MARYAMA

Page 29/30

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

                     29/30

                 BY

            Ummu Fadeela



Bayanta yake shafawa gently. Da sanyin murya mai nuna halin da ya ke ciki ya ce, "What happened pretty? ki daina kukan haka kar kan ki ya yi ciwo,..." kamar wadda ya ce ta ƙara karfin kukan ta buɗe murya tana kuka mai cike da shagwaɓa, haɗe da bubbuga ƙafafu a ƙasa, wani irin yamutsawa jinin Jabeer ke yi sakamakon taɓarar da ta ke masa yayin da yake jin ƙafafunsa suna ƙoƙarin gaza ɗaukarsa, da shaƙaƙƙiyar murya ya ce, "me ya sameki ne MARYAMA? akwai abin da ya faru bayan fitata ne? yi shiru ki faɗa min mene ne?"

Da kuka ta ce, "ba kai ne ba ka tafi ka barni kuma kasan inajin tsoro ni kaÉ—ai,"

Baya baya ya koma da ita ya zauna saman kujera ya ajiyeta saman cinyarsa. Still holding her tightly ya ce, "Sorry wife gani nan na dawo daga yanzu ban ƙara fita ko ina idan dare ya kusa kin yi haƙurin?" Ya faɗa saitin kunnena. kaina na kifa saman kirjinsa saboda wani irin kunya da na ke ji, hakan da nayi kuwa ba ƙaramin ƙara birkita shi ya yi ba, amma yayi ƙarfin halin cewa "Ohk idan har kinyi haƙuri then wipe your tears and smile ina da wani labari mai daɗin gaske da zan baki".

Da sauri na ɗago kaina ina jin wani irin excitement dan na gama sawa a raina cewa maganar makaranta ta zai min dan yanzu shi ne kaɗai labarin da zan ƙirashi mai daɗi a wajena.

Shi ya sa hannunsa duka biyu ya goge min hawayen kana ya riƙe duk kumatuna ya ce, "Bani son ƙara ganin waɗannan hawaye masu tsadar da sukafi gold daraja a wajena, ki daina zubar min su a banza kinji hayatie na?" Ba tare da na ce komai ba ya ci gaba da magana.

Yana kallon cikin idanuna still bai sake min kumatu ba ya ce, "Albishir!".

Cike da annuri da ke kwance saman fuskata da kuma zaƙuwa na son jin abin da zai faɗa na ce "Goro"

Ɗan chukling ɗina ya yi a gefen ciki, ta ke na fara dariya, ya ce, " yawwa ko kefa amma da kin haɗe rai kamar wacce zanyiwa albishir ɗin kishiya,...Murmushi na yi wannan karon har dimples nawa suka loɓa, ɗan yatsarshi ya ɗaura saman dimples ɗin gami da faɗin, "tha's my wife"....

(Nasan mai karatu zaiyi mamakin yadda ni Maryama na sake da Hamma Jay wato ya yi bala'in sanin makamar Æ´a mace a cikin zuciyata ba ni son abin da ya ke min, amma gangar jikina ya kasa janyewa daga gareshi, wannan wani sirrine dake tattare dashi da ba kowanne É—a namiji Allah ya bawa ba.)

Still looking into my eyes,ya ce, "Albishir!", turo baki na yi gaba na ce, "kai dai hamma jay ba na ce goro ba,"

Jabeer bai gajiya da kallon kyakkyawar baby face na ta dake cike da shagwaɓa, yana jin wasu abubuwa suna bijiro mashi cikin kai...Iska ya hura min a kunne ganin yadda na kafeshi da idanu ba tare da nasan nayi hakan ba.Da sauri na rufe idon ban ankara ba naji saukan wani sassanyan kiss saman idanu na, da sauri na kuma biɗewa ina ƙoƙarin tashi amma bai bani dama ba.

Cikin low voice ya ce, "Na samu aiki pretty!".

Wani irin miƙewa na yi da sauri na tsaya haɗi da ɗaura hannayena duka biyu saman bakina, tsabar murna na ma rasa abin da zance.Tashi yayi shima ya rungumeni ta baya gami da zuro kanshi ta saman kafaɗata ya ce, "Kina farin ciki ko pretty?,....nima ina farin cikin cewa na samu aiki yanzu zan iya ɗaukan nauyin karatunki dan ganin kin cika burinki,.

ÆŠan ajiyar zuciya ya sauÆ™e sannan ya cigaba da cewa, "amma baki tambaye ni wani irin aiki na samu ba? bai jira na bashi amsa ba ya ci gaba da faÉ—in, 

"Na samu aikin koyarwa a makarantar firamare, Insha Allah duk wata zamuke samun naira dubu talatin da uku kinga ai ba kananan kuɗi bane wannan ne abin da muka yini yi tare da Baffanmu a yau kuma alhmdllhi mun kammala komai,". ya ƙare da murmushi yana shafa fuskata zuwa saman wuyana.....

A hankali na fara jin wani abu mai kama da zare yana kwancewa daga cikin ƙwaƙwalwata yana bin jikina har zuwa tsakar kafata..."aikin karantarwa a firamare? dubu talatin da uku ne hamma jay ke kira da manyan kuɗaɗe a hakan ma sai yayi wata ɗaya cur sannan ya same su? 33k ai ko monthly allowances da nake fatan mijina zai ke bani bai kai ba.....A cikin kunnena ya raɗa min, "hmmm kinyi shiru baki ce komai ba,"..

Gyara tsayuwa nayi da niyyar matsawa daga wajen, hakan ya bashi daman juyowa yana shigar da idanunsa da suka sauya kamanni cikin nawa, zaro ido nayi da sauri kirjina na bugawa ganin abin da hamma jay ya fara.......

  ************--------------------************

Wannan dare dai Sadeeq a cikin ruɗani ya yishi, duk yadda ya so daure wa kasawa yayi a autoreadialling yasa layin Maryama sai kira yake duk kuwa da cewa matar nan ta MTN tana tabbatar mishi layin da yake nema a kashe take zama yayi a ƙasan rug dake bakin gadonsa ya riƙe kanshi da hannu biyu, "What's happen to me? meke damu na ne?" ya yiwa kanshi tambayar kome ya tuna kuma ya yi saurin sauƙe hannunshi yana katse ƙiran da yake ta zuba wa Maryama kana ya juya akalan ƙiran zuwa kan wani layi ya ɗaura saman kunnenshi haɗi da lumshe idanu kamar mai bacci.

____________***********______________

     FEDERAL LOWCOAST GOMBE.

         
                 GOMBE STATE.

Cikin É—aya daga jerin gidaje na alfarma dake shaÆ™e a anguwar mai É—auke da tsarin zamani na shiga 

Daga compound ɗin gidan zaka iya fahimtar mamallakin wannan gida ya samu na duniya kam saidai yayi harin lahira. gida ne na alfarma mai ɗauke da bene hawa ɗaya, sai wani babban duplex shima mai kama da aljannar duniya a gefen hagun babban building ɗin, daga inda kake kana iya hango boysquarter's a can karshen gidan bayan su garden swimming pool da kuma wawaken parking space,kutsa kai na yi cikin gidan bayan na buɗe kofar palon,tsayawa faɗan haɗuwar wannan palo dai ɓata lokaci ne A kalla paluka ukune cikin downstair ɗin da kuma kitchen da store da sauran bedrooms.

Zaune ta ke bisa stool dake gaban dressing mirror a ɗaya daga ciki kyawawan ɗakuna kuma mafi girma dake upstair,tana ɗaure da babban towel da ya kai har guiwanta tum daga kirji,gashin kanta mai walƙiyar da kallo ɗaya zaka mishi ka san ba ƙaramin laushi zai yi ba a baje har saman kafadunta,hannunta ɗauke da handrayer tana busar da gashin,duk da a zaune ta ke amma zaka iya fahimtar bata cika tsawo ba kuma baza'a ƙirata da gajera ba,kai tsaye zamu iya ƙiranta baƙa amma ba ƙirin ba dan da gani skin nata yana samun kulawa ta musamman sakamakon shining dim da ya ke yi,idanunta farare tas da ɗan madaidaicin baki mai ɗauke da cikakkun lips irin mai tsoka ɗinnan kana da jerarrun haƙora farare tas masu dauƙe da babban wushirya a tsakiyarsu,she's just a black beauty, a ƙalla zata kai shekaru ashirin a duniya,tana gyara kanta amma fuskarta cike da annuri da ganinta zata yi fara'a, bayan ta gama ta shafa mashi mayuka masu daɗin kamshi sannan ta ɗaure gashin da band hot red kana ta kama jelar ta kitsa shi ya sauƙo har gadon bayanta ya kwanta lib gwanin sha'awa, hair spray ta fesawa gashin sannan ta ɗaga container ɗin lotions dake wajen ta fara dubawa, duk ajiyewa tayi dan ba wanda ya mata ta ɗauki body spray ta yiwa jikinta wanka dashi kana ta ɗau wani kwalban humra ta dinga bin lungu lungu a jikinta tana gogawa, take ɗakin ya ɗau wani irin kamshi har yana hawa kai amma ita ko a jikinta kamar ma hakan wani nishaɗi yake bata. Tana tsaka da goge gogen turarukarne wayar dake zaune kan mirror ɗin ya ɗau ƙara. Dagawa tayi dan ganin mai ƙiran a wannan lokacin Imoji ɗin love guda biyu da ta gani fuskar wayar ne ya sata picking cikin gaggawa tana faɗaɗa fara'ar dake fuskarta.

Cike da É—okin murna mara misaltuwa ta ce, "Yayaaaa!".

A ɗaya bangaren Sadeeq ya ɗan muskuta daga zaunen da ya ke kasan rug ɗin ya yi murmushi ƙaɗan wanda baisan ma yayi ba yace, "Lilsis kin manta da yaya ko?".

Wannan karon turo baki tayi ta ce, "Ba wani nan yayaa so kake kar inyi korafin ka manta dani, amma sau nawa ina ƙiranka ko amsa wayata ma bakayi"

"Ohhh sorry my lil, kinsan yayannaki lebura ne so ba ko da yaushe nake da lokacin kaina ba,"

Cikin fara'ar da yake É—abi'arta ta ce, "To yayaa Allah ya bada sa'a amma....sai kuma tayi shiru"

"Amma me?" ya tambayeta duk da ya san abin da zata faÉ—a...."Just to told you munyi missing naka" ta faÉ—a da sanyin murya.

"Where's Mom?" ya tambayeta ba tare da ya bi ta kan maganar da ta faÉ—a ba. Mom tana side É—in Abbu ba ta jima da fita ba. In kai mata wayar ne?".

"No ki barta, kawai idan ta shigo kice mata am on my way tomorrow morning bala yaje ya ɗauko ni a airport, ohk?" wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyarta da sauri ta miƙe har towel nata na kwancewa ta ce,"Da gaske kake yayaaa".

"Da wasa nake lilsis" ya kwaikwayi abinda ta faÉ—a da irin muryarta, dariya ta kumayi ta ce, "Allah ko kayi suprising namu bari inje in faÉ—awa Mom byeeee" .

Ba tare da ta jira jin abin da zai ce ba ta yanke wayar ta nufi ƙofa da ɗan gudunta...karo suka ci da wata dattijuwar mata fara sol kai da ganinta kasan ba ƙaramin kyau ta yi lokacin kuruciya ba,baya ta dawo tana haƙi kamar wacce tayi gudu mai nisa.

"Wai sai yaushe zaki girma ne KHADIJA? kullum kina girma kinacin ƙasa. yanzu me ya haɗaki da gudu haka?"kafun budurwar da aka ƙira khadija tace wani abu mom ta gama shigowa ɗakin tana bubbuɗe hancinta.

"Me nake ji haka khadija? yanzu perfumes nawa ne kika bulbular a jikinki kamar mara lissafi ko?.'

Rungumeta khadija tayi cike da farin ciki ta ce, "Sorry Mommy,!bazan sake ba, "bata bawa mom daman magana ba ta ci gaba da faɗin, "Albishir Mommy,yanzu yayaa ya ƙira wayarki na ɗauka ya ce min yau in sanar dake gobe zai zo da safe, bala ya je ya ɗauko shi a airport plsss mommy ni zan je ɗaukoshi karki faɗa mishi plsss plssss plssss Mommm." ta ƙare tana ɗan bubbuga ƙafa a ƙasa...

Sake baki kawai Mommy tayi tana kallonta, "say something mana mom".

"To Allah ya kaimu zaki jira goben ya yi ai ko,? irin wannan rawar kan da kike yiwa MAN shi yake sa shi yana basar dake ke kuma baki gane ba".

"Nidai ki barni kawai mom, ta faÉ—a tana turo baki...yauwa bari inje in fara haÉ—a masa favourite nashi kamun ya iso."

" Na shiga uku ni Hauwa mutumin da sai gobe zai zo ne kike ƙoƙarin shiga kitchen tun yanzu?"

"Ahhhh na manta ne mom"cewar khadija tana dawowa bakin gado ta zauna.