18
Chapter 18
Washe gari.
Kasancewar yau Monday ce ya sa tun shida da rabi ta fita aiki bata ko samu damar taya Ammie aiki kamar yadda ta saba, tana tashiwa bayan iddar da sallar asuba ta shiga wanka yau ko breakfast bata samu ta tsaya ta yi ba ta wuce aiki.
Tana zuwa kuwa ta hadu da Hajiya Binta hakimce a palo tana waya, ga dukkan alamu kuma da mai gidan ta ke magana ko daga yadda take ƙasa ƙasa da murya za ka fahimci haka, har ƙasa Nazli ta tsuguna ta gaishe ta kana ta tambaye ta abin da za ta ɗaura na breakfast, inda ta ce ta fara ɗaura tea wa su Abla su fara karyawa tukun tunda su za su makaranta. Ba musu kuwa ta shiga kitchen ta ɗaura tea da toast bread, har sama cikin ɗakin su ta kai musu kana ta koma kitchen ta fara shirya masu lunche boxes ta saka masu komai da suke bukata a ciki, dama already Hajiya Binta ta gaya mata inda snacks dinsu ya ke aje dan haka bata sha wahalar haɗa masu lunch box ba ta fitar musu, a daidai sanda suke saukowa driver zai kai su school. Tare da fari suka fita tana da lectures din safe yau.
Har mota ta raka su da lunche boxes suna shiga ta ɗaurawa kowa na sa gabansa, driver ya tada mota suka fita tana daga masu hannu da murmushi a fuskarta, Araf kaɗai ya ɗaga mata hannu amma ban da Abla da ko kallon inda Nazli take bata yi ba. Sai da ta ga fitar su ta koma ciki, bata samu Hajiya a palon ba hakan ya sa kawai ta wuce kitchen ta soma tsaftace ko ina, tana cikin aiki Hajiya Binta da fitowarta kenan daga ɗaki ta soma kwaɗa mata ƙira. Tsome hannayenta daga cikin ruwan kumfan wanke wanke ta dauraye su ta fita da sauri dan amsa ƙiran Hajiyarta.
"Na'am Hajiya, ga ni kin ƙira ni." Kallonta Hajiya Binta ta yi a yamutse ta ce. "Me kika dafa?" "Ai Hajiya ba ki faɗi abin da za a dafa ba." Nazli ta fada. "Okay ɗan haɗu min tea the bread." "To Hajiya." Daga nan ta koma kitchen ta kawo mata shayin, kana ta koma kitchen dan ƙarasa ayyukan da suka rage mata.
Misalin 11:00 na rana Hajiya Binta ta sake ƙiran ta, a lokacin ta gama aiki har ta haɗa ma kanta farin shayi marar madara ta haɗa da ragowar toast bread da su Abla suka rage ta yi kari ta koma waje bayan gida kusa da kitchen ta zauna ita kaɗai kamar mayya, tana jiran rana ta yi ta gama da su ta koma gida.
Jin muryar Hajiya Binta na kwala mata ƙira ya sa cikin hanzari ta miƙe ta nufi cikin gidan, a bakin ƙofa suka ci karo da Hajiya Binta da ta fita neman ta. "Na'am Hajiya, ga ni." Ta fada cikin rusunawa. "Ina kika shiga tun ɗazu na ke neman ki ban gan ki ba, aikin da ya kawo ki kina fita a duk lokacin da kika dama ba tare da kin nemi izini ba, tukun ma wa kika sani da har kika fita ba tare da kin tambaye?" Hajiya Binta ta yi maganar tare da bin ta da wani irin kallo me wuyar fasaruwa.
Nazli bata ji daɗin kalamanta ba sun yi matuƙar sosa mata rai sosai amma sai ta danne zuciyarta ta hanyar faɗin. "Ki yi haƙuri Hajiya, amma ban je ko ina ba ina ta bayan gida ne kuma na riga da na gama aiki na kafin na zaga."
Ɗan tsaki Hajiya ta ja. "Biyo ni." Abin da ta ce kenan ta juya ta koma ciki, yayin da Nazli ma ba musu ta mara mata baya guiwa a sanyaye da abin da Hajiya tai mata. A palo suka tsaya Hajiya ta juya ta kalle a fizge ta ce. "Abincin rana za'a yi kuma miyar ganye, amma before that zan haɗa ki da driver ku tafi kasuwa akwai abubuwan da muke da buƙata na kayan abinci, gobe Alhaji zai zo dan haka we need some certain things da za'a tarbe shi da shi." zama ta yi kan kujera ta ɗau wayar ta latsa number Ali driver. "Hello?" Ina kake ka zo yanzu ina da aike." Iya abin da ta ce kenan ta katse ƙiran, maida kallon ta yi ga Nazli wacce har yanzu take a tsaye bata zauna ba don Hajiya Binta bata bada umarnin zama ba ta ce. "Hope ba ki manta yarjejeniyar mu ba?" Ta cigaba. "Gobe mijina zai dawo, karki kuskura, ina nufin ko kusa kar na ganki a gabansa koda wasa har kika bari ya ganki to ba za ki ji daɗin na ba haka zalika ba za ki ji dadin abin da zai biyo baya. Ni bana wasa da mijina kuma ina matuƙar kishinsa zan iya yin komai a kansa, dan haka gobe ki tabbatar kin zo da hijab da niƙab ɗinki." Ta ƙare maganar cikin huce sai bude hanci take tana sirfa magana kamar wacce a ka cewa za a ƙaro mata kishiya.
"In sha Allah zan kiyaye dukkan sharuɗan ki hakan ma ba za ta faru ba." Nazli da mamaki dabaibaye a zuciyarta ta ta fada, ita dai kam za ta so ta ga wannan mijin da ake ta tada jiyoyin wuya a kansa, ita da gaba daya ta riga da ta goge babin maza duka a rayuwarta, ina ita ina wani mai mata da yara? "Shiga ɗakin yara ki kawo min bero da peper." Na miki jotting abin da za'a siya." Ta amsa to kana ta juya ta nufi ɗakin su Araf, cikin bedside drower ta samu jotter da biro ta ɗauka ta fita.
Bata ga Hajiya a palon ba sai motsin da ke tashi a kitchen hakan ya sa ta nufi can ɗin da takardar a hannunta, ganinta tsaye a kitchen tana duba kayan abincin da ya rage a gidan tana lissafi. "Hajiya ga takardar." "Okay ta ce kafin ta karɓa ta soma rubutu a ciki, bayan ta gama ne ta miƙa ma Nazli takarda da cewa. "Ga abin da za a siya, komai da muke da bukata kenan." Hannu ta sa ta karba tare ta duba abubuwan da ta rubuta.
"Mu je na baki kuɗin ku tafi, Ali ma ya zo yana waje yana jiran ki." Har ɗaki Nazli ta bita ta cire kuɗin ta bata kana ta ɗaura da faɗin. "Dan Allah karku ɓata lokaci kin ga rana ta yi, yara za su tashi a makaranta kar su yi zaman jiran driver." "To Hajiya." Daga haka ta fita ta samu Ali wanda ke jiran ta a parking lots, tana zuwa ta buɗe gidan gaba ta shiga ya tada mota suka fita.
Suna isa ta fara fita ta shiga cikin kasuwa shi kuma ya tsaya neman wurin parking, komai da ke rubuce a takardar sai da ta siya kana ta juya ta koma. Koda ta fita bata ga Ali driver ba, waige–waige ta soma can ta hango sa gaba kaɗan ya parker motar, ba ta tsaya ba ta nufi sa da kaya a hannunta. Shima yana ganin ta ya bude booth ta saka kayayyakin hannunta kafin ya maida ya rufe suka koma cikin mota ya tada suka kama hanyar gida.
Hajiya Binta na palo tana waya tana odering snacks wa gobe Nazli ta yi sallama a bakinta ta shiga da ledodi niƙe niƙe a hannunta, darect kitchen ta wuce da kayan ta aje kan ta koma palo ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa pure water mai sanyi ta sha kan ta koma ta nemi wuri a kaƙa kusa da Hajiya Binta da har yanzu tana magana a waya, Sai sauke numfashi da ajiyar zuciya ta ke saukewa ajajjere saboda da gajiya da ranar da ta ɗebo.
Bayan gama wayarta Hajiya Binta ta dube ta ta ce. "Sai yanzu kuke dawowa me ya tsaida ku har haka bayan na faɗa miki za ki zo ki dafa abinci yara za su zo daga makaranta ba abinci." Cikin sanyi da gajiya Nazli ta ce. "Ki yi haƙuri Hajiya, wuri ne ba ɗaya ba wasu abubuwan ma sai da na zaga kafin na same su." Tsaki Hajiya Binta ta ja. "Sai ki tashi mu je na ga me kika kawo." Daga haka ta miƙe ta nufi kitchen Nazli ta mara mata baya jiki a saɓule.
Bayan duba kayayyakin, still Nazli ta barwa kayan ta jera ta maida komai a mahallinsa. Ba tare da ta samu damar hutawa ba Hajiya ta ce a ɗaura girki. Haka nan ko ta kunna gas ta ɗaura tukunya, kamar yadda Hajiya Binta ta ce miyar ganye ta dafa da tuwon semo da yar shinkafa wa yara don basa cin tuwo su. Haka ta zage ta yi girkin cikin ƙanƙinin lokaci ta gama ta kwashe, ta gama komai tana cikin mopping Hajiya Binta ta shiga, ta fara bude coolers tare da kaɗa kai cikin gamsuwa da abin da ta gani ta ce. "Sannu, idan kin gama da nan ki shiga store akwai ruwa da lemo ki sa a fridge dan na ciki ya ƙare."
A gajiye Nazli ta amsa mata, tana gamawa kuwa ta shiga store ta dauki ruwa park daya da lemo pack daya ta jera a fridge. Sai a lokacin ta samu lokacin sararawa, can bayan kitchen inda ɗazu ta zauna ta sake komawa ta zauna. Tana nan a ka ƙira sallan azahar, ta tsaya bakin famfo ta daura alwala ta shinfiɗa ɗankwalin kanta a wajen ta yi sallar ta.