EELHAM🌹

Episode 4

by @rabearhwakili



Episode 4📲



بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai




Raihana da su Sarah ne kwance a gado suna ta fira abinsu kaman ba dare bah,yawwa wai kunsan da muka shiga part din ammie kunga irin mugun kallon da su yaya sadeeq sukayi mana kuwa cewar ummi, kede bari mun gani ai tsofaffin mugaye ne kullum suna nan dukum fuska ba fara'a,atoh Nima shiyasa bana sakar musu fuska cewar yusrah,ai basu san sanda suka hau mata dariya bah dan a Lokacin duk tafisu birkicewa shine yanxu take wani cika baƙi, mallamai wai lafiya kuka tasani a gaba kuna dariya?ta ƙare tambayar cikin masifa,mufee ce ta juyo daga kwance da take tace haba dan Allah kun hana mutum bacci fa kuma gashi dare  ƙara nisa yake,duk kallan ta sukai suna taɓe baki da faɗin mai baƙin hali kawai,ganin dai Ba shiru zasuyi bah yasa ta fice a dakin,daman bata cika hayaniya bah Amman idan taso har finsu take,haka dai da dadɗaya bacci ya fara gaba dasu kafin daga baya daƙin yayi shiru alamun duk sunyi bacci asuba tagari yan matan momma
   
        __________________✨haka rayuwa keta tafiya yau daɗi gobe kuma babu daman rayuwa ya gaji haka Saida muyi fata Allah yasa mugama da duniya Lafiya Amin, 
       Bayan kammala ssce din su aunty sadiya akayi musu aure zasu cigaba dayin karatun a dakin mijin su inda su aunty intesar ma har sun fara zuwa University na FUT, Amman an sanya auren su nan da wata 2 zasu cigaba da nasu karatun a dakin su 
   Cikin samarin gidan ma wasu sunyi aure abun su,
    Yan matan gidan ma yanxu an shiga ss3 suna kan rubuta ssce dinsu kenan ma,iyayi sai abinda ya karu saide sunyi hankali sosai kuma basu cika hayaniyan nan ba Amman iyayin kam ba abinda ya ragu 

        ______________________✨dan Allah momma ki barni in ƙara bacci koda na 5mint ne,ikon Allah baza ki tashi bah sai kin makara kinsan kunada exams koh, momma sai 10 mukeda,to kwanta kiyi ta bacci karki tashi bari na gayawa su Sarah suyi tafiyar su, saurin janye blanket din datayi rufa dashi ta buɗe kanta momma ganin nan maida dubanta tayi akan time ganin 9:20 yasa ta Zubur ta mike ta faɗa cikin bathroom gudu gudu tayi ta fito shima shiryawa a gurguje tayi shi koda ta duba time ganin 9:40 yasa ta dauki abinda zata bukata a gurguje ta sallami momma sannan ta fita wajen mota inda su raiha ke jiranta, haƙuri ta basu sannan suka shiga motar,
     Koda suka isa school 9:55 sauran musu 5 mint duk ajiyan zuci sukai sannan sukai maza suka shige hall ɗin exams (Allah ya bada sa'a)

     _______________________✨innace ke zaune a falon ta ga waya kare a kunnin ta faɗi take eh ai bikin ya matso sosai tunda kwatakwata wata biyu ne,shiru tayi alaman taba sauraren ɗayan bangaren, a'a daman ban faɗa musu bah Kinga sai ki gaya musu dan Allah,to to ngd sai anjima sauke wayar tayi tana mai cigaba da kallo a tv 
       __________________✨ part din ammie naje Amman tana tare da bakuwa zancen auren su anty delarh ta kawo mata haɗi da faɗin tana Niman mai gyaran jiki wacce ta iya sosai,
      Aikuwa kaman kin samu dan akwai wata dana sani Hajiya maimuna likitan mata ta iya gyara sosai tundaga ciki har waje dan lokacin auren su kubra ai nan na miƙa su Kinga yadda ake magana akan yadda jikin su ya koma kuwa dan sunyi tar dasu sannan ana gyaran ana baki maganin mata wanda bazaiwa amarya illa ba amman fah kafin afara shan maganin sai anyi Miki treatment din infection haka tsarin ta yake Bara dai nabaki number ɗinta sai kuyi magana  *** Masha Allah aikuwa Nagode sosai Allah ya bar zumunci,Amin Amin wai ina yar gidan goggo tunda nazo ban ganta ba ko ta koma wajen ta ne,tana chan kuwa tin jiya ta koma kinsan daman bata cika zama anan bah,hakane kam Allah dai ya musu albarka, Ameen ya rabb hakadai suke ta shan firan su 

      ___________________✨haka dai rayuwa ke tafiya gashi yanxu su yusrah sun kammala ssce sai kuma jiran result a gafe kuwa shirin bikin su aunty delarh ake ba kama hannun yaro dan bikin bai wuce sati biyu ba gidan sai hada haɗar biki ake amare ma sun fara zuwa wajen dilka a gidan Hajiya maimuna likitan mata idan suka fita tin 6 basu dawowa Sai dare satinsu biyu kenan da farawa daman ammie na wata daya tace ayi musu,gashi kuma tin kafin nan sunyi wani tar dasu sai kamshi suke zubawa duk ya suka gitta sai sun bar kamshi a gurin 

      ___________________✨haba dan Allah kiyi sauri ki fito mana ke kin iya nawan tsiya kaman ba mace bah cewar Sarah tana yiwa raihana magana,dan Allah karki dame Ni mallama inace duk saurin mu sai munjira driver ya dawo dan haka barni biyu shiri cikin nutsuwa toh,inkin gadama karma ki gama ki shekara nan ins ruwan wani karshe dai Saida mu aje Miki kayan ki inyaso duk shekaran da kika gama saiki same mu chan, oho dai sauƙin abin nasan hanya sannan kufi jirgi tashi sama,nide in Kingama ki same mu a parking lot in Kuma bakiyi sauri bah mu wuce,wai dan Allah wucewar zakuyi da gaske dan Allah ku jirani gani nan bata kammala shirin bah haka ta fito jerawa sukai zuwa parking space shiga sukai ya tafi dasu zuwa shagon dinki bayan sun miƙa  suka faɗa mishi style din da suke so daman yana da measurement dinsu daganan gidan aunty Billy sukaiwa tsinke daman sun faɗa daga wajen tailor zasu gidan aunty Billy,
      Sannunku da zuwa ammatan momma,yawwa ina yini antynmu, lafiya qlau ta mutanen gida fatan kowa na lafiya, Alhamdulillah aunty,kunshawo rana da yawa fah kuje kitchen ku samu abu mai sanyi ku kora, toh aunty
   Aunty billy kenan tana dason yan uwanta dan idan suka zo gidan nata har bata son su tafi 
    Anty wai nikam ina su Ameer ne banji motsin su bah ko suna bacci ne,
    Sun fita da abban su Amman nasan baza su jima bah,aiko dasu zamu wuce chan gida  yau zasu wuce biki ayi shirye-shirye dasu Koh aunty,
   Kunfi kusa ai Ni yar kalloce,wai ina namesake din inna ko haryanxu tana a gidan goggo?,sunyi tafiyama suna kd matar dady babu lafiya shine sukaje su dubata!jiya suka wuce wai baza su dawo bah sai an kusa biki dan babu wani akusa da ita kuma ga Rashin lafiya shiyasa,
      Allah sarki Allah yasa kaffara ne ai banji dana kira goggon na mata ya mai jiki Amman Insha Allah zan kirata ko zuwa anjima,
    Aunty nifa nafara jin yan garin mu abincin bai sauka bane har yanxu?
Duk dariya suka hau mata wai acici Mala'ikun tauna, a'a barni inci saukin abin ma idan naci ana ganin improvement a jikina Amman su o'a fah ba labari,tsaf mufee tasan da ita raiha keyi dan bata da jiki Amman fa akwai ci,
    Alhamdulillah haka Allah yaso ya ganni kuma ina gode masa da baiwar da yayi min to!
      Dan Allah aunty billy danayi magana na kira suna ba o'a kawai nace bah Amman kiji tana Niman yimin sharri ƙiriƙiri kice dai kin tsargu Mallama
    Bata tanka mata bah dan halin raihana sai ita 
      Nide baxan shiga tsakanin ku bah anjima ku watsa min ƙasa a ido ina zaune lau!dan haka kekuma raiha Kije kitchen ki duba mi yarage a dahuwar  dan ko Ni nafara jin yan garin mu toh aunty 

     Wai anty yaushe zaku iso ne Gashi anshiga hidimar bikin,toh yar kanzagi bikin fah saura 2weeks Amman kin bi ki addabi mutane cewar Ummi,ganin zasu fara halin nasu ne yasa aunty Billy cewa dan Allah kuyi hakuri ba dan Ni ba da Allah na haɗa ku,allah yasa mu koma gida lafiya zaki gaya min wa kike cewa yar kanzagi cewar Sarah,ohoooodaaaaai 
      Tab da saura fah a dahuwar shi dan yanxu ma ruwan ke daukan hanyan tsotsewa,
     Ai ya dahu kenan tunda tsotsewa ya rage yanzu zakuga yagama da wanda bazai iya jiraba ya haɗa cornflake,nide zan tsaya ya dahu inci ne kar inje in cika cikina da cornflake in kasa cin abinci cewar ummi ganin hakane yasa suma sukace zasu jira minti nawa ne 
   Aiko cikin kankanin lokaci ya dahu a plate daya suka zubo hadda aunty Billy sai zuba mata santi suke wai zasu zo yin training a gurinta haka dai har suka kammala! kankanta wajen sukai sannan suka nufi daki danyi sallah azahar ganin lakoacin yayi basu ne suka bar gidan ba sai wajen 8pm inda mijin aunty billy ya maida su gida sunso su wuce dasu Ameer amman yaran sunki koda suka koma gida bayan sun gaida iyayen nasu sannan sukayi wanka haɗi da bin lafiyar gado dan yanxu basu cika shiga wajen inna bah (Toh yan matan momma asuba tagari).........................................✍️