Episode 8
Episode 8📲
***
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
Rana bata karya saidai uwar ɗiya taji kunya,a yaune suke meeting dan kowa ya gama isowa, gidan cike yake da mutane tindaga kansu mama har ƴaran su, masu aiki se shige da fice sukeyi cikin dakin taron bayan sun kammala aikin sune kowa ya fice.
Saida sukayi azahar sannan suka fara fitowa wajen taro dan anan zasuyi lunch daman haka sukeyi saida aka gaigaisa kafin Anty lawisa da Anty A'isha suka fara zuba wa iyayen su da sauran yan uwansu abinci,nan suka faraci cikin farin cikin kara haɗuwa waje daya.
Bayan sun kammala,aka buɗe taron da addu'a sannan suka hau tautaunawa kafin a juyo kan samarin gidan cewan ya kamata su aje Iyali shekaru gaba yake ba baya bafa in kuma kunce ba haka bah sai muyi sadaka daku masallaci.....
Saukar da kai kasa sukai cikin kunya haɗi da faɗin za'a gyara, a'a karma ku gyara wannan karan ina daidai daku,
Toh ina dalili ace kaman ku din nan gandara gandaran nan babu aure a kanku toh bada Ni bah ahem.....
Ƙin tanka mata sukai saisu Abba ne ke bata baki da fadin ai in Allah ya yadda basu isa ƙetare shekaran nan haka bah......
Amin idan kuma da gaske kuke Ni sai naga kaman kune ke kara ingizasu akan karsuyi aure Koh?,sudai nasu kiyi haƙuri inna za'a kiyaye,
Sannan sukuma waɗan nan uwayen matan sun zaunawa mutane a gida ba aure suna gwada tsayi da iyayen su,duk da ansan ai aure lokaci ne, toh ku fiddo da mazajen ku......
Saida aka kara faɗa musu mahimmanci aure kafin Abbie ya dube su yusrah haɗi dacewa ku gayawa mani manku muna son ganin su
Saida gaban su ya faɗi dan duk dinsu basa kula kowa yanzu kuma za'a tasar da wani batun? Kuna dai jina bah, amsawa sukai suna jimami,bawai sun rasa maniman bane a'a sune dai basu bada fuskan hakan bah.......
Haka dai suke ta tautaunawa har lokacin sallar la'asar tayi inda aka rufe taro da addu'a ana kuma fatan Allah ya kara hadasu haka wani shekaran......
Anam ce ta shigo (yarinyan mama kanwar su Abbie)sarah yaya khaleel na kiranki,
Shaff ita fa ta mance shekaran jiya yaya khaleel yace tazo yanason ganin ta Amman sai ta fuske,yana ina ?
Yana waje yace kiyi sauri fah wai zaki raka shi wani waje, da yake taji maganan fita ai ba shiri ta mike Saida ta kara gyara fuskanta tayi rolling vail ko kallan su mufee batayi ba tayi gaba,dakin momma ta shiga daman ana part din suke,momma yaya khaleel yace zanyi masa rakiya yana jirana a waje,
Toh Allah ya kiyaye hanya a dai kula,
Insha Allahu sai mun dawo momma
Bye
Koda ta isa parking lot a nan ta ganshi yana jiran ta,ya wani yi mata ƙur da ido,ganin haka ne saita dan zumbura baki gaba yaya khaleel karkasa na faɗi fah
Allah ya baki hkr toh yaya Sarah bismillah shigo muje kar dare yayi kinsan yanxu lokaci ba wuya,ba musu kuwa ta shiga shiga suka fice daga gidan
Saida suka fara zuwa gidan wani abokin shi da yayi aure ba jimawa har ciki suka shiga inda yaya khaleel yayi kiran shi gashi nan a compound ya fito.
Ba wani daukan lokaci saiga shi nan ya fito shi dinma sa'an yaya khaleel dinne, a'a sannunku da zuwa buddy yawwa ya amarya,
Lfy qlau,bismillah muje ciki,nan yayi musu jagora zuwa ciki bayan sun zauna shi kuma ya shiga ciki dan kiran matan shi.
Yaya khaleel ka ce ka kawo Ni cin Chin-chin ne, ai da ka faɗa min gidan amarya zamu zo da na taho da ledar ta kare maganan cikin wasa.
Duk dariya sukai a lokaci daya,ce wa yayi ai ledar yayi miki kadan sai bakko, da sauran murmushi a fuskanta ta ce haba ai se su koramu ba shiri,
kafin ya bata amsa sun karaso cikin falon, amaryar shi bata wuce tsaran su Sarah,
Sannunku da zuwa ina wunin ku,lfy qlau ya mun same ku lafiya, alhamdulillah
Nan dai suka gaisa da Sarah kafin ta shiga kitchen ta fito musu ruwa da snack tana ajewa kuwa yaya khaleel ya kalli Sarah yana sakar mata murmushi ita ma ta mayar me dan tagane manufan shi,
Saida ya faki idon masu gidan ganin hankalin su bai kanshi ne yasa ya ɗan karkato yadda ita ɗaya zataji abinda zai ce ko akawo ledar ne
Allah ya kiyaye,toh shikenan tunda kince haka
Maida hankali yayi ga abokin nashi inda suke tashan labarai,kafin yace zasu wuce
Gashi kunzo ko ruwa baku sha ba banji daɗi bah cewar lubna.
A ƙoshe muke alhamdulillah ai haka ma mun gode cewar Sarah,tunda kince haka Bara nayi muku packaging dan Allah karki ce a'a pls,
Babu yadda ta iya bare kuma an haɗa ta da Allah toh shikenan,da sauri kuwa taje kitchen tayi musu packaging sannan ta miƙa musu inda kafin su bar gidan Saida sukayi exchanging contact.
Suna kan hanya ne yake gaya mata yana da important talk da zaiyi da ita wani garden zamuje,
Muje ko wanne Toh,ok toh bara mu karasa kafin magrib tayi
Koda suka isa garden din babu abinda suka bukata,
Cikin komawa serious kaman ba yaya khaleel din da suka sani ba ya ce dan allah gaskiya nake son ki faɗa min idan na tambaye ki kinji
Toh yaya Allah yasa nasani Allah kuma ya bani ikon haka.
Amin,kina da wanda kike so ne?
Saida ta ɗanja fasali haɗi da sauke boyayyar ajiyar zuciya,kafin ta jijjiga kai alamar a'a babu
Cikin murna ya ce Are u serious?,
very sure yaya,
Tin ba yanzu ba Sarah nakamu da soyayyar ki dan Allah ki yadda ki soni koda bai kai yadda nake miki bah dan Allah yana haɗe hannuwan shi alamar roƙo.
Jin maganan tayi wani banbara kwai toh abinda ba tayi expecting ba ai dole ta shiga shock.
Saida ya kira sunan ta kafin yace zan baki dama kiyi shawara Amman dan Allah idan baki sona karki tilastawa kanki ki fito ki gaya min zan fahimce ki kinji ko?
Cikin kunyan da bata san tana da shi ta gaɗa kai kurun
Tashi mu tafi gida yamma na daɗa yi,tashi tayi inda suka nufa motan shi,shiga sukai sai gida,da yake yaya khaleel akwai iya gudu da mota cikin kankanin lokaci suka isa.
Bata kara ce mishi komi bah tayi hanyan part din momma dan tana tunanin sauran yan uwan nata suna ciki dan sunfi yawan zama wajen momma,
Mufee ne ta fara ganin ta ta ce sai yanxu kenan? toh ina staraban mu
Saida taji tsaraba sannan ta tuna da cewan anyi musu kyauta dazun kuma gashi ta fito bata dauka ba,balle a halin yanzu kam bazata iya komawa motar shi tace zata dauka abu ba dan wani mugun kunyan shi take
Kaji ta muna mata magana amman hankalinta na wani gun, a'a karkiga laifin ta inaga bata gaji da kallon shi bane.
Wani wawan tsuka taja amman ku kam daga ku sai munafikai yan sa ido kawai,
Hehehe chaas mallama mun san komi sai a daina boye boye a sanar mana da yadda aka kwashe!
Saiku zo ku matsi baki na na faɗa muku gulmanmu kawai ta ƙare maganan tana shigewa ɗaki.
Kice dai kinji tsoro yarinya,
Bata ma san sunayi ba dan tayi gaba zuwa daƙin momma sannu da gida tayi mata kafin ta fito ta shiga dayar dakin, toilet ta shiga dan daura alwalla jin kiran Sallar magrib
Tana fitowa kuwa kaman jira saiga su ummi sunzo sallah,bata bi ta kansu ba dan yanxun tana iya biye musu magana yaje kunnin momma ita kunyan haka take shiyasa tayi gum
____________✨bayan salla isha'i Ummu da mama ne zaune suna fira harde firan nasu ya gangaro kan yaran su,
Nima dai yaya abun mamaki yake bani na rashin auren zumuncin nan nasu ki dubafa duk din su a waje sukai aure wayen nan ma da suka rage nasan a wajen zasuyi inba wani ikon Allah bah
A'a wannan karan kam da gani za'ayi abin arziki dan naga kaman idon su a gida yake
Allah ya tabbatar muna da hakan,"Amin"
Inna ce ta fito daga ɗaki inda ta samu su mama na fira,
Sannu da fitowa sukai mata
Amsawa tayi kafin tace gobe da karfe nawa zaku tafi ne?
Ni dai misalin ƙarfe biyu zan tafi
Mama kuwa tace ita sai ƙarfe hudu ne tafiyar nasu,
Madalla to kafin ku wuce sai kuje chan gidan goggo kuyi mata sannu da jiki,
Insha Allah zamu da safe Allah ya ƙara mata lafiya Amin.
Wani chapter din fira suka bude hadda inna daman akwai ta da son labarai.
____________✨ wa she gari ummu duk suka wuce babu wanda yayi saura Amman kafin su wuce din Saida suka fara dubo jikin goggo,
Gidan shiru ya koma baza a ce akwai mutane a cikin shi ba dan yayi shiru
Su Yusrah kuwa ji sukai gidan baiyi musu daɗi bah daman su dawo haka suke ji
Yan matan sun gama cinye hutun su har sun koma hadda su mufee da yar uwarta,kafin su koma saida yayun nasu suka gabatar musu da manufan su aiko suma sun karɓi tayin nasu da hannu biyu
Sun maida hankali sosai akan karatu fiye da baya dan sunce ai gwara mutum yayi ya wuce kar hustling da sukai ya tafi a banza, sun duƙufa karatu har yar rama sunyi dan daga wannan semester din shikenan sun kare
__________✨lapai
A yau suke yin sin out na kammala karatun su wanda kaman jiya suka fara Amman gashi wai yau suna sin out,sunyi kyau sosai da sosai cikin dressing dinsu na white shirt da black wando irin masu girman nan da faɗi sai sukayi rolling da black vail,takalmin kafafun su bot ne masu girman nan ya kasance white,
wow masha Allah they all look like take away.
Suda kansu sun san cewa sunyi kyau dan dressing din ya karɓe su,nan fa suka hau yiwa junan su hoto da kuma video.
Naga har yanxu su anty intee basu ƙaraso bah gashi lokaci ya kusa,kokuma bara nayi kiransu muji suna ina?
Zatayi kiran nasu kenan saiga sallamar su,aida gudu sukayi kansu sunai musu sannu da zuwa anties
Dan Allah mallamai ku dagani haba ga gajiyar hanya zanji ko daku? kun wani zo kuna niman kada mutane cewar Anty sadiya
Aunty kewar ku mukayi fah,
Muma munyi kewanku da rigimanku
Anties ga ruwa ku kora sai mu tashi mu fice,ku muka tsaya jira fah shi yasa bamu tafi ba!,
Ai nikam ba inda zani sai na huta dan kuji kenan daga zuwan mutane ku wani ce muje to anƙi!
Haba aunty narnarh ai achan akwai kujeru ga kuma iska na kaɗawa.
Ni kam kuyi ta tafiya idan na huta zan biyo bayanku insha Allah,
yan kannen mu kumuje ita ɗaya dai bazata hanaku abinda zakuyi ba balle tayi muku yanga.
Haka kam suka fice zuwa school ɗin su dan anan zasu gabatar da abinsu
Suna fita daga gidan saiga tawagar su yaya adam duk dinsu, sallama sukai a bakin entrance din,
anty intee ce ta buɗe musu kofar da mamaki take binsu da kallo ganin su yaya khaleel dan batayi Tinanin zuwan nasu ba dan koda suka bar gida duk suna wajen aiki haka dai ta watsar ta hau yi musu sannu da zuwa saida suka gaisa sannan ta gabatar musu da abu mai sanyi dan su kora.
Naji gidan shiru ko sun rigada sun wuce ne?
Eh sun wuce ba jimawa,toh Bara muje ki shirya mu wuce tunda bazaki zauna gida ke ɗaya bah
Badan taso ba tasa mayafi sannan suka fice
Koda sukaje sun iske an fara gudanar da taron bayan an kammala ne,aka basu filin sinning inda wasu ke tafiya wajen lecturas dinsu wasu kuma abokai wasu kuma dangin su
Gasu ummi ma hakan ya kasance su wajen familyn su suka nufa da maker dauke a hannun su,
Duk mika makern sukai nan fa su aunty billy,aunty A'isha,aunty sadiya,aunty intee,aunty narnarh, sukai musu sininng
Su yaya khaleel ba'a barsu a baya ba suma sunyi musu signing suna kuma taya su murnan ƙare karatu
Haka dai aka cigaba da gudanar da taron wanda duk student da hakan ta shafa zaka ganshi cikin farin ciki,
Taro ya waste lafiya; bayan sun koma gida ne su anty billy suka taimaka musu ɗauka abun bukatar su sun kuma kashe komi na gidan dan sun san ba lailai su kara dawowa su kwana a cikin shi ba,
suna tuna lokacin da suka zo gidan farko kuma a sabbin ɗalibai amman gashi yau zasu barta a daliban da a ka yaye..
Idan kallan gidan zaku tsaya sai muyi tafiyar mu fah, kun wani shanya mutane sai jira suke,
Basu kula da masifan ta ba suka shige motar dasu aunty Bily suka zo dashi da yake mota hudu suka kawo ga kuma nasu yaya khaleel sai motar ta dauke su tsaf
daga lapai zuwa minna ba wani tafiya bane kwata kwata bayi wuce 3to4 hours,balle kuma gudu suka sharara
Suna isa gida ana kiran magrib inda matan suka karasa ciki mazan masallaci suka yi
Lale lale maraba da yan lapai sannun ku sannun ku daughters ku ƙaraso masha AllAh congratulations Allah yayi ma abinda aka koya albarka yasa kuci moriyan hakan da mu ma baki ɗaya,momma ke wannan maganan cikin farin ciki dake mamaye da zuciyar ta
Aiko da sauri suka ƙarasa gareta suna rukumkumeta, shafa musu kai tayi tana Allah yayi wa rayuwan ku albarka yan matana yanzu kuma sai aure ko,
Boye fuska sukai waisu kunya magulmata kawai idan ma zaku ɗago ku ɗago ahem cewar anty Nanarh
Duk wacce zata takurawa yarana nikam ta tattara inata inata tayi gaba mun gode hakan nan
Basu kara tofa komi ba kuwa dan sun san momma akan yaran nan
Kowa yaje yayi salla idan kun idar sai ku shiga cikin gida kuyi gaisuwa,
Amsawa sukayi da to sannan suka shige ciki
Bayan salla isha'i ne suke zaune a part din momma ga laptop a gaban su da gani akwai abinda suke sonyi yadda suka maida hankali anan
Video call suke ƙoƙarin yi da su mufee dake a Sokoto dan basu kammala nasu exams din ba sai next week
Mufee ce ta dauka fuskanta dauke da tautausar murmushi inda kamannin ta da momma kara fito sak
Hy babies dan Allah kuyi mana hakuri bamu samu munyi kiranku ba sabida munyi exams yau kuma bamu fito da wuri ba sai around six.
Ai da kam munyi fushi toh yanzu ya pepar,
Alhamdulillah,ni duk na matsu mu kare mu taho gida,
Ke kuwa mufee kwata-kwata kwana nawa ya rage?ai kaman gobe ne so baby relax,
Ina inna take ne halan banji motsin ta ba se ke ɗaya,
Ki dage ta jiki kina kiranta da inna zaki sani ne ai ko name sake din inna da muke ce mata ba so take ba!
Hhhhh wake tsoro inde tana iyawa da baki na ta zo,
Ok bara ta fito daga wankan
Ni dai yasu ammie momma mommy umma mamy da kuma inna fatan kowa na lafiya,
Kowa na lafiya sunce a gaida ku,iya masi kuwa tana ɗakin ta
Lailai ma inna ce iya masi ko?to kamar a kunnin ta akayi hakan dan sai na shafa mata,
Dan Allah kifi ruwa gudu wajen faɗa mata! bara dai na tina miki inna dai ba'a iya mata kina iya zuwa ki faɗa ta ce ke ce da wannan aikin gwara dai ki rufawa kanki kafin ta tara miki jama'a atoh,
Dariya sukai suna hango tereren da za'ai wa mufee haka dai suke ta fira,name sake din inna ita ma tayi musu Allah ya sanya alkhairi kafin ta duƙufa karatu
Ganin haka ne yasa mufee tayi musu sallama akan ita ma zatayi karatun
Aiko suna zaune a wajen har wajen 1 waisu suna karatu kafin su miƙe da niyan kai kukan su wajen mai duka
Saida suka idar da nafillar ne suka biɗa waje sai bacci (asuba ta gari).............✍️