Page 23/24
💫MARYAMA💫
BY
Ummu Fadeela.
Typing📲
Episode,23/24.
A hankali na buɗe idanuna waɗanda na ke jin su tamkar bishiyar da ta kakkafa rassa, ɗakin na fara bi da kallo duk da kamar dare ne hakan bai hana idanuna sauƙa a kanshi ba, yana zaune bisa farar kujera sanye da kayan da ya je ɗaurin aure da su, sai dai babu babbar rigar yar ciki ce kawai da wando hannunshi riƙe da hula kanshi ya ɗan karkace kaɗan bisa kafadunsa, idanunsa rufe da alama bacci ne ya ɗauke shi ba tare da ya shiryawa hakan ba.
Fuskarsa ta faɗa ta yi fayau sosai sai wani haske da ya yi. Daga can gefe kuwa Inna lami ce ƙanwar Innarmu ta ke sallah sai baaba fa'iza yayar mamar su hamma jay ta na zaune bisa wani gado dake ɗaya bangaren ɗakin ta yi tagumi da hannu biyu.
Dogayen hannayena da ke ɗauke da canulla na bi da kallo, a hankali na ke jin tafiyar ruwar da aka maƙala min yana bin jijiyoyina zuwa cikin jikina wanda ke alamta min cewa asibiti na ke, ta ke abubuwan da suka faru har ya haddasa min ɗaukewar numfashi ya shiga rige rigen dawo min cikin ƙwaƙwalwata, gefen yatsa ta na sa na share wasu hawaye da suka gangaro min cikin idanuna zuwa kan filon da na ke kwance a kai...
Ɗan motsin da ta yi ne ya farkar da jabeer da dama baccin nasa bai je ko ina ba tsabar stress, suna wajen reception da za suyi na ɗaurin aure ya samu mummunar labarin cewa pretty ta faɗi a sume a na ta yayyafa mata ruwa amma ko motsi batai ba,ai bai jira ya gama jin labarin ba ya nufo gida hankali a tashe, isowar shi kuwa ya zare babbar rigar shi ya cicciɓi maryama sai asibiti inda inna lami da baaba fa'iza suka rufa masa baya, da gaggawa likitoci suka amshe ta a ka fara bata taimakon gaggawa da kyar suka yi nasarar janyo numfashin Maryama da yayi nisan zango saida aka tabbatar da ta zama normal sannan suka mata allurar bacci daga bisani aka turata daƙin marasa lafiya, tunda suka zo jabeer ke tsaye bisa kafafunsa ya kasa zaune, dole ka tausaya masa yadda ya zama shima kamar mara lafiya har yanzu da ya kasance karfe bakwai na dare sallah kawai ke matsar da Jabeer daga kusa da Maryama
Ba yadda su inna lami da sauran yan bikin da suka biyosu daga baya basu yi ba akan ya je gida amma jabeer ya kasa tafiya, yana ganin kamar idan ya matsa wani abu zai faru da maryamar shi.
"Pretty kin ta shi? me kike so kici yanzu? akwai inda ke miki ciwo ne? ko in kira likita ya zo ya ganki?."
Waɗannan sune jerin gwanon tambayoyin da hamma jay ke jero min fuskarshi ɗauke da tsananin kulawa da tausayawa kana da zallar soyayya mara algus, har cikin raina ya bani tausayi dan haka ban san sadda na fashe da kukan da ni kaina ban san dalilin yinsa ba....Kuma rikicewa ya yi yana faɗin "ina ke maki ciwo pretty? ko in kira likita? ki daina kuka mana karki ƙara wa kan ki wani ciwon kuma, gaba ɗaya ya fice a cikin nutsuwarsa, ji yake kamar ya maida ciwon jikinsa a gefe ɗaya kuma kukanta na ƙara tayar masa da hankali.
Dafa goshina baba fa'iza ta yi tun maganar da hamma jay ya yi da farko ta taso ta matso garemu. "Sannu yata, ki daina kukan haka, Jabeer maza kirawo likitan dan ya shigo É—azu ta na bacci" ta faÉ—a ta na kallon jay, bai jira ya gama jin abin da ta ke faÉ—a ba ya nufi waje da hanzari.
Kicibis suka yi da likitan yana shigowa don haka jabeer ya koma baya ya ba shi hanya, da fara'a irin nasu na likitoci cike da barkwanci ya ce, "a'a kaga ango, bada kanka a sare kaje gida kacewa amarya ya faÉ—i, amaryar ta mu ta farka ne?."
Murmushi ne ya kubcewa Jabeer ba tare da ya shirya ba, haka kuma baice komai ba, dan shi kaÉ—ai yasan abin da ke damunshi a jiki da zuciya...
Ƙarasawa gaban gadon dr ya yi, ya ɗan dudduba Maryama abun gwada bp ya fitar ya gwada ta ya na kallonta ya ce, amarya a dinga rage damuwa Allah ya ƙara sauƙi, da hannu ya yiwa jabeer alamar ya biyoshi zuwa office,suna fita inna lami ta idar da sallah ko addu'a batai ba ta taso gareni tana jeramin sannu itama.
Da kai na amsa mata sannan cikin dabara na kai hannuna cikin bra ɗina, dan wannan tunani ke man yawo tun ɗazu... wani irin ajiyar zuciya na sauƙe jin na taɓa wayar Alhmdllh tana inda na maƙala ta bata faɗi ba.
Bayan shiru na kimanin minti biyu likitan na ƴan rubuce rubuce cikin wani takarda ya ɗago ya kalli jabeer ya ce, "ku kwantar da hankalinku jikinnata da sauƙi sosai, sai dai jininta ya na ƙoƙarin hawa kuma hakan ya bani mamaki matuƙa because ta yi ƙanƙanta dayawa dan haka ku dinga kiyaye bacin ranta, zuwa gobe za'a iya baku sallama Insha Allah..."Ƙuri jabeer ya ma likitan da idanu ba tare da ya samu zarafin cewa komai ba, zuwa can ya yi karfin halin cewa, "dr. nima inaso ka duba min nawa bp ɗin".
Kallonshi likitan ya yi ya ce, "akwai wasu alamomim da kake ji ne?"
Jinjina mishi kai ya yi, janyo abin gwajin dr yayi ya ɗaure a tsintsiyar hannun jay ya fara gwada shi, bayan wasu ƴan mintuna ya cire haɗi da dafe kumatunshi da hannaye biyu sannan ya ce,"meke damunku ne kai da amaryar taka? gashi nan kaima jininka ya hau fiye da ƙima and your condition is not encouraging karka manta da halin da kake a ciki, kuma na ga kana wasa da karɓar magani akan lokaci Jabeer ki....."
Katse shi Jabeer ya yi da sauri ta hanyar faÉ—in, "Na gode dr, what next yanzu?
Rubutu ya yi kaɗan saman wani paper ya miƙa mishi yana gyara zaman glasses na shi ya ce, "kaje pharmacy a baka wannan, kuma ka dinga ƙoƙarin ganin ka ragewa kan ka damuwa karka manta da health status naka, tun bayan da aka cire maka kidney guda ɗaya, ga ɗayar ta fara bushewa and kana wasa da magani Jabeer ka dinga kulawa shi rai guda ɗaya ne fa, idan ya fita shikenan".
Hannu jabeer ya miƙawa dr bayan ya miƙe sukayi musabaha ya fita.Tun bayan da Jabeer ya donating wa Maryama ƙodar shi guda bai daɗe ba ya fara wani irin rashin lafiya a tsaye amma bai faɗiwa kowa ba lokacin yana university abun ya ci karfin shi saida aka kaishi asibiti a hannu nan likitoci suka tabbatar da ƙadar shi ɗaya ce kuma ta fara samun matsala, an daura shi akan medication ba laifi ya ji daɗin amfani da su har dawowar shi gida idan abun ya tashi mishi yakan je ya ga likita ba tare da kowa ya sani ba. ...
Lokacin da ya dawo ɗakin ina zaune kan gado da pillow a bayana hannuna riƙe da kofin shayin da inna lami ta haɗa ta kuma tilasta min sha, haɗa idanu muka yi dashi ya sakar min lallausan murmushi, gabana ne ya wani irin faduwa har na kusa sakin kofin dake hannuna, amma na yi saurin damƙewa.
"How you feeling now pretty?."
Ya tambaye ni lokacin da ya iso saitin gadon da nake kai." da sauƙi na faɗa ba tare da na yadda mun haɗa idanu ba dan wani irin kwarjini na ga ya min yau ɗin, juyawa ya yi yaiwa su inna da baaba sannu sannan ya janyo kujera ya zauna ya jinginar da bayanshi da lumshe idanu, samun kaina na yi da kasa barin kallonsa tabbas akwai abin da ke damunsa dan ba ɗabi'ar hamma jay ba ne zama shiru musamman in ya kasance ina wajen...
Yana zaune É—akin har wajajen 11 na dare sannan inna lami ta sa baki ya koma gida.
Washe gari aka sallamo ni muka dawo gida, yawancin yan biki sun watse sai ɗaiɗaiku da kuma tawagar daada, faɗa baffanmu ya dinga yi wai me aka kawo ni in masa a gida,? gidana za'a wuce dani ai, saida Daada ta sanya baki sannan ya haƙura a miƙani zuwa dare,...duk abun da aka sanyawa lokaci tabbas zai zo sai dai mune bamu da tabbacin kaiwa lokacin...
Ko motsin kirki ban yi ba naji har isha ta yi, ana idar da sallah kuwa aka sani ƙara yin wanka na shirya cikin wani haɗaɗɗen leshi coffee colour mai touches na cream colour cikin kayan da inmarmu ta dinka min na fitar biki, riga da zani sai ɗankwali da umaima ta ɗaura min nidai binta kawai nake yi duk ta yadda ta juya ni kamar mutum mutumi, su uku ne suka rage cikin ƙawayena da zasu min rakiya, ba shakka na yi kyau matuƙa tamkar ka sace ni ka gudu, ga wani irin walƙiyar da jikina keyi na gyaran da yasha hannu da ƙafafuna zane suke da lalle ja da baki mai ɗaukan hankalin mai kallo kasancewar ya samu farar fata, wani zani aka ɗaura min saman gyalen da na lulluɓa dashi ya rufe min fuskata ruff wannan karon daada ce ta riƙe ni muka fito, kukan dana ke ta riƙewa ne yayi nasarar kibce min, kuka nake yi kamar zan mutu, "dole ki koka yannan, aure yaƙin mata kana zaman zamanka da iyayenka rana tsaka a dauke ka a damƙawa wani ƙato idan ba Allah ya haɗaka da mai hankali ba duk sai ka firgice a take ka zama kamar mai shekaru ɗari a duniya, to dai bance ki raga masa ba idan ya taka ki ki takasa kema dan yanzu maza duk sun zama yan banza sai kin nuna musu kema yar iska ce zaku daidaita".
Cewar daada tana gyara zaman mayafinta tamkar ma ba abun da tace,.
Ɗakin Innarmu ta fara kaini, tana zaune a bakin gadonta, daada ta ce, gata nan dai Dijah sai ki mata nasiha, koda dai babu abun da ya rage ban faɗa mata ba, amma saboda haƙƙin zama tare gata ki faɗi wani abu a gurguje kar mu makara," murmushi inna ta yi tace , ai daada tunda kin mata nasiha basai na ƙara cewa komai ba, myaryama dai ba yarinya bace, ta san dai dai ta san akasin sa dan haka kiyi amfani da iliminki, shi aure dai ibada ne, shi ibada kuma sai an dage an jure an sanya haƙuri kamun ake yinsa yadda ya kamata.
Ba sai na tuna miki waye Jabeer a wajenki ba, duk sanda kika so sanin waye shi a wajenki, ki dubi bangaren cikinki na dama, idan kinyi da kyau kan ki idan akasin hakanma kan ki, je ki Allah ya maku albarka ya sanya farin ciki da zuriya na gari a cikin rayuwar aurenku...
Wani kukan da ya fi na farko karfi na saki na tashi na rungume Innarmu, da kyar aka bambare ni a jikinta, Baffanmu ma ya min nasiha sosai mai ratsa jiki da ɓargo...haka inaji ina gani aka fita dani zuwa gidan Hamma Jay dake kasan layinmu, yan rakiyar basu fi minti talatin ba kowa ya kama gabansa riƙe rigar Umaimah na yi ina kuka da faɗin, "Umaimah kema tafiya zakiyi ki barni,? dan Allah karki barni ni kaɗai a gidan nan tsoro nake ji".
"Ba tafiya zan yi ba pretty rakasu zan yi in dawo ki jirani yanzun nan" cewar Umaimah sakinta na yi ba don na so ba sai don yarda da ita da na yi, na koma saman doguwar kujera na zauna,..tashin hankalin da na ke ciki bai barni na ga irin kayan da iyaye na suka kashe kuÉ—i wajen sai min ba...tun ina irga mintuna har na gaji ba umaimah ba alamunta, wani irin tsoro ne ya fara mamaye ni...haka na daure na ci gaba da zama ni kaÉ—ai tamkar mayya...
A kofar gida Jabeer ya ja ya tsaya,yana kallon abokanshi da sukayo gayya zuga guda wai zasu sayan baki ya ce, "to duk na gode muku da rakiya kowa ya koma gidanshi mai mata yaje ya rungumi abarshi gwauro kuwa ya rungumi pillow ya haÉ—a da istigfari". ta ke wajen ya kaure da hayaniya har kowa baijin abinda É—an uwanshi ke faÉ—a, masu zolayanshi wai kishi ya ke nayi, masu rama gorin da ya musu suna yi daga karshe dai suka rabu a wajen shikuma ya shige gida haÉ—e da garkame kofar da sakata fuskarshi cike da farin ciki yai gashi ga pretty zasu kwana gida É—aya a matsayin ma'aurata shiko mai zaiyi ya tabbatar da godiyar shi ga ubangiji?.
Da murmushi ya iso bakin kofar palon dake ta kamshin sabon fenti da sababbin furnitures...Ina zaune saman doguwar kujerar har lokacin gabana sai dukan tara tara yake yi ba tare da wani dalili ba, ban yi aune ba naji wayar dake maƙale cikin jikina ya fara vibrate, da sauri na fitar da shi zaro ido nayi kirjina na luguden daka ganin mai kirana, "SADEEQ?" Na faɗa da ɗan sound kaɗan ina ci gaba da zare idanu hakan kuwa yayi daidai da shigowar hamma jay hannunshi ɗauke da wani katon leda baƙa, wani irin hantsilowa nayi daga saman kujerar na koma edge na ɗakin ina ɓoye hannuna dake riƙe da wayar a bayana jikina yana rawa kar kar kamar naga dodo, ajiye ledar Jay yayi sannan a hankali ya fara takowa zuwa inda na ke.........