Page 21/22
💫MARYAMA💫
Typing📲
Episode 21/22
By
(Ummu Fadeela).
Tsayawa na yi ina ƙarewa gidan namu kallo wasu zafafan hawaye su na gangarowa saman fuskata,a hankali na juya na nufi hanyar fita.....Taku ɗaya na biyu na ji an riƙe hijabi na ta baya,dum dum dum haka kirjina ke bada sound kamar zai faɗo ƙasa.
"Ina za ki je da dare haka ba ki tada ni na raka ki ba?,ke bakya jin tsoron dare ne?".
Muryar umaimah ta da ki dodon kunne na,Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un,na ke ta nanatawa a raina," umaimah why now?". Da kyar na yi gathering courage na juyo ina É—aura fake smile saman fuskata, muryata ta na makyarkayata na ce, "ehmm ammm ehhh umaimah toilet zanje me ya hanaki bacci,? da ba ki fito ba ai".gaba É—aya na birkice kallo É—aya zaka min ka fahimci zallar rashin gaskiyar dake tattare dani.
Bacci ne ba bu a idona thats why"cewar umaimah tana kamo hannuna, kamar raƙumi da akala haka na bita har bakin randunan Innarmu ta tsugunna ta ɗauki buta kana ta miƙamin ta na ɗan murmushi ta ce, "Kin manta ba ki ɗauki buta ba amarya,and can ne hanyar bayin ba inda kika nufa ba, kodai duk fargabar haɗuwar ku da hamma jay gobe ne ya fara rikita ki tun yanzu?" ta faɗa ta na ɗan sakin karamar dariyar da iyakarshi leɓenta.
Girgiza kai na yi cikin rashin sanin abin yi na karbi butar na shiga bayi...kasan hijab nata umaimah ta kama tana share wasu hawayen da suka silalo mata a ranta ta na mamaki halin Maryama,ba dan ta gano take-takenta ta ƙi yin bacci ba da yanzu shikenan tafiya fa zata yi,Hasbunallahu wani'imal wakeel...jin shirun ya yi kamar an tsikare ta umaimah ta kwasa a tamanin ta nufi toilet ɗin tunawa da ta yi kar fa ta kama katanga ta gudu.kicibis suka yi bakin kofar umaimah ta na sa kai ita kuma ta na fitowa, a razane ta koma baya ta na zaro ido ga mi da faɗin mene ne umaimah?.
"Babu komai fa, kamar kyankyaso ne ya hau min ƙafa shisa na tsorata"...."Allah har kin tsorata ni nima,"
"To a yi hakuri amaryar gobe,zo mu koma ɗaki kinsan ba'a barin amare su kaɗai, still na yi a wajen ban motsa ba saidai idanu na dake karewa umaimah kallo duk da cewa dare ne yayinda kirjina ke luguden bugu, a mamaki na kuwa na kasa yin ko wani irin tunani,ji na ke kamar ƙwaƙwalwata ta zama blank...ganin na tsaya kamar statue ya sa Umaimah kamo hannuna yanzu ma ta jani har cikin ɗakinmu ta maida ni kan gado inda na tashi tunda farko, ina zama na ji wayar da ke jikina ta ɗau vibrate,rumtse idanu na yi da karfin gaske dan na san Siyama ke kira na.
A ɓangaren Siyama kuwa tun tana tsaye ta na jiran Maryama har ta nemi waje ta zauna,ga sanyin da ake tabkawa ga tsoron da ke shigar ta na dare bata jin motsin komai sai kukan dabbobi da tsuntsaye mabanbata sauti.sa ke ƙiran layin Maryama ta yi a karo na barkatai amma no answer, "Me yarinyar nan ta ke nufi ne?,...ai wallahi ba ki isa ki ja min asarar dubu ɗari biyar ba a na zaman lafiya,yanda na ƙwallafa rai a kan kuɗin nan sai na cisu wallahi, kuma na san wannan so min taɓi ne yadda oga ya kwallafa rai a kankin nan,".Sake gwada layin ta yi wannan karon matar mtn ce ke sanar da ita layin a kashe yake."What the f**k"cewar Siyama ta na kallon screen na wayar ta, da hanzari ta miƙe ta kama hanyar gidan su Maryama. (niko na ce ayye karfin hali, ko mai zata je ta yi gidansu pretty da tsohon daren nan?).
Baifi ta ku goma ta yi ba ta ji haushin kare a bayanta,a zabure ta juya za ta gudu ta ji wani haushin ta gabanta kamun ta ankara ta fara jin haushin karnuka ta ko ina kamar ta shigo kejinsu, a ɗari da tamanin siyama ta fara gudun ceton rai, karnukan ma ba su yi ƙasa a guiwa ba suka rufa mata baya.Gudu Siyama ke yi kamar na famfalaƙi ga dare ga duhu ga tsoro da fargaba,garabb ta ji ta bugi wani katon dutsi sama sama ta yi ta faɗo ribbb a ƙasa hakan ya ba karnukan daman wuceta,wani irin marayan kuka ta sake jin wani irin azaba ya ziyarci kwanyar ta, ta ke hakorinta na gaba guda ɗaya ya faɗi ƙasa duk da azabar da ta ke ji haka ta miƙe ta ƙara ƙaimin gudunta ba ta yi aune ba ta ji ta afka cikin wani ƙaton rami dake gabanta,wani irin wari ne ya ziyarci hancin ta,kana wani kalar ruwa ya cika mata baki, ashe lambatu ne mai cike da ruwan dauɗa hajiya siyama ta faɗa a ciki lokacin da ta ke gudu. wannan karon ma da kyar ta fitar da kanta daga lambatun tana tafiya cikin dingishi sai sa'a ma idan bata samu dislocation a guiwar kafa ba tsabar azabar da ta ke ciki, da kyar Siyama ta kai kanta gida, da ya ke ita ke mulkar iyayen su kuma bayinta, kamar yadda ba wanda ya san fitan ta, haka ba wanda ya san dawowar ta, tana shiga ɗakin ta ta faɗa bathroom ta haɗa ruwan zafi cikin dauriya ta gasa jikinta mai kyau, madubi ta kalla ganin ba hakorinta guda tayi saurin rumtse idanunta ta na jin wani irin tsanar kanta, a gefe guda kuma ta na tunanin irin sakamakon da zata tanadarwa Maryama.kafun wani lokaci zazzabi mai zafi ya rufe siyama sai makyarkyata ta ke akan gado ita kaɗai, ta yi kokarin laluben wayarta amma bata gane ba, ta na ma tunanin ta yar da ita a hanya ne.....
..................+++++....................
Yadda na ga rana haka naga wannan daren ba tare da na rintsa ba nayi kukan zuci da na bayyane marar sauti, kukan da na kwana yi shi ya haddasa min ciwon kai mai tsananin gaske da har bana iya ganin abu mai kyau sai dishi dishi.ga wani irin nauyi da kaina da kirjina suka yi tamkar an danne su da dala da gwauron dutse, da wannan yanayin na wayi gari da asuba ma a zaune na yi sallah shima ina idarwa na kwanta a nan saman abun sallar. a hankali na ke jin duniyar ta na sauya min wani irin sanyi yana shiga duk wata hudar gashi dake jikina, ko wacce second na bugawar agogo tana bugawa ne ta re da tunanina na kubcewar wata dama da nake da ita, kana ko wacce second tana wucewa ne tare da kusantowar wani al'amari mai girma a rayuwata, ya kamata mai karatu ya sani, ba wai hamma jay ne a karan kanshi bana so ba,a'a yanayin talaucin da ya ke ciki ne ba naso.
Haba mana na taso cikin talauci sannan in yi aure cikin talauci duk da kyau da na ke dashi? Inna lami ce ta zo ta tada ni daga kwancen da na ke, sama sama nake jin abin da ta ke faÉ—a kamar daga nesa ta ke min magana, jijjigani ta yi tana faÉ—in, "Lafiya kike kuwa Maryama,? ga ruwan wanka can an haÉ—a wuce muje a miki wanka"
Umaimah ce ta shigo ɗakin sai warin hayaƙi ta ke yi, tun asuba dama suka shiga cikin masu aikin girki su na ta aikace aikace, ta na murmushi da salon tsokana ta ce, "ta zama ta zama ta zama woo ta zama ɗauko rig,...." kafun ta gama na fashe da wani matsanancin kuka, dama mai neman kuka ne aka harbeshi da kashin awaki.
Inna lami ce ta ce, "ke umaimah ba ni son tsokana yaushe ta zama wani abu,"maza wuce ki fitar mata kayan da zata saka idan mun fito wankan sannan ki haÉ—o mata abun breakfast da wuri kinga lokaci yana tafiya ga mutane sun fara taruwa amarya bata yi wanka ba."
Ƙeyata inna lami ta tisa gaba muka fito, aikam gidan namu danƙam yake da mutane ta ko ina sai hada hada ake yi Innarmu dai ban ganta ba, kodan dishi dishin da nake ganin kowa ne ban sani ba, kaina a kasa muka shiga bayin yauma ita ta min wanka ta sille ni tas, na dawo ɗaki,duk yadda umaimah ta so yiman light makeup ƙi na yi, da ace ta san irin haushin da take bani ko inda na ke bazata matso ba, amma ita ba ruwanta sai wani rawar kai ta ke yi.kaya kawai na sanya na kwanta ko mai ban shafa ba, sanyi na ke ji sosai yana shiga jikina, duk magiyar da umaimah ta ke min na in tashi inci abinci ƙi na yi, ba don bana jin yinwa ba sai don jirin da ke kwasata, ina daga kwance bansan ta fita ba sai shigowar su ita da daada na ji,rarrashina daada ta dinga yi har na tashi nasha ruwan shayi kadan da shinkafar da aka dafa shima baifi spoon uku na ci ba na fara kwarara amai a wajen..
Ina kwance har kusan sha daya na safe, aman da nayi ɗazu ya ƙara bada gudunmawa wajen rashin kuzarin da na ke tattare dashi a yanzu, jikina yayi zafi zau kamar ana hura wuta ta ciki.
.....................................
A massalacin dake anguwar mu za'a ɗaura auren dan haka anguwar a cike take danƙam da mutane matasa sa'annin hamma jay da dattijai da kuma yara, can na hango Jabeer cikin wani rantsatstsen getzner fara sol sai maiƙo ta ke yi, babbar riga da yar ciki da wando, ya murza hular dara sai walkiya take yi, ba shakka Jabeer ya yi kyau a wannan rana fuskarshi ta yi fayau ya dan faɗa kaɗan sai fara'a ya ke yi tamkar mai tallan closeup...zagaye da shi abokanshi ne da sauran yan uwa da abokan arziki da suka hallara don shaida wannan daurin auren dake cike da soyayya mai daɗaɗɗen tarihi,can gefe kuwa baffanmu ne da abokanshi su baban umaimah sai liman da sauran dattawan anguwa.baffanmu ne wakilin Jabeer, sai liman da ya zama waliyyin Maryama.
Bugawar agogo karfe sha ɗaya ya yi daidai da bugawar zuciyata da karfin gaske wanda ya sanya ni mikewa da sauri daga kwance da na ke zuwa tsaye, a lokacin ne kuma na jiyo muryar wani maroƙi ya ratsa loudspeaker zuwa cikin kunnena, " Alfatihaaaa, an ɗaura auren Jabeer da amaryarsa Maryama akan sadaki.......laƙadan ba ajalan ba, mu ƙara yiwa Annabi salati, (S A W).
Take na fara jin ɗakin yana juya min, sautin guɗar da mata keyi a tsakar gidan na fara jiyo shi kamar ihu, a hankali ji na ya fara ɗaukewa, duhu ya fara mamaye gani na cikin ƙasa da second biyar na sulale ƙasa sumammiya........ ..