Farautar Mutunci

Chapter 6

by @oumfatayat

*FARAUTAR MUTUNCI*

Na’ima Sulaiman Daƙayyawa ( Oum Fatayat)

page:6

Bai jira Mutum ya gama ba shi amsa ba, ya yi sauri ƙarasawa ai kuwa Hajjo ya ga ni ido ya mata tsilli-stilli, sai dai ba abunda ya sameta, wai garin ta tsallaka titi ne wani mai adaidai ta sahu ya kusa bigeta.

Da Allah da Annabi, da bakin mutane Hajjo ta bi Mahmod tare da alƙawarin ko gidan ba za ta shigaba mota kawai zai ɗakko ya maida ta gida, don ita kam tace ba za ta sake zuwa gidansa ba don kar ta haɗu da muguwar matar nan da take so ta gurgunta mata ƙafa, da shegiyar allurar ta mai ɗankaran zafi.

Haka kuwa akayi Mota Mahmud ɗin kawai ya ɗakko ya fito, Hajjo ta shiga ya miƙata gidanta da ke Hayin ɗanmani Kaduna.

“A gaskiya Mamuda ba zan sake zuwa gidanka ba har a bada, indai da wannan makirar matar ta kace, don haka dole ka ƙara aure in ba haka ba kuwa babu ni babu kai ba kai kuma ba ‘ya’yana, idan har ka maidani uwar da kake iƙirari to ya zama dole ka bi umarni na”.

Kan Mahmud a sun kuye a lokacin da Hajjo take masa maganar, bai kuma tanka ba bayan ta gama faɗe-faɗenta ne ya miƙe zai tafi, ba tare da ya ce mata uffan ba.

“ Wato dai na ga alama Mamuda ka zaɓi matarka da ni ko? To ka sani matuƙar baka bi umarni na ba babu ni babu kai”, Bata jira mai zai ceba kawai ta tashi ta shiga cikin ɗaki”.

Hmmm!!! Wani nunfashi Mahmud ɗin ya sauke, tabbas ya sha jarabawa kala-kala a rayiwarsa amma Hajjo itama jarabawa ce mai zaman kanta. Kamar yadda take faɗa cewa ko tsine masa ta yi dole tsinuwa za ta bishi haka ne, saboda ta masa riƙon da ko Mahaifiyarsa ba ta masa ba.

*Waiwaye*

A lokacin da Mahaifin Mahmud ya rasu, bayan Mahaifiyarsa ta gama ta kaba, ta tattara komai nata ta siyar, ta samu wani agent ya fita da ita Saudiyya aikatau, a lokacin Mahmud ɗin yana ɗan shekara ɗaya.

Hajjo kuwa ƙanwar Mahaifinsa ce,kuma suna aminci sosai da Mahaifyarsa, shi ne ta kawo mata shi, Hajjo ta yi al’ƙawarin riƙe shi amma da sharaɗin in ta je can, za ta dinga aiko musu da kuɗaɗen yin amfanin na yau da kullum, haka kuwa aka yi da zuwanta ta samu wajen aiki mai kyau, ta dinga ai kowa da Hajjo diloli masu yawa don ta na siyarwa tana kuma kula da shi, ban da tarin kuɗaɗe.

Tunda ga wanan lokaci Hajjo ta zama hamshaƙiyar ‘yar ka suwa, ta kuma riƙe Mahmud ɗin tamkar mahaifiyar da ta haife shi, ba kuma ta nuna banbanci da ‘ya’yan da ta haifa, sai dai kwatsam bayan wasu shekaru ne suka daina jin ɗuriyar Mahaifyar Mahmud ɗin babu aike, komai ya tsaya cak har ake tunanin ko itama ta rasu ne.

Babu abunda ya canja tsakanin Hajjo da Mahmud, duk da abubuwan da take samu ta dalilinsa sun tsaya, domin itama a yanzu ta riga da ta zama  hamshaƙiyar ‘yar kasuwa, ga kuma wata shaƙuwa da Allah ya haɗa ta a tsakanin Hajjo da Mahmud ɗin, don yadda take ƙaunarsa ko ‘ya’yan da ta haifa bata nuna musu irin wannan soyayyar.

Ya yi karatu mai kyau ya kuma zama ɗan gata sosai a cikin abokai, wanda a yanzu ya kammala P.H.D ɗin sa a Business administration, ya ke Kuma aiki da wani babban kamfanin Siri na ‘yan India wanda suka kawo Branch ɗinsu Kaduna.

Lamarin Allah ya fi gaban wasa, a duk cinikn ‘Yayan Hajjo ba wanda take mora kamar Mahmud, duk da dai ta cancanci hakan daga gare shi, yana samun aikin ya canja mata gida ya kuma zuba mata komai na more rayiwa, dalilin da yasa suka samu saɓani shine auran Nuriyya don ita Hajjon ta so ta haɗa shi da ‘yarta Nana don ta daɗe da saƙa hakan.

Kwatsam tana faɗawa Mahmud ya nuna sam shifa a kwai wacce yake so, don sun haɗu da ita ne tun a jami’ar Bayaro (B.U.K) Sunje wani taron da ya haɗa harda ɗalibai a ciki, inda Nuriyya ta fito ta yi wasu bayanai masu muhimmanci a kan dabarun kasuwanci, ba ƙaramin tafiya da hankalin Mahmud ta yiba.

Da ya yi binci ke sai akace masa ai ɗaliba ce, amma ita ce Overall ta Department ɗinsu na Business administration, Kuma Yar Kaduna ce, kafin ya bar wajen taron sai da ya samu har lambarta, daganan soyayya ta ƙullu a tsakaninsu mai ƙarfin gaske.

*~~Wannan kenan~~*

بقلم أم فتيات 👧👧👧✍🏼……