Episode 7
p.com/DUfzxeqU5D174LvqBxcmmu
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
Su Sarah yau suka tafi zuwa lapai dan sun tsufa s chan ɗin,
Kamar yadda aka siyawa su mufee gida suma haka take saide nasu yafi nasu mufee girma tunda daman ai su sunfi yawa
_____________✨Bacci take cikin kwanciyar hankali daga gani baccin yana yi mata daɗi.wayarta dake ƙarƙashin pillow ya fara vibrating wanda hakan ya katse mata jin daɗin ta,dauka wayar tayi tana duba wake kiranta nata sai taga yaya sadeeq ne,dauka tayi cikin muryan bacci tace ina kwana yaya.
Daga chan gefen ya amsa mata da Lafiya qlau bacci kikeyi haryanxu baki tashi ba,ko ba yau bane zaku farayin abinda ya kamata bah
Bai daɗe dana koma baccin ba zuwa cikin school sai in Allah ya kaimu gobe zamu fara insha Allah
Ok toh,fatan dai kinyi break fast
A'a Yanzu zanyi,
cikin faɗa-faɗa yake cewa wai mi yasa kike wasa da cikin kine kinsan bakiyi breakfast bah kin samu waje sai bacci kike idan kuma wani laluran ya kamaki ki barni da lahaula ko?
Kayi hkr yaya zan gyara,ai daman kullum cikin bada hkr kike, toh naji, yanxu dai kije kiyi break anjima zan kara kira, Nagode yaya,bayan sunyi sallama ne ta kifa kanta akan fuskan gado tana mamakin sauyawar shi dan ai ba haka yake musu ba a gida Amman yanxu taga sai wani bata kulawa yake kaman wata yar yarinya,watsar da batun tayi ta fice dan nima ma kanta abinda zatayi break dan
madaidaicin kitchen ɗinsu ta shiga Saida ta fara daura abinda zatayi sannan ta fito dayar dakin ta shiga ganin ta kwance tana bacci tayi bata tasar da ita ba dan tasan batason tana bacci a tashe ta,komawa kitchen tayi ta cigaba da aikin,gidan nasu 2bedroom flat ne da kitchen ɗinsu ɗan madaidaici sai falo,,,koda ta gama haɗa musu break diban nata tayi ta kuma ajewa yar uwarta,falo ta fito tanayi tana kallon tv daman su Abbie sunsa mussu komi dan ba abinda basu dashi,
_______________✨ Kinga tunda ke bazaki shiga school ba dan Allah ki taimaka kiyi mana better kafin mu dawo cewar raiha danfa ita bata da sauki a gurin abinci
Dan zaku barni shine hadda wasu inyi muku better ko?oya nah bakomi kuje ku dawo zakuwa ku samu kala-kala
Daɗina dake baki san abin arziki bah taimako zakiyi mana fah haba anty Sarah
A'a niba antyn ki bace mallama kira Ni da sunana tsirararsa ato kar azo anamin daɗin baki a cuceni,
Toh karkiyi mana inace in kinyi kema zakici ?
aiko dole hadda style dan kiji kenan,
Saida sauran suka sa baki Sannan ta yadda zatayi danfa sarah alanƙosace baka moru, sallamanta sukai sannan suka fice daga gidan zuwa school daman gidan nasu bayida wani nisa da makarantan su (Allah ya bada sa'a ammata)
_____________✨haka rayuwa yake tafiya da daɗi da babu daman rayuwa ya gaji haka,ammatan sun sha, gwagwarmaya kwarai da gaske Allah kuma ya dafa musu dan yanxu gasu s final year
________________✨A chan gida kuwa shirin meeting suke wanda suke gudanarwa duk shekara kowa na gidan zaizo tundaga na kusa hadda yan nesa
Ankara gyara gidan sai yaƙara kyau sosai dan an sabunta paint! sosai hakan ya kara fito da gidan daman kuma yana da kyau Saidai ya ƙara ya koma kaman sabo
babban ɗakin taron shima an sauya masa komi an zuba sabbin kujeru an chanxa masa paint da sauran furnitures da ke a dakin
sauran part na gidan suma ba'a barsu a baya bah komi dai ka gani yayi zam gwanin birgewa ~~~~~~~~~~~~~
____________✨Gida ne dan madaidaici shi bai cika girma ba compound din zai dauki mota uku wanda baza su matse juna ba gidan kam duk da ya kasance dan madaidaici Amman akwai kyawu kwarai,
Karasawa cikin gidan ammie tayi tana zuwa kofar shiga turawa kawai tayi Daman tasan ba'a kulle kofan da sallama ta shiga tana jin daɗin ganin mamar Tata cikin koshin lafiya, kyakyawar matace dan ammie da mahaifiyarta take kama,
Goggo Barka da rana inayini, ya karfin jiki,jiki kam alhamdulillah naji sauƙi sosai,Allah ya ƙara lafiya Amin Amin Allah yayi albarka,Amin goggona,
Ya yaran da kuma mutanen gidan naku fatan kowa dai na lafiya,kowa na lafiya qlau sunce ai Miki sannu da jiki,Masha Allah ina ansawa Allah ya raya zuri'a,yanxu kuwa na gama waya da yar gidata, Masha Allah taga dama kenan Toh Bamu gode ba cewar ammie, nida aka kira kuma Nagode ahem,shiru ammie tayi bata ƙara tofa komi ba akai,
goggo yaya ya koma ne halan( ƴaƴanta) dan jiya munyi waya yake faɗa min yau zai wuce,
A'a bai samu wucewar ba dan akwai wani uzurin da ya tsaresa Saidai in Allah ya kaimu, Allah sarki ya kuma aunty ta ƙaraji da jiki dukda dai nayi kiranta jiya, alhamdulillah ai jikin nata yayi kyau dan ta miƙe, Allah ya ƙara sauki, hakadai suke ta fira tsakanin uwa da yarta~~~~~~~
_________________✨Bangaren su mufee da su raiha yan lapai momma ta yi kirasun a kan su taho dan suma su halarci meeting aiko suna ta murna dan abin yazo adede daman paper guda ya rage musu yusrah kam ta kammala jiransu take dan su tafi tare kamarbyadda suka saba,sabida zumuɗi harsun fara shirya kayansu dan suna kammala paper dinsu na gobe zasu wuce neh ba wani jira (nikam nace yan zumuɗi😎)
Washegari bayan sun kammala paper ne ba abinda suka tsaya jira sukayi haraman tafiya,koda sukaje tashan mota drop suka dauka haka suka dauki hanya har Allah ya sauke su lafiya,a bakin gate mai motan ya ajiyesu haɗi da bashi kudin shi
Knocking sukayi da yake gateman yana kusa budewa yayi ganin su ummi ne ya hau musu sannu da hanya sun gaisa sosai cikin girmamawa kafin suyi cikin gida rasa part dinwa zasu shigane yasa suka ƙwala ihun kiran momma, Ammie,mamy,umma,mommy mun dawo kaman wasu yan yara
Da yake umma tana kofan entrance dinta Amman ba'a ganin mutum,yasa ta riga kowa fito,muryan wa nakeji haka kaman na yan matan gidan nan ne cewar umma tana ƙarasawa wajenta,
Ai kafin ma ta ƙaraso gunsu sun watsar da kayan
nufan ta sukai suna umma we really miss U over much, suka ƙare magana kaman zasuyi kuka danfa da gaske sunyi missing na mutanen gidan,
kafin umma ta maida musu reply sukaji muryan mamy ai da gudu sukayi kanta nan ma suka hau faɗa mata yadda sukai kewar su
Ita kuma mamy na biye musu
Waya muje ku huta kun shawo hanya,cewar mamy part dinta sukaje
Bayan sun zauna ne yusrah tace halan su momma na Bacci ne basuji dawowan mu bah,
A'a sun dan fita suna gidan goggo sunje duba jikinta kunsan bataji daɗi bah,Allah sarki bamu sani bah Allah ta ƙara sauki duk amsawa sukai da Amin,gabatar musu da abinci tayi dan da complain din suka fara,nan fa suka naɗa Saida sukai nak ne sannan suka shiga cikin daki dansu huta ~~~~~~~~
Sun sha bacci sosai se daf da magrib suka tashi shima mamy ce ta tashe su ganin magrib tayi,suna a zaune anan saiga kiran sallar magrib, alwalla sukai sukai salla bayan sun idar ne suka sallami mamy zasu cikin gida,
wajen momma suka shiga Amman bata falo tana bedroom chan ɗin suka nufa Saida suka fara knocking
basu izinin shiga tayi,da sallama a bakinsu suka shiga mommanmu munyi kewarki da yawa da yawa, Nima haka yarana ya school ɗin da kuma gajiyar tafiya
alhamdulillah gajiya kuma duk sunbi gado,Masha Allah ai danaji ance kun dawo inata zuba ido naji shiru nace Bara dai nayi sallah sai nayi bikon ku,
Momma Bacci ne yayi awon gaba damu tashin mu kenan mukai sallah
Madallah kun gaisar da mutanen gidan daiko? A'a yanzu dai zamuyi hakan,waya maza atashi aje kafin ku zauna,amsawa sukai da Toh haɗi da ficewa daga dakin
daga nan part din Ummu sukaje dan su kara gaidata, tarba mai kyau suka samu,nan na kara sanin cewa sudinfa yan gatane,
Suna a part din har akayi isha'i bayan sun gabatar da nasu sallahn ne yasa umma kiran su dan suyi dinner suna gamawa sun kankanta wajen sannan sukayi mata sallama wai zasu part din mommy nan ma sunjima dan sun samu tarba da kyau bazaka taba cewa wai ba mutum daya ta haife su ba dan suna bawa yaran kula sosai basa nuna musu banbanci yan matan nan deh yan gata ne kota ko ina,part din ammie sukaje Amman sun tadda bata dawo daga gidan goggo bah,
Part din inna suka nufa inda a hanya suka gamu da yaya khaleel sun gaishe shi ya amsa hadda musu wasan da ya saba kafin ya maida duban shi gun Sarah yace karki dade ina jiran ki akwai abinda zakiyi min, insha Allah,nan suka rabu suka karasa part din inn
tana zaune mai aikin ta na mata tausan ƙafa dan yau sun tashi mata da ciwo daman jikin tsufa sai a hankali tana ganin su tafara washe hakora tana ga yan lapai ga yan lapai sannun ku da hanya,yawwa innanmu munsame ku lafiya, alhamdulillah, sunji kewar kakar tasu sosai nan suka fara janta wai mita tsaya jira ne har yanzu bata wuce inda Mallam Adamu yaje bah anya tanason mijin nan nata kuwa, aniyarku ta biku yan baƙin ciki ai Insha Allahu sai naga auren ku sannan,amsawa sukai da Allah yasa,toh Amin idan da gaske kuke,
aide zakuyi mana kwana biyu anan koh, munyi hutu ai muna nan tare dake,madallah abu yayi kyau,
Suna ta firan yaushe gamo shima anayi ana faɗa,afff kunga zan mance bah jirgin umman ku (yayar su Abbie Hajiya Hauwa)zai sauka karfe 10 seku tashi ku shirya dan ku tarbo su daka tsalle sukai suna jin murna (nace ikon mai sama)haka ko suka fice suka hau shirin tafiya airport dan itafa Sarah ta mance yaya khaleel na jiranta nan da nan suka gama lokacin har 9:30 mota biyu suka dauka dan zuwa tarbo su umma,suna zuwa ba jimawa jirgin yayi landing ba'a dau lokaci bah suka hango ummu dasu yaya Mubarak nan suka karasa wajen suna hugging din Ummu itako tana shafa masu kai tana Allah ya albarkaci rayuwan ku,iyee ammata na sun girma Masha Allah Allah ya kawo miji na gari amsawa amsawa sukai da Amin kafin kuma su faɗa jikinta suna boye fuska waisu kunya,yaya Mubarak ne yace wai baku ganmu bane,ɗagowa sukai suna dariya kuyi hakuri hankalin mune yayi nisa ina yinku fatan kun iso lafiya suka haɗa baki, alhamdulillah,nifa na gaji da tsayuwar nan mu karasa zuwa mota mana kun wani bar mutane a tsaye cewar yaya Khalid haka suka ƙarasa wajen Mota inda umma da su mufee suka shiga Mota ɗaya su yaya mbk ma suka shiga ɗayar,haka deh har suka ƙaraso gidan part din inna suka wuce direct su yaya mbk suka hau jan inna da tsohuwa mai ran ƙarfe kinci zamanin ki kinci na ƴaƴa kuma kina cin na jikokin anya kuwa inna,
kaga tin kafin raina ya ɓaci ka tashi ka barmun daƙi tunda ba ko sisin ubanka,
tab ai ingaya Miki ba inda zani ahe mutum yaga gaskiya ache kar ya faɗa mutuwa de tazama dole kilan ma kina cikin list din yau,
ai sega hawaye idon inna dan bataso taji kalmar mutuwa bare kuma gashi suna dangantata dashi haka ɗaxu su sarah suka sata agaba sai kira mata mutuwa suke kamar akwai abinda ta tare musu,ganin haka ne yasa Umma dake ta danne dariyar tace waya mubarak zoka fita kafin in ɓata maka rai,
hakade ya tashi ya fice yana dariya su raiha ansamu nayi daman ya lafiyar kura bare kuma tayi Hauka?nan suka tasa inna gaba suna dariyar shaƙiyanci shiko yaya Khalid saida ya dara dan tsakani da Allah inna ta basa dariya wai tsohuwa da'ita ace tana tsoron mutuwa eh ai duk wani mai rai yana tsoron mutuwa amma na inna yayi yawa tinda gashi hadda kuka kamar wacce aka daka,
ganin kallon da take binsu dashi ne yasa suka tashi sadab-sadab suka gudu dan yanxu sai ta juyo kansu
maida kallanta gafuskar umma tayi tace yanxu kina kallon yaranki suka gama cimin mutunci kika gagara yi musu komi sai naga kamar ma daɗi kikeji ana min fatan mutuwa koh, idan ma sukayi min fatan mutuwa waye da hasara inba kuba sai ga wasu sabbin hawaye wani na korar wani
umma kam da dariya ke shirin fin karfinta ta daure de a haka tace inna kiyi haƙuri Insha Allahu keda mutuwa ai sekinga huhunhu Bama tabtaɓa kunni bah,bako kunya tana washe haƙora Amin Amin Allah ya maku albarka ai ba mutuwar nakewa kuka ba gudun de kar in barku cikin maraicine (jama'a kuji min inna fah😂)Umma dake kofa tanajin duk abinda suke tautaunawa daman ta shigo ne taiwa ummu sannu da hanya shine taji wanga batu wanda batasan sanda dariya ya kwace mataba,
Eh gaskiya kam ba shakka yanxu sabida Allah da Annabi Ni kuka mayar kakar ku kun tasa Ni agaba sai dariya kuke min hadda ke dana ke daukan ki mai hankali yarinya? (ummu take nufi bata kiran sunan ta alkunya irin na yar fari take nuna mata)dan na lura tin ɗaxu kike son kiyi dariya dande baki samu abokin fakewa bane toh duk kun kyauta ku tashi ku barmun ɗaki(ana shande gori a kan ɗakin nan 😎) haƙuri suka bata harde ta haƙura,
ina yini yaya ya hanya ya gajiyar tafiya, alhamdulillahi Umman yara na same ku lafiya ya yaran duka,kowa alhamdulillah,lawisa sun iso ne a'a suna kan hanya de da yake itama Flight taɓi sabida yanayin Amman nasan yanzu sun kusa dan tace 10:30 dan na tura su dauko ta, Allah ya kawo su lafiya Amin ya rabb,suna na nan dai suna fira wannan karan hadda inna,
jin horn din mota ne yasa sukace lawisa an iso kenan aiko itace da ɗanta guda sai ciki dake tare da'ita daman duk suka zo sashen inna suke fara zuwa tukuna shiyasa ma yanxu ta wuto nan saida ta fara gaida ummu da Umma sannan ta gaida inna, mutuniyar taku kuwa cewa tayi aida kin jira kin gama gaida uwayen naki hadda na ɗaki sannan ki gaida Sa'ar ki,daman anty lawisa da gangan tayi tana faɗin nide na fita hakkin ki na gaida ke atoh, iyeeee nikike faɗawa magana haka, Umma na ganin haka tace maza tabawa inna haƙuri haka ko akayi ta tashi ta wuce cikin gida wajen momma
bata falon tana bedroom chan kuwa anty lawisa ta taddata Oyoyoo momma I miss U juyowa tayi taga anty lawisa ai kamar wata ƙaramar yarinya haka ta shige jikin momma ohni yaushe wai yarinya ta zata girma neh,dariya tayi haɗi dacewa inde a gabanki ne bana girma ammie,
duk dariya sukayi suna fitowa falo daman ta gama abinda take,Bara na kawo miki abinci kici tunda Kinga ba ke ɗaya bace a'a momma saina dawo daga gaida mutanen gida okay sekin dawo haka ta fice part din momy ta shiga nan ta iske su Sarah sarakan son jiki sun kanadnaɗe momy,waiku lafiyar ku kuwa xakuzo ku danne mana mama wlh in Baku tashi bah saina falfalla maku mari sunsan halin masifar ta yasa suka miƙe suna komawa gefe,haɗi kuma da cewa ai tazo kenan
ya da zuwan ki zaki fara takurawa yarana banson takura fah,haba mommy gasu ba kaɗan ba zasu wani zo su ɗane kafar ki kamar sun sami kujera,ikon Allah lawisa kenan toh ƙaraso idan kin gama yi musu masifar,karasawa tayi tana gaida momy cikin girmamawa
ya hanyar ya kuma nauyin jiki cikin kunya ta amsa da alhamdulillah mommy Bara naje mu gaisa da ammie
Se na shigo zuwa da safe,Allah ya tashe mu lafiya,tana fita kuwa suka koma inda suke wato jikin mommy,
da sallama ta shiga part ɗjn ammie dake zaune ita ɗaya amsawa tayi haɗi da cewa yan Kaduna an iso kenan ya hanya ya Kuma nauyin jikin lafiya qlau Ammie Masha Allah Allah ya raba lafiya a zuciyarta ta amsa,a fili kuwa cewa tayi ammie wai ina su Fahad ne banji motsin suba,
sarakan yawo kenan ai yanxu khaleel da khalid suka shigo suka fita dasu,ai ammie suke koya masu yawo,tashi ammie tayi ta kawo mata ruwa da kuma papper chicken,
Ammie da kanki aida kin barshi nayi da kaina,naƙi na barki din Bara na gaida yaya na dawo,toh ammie saikin dawo, haka ta fice zuwa part ɗin inna koda taje har Umma ta wuce
gaisawa sukayi sosai da umma har tana tambayan ina sauran yaran wato su twince,cewa tayi sun fita da ƴaƴansu ba dadewa,Allah ya albarkaci rayuwan su duka amsawa ammie tayi da Amin suna zaune sega inna ta fito Barka da dare tayi mata,amsawa tayi da sakin fuska tana ina sarakan gyaran nan duk dariya sukayi kafin tace sun fita da ya'yansu, oh to Allah ya dawo dasu lafiya,Amin sallamarsu tayi tana ficewa dan tabar anty lawisa ita ɗaya~~~~~~~~~
________________✨mufee ma dai ta kammala nata exams din kwana hudu da suka wuce yar uwarta kuwa basu gama bah, dukda tanason taje gidan amman bazata iya barinta ita ɗaya bah,shiyasa tayi cancel din tafiyarta,
Ganin haka ne yasa namesake din inna tayi convincing dinta da kyar ta yadda zata tafi din Amman ba dan ranta yaso bah,Saida ta shirya kayanta sannan tayi kiran yaya sadeeq tace mishi gobe zata dawo daman yace idan sun shirya tafiya tayi kiran shi,
Ok toh ba matsala basai nazo ba kennan tunda ku biyu ne
A'a yaya kazo Ni ɗayace fah ai ita bata gama exams,ok naji insha Allah idan nasamu Flight zaki ganni yau idan kuma bansamu bah Saida zuwa da safe din Kinga tafiyar rana ta kama mu
Allah yasa ka samu na yau din
Akwai abinda kika shirya min ne da kike son ki ganni a yau din
Yaya kaide kazo plsss,ok ok zanzo din karki damu take care kinji yan matana
Yanmatan momma dai ba naka bah
Oooh to baki gayyace Ni ba kenan insha zamana
Wasa fah nake yaya
Naji yanmatan ne ko na momma
Na kane yaya
Babu koh yayana sai yaya kawai Koh
Toh yayana
Gud gurl sai Nazo kinji yan matana
Toh Allah ya kawo ka lafiya yayana
Amin bye
sauke wayar tayi tana mijin bakon yanayi akan ƴaƴansu haka kawai taji tanason tayi masa tarba na musamman dukda tasan a hotel zai sauka Amman bari tayi ko zai shigo bata sani bah,
Kitchen dinsu ta shiga ganin ba wani kaya Wadatacce yasa ta xari mayafi zuwa kasuwa haka ta dawo da kaya niƙi-niƙi
Nan fa ta duƙufa akan aikin da take dama yar uwar Tata na gida ne sai ta tayata amman tana school,
Tayi busy sosai a aikin da take jin ringing din wayartane yasa ta wanke hannun ta hadi da fita falo daman anan ta ajewa wayar ganin Ummi ne yasa da murmushi mai faɗi a fuskanta ta dauka tana cewa wato ku kuna gida kun mance damu bah shikenan Munsan zaman mu daku
Allah sarki ba haka bane sam kuna cikin ranmu abubuwa ne sukai mana yawa
Shikenan munyi muku uzuri
Godiya muke ina namesake din inna ne
Ta shiga school kunsan basu kammala nasu exams din bah
Allah ya taimaka yasa agama lafiya
Akwai labari fah amman sai kun dawo zan faɗa muku
A haba kice duk mu karkaɗe kunniwan mu
Aikuwa dai ku shirya
Kitchen din ta koma sa wayar tayi a speaker tana aiki suna fira kai bazakace da card ake amfani ba
Saida suka taya ta fira sosai sannan sukayi sallama tana ƙara maida hankali akan abinda take, cikin ikon Allah kuwa ta kammala haɗa komi da tayi tasa a wormer (niko nace abin nayi ne)
6:10 kuwa saiga kiran shi daman tasan zai kira shiyasa itama ta kafe idonta akan waya (karki bada mu mana mufee 🥱) dauka tayi bai jira komi bah yace gani a kofa xoki bude
Saida ta kara gyara vail din da tasa sannan ta buɗe kofa da sallama ya shigo zaune yakai bisa kujeran da suke a falon ko ina tas sai kamshi ke tashi kaman ba gidan student bah
Yaya sannu da zuwa
Yawwa kanwa sannu
Dan kallan shi tayi
Cewa yayi lafiya
A'a babu komi haɗi da miƙewa tayi kitchen abu mai sanyi ta kawo mishi da cup,tana zuwa ta zuba a cup din tace yaya Bismillah
Ngd,inda ita kuma ta koma kitchen abincin da ta dafa masa ne ta haɗo a tray mai kyau,
Bata ko kalleshi bah ta fara zuba mishi abinci saida ta zuba daidai wanda zai iya cinyewa sannan ta miƙa zuwa gaban shi daman akwai wani center table dake a falon shi taja sai ta daura masa abincin anan,bata kalle bah ta ƙara cewa yaya Bismillah
Toh kanwa Nagode
Yanxu dinma saida ta ɗago ta kalleshi Amman batace komi bah,tashi tayi ta duba yar uwarta inda take sanar mata yaya sadeeq yazo,Saida tasa hijab sannan ta fita dan ta gaida shi
Sun gaisa sosai kafin ta mike ta koma ciki daman karatu take
Wai fushin nan na mene dan Allah yanmatana
Ni babu komi
Toh kona koma me
Nide bance bah haka dai yake ta hanta da fira har lokacin sallah yayi tunda ya fita salla bai dawo bah Saida akayi isha'i sannan nan ma bai wani jima ba ya musu sallama yana kara jaddada wa mufee ta shirya Flight ɗinsu na karfe 7 ne amsawa tayi da Toh shi kuma ya fice abinsa
kamar yadda yace kuwa 6:30 yazo da mai taxi,ita kuwa mufee hadda kwallarta wai zata bar namesake din inna
Wacce akeyi domin ta abin dariyaama ya bata
Haka dai suka shiga motan ita da yaya sadeeq sai airport (safe trip)....................✍️