Episode 3
Episode 3📲
***
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
baiwar Allah bata san inna nayi ba ita kam,koda ta isa sashen nata bata tsaya falon bah,shiga dakin ɗiyar Tata tayi dan ta tashe ta ganin magrib ya kawo jiki,koda taje bata same ta a daki ba saide taji motsin ruwa alamun tana cikin bayin,fitowa tayi ta wuce kitchen dan daura musu dinner aiko cikin kankanin lokaci ta kammala dafa musu taliya fara daman tariga da tayi miyan tini bayan ta gyara wajen da tayi aiki ne ta fito, kaman jira kuwa saiga kiran sallah dakin ɗiyar ta takoma nan ta iske ta akan sallaya jawo mata kofar tayi ta wuce dan ta gabatar da salla
___________________✨cikin gidan kuwa yan islamiyya sun dawo babu jimawa masu zuwa aiki ma haka sai daddaikun da suka rage basu dawo ba
Bayan idar da salla isha'i yaya khaleel ya nufa part din momma dan gaishe da ita da sallama ya shiga,amsawa momma tayi fuskanta dauke da tautausar murmushi,Barka da warhaka momma ina wuni,lafiya qlau ya aiki, alhamdulillah naji shiru halan yaran naki basuyo nan bane,Saida ta murmusa sannan tace kundai sawa yaran nan nawa ido bansan mi suka tare muku bah ta ƙare maganan da wasa
Shima Saida ya dara sannan yace da yawa ma kuwa,ooooh na gane kishi kukeyi dasu bah toh a ƙyalemun yarana ahem ni nariga da nayi sadaka daku,yanxu momma hadda ni kikayi sadaka toh shikenan Bara naje wajen mamana,a sauka raɓaɓa ina gaidata,ya miƙe kenan zai wuce sai ga sallamar yaya muzammil hannun sa dauke dasu twince aiko suna hango yaya khaleel suka fara daga mishi hannu wai ya dauke su, dungure musu kai yaya muzammil yayi cikin wasa yace ba inda zaku munanan tare, momma ne tace son ka fita idona na rufe bani yarana nan,yana dariya yace momma da kin barni dasu hadi da mika mata yaran,karban su tayi tana yi musu wasa yaran kuwa sai faman kyalkyale dariya suke da gani sun saba da ita sosai da sosai,ganin kaman ta manta dasu a falon ne yasa sukace wai sun wuce wajen maman su cikin shagwaɓe fuska kaman wasu twince,sai kun dawo ina gaisheta da kyau karku manta fa,kunga zan manta ko! inna ta kawo karan ku wai baku zuwa part ɗinta yanxu dan haka yaude a kokarta ashiga dan Allah,Ni in koma part din inna kuma! lailai ai tasan batada gaskiya shi yasa ta biyo ta wajen ki, rannan daga shigan mu nida muzammil wai bamuyi sallama bah mu fita kaman wasu yara fah haka ta kora mu,hakuri zakuyi tsufa ne dan Allah kudai je mata yau, tunda kinsa baki bakomi momma zamu shiga insha Allah,Allah ya bada iko,Amin Amin momma Bara muje sai anjima haka dai suka fito part din ummi suka shiga nan ma dai sun dan jima kafin su fito
__________________✨ haba sabida Allah kun takuramin, Gaskiya kuzo ku wuce sashen iyayen ku Ni nama yafe muku shigowan basai Kun shigo ba,haka kawai ku cikawa mutum kunne da surutun banza dana wofi!ikon Allah wai badaku nake bane kun wani tsira min ido ko sai na tashi kunga tsawo nane iyeeeee,
Babu inda zamuje muna anan tare dake duk mi zakiyi kiyi zaman mu daram cewar mufee,
Gaya mata dai yaruwa dan ta kara sani in ta saba da koran wasu su fita to mukam yanzu muka fara tarewa anan ko ba haka ba sisters?
Hakane kam muna bayan ki ummi 100%,
Nanfa suka hita batunta fira suke hadda na gayya dan ihun yanxu yafi na ɗazu
Babu yadda ta iya dan duk masifanta bata iyawa dasu tashi take tabar musu gurin,yanxu ma haka take miƙewa tayi abinta tayi daki
Dariya suka hauyi suna mata waƙa wai taji tsoro,Saida suka gaji dan kansu sannan suka barnan zuwa part din momma,
Assalamu alaikum momma we miss you,yan matana i miss You too
Aifa jin ankirasu da yan mata sai kansu ya ƙara kato sufa a dole ga yan mata,haka dai suka zagaye ta suna zuba mata surutu wanda bakin nasu ko ciwo baya musu,aunty sadiya ce ta miƙe ta bar musu falon haɗi da hararan su dan sun hana kunnin su sakat tunda suka shigo, basu san ma tanayi bah dan hankalin su gaba ɗaya yana kan surutun da suke ne,
Yan Matana wai kun dubo jikin yaruwarku kuwa
Sai an jima zamuje momma, toh Allah ya bada iko,duk amsawa sukai da Amin hadda su aunty delarh dake a falon
__________________✨su yaya khaleel ne zaune a part din ammie dan tindazu suke anan sai hira suke sha Abunsu suna dariya,yawwa ban gaya miki bah ammie Amman kuma sai munfi haka yawa sabida yan sa ido,karab kuwa yaya adam yace kaide kasani daman wa yace maka yanason yaji?ko ance maka kowa ma magulmaci ne, a'a fito fili dai kace nine magulmacin an bata maka rai a waje zaka wani nima ka sauke a kaina bah? kuma ga haushin bazakaji labarin da zanbawa ammie ba!ai nasani dan haka kwalelenka ya kare maganan cikin son ya tunzura yaya adam,kin kulashi yaya adam yayi dan idan ya biye mishi sai bakin shi yayi tsini, yaji tsoro da ka kara magana kagani,su ammie kuwa dariya sukeyi musu daman ai sun saɓa kullum sai sunyi kaman wasu yara,haka kuma kullum suna tare da juna, suna cikin wannan draman ne saiga sallaman mutanen namu wato su mufee iyayen surutu,nan take kuwa suka koma kaman basu ba ganin yaya adam da yaya sadeeq a wajen dan basu cika sake musu face ba wai suna gudun raini, kaman wasu masu hankali kokuma baƙi suka raƙuɓe daga wajen kujera suna gaida ammie da sauran yayun nasu,kaji min ikon Allah wai raiha anan zaku tsaya baza ku ƙaraso ciki bah, a'a ammie daman munzo duba jikin namesake din inna ne,
Da yake yaya khaleel akwai shi da wasa da dariya cewa yayi kuce dai kunga dodonnin ku awajen shiyasa,
Momma ke jiran mu zata aikemu wajen inna shine mukace Bara mu fara duba mai jiki,
Ai kuwa kun kyauta yan matana!
tana ciki ku shiga, a'a ammie Bara dai muje zamu dawo Allah ya ƙara sauki haɗi da miƙewa suka fice
Cikin dariya yaya khaleel yace ammie kalli yaran ki kamam wasu masu hankalin gaske,
Ooo da basu da hankali kenan kunfa sawa yarana eyes a gidan nan gwara ku fitar mana a ido kafin mu datse daku, duk dariya sukai ganin yadda ammie taci serious tana kare yaranta,ammie yaran nan naki ne basa ji Saida tsare gida cewar yaya sadeeq,toh idan kuna tsere gidan da suwa zasuna rinka wasa iyeee?ayi hkr zamu gyara ammie yaran ne abin tsoro,dodonnine su ƙarshe tsoro,
Duk dariya sukayi kafin su miƙe cewar Akwai inda zasuje, adawo lafiya taimusu,amsawa sukai haɗi da ficewa ..........✍️