MARYAMA

Page 27/28

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

                            BY 

                   Ummu Fadeela

Typing📲

Episode 27/28.....


Yatsar shi manuniya ya ɗaura saman leɓena idanunshi a lumshe ya furta, "Shhhsshhshttt, bacci pretty".

Daga haka bai ƙara bani damar yin magana ko kuka ba ya rufe idanunshi gam haɗi da matse ni sosai tamkar dai zai maida ni ciki ko mai tsoron kar wani ya kwace masa ni. da haka bacci mai cike da nishaɗi da annashuwa ya ɗauki Jabeer yayin da ni kuma kamshin turarensa na oud essential ya cika min hanci ya hanani nutsuwa gefe guda kuma irin riƙon da ya min da ko numfashin kirki bana iyawa.tunani ne suka min rubdugu nima bansan sanda bacci ya ɗauke ni ba.....

Sauƙar numfashinta a hankali ne ya tabbatarwa Jay cewa ta yi bacci, a hankali ya ɗan sassauta riƙon da ya mata yana gyara mata kwanciya yadda zata zama comfortable, still kanta yana saman damtsen hannunsa suna fuskantan juna, addu'a ya yi masu su duka sannan ya gyara masu duvet ɗin kana ya cigaba da shafar gashin kanta wanda yana cikin abin da ke burgeshi a gun ɗiya mace, balle na Maryama da ya kasance na musamman,da haka bacci na gaske mai cike da mafarkai barkatai ya ɗaukeshi....

A hankali ya fara buɗe idanunshi sakamakon hasken rana da ya ɗan shigo ta window ɗin dakin,da sauri ya gama buɗe idanun yana mai tasbihi da tsarkake sunan Ubangiji ganin karfe shida ta yi, Jabeer zai iya cewa tunda ya mallaki hankalin kanshi sallar asuba bata taɓa kubce masa ba matuƙar yana halin lafiya sai yau...idanunshi ya sauƙar a kanta, tana kwance a jikinshi kamar yadda ya sakata tun jiya bai jin ko motsi ta yi,hannu ya sa ya shafa saman fuskanta yana ɗan murmushi kaɗan kaɗan,a can kasan maƙoshi ya ce, "Pretty!"

Mar mar ta farayi da idanu, tun kiran sallar farko idanunta ke buÉ—e sakamakon sabo da tayi na tashin asuba suyi sallah a gida da kuma baccin rashin sukunin da tayi, sai dai yadda zata tashi daga jikinsa ne ya zame mata matsala dan wani irin masifaffen kunyar shi takeji.

Zare hannunshi ya yi daga kanta a hankali ya fara kokarin miƙewa,jin ya sake ta Maryama tayi wani irin juyi sai gata a karshen gadon,kamar rufe ido ta miƙe da sauri ta sauƙa saman gadon ta maƙure jikin gini tana ta zare ido kamar tayiwa sarki ƙarya, dogayen laps nata farare sol Jabeer ya bi da kallo dariyan abin da tayi na cinsa amma ya danne, bin inda yake kallo na yi da ido....zaro ido nayi gami da kwalla ƙara da karfi na durkushe a wajen ina haɗe jikina waje ɗaya....Jabeer could'nt help it sai da ya yi dariya,sannan ya miƙe ya fita ɗakin ganin matuƙar ya ci gaba da zama sai 8 zaiyi sallah.

A gaggauce ya cika bokiti da ruwa da kuma babban buta ya shiga bayi. Sai da ya gabatar da uzurinsa sannan ya yi wanka kamar yadda ya saba safe da dare kana ya janyo butar ya fara wankan tsarki baiyi niyyar kusantar ta ba har sai ta saba dashi kuma ta amince masa, amma yana son ya cire kunya a tsakaninsu dan samun happy home shiyasa yai mata abin da yai jiya,sai dai da ƙyar ya iya controlling kanshi....


Babban towel da ya shiga dashi ya ɗauko gami da goge jikinsa ya saka wata boxer daban ya fito,yana shiga ɗakin fittt ya ga gilmawarta ta fice a guje kamar walƙiya shafa kanshi ya yi yana ɗan murmushi,.....har Jabeer ya idar da Sallah Maryama bata shigo ba, ita ko tana maƙure bakin kofa ta ɗauro alwala tun ɗazu amma ta rasa yadda zata shigo dan wani irin kunyar shi da take ji mai haɗe da ɗan tsoro tsoro.

Da hanzari jabeer ya cire jallabiyar da ya yi sallar ya rage daga shi sai singlet da boxer ya na ƙoƙarin fitowa ita kuma ta yi shahadar kutsa kanta cikin ɗakin,karo suka yi ba tare da kowannensu ya kula ba da hanzari ya riƙo ta ya bata wani irin hug yana sauke ajiyar zuciya, hannunshi ya ɗaura saman gashinta duk da sanye take da hijab babba, ya na shafawa murya a shaƙe ya ce, "Morning my angel how was your nyt?hope you enjoy it?".

A hankali yake maganar kuma kusa da kunnena, ga riƙon ba zatar da ya min hakan yasa jikina sakewa sai dai duk da mutuwar da jikina ya yi na Hamma Jay ya fi nawa dan yadda muryarsa ta koma da yadda kafafunsa ke rawa suna son kaimu ƙasa.

Da wannan raunin da ya samu na yi amfani yana gaf da ɗora bakinsa saman nawa na hankaɗa shi na shige ɗaki a guje na maƙala sakata dan na san ko na sa makulli a banza ne zai buɗe kamar dai jiya. Zama na yi a bakin gadon ina sauƙe numfashi sama sama tsakanin jiya da yau duk sadda hamma Jay ya taɓa jikina sai in riƙa jin tamkar an jona mun electric shock haka kuma gabana ya dinga faɗuwa, the worst part of it kuwa shi ne I like the feeling da na ke ji duk sanda muka samu body contact ɗin, ya Salam! na faɗa ina dafe goshi na.....

Jabeer dake jin kanshi yana yawo a sararin samaniya, baiyi aune ba yaji ta tureshi akayi dace kuma gaba ɗaya karfin shi ya koma kanta hakan ya sa ya yi baya baya ya faɗa saman kujera mai zaman mutum ɗaya dake gefensa da gudu ya ga shigewarta ɗaki. Ba haka yake so ba so ya ke suyi zama mai aminci zama mai cike da shaƙuwa da soyayya. Bai son yadda take nuna ta na jin tsoron nan nashi ko kaɗan. Amma ta ya zai cire mata tsoron? ɗan murmushi ya yi yana shafa kanshi jin wani tunani ya faɗo mishi a hankali ya kwantar da kanshi jikin kujerar haɗi da lumshe idanu. Sauri ya ke dama yanason yin exercise ko kaɗan ne amma gabaɗaya Maryama ta kwance mashi notinan jikinsa bai jin zai iya taɓuka wani abin azo a gani ko da ya fita ma.

Jabeer na zaune a wajen doing nothing bai san iya adadin minutes da ya kwashe ba ya jiyo sallamar fatima, sai da ya maida jallabiyarsa sannan ya amsa labulen palon ta É—aga haÉ—i da shigowa bakinta É—auke da wata sallamar.

"Ina kwana Hammanmu,"

Cewar Fatima lokacin da ta ke duƙawa kasa.

"Lafiya lau Fati ya su Innarmu, ina baffa da su daada? Ya amsa haÉ—i da tambayarta fuskarshi É—auke da murmushi.

"Duk lafiyansu. Innarmu tace in kawo muku abin karyawa ta faÉ—a tana matso da kular da ta shigo dashi tare da tea flask....

Still smiling Jay ya ce, "ki ce da Innarmu mun gode miƙewa Fati ta yi har ta kai kofa sai kuma ta juyo ta ce, "Hamma Jabeer Ina antynmu?".

"Antinku ta na wani aiki kaÉ—an a ciki idan ta fito zan faÉ—a mata kin zo".

Da "to" ta amsa kana ta ta koma gida...Buɗe food flask ɗin ya yi yaga doya ce aka soya da kwai sai kamshin spices ke tashi tea flask ɗin kuwa tea ne a ciki as he expect shima sai tashin ƙamshin su ginger ya ke yi. A gefe ya musu mazauni ya daga ledar jiya da dare da ba wanda ya taɓa ya fitar da kayan shayin suma ya ajiye a gefe ledar kazar kuma ya fita da ita zuwa kitchen. Girki ba baƙon abu bane ga duk ɗan talakan da ya je jami'a, dan haka Jay ya fara ƙoƙarin warming kazar luckily kuma da akwai stove mai cike da kerosine a cikin kitchen ɗin da Innarmu ta siyawa Maryama komai yana zaune a muhallinshi dan haka kunnawa kawai ya yi haɗi da ɗaukan karamar tukunya ya ɗaurayeta sannan ya jefa kazar a ciki.....Bayan mintuna kaɗan ya samu plate ya juye yasa wata ya rufe saman namar ya shigar ɗaki ya kuma dawowa ya ɗauki wata tukunyar madaidaici ya cika da ruwa ya mayar saman stove ɗin ya rufe wasu plate din guda biyu, fork, knife, da kuma cup ya dauka suma ya shigar ɗakin....anan tsakar ɗakin ya jere komai yadda ya ke so sannan ya nufi bakin kofar murya ƙasa ƙasa ya ce.

"Pretty fito kiyi breakfast gashi nan Innarmu ta turo mana favourite food na ki" Ina zaune bakin gado bayan na gabatar da sallah counter ce a hannuna ina azkar duk abin da ya ke ina jinsa lokacin da Fati ta shigo ji nayi tamkar in fito in rungume ta amma na kasa saboda tsoro da kunyar hamma jay da nake,...sosai ya Jabeer ya ke ma ta magiya kan ta fito su karya amma ko gezau Maryama ba ta yi ba kasancewar yana son zuwa can gida kafin Baffanmu ya fita yasa shi dawowa kan breakfast ɗin ya ɗeba komai yadda zai iya ci ya haɗa shayi ya fara karyawa a ransa yana aminta da shawarar da zuciyar shi ke bashi wanda ya ke ganin ita ce hanya ɗaya tilo da zai cire wannan tsoron a tsakaninsu. A gurguje ya gama ya maida kayanshi da ya cire jiya dan ba wasu kayan a nan dole sai ya je gida ya ɗauko akwatinsa bakin kofar ya kuma dawowa pleadingly ya ce, "Plsss Pretty ki fito ki yi breakfast ni fita ma zanyi don Allah karki zauna da yunwa plsss wife ya ƙare da sassanyan muryar da wanda ya taɓa tsintan kanshi a irin wannan bahagon soyayyar ne kawai zai iya karantar abin da ke zuciyarsa.

Har ya juya xai fita sai kuma ya dawo cikin nutsuwa ya ce, "Da akwai ruwan wanka a kan stove na ɗaura miki kar ki manta dashi kero ya ƙare, ki fito plssss ni zan fita yanzu, byeee take care of your selfff.

Tun da ya fara magana na ajiye counter ɗin hannuna ina jinsa amma na kasa furta komai time da ya ce ya ɗaura min ruwan wanka a take naji idanuna sun cika da hawayen da ban san dalilinsu ba, ba tare da na shirya ba hawayen suka fara sauƙa haka kuma banyi tunanin sharesu ba, inajin fitar shi kusan da minti ishirin still ina zaune ga wani irin yunwar da ke kwaƙular yan hanjina ba dan na shirya ba na fito. Komai yana nan yadda ya barshi da sauri sauri na haɗa tea mai kauri na ajiye gefe na ɗauki doya yanka biyu hannuna yana rawa na bude plate ɗin kazar dake ta tashin kamshi. Duk da dai ta fara sanyi amma ban kula ba na fara mata cin yunwa ina bi da shayi Kamin in ankara sai kasusuwa na gani dan haka ban samu cin doyar ba na mayar cikin kula.

Kwanukan na tattara na fitar inda aka tanada musamman dan wanke wanke a gefen kitchen nan na ajiye su kular doya da ta shayin kuma na mayar kitchen na adana. 


Ganin ruwan da ya É—ora sai tafasa take yasa ni juyewa a babban flask na Æ™ara É—ora wani. Baho na É—auka da kwando nazo na wanke yan kwanukan da sukayi datti na shigar na jere komai yadda ya kamata sannan na dawo É—akin duk da babu datti na É—an kakkaÉ“e sama sama na fesa freshner take ko ina ya É—auki kamshi. Ina turo baki gaba na É—aga farar jallabiyar shi dake tashin kamshin mayataccen oud dinnan na linke kana na sama mashi wajen zama a bedroom. 


Sai da na tabbatar komai ya min yadda na keso sannan na je na juye ruwan na shiga wanka,....lokacin da na fito har shabiyu ta kusa mai na shafa da ɗan turare sama sama na shirya cikin riga da siket na wani atamfa blue black sosai farar fatata ta haska aciki, tunanin Sadeeq da Siyama na maƙale a raina kana gefe guda kuma tunanin inda hamma jay ya tafi nake yi.

A hankali na É—aga gefen katifata na É—auko wayar, ina Æ™oÆ™arin kunnata dan kiran Sadeeq naji ana kwaÉ—a sallama a waje da hanzari na Æ™ara turata kasan gadon na fito ina amsawa wasu mata ne su biyu da yaransu kusan biyar suka shigo saida na isar dasu É—aki muka gaisa na fahimci ashe makwafta ne suka shigo ganin É—akin amarya. 

Kamar sun buÉ—e kofa ne, nan jama'a suka dinga É—iÉ—É—ikowa wai da sunan ganin É—aki tuni sun É“ata min sharar da nayi, har bayan azahar wasunsu na nan musamman yara. Kamar daga sama Allah ya turo min su Fati da Salima É—auke da wata kular ta abincin rana..Fati ce tayi karfin halin korar yaran bayan ta basu sauran doyar safe da ya rage da tea tare muka ci abinci da yan Æ™annena da nake ji tamkar na shekara ne ban gansu ba. 

Bayan mun gama salima ta wanke kwanukan da muka ɓata fati kuma ta hau shara da mopping har da su kunna tiraren wuta a burner take gida ya ɗau kamshi da walkiya sak na amarya, a bakin su fati na ke jin wai hamma jay sun fita da baffanmu wani waje tun da safe har fitansu basu dawo ba....sai maghrib su fati suka tafi suka barni cike da kewa Duk yadda na so su tsaya sai ya dawo ƙi suka yi da dabara ma suka gudu na shiga wanka lokacin a darare na shige ɗaki da zan murza makulli naga wayam sakata ma an cireta, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un na furta ina zare ido.

Wa ya taÉ“a kofar nan,? ko dai akwai aljanu a gidan nan. Zaro ido nayi na dawo palo da gudun gaske, sai dai bazan iya fita waje ba da kyar na gabatar da sallar maghrib wacce bansan ko abin da na karanta a ciki ba tsabar yadda nake tsorace ina cikin wannan halin aka kira isha shima na gabatar ba tare da ina cikin nutsuwa ba. 

Wani irin kuka ne ya kwace min na fara kukan a hankali hankali cike da tsoro na jima ina kuka har kaina ya fara ciwo sosai amma ba Hamma jay ba dalilinsa. Wajajen karfe takwas na dare ya nufo gidan hannunsa ɗauke da ledar kazar da ya siyamata da kuma fresh milk, a ransa yana tunanin wane hali ta ke dan yasan Maryama da ɗan karen tsoro kamar farar kura, ana sallar isha suka dawo daga inda sukaje da baffa tafiya mai cike da nasara cikin farin ciki ya shigo gidan dake mamaye da duhu dulum wayar hannunshi ya haska lokacin da ya iso bakon kofar palon, wani irin ƙamshi ne ya ziyar ci hancinshi gefe ɗaya kuma ya na jin sheshshsekan kuka sama sama,da hanzari ya faɗa palon yana dallare tocin wayarshi,tana maƙure jikin kujera akan sallaya idanunta sunyi jawur tsabar kukan da ta ci,."Pretty" ya ambata da ɗan sanyin murya kaɗan, tun da ya haska toci ta kara damƙe jikinta dake rawa waje ɗaya tana ayyana shikenan tata taƙare bataji shigowar shi ba sai hasken toci ta gani so ta ɗauka wani abune daban, jin muryarshi yasa ta tasowa da gudu ba tare da tunanin komai ba ta rungumeshi gam gam tana sakin wani sabon kuka mai cike da shagwaɓa.