Episode 11
Episode 11📲
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
______ eh kamar yadda kika ji haka abin yake an saka ranan auren mu nan da 4 weeks.cikin mamaki take duban sauran yan uwan nata akan su fahimtar da ita mana, suma ɗin dai abinda yusrah ta faɗa mata shi suka ƙara maimaitawa.
Tayi farinciki da saka ranar auren nasu, kuma ita mai biyayya ce ga iyayen ta koda kuwa ace ba wanda take so aka bata ba zata karbi haka da hannu biyu biyu, balle kuma wannan wanda zuciyar ta take so ne! to mi zai hanata farincik? Ita dai abinda bata ji daɗi shi ba shine da yaya sadeeeq ya ƙi ya gaya mata, amma karta yi saurin yanke hukunci zata tambaye shi dan taji dalilin shi nayin haka. suna nan a zaune suna maida yadda akayi sai ga kiran Abba ya shigo wayar mufeeda,ɗagawa tayi cikin ladabi ta mika gaisuwa gare shi, inda ya amsa mata da kulawa haɗi da faɗa mata tazo ta same su a falon su,amsawa tai da "to Abba"saida ta gayawa sauran yan uwanta Abba ne sukai kiranta, a dawo lafiya sukai mata.
Sallama tayi daga bakin kofan falon,amsawa sukai sannan sukace ta shigo. Gaida su tayi cikin ladabi suma da kulawa suka amsa mata suna kuma ƙara taya ta murnan karashe karatun ta lafiya
Daddy ne yayi gyaran murya da ƙara maida hankalin sa gare ta,mufeeda nasan kin dawo daga school kin tadda anyi miki ba dai dai ba Koh? "A'a dady bakuyi min abinda bai kamata ba duk abinda kuka yanke a kaina daidai ne kuma ni mai biyayya ce a gare ku inshaAllah,
Masha Allah Allah yayi muku albarka amsawa tayi da "Amin" zan tambaye ki Kuma ki gaya mana gaskiya kinji ko? Amsawa tayi da "isha Allahu"
Yawwa daman sadeeeq ne ya zo mana da wani batu na Niman auren ki wanda mu Kuma muka yanke hukunci muka bashi ba tare da saninki ba, duk da kafin muyi haka Saida muka tambaya sauran yan uwanki,inda suma suke faɗa mana eh shine mani manki,da gaske haka ne? Nan kam kasa buɗe baki tayi dan kunya, saidai ta a ɗaga kai kawai, dady ya ƙara wurgo mata wata tambayan kinason nashi? indai baki so yanxu sai a warware sai ki fidda wanda kike so! Shiru tayi bata ce komi ba, to ai abin da kunya ka buɗe baki kace kanason saurayi gaban iyayen ka haba dai wannan abun bada ita ba kam wai sa lallen kaza. Wannan karan Abba ne yace "muna jinki mufeeda ki faɗi ra'ayin ki babu wanda zaice miki dan mi" nan ma dai bata tofa komi ba ta cigaba da wasa da yatsun hannun ta tayi. ganin dai bazata yi magana bane sai suka ce ta tashi taje,su kam koda suka ga yanayinta da yadda take yi ne yasa suka san tana son kayanta.............
___________✨ bangaren su baba sun isa lafiya a chan gidan goggo suka sauka daman suna da nasu part din a gidan, bayan sunyi gaishe gaishe sunci abinci sun huta ne,baba ya faɗa ma goggo dalilin zuwan nasu,haɗe rai tayi tace inace na faɗa maka babu inda zani Koh? Eh haka ne goggo, kiyi haƙuri hankali na ne baya kwanciya da barin ki daga ke sai yar gidan ki a gidan nan, kuma ga yanayin jikin ki. Kar ka manta dai ko muna kusa da ku indai Allah ya ƙaddara wani abin zai faru to fah sai ya faru din, dan haka karku damu Allah yana tare damu. "Goggo dan Allah ki yadda muje chan ɗin hakkin kula dake yana a kan wuyan mu dan Allah goggo karkice a'a dan Allah da Manzonsa (SAW),goggo tunda baza ki kd ɗin ba muma zamu zauna anan ɗin" cewar anne.
Ganin dai an haɗa ta da fiyayyen halitta Annabi Muhammadu saw,yasa ta aminta cewa zata ɗin, ita daman abinda take gudu kar ya zam ta takura musu, shiyasa take gudun zuwa, Amman tunda sunce haka Allah yasa haka yafi alkhairi. "Shikenan na amince" cikin murma suka hau yi mata godiya dan gaskiya basuyi tsammanin zata yadda cikin sauƙi haka ba.
Goggo idan babu damuwa sai mu tafi zuwa gobe dan na bar aiyuka da yawa. Allah ya kai mu,kira min auta a sanar mata,amsawa yayi da toh yana danna kiran Ammie.
Tana a part ɗin Abba lokacin da kiran ya shigo mata zaune suke a falo suna Kallan news,suna kuma fira at same time. Jin wayarta na ringing ne ta zura hannun ta dauka daman a saman center table dake a falon ta daura, Picking ba call ɗin tayi,bayan sun gaisa ne yake faɗa mata zai wuce da goggo chan kd dan su zauna tare dan zama ita da daughter a gida ba mai yiwu bane, kuma ga yanayin jikin ta. Sauke ajiyar zuci tayi kafin tace Masha Allah hakan yayi kuwa yaya! ni ma zamanta a nan ɗin ita ɗaya yana damu na Allah ya tabbatar da alkhairin.amsawa yayi da Amin auta. Miƙa wa goggo wayar yayi nan suka gaisa inda take jaddada mata wai zata yi kewarta, goggo tafiyar naku zuwa yaushe ne?idan Allah ya kaimu zuwa gobe yace zamu fltafi dan ya bar ai suka. kai goggo da wuri haka,bayani goggo tayi mata sannan. Toh Allah ya kaimu nima bara inje in haɗa kaya dan nasan yaya da sammakon tafiya. Ki shirya kaya zuwa ina auta? Ai mun hutar dake kisha zaman ki mun gode. Badan ranta ya so ba ta haƙura nan dai sukayi sallama tana aje waya.
Kallan Abba tayi tana kwashe komi ta gaya mashi, Allah ya tabbatar da alkhairi Amman ai zasu bar daughter a nan dai ko? A'a zasu wuce tare da ita, bai ji daɗi ba dan yaso su barta sai ta dawo nan,daman tintini yake cewa ta dawo gurin su amman goggo tace bazata ba,dan bazata ba wa kowa ita ba. Ammie ta lura da chanzawar da yayi, amma kuma bata ce komi ba...............
_________✨ washe gari da safe Abba da Ammie sai su twice ne suka fito part ɗin inna suka nufa dan suyi gaisuwa sannan kuma su faɗa mata fitar tasu
Da sallama suka shiga inda suka same ta zaune a ƙasa tayi rashe rashe tana sauraran wa'azi,amsaw tayi da sakin fuska tana hararan su twice dan jiya sunyi mata barna suka gudu,da yake yaran suma A ne sukayi kaman basu ga abinda take musu ba.
"Inna daman zamuje gidan goggo ne, yau zasu koma Kaduna da zama wajen yaya" cewar abba, Masha AllAH abu yayi kyau Allah ya sanya albarka Amman dai banda takwara ta ko? A'a da ita za'a je,Allah sarki Allah ya tsare hanya duk amsawa sukai da sannan sukayi mata sallama suna wucewa.
________✨su goggo sun gama shirin su tsaff babu abinda ya rage dan hatta da kayan su an sa su cikin mota,abinda yasa ma basu wuce ba suna jiran isowar Ammie ne,
Ammie suma sun iso gidan goggo har ciki suka ƙarasa amma Abba bai shigaba Saida Ammie tayi masa iso,sun gaisa sosai da goggo inda yake musu addu'an sauka lafiya yana kuma aje mata bandir din yan dubu dadɗaya "a'a zoka ɗauka mun gode ai hidimar sai yayi yawa" goggo dan Allah ki ɗauka albarka muke nema, toh shikenan Allah yayi muku albarka. da Amin suka amsa suna anan ɗin hadda Abba Saiga sallamar baba da anne sun shigo inda suka gaisa sosai da Abba itama ammie sun gaisa da anne da kuma baba,kafin yace goggo muje kar rana tayi haka suka rankaya zuwa waje,ita kuma goggo ta hau kiran yar gidanta akan ta fito zasu wuce,
Bata dauki wani lokaci mai tsayi ba ta fito suka fice zuwa waje bayan sun kulle kofa da key,ganin mamanta da babanta da kuma kannen ta ne yasa ta saki murmushi shima ba mai zurfi ba, gaida su tayi cikin ladabi inda suka amsa mata da kula kannen ta kuwa wajen ta suka isa suna yi mata oyoyo, "daughter bazaki zauna a gurin mu ba ko wajen inna? Cikin sauri ta girgiza kai alamar a'a, shi dariya taso ta bashi da murmushi a face dinsa yace to shikenan Amman zaki dinga kawo mana ziyara ko? Insha Allahu Abba, Allah ya bada iko da Amin ta amsa
Shiga mota sukai dukan su inda ammie ta shiga na Abba da suka zo suka koma zuwa gida,su goggo kuma suks kama hanya Saidai muyi musu fatan sauka lafiyar.......
sun isa lafiya,anne tayi musu rakiya har zuwa masaukin su.
Saida suka huta ne yar gidan goggo tayi kiran su mufeeda take gaya musu ta koma kd ita da goggo, "Amman bakida mutumci sister shine Saida kuka koma kike gaya mana?" ita dai hakuri ta basu inda suke kara jaddada mata magana bikin su da "insha Allah" ta amsa suna yin sallama
Rayuwa nata tafiya yana lulawa dan a yanxu bikin su mufeeda sauran kwana biyu.
Sunyi kiran namesake din inna suna yi mata complain wai bata zo ba har yanzu kuma gashi biki sauran 2 days,ita dai haƙuri ta basu akan tana nan zuwa goggo ce bata ji daɗi ba fatan samun lafiya sukai mata kafin suyi sallama.
Kamar yadda tace kuwa sai ana gobe bikin suka isa zuwa Minna dan bata iya wa da hayaniya sam, a gidan goggo suka sauka, Saida suka huta sannan goggo ta tuntuɓi yar gidan ta tace sai ki tashi ki shirya muje gidan bikin ko? Cikin lagwaɓe tace goggo bazan iya zuwa yau ba dan kaina ciwo yake, nan fa goggo ta ruɗe shine baki faɗa ba? To maza tashi kisha magani idan kinsha sai ki kwanta kiyi bacci ko zai sauka. Cewa tayi tasha magani, yawwa to tunda kinsha sai ki kwanta kiyi bacci idan kin tashi zai sauka insha Allah, gaɗa kai tayi alaman toh
Ɓangaren amare sun zuba ido suna jiran suji ance gasu goggo sunzo Amman shiru. Haka dai har uku tayi aka fara yi musu make up Dan yau suke yin sisters event
Har aka gama yi musu,mutane sun fara wuce wa hall din da za'a yi program din amman shiru dai haryanzu bata zo ba.kuma basu fidda rai a zuwan nata ba. Suna a zaune sai ga anty billy ta shigo tace "iyeee yan kanne na kunyi kyau fa anya kuwa angwayen naku zasu gane ku kuwa?" Ta ƙare maganan da zolayar su, rufe fuska sukai waisu kunya, ita kam dariya suka bata haɗi da cewa "kunyan gulma ku taso muje ga motar daukan ku sun iso" Anty mota har sunzo kuma gashi sister basu ƙaraso ba; inaga kilan suna kan hanya, kudai ku taso idan tazo ai zamu zo tare da ita, sun gamsu da haka, sai suka miƙe suna ficewa da sauran ƙawayen nasu zuwa wajen da motan ke jiran su,suna fitowa kuwa aka hau kansu da guɗa har suka isa wajen moto nan suka shiga ciki aka wuce dasu hall ɗin da za'a yi program.
Da yake babu Africa time koda sukaje sun iske hall din makil da mutane,zuwan su ne yasa aka fara abinda ya tarasu gwanin sha'awa da burgewa.
Karfe 7 aka tashi daga wajen program ɗin kowa ya nufi gida harda su amare koda suka koma gida gabatar da sallah da ke kansu sukai sannan suka huta kafin su fito,part din Ammie suka nufa,koda suka je bata falo tana bedroom sai daddaikun mutane ke a falon gaida su sukai sannan suka wuce zuwa bedroom ɗin Ammie,Saida suka fara niman izinin shiga,daga ciki ammie tace a shigo,bakin su dauke da sallama suka shiga,ganin su yasa ta sake murmushi tana amsa sallaman tasu "yan matana kune tafe?" Ciki shagwaban da suka saba sukace Ammie mune sannan sukai mata barka da dare, amsawa tayi da walwala, Ammie daman munzo tambayan ki ne, "Toh ina jin ku" daman Ammie har yanzu su goggo basu iso bane? Kuma mun kira numbern sister baya shiga. Cikin mamaki Ammie tace karde kuce bata je wajen program ba?Eh Ammie bata je ba, cikin fushi ta dau wayarta dan tayi kiran diyar ta'ta dan taji abinda ya hana ta zuwa amma wayar a kashe take,maida a kalan kiran tayi ga goggo
Tana kwance gefen ta kuwa yar gidarta ne itama a kwance tana bacci,jin wayar ta na ringing ne yasa ta daga pillow ta ciro da yake goggo tayi karatu ganin Ammie ne yasa ta dauka da sallama,daga chan gefen ammie amsawa tayi haɗi da gaisheta dayi mata ya karfin jikin nata, "alhamdulillah mun gode Allah"
Daman goggo yarinyar nan bata je wajen bikin yan uwanta bah? "Cikin ɗan gimtse fuska tace batada lafiya ne zata gidan biki ko mi?" "A'a ba nufi na ba kenan,amma goggo kinsan halinta na rashin son shiga mutane,kuma nasan dan karta je bikin ne ta tsiri ciwon ƙarya" ita fa shaff ta mance da halin mutuniyar ta aiko zatayi maganin ta Allah ya kai mu gobe ko bata yiwa Allah sai taje bikin nan wannan zancen duk a zuci take yin shi, a zahiri kuwa ƙara haɗe fuska tayi kamar Ammie na kallan tace "kamar ya ciwon ƙarya? Yanzu yarinya ta wuni kwance babu lafiya amman kice wai na karya ne? Yaushe kika zama haka dan Allah?" Ai fa yau Ammie ta taro ma kanta, haƙuri ta dinga ba ma goggo harde ta sauko sukai sallama,
Duk wayar nan da sukai duk a kunnin ta dan dama ba bacci tayi ba idon ta biyu, inda ta dauƙi alwashin gobe zataje tunda an gano ta kuma tana da tabbacin goggo ma ɗin ta gano karya take ta dai kare ta ne kawai
Ammie ta faɗa masu cewa ashe wai bata da lafiya ne shi yasa basu zo ba, fatan samun lafiya sukai mata sannan suka sallame ta dan zasu su kwanta
__________✨Washe gari ya kama ranar daurin auren
kamar yadda tace kuwa bayan sun idar da salla ne tayi dan abinda zata yi sannan ta shirya tafiya zuwa gidan bikin,kallan goggo tayi a gajarce tace "na wuce" cikin mamaki goggo ke binta da kallo kafin ta buɗi baki tace "zuwa ina?" Itama a gajarcen tace "biki" goggo dai ganin da tayi kaman da gaske take tace "amman da farar safiyar nan? Bakwai batayi ba fa" juyawa tayi alamar dai zata wuce ɗin yasa goggo cewa jira ni bara mu tafi tare, da sauri taje ta shirya cikin kankanin lokaci sai gata ta fito duban ta tayi tace muje, daman kafin goggo ta fito ta kashe komi na part din suna fita kuma ta kulle kofar da key.
Goggo part din anne ta je dan karta zo tana bidar su, knocking tayi a kofa ba wani daɗe wa anne ta buɗe kofar,ganin goggo tsaye sai ta matsa mata tana goggo Bismillah shigo, a'a ba zama ya kawo ni ba nazo sallamarki zamu gidan biki, goggo da safen nan ko bakwai batayi ba fa, toh ya na iya da mutuniya ta. Masha Allah jiki yayi kyau kenan tunda gashi har zata gidan biki. taɓe baki tayi da faɗi daman duk lambo ce, murmushi kawai anne tayi dan ba'a shiga tsakanin rikicin goggo da mutuniyar ta, Bara dai muje kafin ta gaji da jira ta wuce kindai san halin ɗiyar taki.
Har wajen mota anne tayi wa goggo rakiya inda mutuniyar goggo ta mika gaisuwa ga anne amsawa tayi da sakin fuska da kuma yi mata ya jiki,amsawa tayi da Alhamdulillah, kafin suka shiga mota suka wuce ita kuma anne ta koma ciki.
Koda suka isa gidan ba wasu mutane a waje dan safiya ce sosai,part ɗin inna suka wuce direct,nan kam babu kowa dan bata bada idon da za'a zo a dame ta ba, jin ana sallama ne yasa ta ƙwala ma mai aikin ta kira akan taje ta buɗe kofa kila amaren ne, cikin girmamawa ta ansa da to tana isa wajen kofa, buɗe kofar da tayi ne ya basu daman shigowa, gaida su tayi inda goggo ta amsa mata da fara'a daman A kwai ta da fara'a
Inna kam ganin goggo yasa ta fara washe haƙora tana lale lale Hajiya Hauwa barka da zuwa Bismillah ku ƙaraso. cikin farin ciki goggo tace yawwa Hajiya Khadijah mun same ku lafiya ya kuma akaji da taro? Alhamdulillah, sun gaisa cikin mutunta juna bayan sun lafa da gaisuwar ne mutuniyar goggo ta gaida inna, Allah ya gani dai inna tana son wannan yar,nan fa ta ƙara washe baki tace lafiya qlau takwara kun iso lafiya? "Lfy" madalla.
Nan goggo da inna suka hau firan yaushe gamo suna nan a zaune tun gidan babu wani haya niyar jama'a har dai ya cika gidan kota ko Ina da hayani ya kamar yadda a kasan gidan biki dashi
Ammie da su amare basu san da zuwan su goggo ba,dan tunda suka shigo basu fita bah,anan sukayi komi nasu namesake din inna ɗaki ta shige ta hau bacci sai inna da goggo dake fira,
Saida ta sha bacci sosai wuraren sha biyu ta tashi, falo ta fito inda ta samu baƙin fuska biyu suma ɗin tsofaffi ne a jimlance ta mika musu gaisuwa,amsawa sukai suma,
Goggo ce ta du beta tace har kin tashi? Cikin yanayin ta na rashin son magana ta ɗaga mata kai alamar eh, madallah yanzu dai kije kiyi wanka ga kayan bikin ki nan takwarar ki ta ɗinka miki, taji daɗi wannan karamci na inna wanda har fuskan ta ya nuna amma sai ta nuna kaman ita ba'a burge ta ɗin nan ba, da yake daga inna har goggo sun san halinta sarai kuma yadda fuskanta ya nuna tayi farin ciki da haka amman ji yadda ta wani basar.
Koda ta koma ɗaki toilet ta shige wanda ya dauke tsawon lokaci kafin ta fito,daure da wani dan guntun towel sai wani kuma a saman kanta alamar wanka dai tayi ga jikinta sai kamshin su shower jel dinta take daman da abinta tazo,gurin dressing mirror ta ƙarasa tana zama akan kujerar, nan fa ta fara gyaran gashin ta wanda yake da tsawo ba laifi dan ya sauka kan kafaɗun ta,bayan tayi drying dinshi ne ta taje ta kuma bi suman da mai masu kamshi sannan ya kama shi da band mai kyau,komi nata a hankali take yinshi kamar wacce batada jini a jiki, jikin ta kuwa ta bishi da lotion mai kamshi,haka dai ta cigaba da shirin ta komi a tsanake har dai ta zira kayan nata da inna tayi mata riga da skirt ne rigan ya kasance half gown ne skirt din akayi shi single mai tsago amman ba wai an fasa bane tattara akayi amman dai idan tana tafiya zai rinƙa bude wa, ɗaurin ɗan kwali mai step step haka tayi shi ya kuma zauna daram kaman an manna mata ne,ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau har na wuce misali,inda ta dauki vail da phone ɗinta ta fito zuwa falo,wannan karan ta iske wasu mutanen ba sosai ba, wayenda suke a falon sun dauka cikin amaren ne nan fa suka hau guɗa suna Allah ya sanya alkhairi.ai bata san sanda ta zaro mayan Golden eyes ɗinta ba,ganin haka ne yasa goggo cewa ai bata cikin amaren ƙawar su ce. Nan ne fa ta samu salama da wannan ihun cikin kunne. Baro part ɗin tayi ta nufa na momma dan gaskiya tayi missing ɗin matar nan.
Cikin gida kuwa shirin masallaci suka hau yi da kuma na daurin auren da za'a yi bayan idar da sallar juma'a
Inda iyaye mata suka maida hankali wajen sauke wa da daurawa da kuma sauran abubuwa................✍️