SAUTIN KARSHE

Chapter 13

by @amanarcool323

"Gadanga lafiya? Me yake faruwa ne? Kamar sunan Ma'u na ji ka kira?" Inna ta yi maganar a daidai lokacin da ta ƙaraso gurin, turus ta yi ta tsaya, tana kallon Ma'u dake kwance a jikin Aliyu cikin yanayin da ta kasa tantancewa. "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, Ma'u, me ya same ta? Ya a ka yi ta dawo? Ina Yaya Saminun?". Ta jero tambayar a lokaci ɗaya.

Aliyu ba tare da ya ce mata ƙala ba ya ɗaga Ma'u kamar wata ƙaramar yarinya ya shiga ciki da ita, saman tabarmar da Abida ke zaune ya zaunar da ita ya jingina bayanta da gini. "Ma'u me ya same ki?" Inna ta sake tambayarta cikin ruɗani tana zama kusa da ita, Aliyu ya dubi Halima dake zaune ya ce "Ba ni ruwa". Tashi ta yi ta ɗebo masa ruwan ta kawo masa, ya yi addu'a a ciki sannan ya kafa mata su a baki, kurɓa ɗaya ta yi ta kawar da kanta tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. 

Cikin tashin hankali Inna ta ce "Ma'u don Allah ki yi mini magana, me yake faruwa ne? Ina Yaya Saminu? Ya aka yi kika dawo gida a cikin wannan halin?". Cikin kuka Ma'u ta ce "Inna sun kashe shi, sun kashe Baba Saminu, a gaban idona suka harbe shi da bindiga". Ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka kamar ranta zai fita. Mutuwar zaune Inna ta yi, Halima kuwa ta zabura da ƙarfi tana faɗin "Na shiga uku, innalillahi wa'inna ilaihim raji'un". 

"Su waye suka kashe shi?". Aliyu ya tambaya yana tsare ta da ido. "Ƴan ta'adda ne, Yaya ɓarayi ne suka tare mu a hanya, sun kashe da yawan mutanen da ke cikin motar, ciki hadda Baba Saminu". 

"Innalillahi wa inna ilaihim raji'un" shi ne kalmar da Inna ke ta nanatawa, saboda jin abin take yi kamar almara. 

"Ke ya aka yi kika kuɓuta har kika dawo gida? Wa ya dawo dake?". Aliyu ya sake tambayarta "Ni ma ban sani ba, kawai tsintar kaina na yi a ƙofar gida" Ma'u ta bashi amsa tana sake rushewa da kuka. Shiru ya yi yana tunanin wannan wane irin tashin hankali ne? Cikin kuka Inna ta ce "Ma'u ina fatan dai ba su yi miki komai ba ko?" 

Ta jinjina kai tana ci gaba da kukanta, "Ba tambayarki ake yi ba?". Aliyu ya ce yana tsare ta da ido. Ta ce "Ba abin da suka yi mini, sai ɗaya daga cikinsu ne ya mare ni". Haske fuskarta ya yi da filita, shatin yatsun mari ya gani kwance a saman fuskarta, ya kashe fitilar yana nazarin to ya aka yi ta samu damar dawowa gida?. 

****

Sai ƙarfe tara da rabi na dare ya isa gida. A falo ya tarar da su Mammy cikin damuwa, Mammy na ganinsa ta sauke ajiyar zuciya, ta ce "Haba Sudais ina ka shiga ne tun ɗazu muke kiran wayarka a kashe? Faruk ya kira Hanif ya ce ka je wani ƙauye ne, gabaɗaya ka ɗaga mana hankali". Murmushi ya yi tare da faɗin "Afuwan Mammy, inda na je ne ba network, kuma a hanyata ta dawowa motata ta tsaya mini da ƙyar na samu bakaniken da ya duba mini ita, sai kusan magariba na dawo. Muna gama sallah kuma muka shiga meeting a gurin aikinmu sai ƙarfe tara muka fito. Yanzu haka a gajiye nake, ko sallan isha ban yi ba" .

Mammy ta ce "Ah lallai ka kwaso gajiya. Alhamdulillah tun da Allah ya dawo da kai lafiya, sai ka je ka watsa ruwa ka yi sallah, zan sa Zahra ta kawo maka abincinka a ɗaki". Har wani lumshe ido yake yi saboda gajiyar da yake ji, ya ce "To shikenan Mammy" daga haka ya haura sama da sauri, yana shiga ɗakinsa ya jingina da ƙofar ɗakin ya runtse idonsa da ƙarfi, ya daɗe tsaye a gurin kafin ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka. Ko da ya fito an kawo masa abincinsa, jallabiya ya saka, ya gabatar da sallar isha, bai bi ta kan abincin ba ya haye gadonsa, ya jawo bargo ya rufe jikinsa saboda wani irin sanyi yake ji, wanda ya saukar masa da zazzafan zazzaɓi nan take.

****

A daren daga Ma'u har Inna da Yaya Aliyu babu wanda ya yi bacci, kowa da abin da yake saƙawa a ransa. 

Washe gari ƙarfe tara na safe labarin ɓarnar da ƴan ta'adda suka yi a hanyar ƙauyen Gwagwa ya karaɗe ko ina, Aliyu ya kira can ƙauyen, nan ya ji su cikin tashin hankali na abin da ya faru. Saboda an kashe jama'ar garin da dama, kuma an tabbatar musu da Baba Saminu na cikin waɗanda aka kashe, abin da ya ƙara ɗaga musu hankali babu wata mace da aka gani a wajen ko gawarta. Bayan kuma ya kira su lokacin da yake tasha ya sanar da su tare yake da Asma'u. Bayan sun gaisa ne Aliyu yake jajanta musu abin da ya faru, nan ya tabbatar musu da Ma'u ta dawo gida tun jiya, ba ƙaramin mamaki suka yi ba da jin tana gida, Baba Bello wanda ke bin Baba Saminu ya ce "Aliyu ya aka yi ta koma gida?". 

Aliyu ya ce "Baba wallahi bamu sani ba, muma abin da ya ɗaure mana kai kenan tun jiya, ko da muka tambaye ta sai cewa ta yi ita ma tsintar kanta ta yi a ƙofar gida". Baba Bello ya ce "Ikon Allah, to mutanen kanta ne suka mayar da ita gida kenan? Ina fatan dai babu abin da ya same ta?". 

"Eh babu abin da ya same ta, amma dai tana cikin ruɗani tun jiya kuka take yi, in sha Allah zuwa gobe zamu zo daidai hanyar ta samu nutsuwa" Baba Bello ya ce "A'a, ku bari a ɗan kwana biyu tukuna ta ƙara samun nutsuwa, yanzu hankalinmu a tashe yake da bi hanyar nan, ku bari har wannan tashin hankali da ake ciki ya lafa". Ya ce "To shikenan Baba, Allah ya jiƙan Baba Saminu da sauran jama'ar da a ka rasa, ya sa mutuwa hutu ce a gare su" . Ya amsa da "Amin" ya yi masa sallama.

Lokacin da jama'ar unguwa suka samu labarin hadda Ma'u na cikin mutanen da wannan tsautsayin ya afka da su, sai dai ita Allah ya tsiratar da ita ta kuɓuta. Da yawa sun tausaya mata, tare da rashin jin daɗi na kisan da aka yi wa Baba Saminu. Waɗanda suka ga lokacin tafiyarsa tare da Ma'u abin yafi tsaya musu a rai, tururuwar zuwa gidan a ke yi da sunan jaje. Wasu kuma jin ƙwaƙwafi ne yake kai su. Ma'u na ɗaki kwance har yanzu kuka take yi idan ta tuna yadda ta ga ana kashe mutane kamar kiyashi. 

Da Sani ya samu labari. Duk da ya ji babu daɗi amma sai da ya ce "Shegiya, ashe an rufe bakin tsiwa, ta gamu da ƴan iskan hanya. Ai ban so su bar ta haka ba, na so a ce sun bar mata wata shedar da za ta riƙa tunawa da su". 

Zubairu ya ce "Kai Sani, ka ji tsoron Allah, ƴan ta'adda fa aka ce, haba ai duk abin da yarinyar nan ta yi maka bai kamata ka yi mata wannan fatan ba". Sani ya ce "Na faɗa, idan ka ji haushin maganar sai ka yi maganin abin". 

"Babu abin da zan yi maka, amma dai ka canza hali wannan ba rayuwa ba ce". Zubairu ya faɗa tare da tashi ya bashi guri. Ashar Sani ya shiga ɗura masa, bai kula shi ba ya ƙara gaba abin sa. 

Wasa-wasa har aka kwana uku Ma'u ba ta daina kuka ba, gabaɗaya ta ƙi sakin jikinta, ko lokacin da ƙawarta Jamila ta zo ta ga irin kukan da take yi, biye mata ta yi suka dinga rizgar kukan tare. 

Inna ta ce "Ma'u, ina ga ya kamata ki haƙura da kukan nan da kike yi, wannan kukan ba zai tsinana miki komai ba. Ke da ya kamata ki yi godiya ga Allah da ya tsiratar dake, sannan waɗan da suka rasa rayukansu ki yi musu addu'a. Ba wai ki zauna kullum kina ɗaki kina kuka ba, salon ki jawowa kanki wani ciwon. Don Allah ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka". Cikin kuka Ma'u ta dubi Inna da rinannun idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Inna, ni kaina kukan nan da nake yi ya fara damuna, ina son in daina yin sa amma na kasa, kukan ne yake zuwa ba tare da na sani ba, sai dai in ji hawaye na zubo mini. A duk lokacin da zan rufe idona hoton abin da ya faru a gaban gabana nake gani, abin da ban taɓa tunanin ko a cikin baccina zan gane shi ba. Inna wai ni Ma'u a gabana..." Kuka ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasa maganar. Rungume ta Inna ta yi ta shiga rarrashinta, da ƙyar ta samu ta yi shiru. Har ta ɗibi ruwa ta je ta yi wanka ta dawo tsakar gidan ta zauna, kallon Halima ta yi da take aiki gabaɗaya ta zama wata iri dabam. 

"Aunty Halima"

Halima ta juyo a hankali ta ce "Na'am Ma'u".

"Me yake damunki ne? Gaskiya ya kamata a kai ki asibiti, wallahi ramar nan taki ta yi yawa". Halima ta yi murmushi ta ce "Kar ki damu Ma'u, ba abin da nake ji a jikina kawai dai ramar ce da ake gani, amma lafiya ƙalau nake". 

Shiru Ma'u ta yi, ta mayar da dubanta ga Abida dake kwance ta ce "Abida ya jikin?". 

Abida ta ce "Da Sauƙi Aunty". 

"To Allah ya ƙara ba ki lafiya ƴammatana" ta amsa da "Amin" sosai Inna ta ji daɗin ganin yadda Ma'u ta ɗan sake ji. 

Ranar da aka kwana biyar da faruwar lamarin ne Aliyu ya shirya shi kaɗai ya yi sammako ya tafi ƙauye gurin gaisuwa. Inna ta so ta bi shi amma ya ce "A'a shi kaɗai zai je" addu'a ta yi masa sosai. Cikin ikon Allah yana zuwa tasha ya tarar da motar farko ta cika mutum ɗaya ya rage, nan ya shiga suka ɗauki hanyar ƙauyen. 


*****

"Sudais magana nake yi maka tun ɗazu ba ka ce mini komai ba, ni fa wannan iskancin ne yake haɗa ni da kai". 

"Hanif me kake so na ce maka? Ƙarya kike so na yi maka ko me? Na ce maka lafiya ƙalau nake amma ka kasa fahimta ta". 

"Wallahi ƙarya kake yi akwai abin da yake damunka, ina lura da kai a ƴan kwanakin nan gabaɗaya yanayinka ya sauya". 

"Hanif zo ka matsi bakina ya sanar da kai abin da kake son ji, ka ga don Allah ka rabu da ni ba na son takura". Sudais ya yi maganar yana tsare shi da idanunsa da suka canza launi daga fari zuwa ja. 

Hanif ya ce "Idan ka ga na ƙyale ka to sai ka sanar da ni me yake damunka". Sudais sanin halinsa da ya yi na baƙin nacin tsiya ne ya sa shi a hasale ya ce "To auren da za a yi wa Ilham ne yake damuna, yarinyar nan ba ta son wanda za a aurata mata. Duk ta bi ta tashe hankalinta sai rigima da koke-koke take yi mini, gashi auren bai fi sati biyu ya rage ba. Ni duk na rasa yadda zan yi da ita". 

Hanif kallonsa ya yi da kyau, kafin ya tuntsure da dariya, ya ce "Sudais kar dai kishi kake yi saboda ka ga za ta auri wani? Da ma kana son Ilham duk wannan abin da kake yi? Yarinya ta daɗe tana nuna maka ƙauna, kana yanƙwanata sai yanzu ne za ka ce kana jin damuwa saboda za ta auri wani? To me kake nufi da hakan? Kai ma ka san zancen a fasa auren nan a yanzu impossible". 

Cikin takaici Sudais ya ce "Kai banza ne, daga na faɗa maka damuwata shikenan sonta nake yi? Ilham fa matsayin ƙanwa take a gurina, ta ya kake tunanin zan iya aurenta? In yi yaya da ita idan na aureta? Ni gaya maka ne ban yi ba na samu matar da zan aura, sunanta Zuhura". 

Hanif ya ce "Ba Zuhura ba Sahura, kai Sudais kar nake kallonka, kishi kake yi da auren Ilham. Kuma a yanzu sai dai ka yi haƙuri ka riga ka yi wasa da damarka tun farko. Sannan da kake maganar ya za ka yi da ita idan ka aureta? Lokacin da za ka rufe ƙofa da ita, ka sauke mata buƙatarka babu wanda zai sani, sai dai mu ganta da ƙaton ciki tana iza-iza da shi ba". 

Share shi Sudais ya yi, Hanif ya shiga yi masa iskanci sai da ya yi mai isar sa sannan ya bar office ɗin.


Yana fita Sudais ya lumshe idonsa. A hankali ya ce "Ya Allah!". 

******

A ranar Aliyu ya dawo, bayan sallar magariba ya isa gida, ko da ya shiga Abida kaɗai ya tarar kwance a tsakar gidan. Gaishe shi ta yi, ya amsa yana tambayarta ina jama'ar gidan? Ta ce "Suna ciki tun da suka shiga sallar magriba basu fito ba". Ɗaki ya shiga, nan ya tarar da Halima zaune saman darduma, zama ya yi yana jiran ta idar da sallah. Kusan minti goma ya ga ba ta motsa ba, ya ce "Halima wannan wace irin sallah ce kike yi haka? Ai ko shigowata ɗakin nan kika fara ya ci a ce kin gama". Shiru ba ta motsa ba, kuma bai ga wata alama da ta nuna masa ta cewar tana jinsa ba. Tashi ya yi a hankali ya ƙarasa inda take, hannu ya kai ya taɓa ta sai kawai ya ga ta biyo shi. Da sauri ya tare ta ta faɗa jikinsa, nan ya ga idanunta a buɗe baƙin idanun ya janye sai farin ne ya rage. 

"Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, Halima!" ya kira sunanta da ƙarfi.


Amanarcool
***