Episode 9
Episode 9📲
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
__________✨Wa she gari
Ummi da Ammie ne a kitchen suna haɗa break,part din kuwa ya ɗauki kamshi sosai,
Daman haka sukeyi sukan raba kafa wasu sashen umma wasu na mommy mamy, ammie da na momma haka suke basu chakuɗewa guri guda shiya yasa duk dinsu babu wanda bai iya aiki ba.
Ammie zaki gidan goggo din ne yau?
Insha Allahu haka nake so Ummi Amman Bara dai mu gani ko zuwa anjima!
Dan Allah Ammie zan biki na dade banga goggo ba,
Allah ya kaimu sai ki shirya muje da sauran yan uwan naki daman tana ta complain kun daina zuwa dan kunga kawar ku bata nan.
"Goggo kenan yau kam zata ganmu har sai ta gaji! dan nikam a chan zan kwana"
Allah ya bada iko,haɗi da miƙa mata basket mai dauke da womers a ciki masu kyau,"dan kaiwa inna dan Allah,Bara ni na ƙarƙare gyaran wajen"
"Toh ammie amman da kin bar gyaran idan nadowa sai nayi"
Kaji min ummi fa har gyaran guda nawa ne? na hutas dake, wannan da kika yi ma Allah yayi maki albarka da sauran yan uwanki,
Cikin farin ciki ta amsa da amin Ammien mu! kafin ta fice kaiwa inna saƙo,
___________✨ Kaduna
kin yi matukar bani mamaki!ni a tunani na idan nace zan dawo da mahaifiyata kusa dani zaki fi kowa murna da hakan?ashe a gare ki ba haka bane U really disappointed me wallahi,
Sannan kuma ki sani ba abinda zai hana na dawo da mahaifiyata cikin gidan nan saidai ke in baki iyawa ki tattara yanaki yanaki ki barmin gida
Wallahi babu inda zanje ina nan daram dam,bugu da ƙari babu matar da za'a kawo min cikin gida! Wai ma tsaya na tambaye ka! Ita da tayi zaman aure ta zauna da uwar mijin ta ne wai? Nace ta zauna da uwar mi....
Ai kafin ta karasa ya dauke ta da wawan marin da Saida taga star suna yawo daman ai mai haƙuri bai iya fushi bah
"Ke dan baki da hankali mahaifiya ta kike zaki dan baki san darajan furfura ba? Wallahi daraja daya kika ci in ba dan haka ba da bazaki ƙara koda 1 mint a gidan nan ba"
"Sai me To? Kana tinanin hakan zai dame ni ne?to kasan da sani ko a dankwalina! zama kuma da uwarka nace bana yi idan kuma kaƙi kaji ka kawo ta,da daga kai har ita sai kunyi danasani"
Ganin dai idan ya tsaya yana sauraren ta zai iya mata mugun dukan da ko iyayen da suka haife ta ba lailai su gane ta ba,dan haka ya fice daga gidan amman zuciyar shi fal tunanin wannan sabon halin na matar tasa wanda a zama nin ƙuruciya basu yi haka ba sai yanzu da suka aje yara da jikoki cikin gari.
Jiki na rawa sabida masifa ta ɗauki waya,kirar yarta tayi ta fara zaiyana mata a binda ya faru"yaya ai naso ne ya tsaya in nuna masa true color of me,banda baƙin munafinci tunda chan bai san da haɗa ni gida ɗaya da ita ba sai yanzu?
"Kinga kwantar da hankalinki! Yanxu abinda za'ayi idan ya dawo gida koda baiƙara miki magana akan hakan ba sai ke ki tayar da maganar bore zakiyi masa sosai zakiga da kanshi zai janye batun ina fatan dai kina fahimta?"
"Sosai ma kuwa ai shi yasa nake son ki yaya! kuma zanbi duk wani procedure da kika gaya min,daman dan sunga ina shiru shiru ne to yanxu an daina munsa ƙafan wando daya dasu"
Nanfa yarta ta cigaba da zuge ta, ita kuwa sai dauka take tana ganin ai kaman haka shine solution.
Saida ta tabbatar da ta zugu fiye da yadda take so sannan ta barta hakanan suna sallaman junansu.....
__________✨mufee
Hankalinta gaba ɗaya ya tattara gurin karatun da take dan suna da exams har biyu gobe shi yasa ta dukufa karatu!wayarta dake a gefen ta ya fara niman agaji wanda hakan shi ya katse mata karatun,
Koda bata duba ba tasan yaya sadeeq ne dan ringing dinshi daban ne,kai wayar tayi zuwa kunnin ta haɗi da faɗin "yaya"
Na'am kanwa ykk ya kuma studying?
Alhamdulillah yaya ya aiki?
Lfy qlau alhamdulillah!mi kike yi ne yanzu?
"Karatu nake gobe paper biyu muke dashi" ta ƙare maganar kamar zatayi kuka.
"A'a rufan asiri ni tambaya kawai nayi bance kiyi min kuka ba"
Ba shiri kuwa ta fashe da dariya dan yadda shima yayi maganan is so funny.
Mai kuka ta koma dariya kenan?
Ni daman ba kuka nake ba.
Daman nima ai bance kukan kike ba!zuwa yaushe zaku kammala exams din ne?
"Sai Friday zuwa jibi kenan"
Masha allah Allah yasa a ƙare lafiya
Kinji farin cikin da nake ne? daman na matsu ki gama dan ki samu lokaci na,sannan inace a gida ance kuce wa samarin ku Abba nason ganin su ko ba'ayi haka bah?sannan mi yasa baki faɗa min ba?
"Nide ba ruwa na inace kuma ai ance ku fidda matan aure ba?kaima ai kana iya zuwa ka faɗa musu!nikam yar kallo ce ko kuwa? ta ƙare da tsokalan shi,
"Ok tunda haka kikace ba matsala ni zanje in faɗa musu badai kince naje ba?
Ba ko ɗar tace "eh" dan ta dauka wasa yake
Kin tabbata ko? Sannan karki mance da alƙawarin inna akan duk wanda nashi mani man ya shigo gida za'a sanya auren cikin kankanin lokaci kin tina?
"Fes kuwa na tina!kuma na tabbatar"
Yanxu dai kin yadda naje gida na sanar?
Nan din ma babu ko ɗar tace "nace kaje yaya sadeeq"dan ita harga Allah ta dauka wasa yake kokuma yana son ya gwadata (nikuwa nace zakiga gwaji kuwa).
Toh nagode sosai hajiya mufeeda?
Yanxu dai ki maida hankali ki cigaba da karatu kinji? Allah kuma ya bada sa'a! take care dear bye
" Ok bye"
Lokacin da suke waya yaya khaleel na a ɗaki kuma yaji duk dubaran da yaya sadeeq yayiwa sahibar shi,nan fa shima yace ya samu nayi haka zaiyi wa sarah dan ya lura yaran saida dubaran
Kashewa sukai yaya sadeeq yace"inda banyi mata haka ba Allah kadai yasan lokacin da za'a san muna tare,yanzu dai tunda dama yazo bara naje wajen inna na shafa mata.
Gaskiya ya kamata kam! dan da zafi zafi a kan daki ƙarfe Allah ya bada sa'a! Ko kuma bara dai na bika ayi komi gaba na!
Nan suka nufa part din inna inda suka samu yan matan gidan a Wajen ta! sabida niman magana yaya khaleel akan kujerar da sarah ke zaune ya zauna yana wani mata magana kasa-kasa.
Sanin da tayi redio mai jini tana gun ne yasa ta fuske kaman bada ita yake ba.
Abinda sarah bata sani ba kuwa, idon inna na kansu qur kuwa,dan itafa indai ba idonta gizau yake mata ba har wani kallon love taga sarah na ai kawa yaya khaleel,
Tsaf kuwa yaya khaleel yasan idon inna na kansu shi yasa ma yayi wannan salon dan idan suka biye wa shirmen su su da aure ba yanzu ba.
"Inna ina kwana" cewar yaya sadeeq da wasu ladabin da bata sanshi dashi a gare ta ba,
Ganin haka ne yaya khaleel yayi karab yace "inna ina kwana ya karfin jiki" yana yi yana dan shafa ƙeyan shi irin ya ji kunyan nan.................✍️