Episode 10
Episode 10📲
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
_______✨Kallan su take cike da mamakin su wanda har bakin ta ya gagara furta komi.
Yaya sadeeq ne ya kalli su Ummi haɗi da faɗin "dan Allah ku dan bamu waje zamuyi magana" ba musu kuwa sukai musu sallama suka fice zuwa sashen mommy.
Bayan sun fita ne yaya sadeeq cikin wani sinne kai "yace inna daman munzo miki da magana mai muhimmanci ne"
Gaba daya dai mamakin su ya cika ta haka dai ta daure "to ina jinku! wata magana kenan?"
Eh daman nida mufeeda muka sasanta shine nace bara nazo na faɗa miki dan ki sani a kuma yi magana.
Alhamdulillah masha allah ya sanya alkhairi,abu yayi kyau kuwa,madalla bara nayi kiran iyayen naku dan ayi komi cikin lokaci ko kuwa?
"Haka ne kam inna"cewar yaya khaleel
Maida duban ta tayi ga yaya khaleel " "kai kuma kayi shiru ko haryanxu baku gama muna finci bane kaida Sarah? daman tana lura da duk wani motsin su.
"Ayi haƙuri inna daman wai ina jira mu dan kara sasantawa da ita ne kafin na faɗa dan"........ Katse shi tayi da faɗin"dakata mallam banda shirmen ku na banza wani sasantawa ya rage bacin wanda kukai?dan haka ni bansan wannan ba gaba ɗaya zan haɗa ba ruwa na ahem,kai sadeeq kirawo min sauran yan uwan naku suzo yanxu inasan ganin su.
Yanzu haka dai suna wajen aiki saide idan sun dawo zuwa yamma.
To bakomi Allah ya kaimu sannan ai iyayen naku sun dawo sai a haɗu ayi maganar gaba ɗaya.
To inna Bara muje mun gaishe ki,
Allah ya tsare a dawo lafiya
"Amin innanmu"
A chan part din mommy Ummi ce ta tuna kilan fa Ammien tana nan tana jiran su,dan shaf duk sun mance cewa zasu gidan goggo zumbur kuwa ta miƙe "ni ba na mance cewa zamu gidan goggo ba?
Innalillahi ko mu mun mance,Allah yasa ammie bata wuce ba,Amin dai.
"Da wannan muhawaran da kuka tsaya ai da kunje kunyi shiri,amman komi naku surutu yafi aikin yawa" cewar mommy da isowar ta falon kenan.
Nan fa suka kwasa sai part din ammie!koda suka je iske ta sukai zaune gasu twince a gefenta sai rigima suke mata.
Assalamu alaikum ammie barka da hutawa, amsawa tayi da "yawwa haɗi da faɗin halan kun mance fitar mu ko?
Ammie duk mun mance sai yanzu muke tinawa,da mun zata ko kin wuce.
"Banda abinku taya za'ai na wuce na bar yan matana!yanxu dai kuyi maza ku shirya mu tafi" amsawa sukai da toh sannan suka nufi ɗakin da suke kwana idan suna part din,da yake suna da komi a ciki yasa suka chanza shiga suka kara gyara fuska sannan suka fito falon.
"Ammie mun gama,Amman dai bada su twince zamuje ba ko?"cewar Yusrah cikin son ta tsokale su.
Ai ko nan suka ɓare baki wai zasu yi kuka raiha tace "kuyi shuru kunji lilin mu"maida duban ta tayi ga Yusra "ki fitar mana a ido kafin mu datse dake!sannan sedai in dake ne bazamu ba, amman zuwa dasu twince ya zama dole ahem."
"Ammie rabu dasu mu wuce! rana na daɗa yi,dan wadan nan yaran naga hali suke son rabawa"cewar Sarah dan fa tana hidima cikin son yawo.
Ummi ce ta riƙa hannun su fahad da fahid suka fice sannan sauran suka bisu,Ammien saida ta tsaya ta kashe wuta sannan ta fita inda ta same su suna jiran ta jikin mota, shi kuma driver ya shiga ya tada motar
Buɗe mata kofar sukai bayan ta shiga ne suma suka shiga,ganin motar bazai dauke su bane yasa Ammien cewa a kirawo dayan drivern suyi mota biyu, haka kuwa akayi sannan suka bar gidan
_________✨ goggo dan Allah kiyi haƙuri muje chan Kadunan banjin daɗin barin ki da masu aiki cikin gida! dan Allah goggo kar ki ce a'a dan Allah,
ashe fitar da yayi daga gida nan ya nufo
Sai de kayi haƙuri amman ina jin daɗin zama na anan dan ba abinda na nima na rasa, kuna yin iya kokarin ku a kaina dan haka karka damu Allah ya muku albarka,
Amsawa yayi da "Amin ya Allah,"haƙura yayi ba dan ran sa yaso ba,dan yaso ya gwada wa matar shi shike da iko da gidan kuma yana iya kawo duk wanda ya ga dama, amman bakomi tunda goggo tace bazata koma ba Allah yasa haka yafi alkhairi.
Suna nan zaune dai suna fira,bai ƙara mata maganar komawarta kaduna ba dan yasan tunda tace a'a tofah a'a ɗin ne.
Sallamar su ammie ya katse musu firar tasu inda suka ƙarasa ciki, goggo da baba suka amsa musu
Ganin su Raiha ne goggo ta ƙara faɗaɗa murmushin kan fuskan ta,"ah ah lale lale yau babba baƙi muke dashi a gidan namu?"
Ina yini Goggo ya karfin jikin
Alhamdulillah duk da kun guje ni dan kunga kawar ku bata nan.
Haba goggo ba haka bane makaranta ya ɓoye miki mu amman insha Allah muna nan tare dake,dan anan zan kwana cewar Ummi
Gyaran murya baba yayi da fara'a a fuskan shi yace "daughters yau ba magana koh?"
Laaaa baba bamu lura da kai ba kayi haƙuri,ina yini baba ya su Anty?.
Toh shikenan na haƙura, lafiya qlau Alhamdulillah,ashe kun ƙare makaranta Allah ya sanya albarka yasa aci muriyan shi.
Amin ya Allah baba mun gode.
"Toh ni bara na juya na koma inda na fito tunda naga kaman kun manta da ni"cewar ammie
Dariya su Raiha suka sanya mata,kafin baba yace haba dai taya zamu manta da maman yara,mu ah waa?
Shikenan tunda kace haka yaya,ina yini yasu Anty fatan suna lafiya
Alhamdulillah auta, ya sauran yaran,
Alhamdulillah,
Masha Allah Allah yayi wa rayuwan su albarka.
"Amin ya rabb"
Tunda suka zauna firan nan salla ke tada su,baba dai ya wuce tunda la'asar,su Ammien kuwa sai sunyi isha'i zasu tafi amman banda Ummi dan tace nan zata kwana.
Kamar yadda suka faɗa basu ne suka bar gidan ba Saida sukai isha'i, Ummi dai bata bisu ba tace tana nan tare da goggo.
________✨zaune suke a falon inna su uku Abbie,daddy,Abba,inna tayi kiransu akan batun auren su yaya adam inda take ƙara shaida musu sun fidda waɗan da suke so sai kuyi kiran su kuji daga bakin su dan waƙa a bakin mai shi yafi daɗi.
Cikin bin umarnin mahaifiyar tasu Abba ya fidda waya,kiran yaya sadeeq yayi yace ka kira sauran yan uwanka kuzo ku same mu a part ɗin inna, "toh Abba gamu nan"
Ko 10 mint basu dauka ba saiga sallamar su suna masu gaida iyayen nasu,suma amsawa sukai da walwala kamar yadda suka saba.
Daman inna ke mana baya Ni akan kun fidda matan aure ko?
Cikin kunyan iyayen nasu suka amsa da "eh"
Masha Allah abu yayi kyau,yanzu sai ku faɗa mana wane mahaifin yaran, idan yaso ko nan da zuwa jibi sai muje
Ƙara ƙasa da kai sukai dan fa yanzu Kallan su Abba suke a surukan su,
"Wai bada ku ake magana ba kunyi da mutane banza,ko dai ƙarya kuke yi min ne ba haka abin yake bah?"cewar inna cikin faɗa-faɗa
Yaya khaleel ne yayi ta maza yace"ni nawa Sarah ce,shi kuma adam yusrah, sadeeq da mufeeda,muzammil da ummi."nan ya kama baki yiyi shiru bai ƙara komi akai ba,
Wani daɗi ne ya mamaye zuciyan su daddy,dan da gaske sunyi murna da wannan haɗin,nan fa suka hau sa musu albarka sannan suka ce zasu tuntuɓi matan suji.
Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka
Godiya sukai sosai sannan suka fice daga falon.
___________✨baba ya koma gida lafiya inda matar tashi ta tayar masa da sabuwar bala'i,
Shi dai hita batun ta yai,da yaga kaman zata sanya masa ciwon kai ya tattara yana shi yana shi yayi wani ɗakin haɗi da danna key dan karta zo ta dame shi.
Ita kuwa haka ta ƙarashi masifar ta ganin dai ba tanka ta zai yi ba sai ta haƙura tayi shiru.
_________✨wai baki aje karatun nan haka nan sister?duk kinbi kin takurawa kanki haka zata yiwu kuwa? cewar mufee
Kin tanka ta tayi, tana ƙara maida hankali a kan karatun ta, saida ta gaji dan kan ta sannan ta aje books ɗin,ban daki ta shiga ta dauro alwalla tazo ta gabatar da nafilla bayan ta idar sai tabi lafiyar gado, ita kam mufee tini daman tayi baccin ta
_________✨Washegari kafin su Abbie su wuce gunrin aiki saida sukayi kiran su Raiha dan suji ta bakin su,inda suma suka amsa da haka ne duk da kuwa babu ummi da mufee Amman sun faɗi nasu.
Inda su Abbie suka kudira niyan yi musu aure kafin su wuce service, daman su kadai sukayi karatu a gida dan su aunty Billy da su aunty intee duk a ɗakin mijin su suka cigaba da karatu.
Toh daman abu tuwo na maina za'a yi sai komi yazo musu da sauƙi tunda yaran suna son junan su.
Tsayar da magana sukayi akan zasu sanya ranan auren nasu ranan Friday zuwa gobe kenan.
Cikin gida wajen su momma,mamy,umma,mommy,ammie sukai farin ciki da haka, babu wanda ya kawo matsala daman ba'a kawo wannan a lissafin mutanen gidan,dan ko akwai saide na ɓoye.
mufee suna chan a school basu san wainan da ake toyawa ba,dan yaya sadeeq bai faɗa mata ba, su Sarah ma haka sunce Saidai in ta dawo taji labari.
Ummi kam labari ya isheta har gidan goggo da yake Ummi ba kunya nan fa ta hau murna da faɗin"daman ita aure take so Allah dai ya saka ma su Abba da alheri."
Goggo dake jinta kuwa cewa tayi Allah dai ya shirya ki wagga ɗiya inda a zamanin da ne da bazaki iya fitowa koda kuwa kofan ɗaki bane dan kunya amman ku kuma ba ruwanku
Goggo kenan mu yanzu kai ya waye fa babu wannan, barin ma ace wanda zuciyanka yake so aka ba wa mutum.
Allah dai ya kai muna lokaci rai da lafiya idan muna da rabon gani,
Insha Allah Amin ya Allah goggon mu
Rana bata karya bayan sauko wa daga jumma'a aka sanya ranar auren su mufee da yayyin su inda aka sanya ranar aure nan da 4 weeks.
Ai karsu yaya muzammil suji labari dan fa kasa zama sukai suna bige bigen waya suna sanar da auren su.
Mufee dai suna school basu san wai ar da ake to yawa ba,dan har sa ranan da akai babu wanda ya gaya mata shima kuma bai faɗa bah.
________✨ bangare su mufee Allah yayi sun ƙarasa final exams din su,yanzu sauran su service, zuwa gobe suke son su koma gida tayi kiran yaya sadeeq ma ta sanar masa.
Har haɗa kayansu sukai inda suka bayar da kayan amfani wanda bazai yiwu su tafi dasu bah
Kamar yadda sukace washegari suka kamo hanya dan sauƙin su ɗaya da flight zasu bi.
Da yake tafiyar jirgi da mota ba ɗaya ba nan da nan Allah ya sauke su lafiya cikin airport na garin nasu
Mufee ce ta fara hango yaya sadeeq,dan haka suka ja trolley ɗinsu suka isa gareshi
"Yaya"cewar mufee tana ɗan shagwaɓe fuska,"na'am kanwa kun iso lafiya?," ɗaga mishi kai kawai dan haushi taji akan ya kira ta da kanwa,
Ita kam namesake din inna gaida yaya sadeeq tayi cikin girmamawa shima cikin kulawa ya amsa mata da yi musu Allah ya sanya albarka yasa aci muriyar karatun da sukai,amsawa sukai da Amin,kafin ta ja trolley ɗinta da niyar zuwa ta samu abun hawa,ganin haka ne yaya sadeeq yace "ina zaki inace gida zamuje gaba ɗaya" girgiza kai tayi alama a'a kafin ta buɗe baki tace "gidan goggo," ok toh ki shiga muje sai mu sauke ki," nan din ma girgiza kai tayi haɗi da faɗin"nagode" sannan tayi gaba dan samun abinda zai kaita gida tana fita kuwa sai ga napep shiga tayi sannan suka wuce anguwar su goggo,
Mufee kam binta da kallo,dan ta santa indai ba ita tayi niyan abu ba tofa babu wanda zai sata,ganin haka ne yasa yaya sadeeq yace suje gazayawa tayi ta shiga sit ɗin gaba shima shiga yayi haɗi da tada mota suna barin airport din. Koda suka isa gida sun tadda gidan shiru sai masu aikin ke dan kaiwa da komowa,saida sukayi sallama da yaya sadeeeq sannan ta wuce part din ammie,babu kowa a falo ga tv shima an kashe,sanin kilan tana bedroom yasa ta ƙarasa chan ɗin, knocking ta yi, Saida aka bata iznin shiga sannan ta shiga dauke da sallama a bakin ta,haɗi da faɗin "ammie nayi kewar ki sosai" Nima sosai nayi kewar ɗiya ta ya hanya,sannan ta hau yi mata Allah ya sanya alkhairi da kuma fatan suci muriyar karatun, ansawa tayi da "Amin ya Allah Ammie na,wai Ammie ina su Yusrah suke ne da yan lilin mu banji motsin su ba?" Suna chan gurin gyaran jiki kema in Allah ya kaimu sai ki fara binsu daman suma yau din suka fara, su twice kuma suna ɗakin maman su,aikuwa zanje Ammie, badan na gaji ba dana bisu yanxu daman duk na koɗe sabida shiga rana,bari in huta in bisu har chsn dan nayi kewar rigiman su,yawwa ki huta idan Allah ya kaimu sai kuje tare,"ok toh, Ammie bara nayi bacci a gadon ki idan na tashi sai nayi wanka dan bacci nake ji dan duk bamu samun isasshen bacci,namesake din inna tace a gaisar dake." "Toh ina amsawa" nan mufeeda ta bi lafiyar gado da yake baccin take ji ai tuni yayi gaba da ita. Ta daɗe tana bacci dan daidai Ammie tayo tashin ta tayi salla dan lokaci yayi,badan baccin ya ishe ta ba ta tashi,toilet ta shiga,saida ta fara yin wanka sannan ta ɗauro alwalla,saida tasa kaya sannan tazo ta gabatar da salla azahar,bayan ta idar ta ƙara komawa,gashi ba wuya bacci ke daukan ta, koda Ammie ta shigo dan tayi kiranta taci abinci samu tayi ta ƙara komawa wani baccin,ja mata kofa tayi ta fice daga ɗakin dan karta tashi.Su mufee fa an samu nayi dan da tayi la'asar komawa wani baccin tayi Saida Ammie taga yamma tayi sannan ta tashe ta hakanan. Saida da kuskure baki Sannan ta fita dan ta samu abinda zata ci har sannan bata ji motsin su Raiha ba alamar dai har yanzu suna chan............
________✨Nene dai ganin baba kaman ya janye batun dawowar goggo gidan, sai kuma jikin ta yayi sanyi, daman ba laifin ta bane zugin yayarta ce,ita daman bata da wannan akidan kowa nata ne,amman da yarta tazo sai ta nima ta ruguza mata halayya dan dai ma wani abun bata ɗauka. Wanna karan ma bata san mi yasa ta biye mata ba,dan goggo irin mutanen nan ne masu daɗi zama basu da sa ido akan abinda bai shafe su ba. Haka dai take cikin kwana biyun nan suku-suku dan abinda tayi din yana damun ta,ganin dai baza ta iya daure wa ba yasa ta nufi ɗakin baba inda ta same sa zaune yana karanta jarida daman yau bai samu yaje aiki ba.
"Sannu da hutawa Alhaji,"cikin sakin fuska yace "yawwa sannun mu"shiru tayi ta kasa buɗe baki tayi magana shine dai ya lura kaman da magana a bakin ta yace "madam fatan komi dai lafiya naga kama da magana a bakin ki?" Cikin damuwa da kuma dana sani tace eh Alhaji daman akan abinda ya faru kwana biyu da suka wuce ne dan Allah kayi haƙuri sharrin shaiɗan ne. "Kar ki damu babu komi nima nasan ba haka kike ba." "Nagode Alhaji sai maganan dawowar goggo nan ɗin shine naji shiru nace ko lafiya, kuma ga sashen nata na shiga na gyara jiya." Shima mun gode amman goggo tace bazata dawo ba, chan ɗin ya ishe ta.ɗagowa tayi da sauri kafin kuma tayi kasa da kanta haɗi da faɗin "dan Allah Alhaji ka barni naje wajen goggo ɗin ko ni nayi mata magiya ta yadda"
Tunda tace a'a kema kin san bazata chanza ba in ba wani ikon Allah ba. Ni dai ka barni inje insha Allah nasan zata yadda, koma mu koma tare da kai ɗin mu ƙara mata magiya zata Amin ce insha Allah Allah yasa haka dan nima nafison na ganta kusa dani balle kuma ga jikin tsufa sai a hankali. Haka fah Alhaji insha Allah zata yarda, Amin amin
Nan fa suka hau shirin zuwa Minna cikin kankanin lokaci suka gama shirya wa sannan suka kashe komi na gidan haɗi da rufo kofan,daman basu da yara ko ɗaya da suka rage musu dan duk su aurar dasu daman yaran nasu 4 ne
Haka dai suka kama hanyan Minna saidai muyi fatan Allah ya sauke su lafiya........
Amare sun dawo gidan bayan salla isha'i inda suka tadda mufee,sun koyi murnan ganin junansu su,nan suka fara tambayan ina sister take. "Kuma dai kusan baza ta zo nan ba tana chan gidan goggo" hakane kam Saide mu muje,lailai ma in munada time ba kun san fa idan muka fita gyaran jiki sai 8 muke dawo wa ba? Kunga ba lailai mu samu zuwa ba. Maganan ki dutse yar uwa ni kam naga kaman anyi saurin wannan gyaran jikin ace bikin tin ya rage 4 weeks.......... mufeeda ce ta katse ta da faɗin kaman ya? Kuma bikin su waaaaa...........✍️
Dedicated this page to yaya azeema marubuciyar (sarki Sameer and now su waye su?) i appreciate all what U did to me,,may Allah fulfill all ur ambition, jazakumulla Khairan ❣️
Not edited