

 Tana Faɗa tana Share Ƙwallah, Jinjina kai Aliyu yayi kafin yace "Lallai ba Shakka In ko Hakane Tahir bai kyautama kanshi ba ya Cuci kanshi kuma ya Tozarta iyayensa Da kuma Zuri'arsa..Ya bani kunya Sosai, kuma sai na kirashi na mai magana.." Da Sauri Farida tace "Don Allah Abban Walida ka ƙyaleshi ko kayi mai magana bazai Saurareka ba baya ganin Abunda ya Aikata amatsayin laifi Tunda Haryana Ikirarin data bar gidan Gwara ni na Fita na bar mai gida.."

Miƙewa Aliyu yayi Daga kan Sofa yana Faɗin "maganar banza kenan Har office ɗinshi Zani Wallahi..Sai na gaya mai gaskiya sai dai ko karyaji Daɗi.." Daga Haka ya Fice Daga Ɗakin Cike da Mamakin Tahir ɗin Duk da ba wani Kusanci Suke da Juna sosai ba, amma Suna Taɓa Juna Lokaci bayan Lokaci Saboda ƙawancen Matansu Da ba yanzu yake ba, Yana Fita Farida Ta Miƙe zatama Billy magana tayi Saurin Dakatar da Ita tana Faɗin "Kinga Farida Bar maganar nan sai gobe..Yanzu lokacin Abban Walida ne kada mu Shiga Hakkinshi Nasan, Halin yan kaya na.." Daga Haka ta Fice Ta bar Farida Riƙe da baki Tana Binta da Kallo.

****
Washegari kuwa Da Misalin Ƙarfe 3:00pm na Rana Aliyu ya ƙwanƙwasa Ƙofar Office d'in Tahir inda ya bashi Umarnin Shigowa Suna Tare da Ishaq lokacin Suna Wani Lissafi ganin Aliyun sai da yayi mgana Cikin Fara'a Ya Tarbeshi yamai iso Zuwa Kujeran Dake office d'in Ruwa ya kawo mai Ya Zuba mai ya Mika mai ya karɓa yana Mai Godiya sai da yasha Ruwan ne ya Miƙawa Ishaq hannu suka gaisa Cikin Sakin Fuska ya kalli Tahir yana Faɗin "Alhaji Tahir Wajen ka nazo, Wata maganace mai Muhimmanci ke Tafe dani.."

 Shiru Tahir yayi kafin yace "Allah Sarki ba komai ina Jinka.." Ya faɗa Cike da Mamaki Lokaci Ɗaya yana zama agefensa, Kallonsa Aliyu yayi kafin ya maida kallonshi kan Ishaq, Tun kafin yayi magana Tahir yace "Karka damu ka faɗi maganar Ishaq Tamkar Ɗan'uwa yake a gareni.." Zakuɗa kafaɗa Aliyu yayi kafin yace "Kana da Labarin Matarka Farida na gidana Tun Ranar data bar gidanka..?"


Tahir ya Ɗago ya kalli Ishaq shima ya kalleshi kafin  Duka su maida Hankalinsu kan Aliyu Lokaci Ɗaya Tahir yace "Ah...Ina zan Sani kuwa Alhaji Aliyu.." Ya faɗa Cikin Halin Rashin Damuwa, Gyara zama yayi kafin yace "Toh Tana gidana nima bansani ba sai jiya na sani Shine na Turke Ita Bilkisun Shine Take Sanar dani Wani Labari mara Daɗin Ji ban yarda ba sai da Na Kira ita Faridan Na ƙarajin Ta bakinta Wai Alhaji Da gaske ne Maganar da Suka Faɗa min..?"

Miƙewa Tahir yayi yana Kallon Aliyu kafin yace "Wata magana kenan..?" Ya faɗa Jijiyoyin kansa Sun Fara Tashi Saboda Ɓacin Rai Cikin Jimami Aliyu yace "Na kama yarinyar Da kuka Ɗauko Daga Garinku tana muku Rainon Naila Ciki.." Ya faɗa yana Sakarma Tahir ido, Runtse ido Tahir yayi Zuciyarsa na Tafasa kamar tayi Bindiga Haka Shima Ishaq yana Tsinema Farida ne a Cikin Ranshi, shi Wallahi ko Zahra bai yarda ya bata wannan Labarin ba balle ke ace Mijinki amma baki da Buri sai na Tona mai Asiri ki tozartashi.


Taku Tahir yayi Zuwa bakin Window Office ɗinshi ya yaye labulen Wajen Cikin Juya baya yace "Eh Da gaske ne Aliyu..Nama Mufeeda Ciki, amma Duka Abunda ya Faru ba laifina bane Laifin Farida ne Ita ce Sanadiyar Jefani Cikin Halaka amma Wallahi bayan Matata Farida ban taɓa Keta Gonar da ba Tawa ba sai akan Mufeeda Wacce Ƙaddara ta Hau kanmu.." Ya ƙarashe Faɗa Cikin Muryan Kuka, Miƙewa Aliyu yayi yana Faɗin "Ashsha Kaji ko..? Abu baiyi Daɗi ba.."

Tahir bai bashi Zarafin ƙara magana ba, ya Shiga bashi Labarin irin zaman Wulaƙancin Dayayi da Farida da yadda ta banzatar da Rayuwarsa da Ƙoƙarinsa na ƙara Aure da yadda Goggo Take Dakatar dashi har Zuwa Faruwan komai Ya ƙarashe yana Faɗin "Wallahi Tallahi..Farida Ta Cutar dani Cutar da Allah ne kaɗai zai sakamin, Sai Farida tayi Wata Huɗu bata kalleni A shimfiɗa ba, Ku gayamin Ni Dutse ne ko Gunki da bazan Buƙaci mace ba..?" Ya faɗa lokaci Ɗaya yana Juyo da Fuskarsa Wacce Hawaye suka Wanke mishi ita.

 Daga Ishaq Har Aliyu Jikinsu yayi Sanyi Sosai Aliyu ne ya ƙarasa Kusa Dashi ya Dafa Kafaɗarshi yana Faɗin "Cool Down Ka daina Kuka, Haƙiƙa Wannan Abun da ya faru ƙaddara ne ko Kuma nace Darasi ne ga Farida da Goggo, Amma fa maganar gaskiya kana da babban Laifi Tahir na yarda kabar Farida ta Rainaka take yarda taga Dama bayan Kai kake Aurenta aiko Min gatan da iyayenta Suka bata Tunda tabar Gabansu Ta Dawo ƙarƙashin Ikonka ya kamata ka Nuna mata ƙwanjinka na Mulkinka Amatsayinka na Namiji mai Cikakken Iko Agidanshi.. Maganar gaskiya kayi Kuskure.." Ya faɗa yana Murza Kafaɗarsa.

Numfashi Tahir ya Sauke kafin yace "Tabbas maganarka Hakane... Haƙurina da girman Iyayenta Danake gani Da kuma Nasihan Goggo Akaina da Kuma 'ya'yan Dake Tsakanina da Farida yasanya Bana iya Mata Wani abu, In tayi ba Daidai ba Shine Kuskure na barta ta saba da Komai tayi Daidai ne Tabbas nima ina da Laifi ba komai Ake ma Haƙuri ba Gashi Haƙurina yajamin naje na Afkama Marainiyar Allah Daga Ƙarshe na zama Abun YaɗaWar Farida Kamar bamu Haɗa komai da Ita ba, ba komai...Haka Allah ya Tsara min.." Ya faɗa yana Share Hanci kamar Wani yaro.

Kafaɗarsa Aliyu ya Daka kafin yace "Kazama namiji Abokina ka ganni nan bana ma Bilkisu da Wasa Tunda na Lura tana da Rawar kai Ubanta Nakeci tasan Halina ko yanzu ɗin ma ina komawa zan Koro Faridan Dole ta Dawo Tunda bata da Wajen Zuwa..."
 
 Da Sauri Tahir yace "No..no plz ka ƙyaleta Ka barta ta Zauna Da kanta zata Dawo ba sai kamata magana ba ai zataga Abunda saɓanin Shi Suke gaya mata zata ma kanta Faɗa Tun kafin Wani ya mata.." Ishaq yace "Shawara mai kyau Tahir..."

Aliyu ya Saki Hannu yana Faɗin "While Tunda kace Haka zan saka musu ido.. Amma True Tak, Yarinyar nan ta Haihu ka Aureta Wallahi Sweet Sixtyn suna da Daɗin Sha'ani, Tuni Farida zata Rena kanta Ta Dawo Tana begenka Lokacin Da ka mata Nisa.." Dariya Ishaq ya saka kafin yace "Shawara mai kyau..Dama Shi ya Chanchanta yayi Wuf da Ita.." Hararanshi Tahir yayi Bai yi Magana ba, Shima Aliyu Dariya yake kafin su Cigaba da Tattauna maganar Tare Suka Fito Sai da Sukayi sallar La'asar Cikin Jam'i kana suka Rako Aliyu ya Hau Motarsa Zuwa gida, su kuma suka koma Office d'in Tahir Ishaq bai Dawo da Maganar ba ganin Tahir ya basar da Zancen ya Ɗauko Lissafinsu suka cigaba dayi amma Cikin Ran Tahir Tsanar Farida ce ke ƙara Ninkuwa in ya Tuna Tana chan tana Yawo Dashi Acikin Duniya kamar babu Igiyan Aurenshi Akanta.


******

*BAYAN SATI ƊAYA*

Lokacin Tuni Har Su Basma Sun koma Makaranta Hadda Itama Mufeedan Don Da Tahir ya nuna kamar Ta Haƙura da Karatun Saboda Gujema idon Mutane sai Ta Fara Share Ƙwallah Shi kuma ƙwallar Mufeeda kamar dalma yake Acikin Ranshi, dole ya barta ta cigaba da Zuwa Makaranta amma bayan yaje yama Shugaban makarantan Bayanin Cewa Mufeeda matar Aure ce, Kuma tana Ɗauke da Juna biyu So School Authority Su kula da Ita, basu Tsaya Tambayan Waye Mijin Ba Illah Suka yarda da maganar Tahir Suka kuma Rubuta Cikin Record Book.

 Hatta da Islamiyya ta koma Abunta kamar ba Ita ba, sai dai Tayi Kiɓa Sosai, Ta ƙara Fari ta Cika ta Ko'ina Saboda tana samun Abunda Take so Abincinta Dama Shine Faten Wake, sai ƙosai da Koko sai kayan kwaɗayi Irinsu Goriba, yalo Sai Ice cream Wanda In Mufeeda bata Sha ba kamar Cikin zai ɓare, Shiyasa Tahir kullum zai Dawo sai ya Shigo mata Dashi, Ba laifi Iya na Kula da Ita sosai su Basma ba'a barsu Abaya ba Lokaci kaɗan Mufeedan Ta Saki Ranta sai dai Tunanin Innarta Dayaki barin Ranta.

Ɓangaren Su Goggo Abu kuwa ba Wani Cigaba, Tahir Sau Ɗaya ya Kira Baba Hakimi Awaya Tunda yaji ya fara mai maganan Goggo Abu ya Datse Kiran, Tun daga Ranar ko ya Kirashi baya Ɗauka Dole ya Haƙura sai dai yana Kiran Goggo Akai akai Yana ƙara bata Haƙuri amma ya Ɓoye mata Shima Saboda Ita Baba Hakimi ya Daina ɗaga Wayarsa sai dai ya Dinga Nuna mata ta kwantar da Hankali komai xai Daidaita.

*******

Yana Toilet yana Wanka, Akayi ta Kiran Wayarsa bai ji ba sai da ya gama Wanka ya ɗauro Alwala ya Fito Ɗaure da Towel A ƙungunsa Ƙaramin na Saman kansa yana Tsane Ruwan Jikinsa, Yaji Kiran Wayarsa Cikin Sassarfa ya isa Kusa da Wayar, Abunda ya bashi tsoro ganin Kiran Baba Hakimi, Da Asuban Fari Domin Lokacin Wajen ƙarfe 4:43am ne.

  Cikin Firgici Da Tsoro ya ɗaga Kiran yana Faɗin "Salamu Alaikum Baba..?" Ya faɗa Cikin Rawan Murya banji me akace ba Sai dai naji Tahir ya saki Salati yana Faɗin "Innalillahi Wa'inna Alaihirraju'un..Allah ya Jiƙanta da Rahma Allah yasa ta Huta..."

Ya faɗa kafin ya Ɗauke Wayar A kunnensa Cikin Mutuwar Jiki ya Faɗa gefen gado yana Dafe kanshi Ko'ina na Jikinsa na Rawa, lokaci ɗaya Yaji Hawaye Sun Cika mai ido Har Sun Fara gangarowa.


Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.


*Janafty*
*Aisha Alto*