EELHAM🌹

Episode 2

by @rabearhwakili


Episode 2📲




بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai 





Da misalin takwas 8 na dare gidan shiru kaman bawasu halitta a gidan ga tsakar gidan fayau kamar ba mutane baka Jin motsin komi  
  
Part din inna na nufa ina isa kofa naji hayaniyar surutu da dariya tura kofar nayi na shiga, sun cika falon suna ta shan hira dan daman hakan kamar al'adan yaran gidan ne zuwar mata hiran dare Amman duk da haka ba kullum suke zuwa bah,haka ma cikin su ba kowa ke zuwan ba. Tanajin dadin firan da suke zuwar mata  kwarai da gaske Amman randa yan tsiwar Tata suke kusa ta korasu kokuma taita masifance su wanda da kanka zaka Nima hanyar kofa.
     Hakadai suke ta fira cikin so da kaunan junan su dan familyn suna da hadin kai,ganin dare na jaaa yasa sukayi mata sallama suka wuce makwancin su 
 
Washegari bayan sunyi kari suka fito wajen mota suna jiran sauran yan uwan su,ta dayan side din kuwa manyan sune suke fira cikin fahimtar juna, ganin kannan nasu sun fito ne yasa suka shishiga motar driver yaja sai zuwa makarantar su 
  Bayan sun isa kowacce ta fito daga Mota suna nufan hanyan class ɗinsu, yayun su suna aji na karshe ne wato ss3 inda masu bi musu wasu na ss1 wasu kuwa ss2 inda sukuma yan matan nan suke js3 
   Wai dan Allah saurin mi kuke yi ne kaman wayenda zasu tashi sama to duk saurinku dai babu teacher a class din aheem,juyowa duk sukayi suna mata dariya dayar cikin su ne tace haba yusrah ki dinga shan ruwan buta ko zaki samu saukin masifan nan naki na gado wanda kika gada Wajen inna, aiko mi sauran zasuyi inba dariya bah,yusrah kam ta shaka dan takai wuya aiko tayi kansu wai sai ta dake su nan fa suka kwasa a guje sai class,suna shiga sai ga teacher din ya shigo, inda Allah ya cecesu wajen yusrah kenan shugaban bala'i 

Duk nutsuwa sukayi sosai suna kara maida hankalinsu ga board, sosai kuwa suke fahimtan abinda akeyi musu dan suna da ilimi daidai gwargwado, bayan fitar sane wani malamin kara shigar musu haka dai har aka tashi musu break, da yake da Abunsu suke zuwa kaman wasu yara tin yan class na musu dariya harsuka saba da hakan suma suka rabu dasu 

Bayan sun koma class ne kaman yadda yake haka aka dinga shigo musu har  lokacin tashin su yayi karfe 2 koda suka fita sun iske dirvern har ya iso,shiga ciki sukayi suna jiran sauran yan uwan su,da yake bakin su baya shiru ko kadan nan fa suka fara korafin wai su aunty narnarh sunƙi su fito kuma sun san suna jiran su kuma ga islamiyya zasuje (kamar su aunty narnarh din bazuwa islamiyyar zasuyi bah suma),hakadai suka cigaba da complain hardai sukayi shiru dan kansu sai wajen 2:20 su anty narnarh suka fito suka shiga motar ko kallon kannan nasu basuyi,

"Nide Gaskiya zan fada a gida kowa ya dinga tafiyan shi daban to ina dalili a saka Mutane jiran dole kuma a kasa basu haƙuri toh baza ta saɓuba Allah ya gani" da yake aunty intesar akwai saurin fushi waigowa tayi tace sannu rasa kunya kece mai baki isasshiya bah? sauran sunyi haƙuri sunyi shiru saike ko? "To karki fasa yin haka watara sai na miki dukan tashi kisha gari" ta ƙare maganan dayin kwafa tana ƙara haɗe fuska dan bata son rainin barin ma nasu 
    Sukam gum sukayi basu kara tofa komi bah dan sun san halinta yanzu sai tace zata dake su gashi babu momma a wajen shiyasa hanyan shekaru a bita da lafiya. 

Sun isa gida lafiya da izinin Allah, sanin dasukayi basuda isasshen lokaci yasa ko kallan part din kakartasu basuyi suka nufi sashen iyayen su 
  Anan ma babu wacce ta zauna sallah sukayi sannan suka ci abinci akayi shirin islamiyya, la'asar nayi bayan sunyi salla duk suka fice zuwa islamiyya dan shima basa wasa dashi, saide muyi fatan dawowar su lafiya 

Wata black beauty mata ce zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon ga waya kare a kunnin tah ji nai tana cewa toh sai kin aiko din Nagode nan sukayi sallama tana aje wayar,matar kyakkyawace sosai skin ɗinta  chocolate color  batada wani jiki kuma baza'a ace mata mara jikin bah dukda azaune take hakan bai hana in gano cewa tana da tsayi shima tsayin bawai chan bah,jin ana knocking ne yasa mai aikin tazo ta buɗe hadi da gaisar da mai shigowan har kasa,bata ko kalli inda take ba ta wuceta tana korafin wai sun wani kama kofa sun rufe sabida Rashin gaskiya. 
   Mikewa ammie tayi jin muryan inna sannu da zuwa ta hau yi mata ita kuwa sai wani cin magani take ita a dole an bata mata rai 
  Inna baki zauna bah ga waje Bismillah, a'a ba zama ya kawo Ni bah nazo duba jikin takwara ne ya jikin nata, jikin kam alhamdulillah dan tasamu sauki,Masha Allah Allah yasa kaffara ne,Amin ya Allah! inna dan Allah ki zauna ga kujera haɗi da nuna mata kujeran dake gefen ta,itama zama tayi dan ta gaji da tsayuwar iyayine dai irin nata, kitchen Ammie ta shiga ruwa da danbum naman kazan da tayi ta daura a tray ta kaiwa inna,aiko bawani kunya ta buɗe ciki ta naɗa alhamdulillah Allah yayi albarka,amsawa ammie tayi da Amin, wai ina takwarar tawane,tayi bacci amman Bara na dubota, a'a barta tasamu Bacci sosai Allah yasa kaffara ne Amin ya rabb,
   Kinga ni bara naje daman naji shirun yayi yawa ne nace Bara na leko,Toh inna Nagode, itama ta nufan kofa dan yiwa inna rakiya Saida ta kaita har haraban gidan sannan inna tace ta koma hakanan,duk da ba haka taso bah dan tasan halin inna sarai,aiko dai tana wuce wa inna tahau surutai wai daman batayi niyya bah inda tayi ai da ko tace ta koma bazata koma bah sauƙin abin dai ni na kawo kaina ba wani bah!balle kuma kana tafiya da mutum kaman wani kurma Toh bada ni bah ahem, hutarere na hutar dake atoh kafin aje anayi dani azuci (dan Allah ku jimun matan nan fah;waii Bara nayi shiru ba ruwa na)......................✍️