Episode 6
Episode 6📲
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
Yan bikien duk sun waste gidan yayi dif,su anty billy ma duk sun koma gidajensu,baki yan nesa ma haka
Ko ina na gidan ya koma normal kamar ba'ayi wani sha'ani ba,
_______________✨part din ammie na shiga nan na iske ta tana kokarin yin waya cikin Sa'a kuwa bugu biyu aka dauka,cikin nutsuwa ammie ta gaida mahaifiyarta, amsawatayi da tambaya mutanen gidan nasu, goggo kowa na lafiya qlau, ashe an maida aunty suwaiba asibiti wai jikin nata ya motso, subhanallahi banda labari kuwa Allah ubangiji yasa zakkan jiki ne,Amin ya Allah daman Nima yanzu yaya ke gaya min shima din duk a firgice yake,
Ashsha abu baiyi daɗi bah Amman Bara na yi shiri idan Allah ya kaimu sai in kama hanya
Nima gobe zan je kd din tafiyar namu zaizo daya kenan cewar ammie
Atoh hakane saikiyi sammakon fitowa,insha Allahu goggo
Sai anjima agaida yaran duka Insha Allahu nan sukai sallama tana aje waya
Alhamdulillah result ɗinsu yusrah ya fito kuma yayi kyau sosai inda aka fara bidar musu admission dan cigaba da karatu kafin Allah ya kawo musu miji na gari
_______________✨banso sauran su samu addimission nisa da gida bah Amman Allah yasa haka yafi alkhairin cewar Abbie, inda su dady suka amsa da Amin,ina ganin kai sadeeq sai kaje kayi musu albishir Ammanfa suyi hkr haka Allah yaso,insha Allah Abbie
Koda yaje saida ya fara basu baki Sannan ya gaya musu cewan sun samu admission Amman a mabanbanta institution duk ɗagowa sukai suna kallansa
Eh ai shiyasa na fara da baku baki wannan ba kaman secondary school yake ba dan bai zama lailai ku samu University ɗaya ba bayan haka kuma inace kowa da abinda zai karanta,eh yaya kowa da abinda zai karanta,
Kunga dan haka kuyi hkr!da mufee,da namesake din inna sun banbanta da naku dan su udus suka samu inda kukuma suka baku a ibbul dan hakan sai muyi fata Allah yasa haka yafi alkhairi duk amsawa sukai da Amin
Ganin dai jikin nasu yayi sanyi ne yasa yafara basu baki harde suka dan sake sannan ya wuce abinshi,,, aranar haka suka yini suku -suku kaman basu bah
Nanfa aka hau yimusu abinda ya kamata na wucewa makaranta,gefe kuwa wayenda akeyi dansu duk sun shiga damuwa dan basu taɓa rabuwa ba,barin ma mufee duk tafisu shiga damuwa dan ita ai kaman ita ɗaya aka tura chan ɗin Toh ita ɗaya mana dan su yusra kukan daɗi suke
Ayau mufee zata wuce Sokoto ita da yaya sadeeq shi zai mata rakiya aiko tasha kuka kaman mene Saida Takoma bawa su dady tausayi Amman ya suka iya haka dai zata saba bare ai ba ita ɗayace ba namesake din inna tana nan ai
Saida su yaya adam sukai mata jan ido sannan ta shiga mota suka tafi airport,Sarah suma sai share hawaye suke dan sun saba sosai da junan su! Sunso suyi mata rakiya airport Amman basuga fuskan hakan ba wajen yayun nasu
Kinsan Allah idan bakiyiwa mutane shiruba zan Miki mugun duka;kin wani tasani a gaba sai kuka kike kamar wacce na sato,idan makaranta ne baki so basai kita zama a gida ba har zuwa next year ina ruwan wani
Ai tunda ya fara magana tayi ɓam da bakinta dan tasan halinshi daman ba wasa yake dasu bah"kayi hkr yaya
Naji kiyi shiru kar kanki yayi ciwo muje ana kiran passengers! Gyaɗa mishi kai kurum tayi,
Alhamdulillah sun sauka a Sokoto lfy qlau taxi ya tare musu suka hau zuwa gidan da abbie ya siya musu,gidan dan madaidaici ne amman yana da kyau dede nashi,tayata kwasan kaya yayi zuwa cikin gidan,ya kuma tayata jera komi a wajen da ya dace, suna kammalawa ya fice a gidan zuwa Masallaci dan lokacin sallar la'asar azahar tayi,itama dai salla tayi!tana nan a inda tayi salla saiga sallamar yaya sadeeq ya dawo,ki fito waje,;, Toh yaya
Fitowa tsakiyar gidan tayi inda ta same shi bisa kujerun da suke wajen itama isa tayi wajen tana kai duke haɗi da faɗin yaya gani
Tashi ki zauna, ba musu kuwa ta zauna haɗi da sunkuyar da kanta dan basu wani saba dasu bah sunfi sabawa da yaya khaleel dan yana wasa dasu,
Wai kukan ne haryanxu mufeeda banace kiyi shiru haka nan ba ko dai kinason kanki yayi ciwo ne uhmm?
Gyaɗa kai tayi Alaman a'a,to waya share dukkan hawayen nan kuma banso na kara ganin wasu sun zubo kinji Koh?insha Allah na daina,kinyi alƙawari,nayi,gud gurl
To yaya nida waye zan kwana a gidan,
Karki damu yaruwanki tana hanya nasan dai kafin nan da 5 ta iso,sai a maida hankali akan karatu banda kula samari kinji Koh,insha Allah,idan na kamaki da hakan fah wani hukunci zanmiki,ka dake ni,haka kikace ba,eh yaya,ok Allah yasa Bara nazo na koma kafin yamma tayi,
Ni kadai kenan zan zauna a gidan nan nide dan Allah kayi hkr kajira isowarta dan Allah
Toh shikenan Amman da sharaɗi zakiyi min fira kafin ta iso inkuma ba haka bah inyi tafiyana
Shiru tayi kafin tace shikenan ta yadda Amman wani labarin kakeson na baka,
dan saurarene Ni dan haka banida zaɓi,Ni bansan lbrn da zan baka ba ai,
Okay naji kin yadda duk abinda na tambayeki zaki gaya min, Toh,samarin ki nawa ai ba shiri ta ɗago ta kalle shi ganin ya ƙara wani kicinkicin da fuska ne yasa ta ƙara shan jinin jikin ta,
A'a bamu kula kowa wallahi
Kin tabbatar, sosai kuwa,madalla to kici gaba da haka kar in sake inji wai ance gaki da wani idan kuma hakan ta faru zaki sani ne,bazaka same Ni da hakan ba da yaddan Allah,Allan yasato yanmatana kallan shi tayi shima daman idonshi na akanta koke ba yanmata na bane, a'a na momma ne,oooh kenan banda Niko to Bara na tashi na wuce tunda abin haka ne
Yanmatan kane yaya kayi hkr kaji ta ƙare maganan kaman zatayi kuka dan batason zama ita ɗaya bare a wajen da bata saba bah,
Kuka kuma wai ke bakya gajiya da kuka ne kam Bara hawayen naki ya kare!to yaya ba kai bane kake cewa wai zaka wuce ka barni Ni ɗaya bah,inace na fasa ai Amman kina kara yin wani kukan wucewa zanyi, toh na daina,karma ki daina ki cigaba
Fira suke jefi jefi kafin daga baya ta sake kaman daman sun saba suna a zaune a gun ne saiga sallaman wata budurwa fuskanta dauke da face mask oyoyo namesake din inna sannu da zuwa ya hanya cewar mufee wacce ta iso gareta,nan fa suka gaisa sosai itama sayar ta gaida yaya sadeeq,Saida ya ƙara musu nasiha da tini sannan ya wuce .................................................✍️