EELHAM🌹

Episode 12

by @rabearhwakili

Episode 12📲









بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai




Da sallama ta ƙarasa cikin falon momma,ga yan bikin nan a falo gaishe su tayi ganin ba momma a gallon ne sai ta shige bedroom knocking tayi,daga ta ciki aka amsa mata da ta shigo,da sallama dauke a bakin ta ta shiga,sun gaisa da sauran mutanen da ke a bedroom ɗin, Amman bata ciki sai kawai ta fita,nufin ta ta bar part din tunda bata ga momma ba,har ta kai ƙofa taji ance daughter, koda bata juyo ba tasan momma ce cikin farin ciki ta juyo da ƙaya tacce murmushi a face ɗin ta,ƙarasawa tayi wajen momma,inda ta buɗa mata hannu aiko ba wata wata ta shige jikin ta tana sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah tana daukan wannan matan a matsayin uwa wacce ta tsugunna ta haife ta,shafa bayanta momma tayi jin yadda take ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ciro ta daga jikin ta tana jan hannun ta zuwa gudan ɗakin da babu kowa a ciki.
   Saida suka shiga ne sannan ta gaishe ta,amsawa momma tayi da kulawa kafin tace "daughter akwai abinda ke damun ki ne?" Cikin ƙara sauke ajiyar zuciya tace "momma ƙirjina nake jin yayi min nauyi kuma gashi gaba na sai faɗiwa yake" ta ƙare maganan kaman zata yi kuka, kiyi ta addu'a babu abinda zai faru sai alkhairi kinji, nan dai ta dinga bata baki harde ta ɗan fara sake wa kaɗan. "Momma Amare fah?" Suna chan ɗakin maman su (wato Ammie).tashi tayi tana cewa momma bara naje na duba su,toh a dawo lafiya.

Koda ta isa part din Ammie bedroom ɗinsu ta buɗe kai tsaye dan tasan suna ciki, ai kuwa suna ciki da ƙawayen su,buɗe ƙofar da akayi ne yasa yan ɗaki suka zubawa kofar ido dan su ga wake tafe,ai ƙur sukai mata da ido amman sai ta fiske kaman bata san suna yi ba. Ummi ce ta saki ihu tace wa muke gani kaman sister nan fa sauran yan uwan nata suka juyo dan su ga gaske take ko jan su take! Juyawar da zasu yi kuwa sukai kyakyawar gani.nan suka hau yi mata oyoyo,ita ma dai ta saki fuska sosai dan taji kewar surutun su, juyawa tayi tana yiwa yan ɗakin sannu dan sun zuba musu ido babu ko ƙeftawa, Raihana ce ta gabatar musu da sister  kuma friend ɗinsu wa kawayen su, daman sun jima suna jin labarin ta wajen su saidai basu taɓa haɗuwa ba,ga wayenda basu taɓa jin labarin ta ba jiya zuwa yau sunji a bakuna su Raiha.
     Samun waje tayi ta zauna tana sauke boyayyar  ajiyar zuciya haɗi da lumshe manyan idon ta. Janta da hira suke tayi duk da sun san halinta na rashin son hayaniya da kuma yawan surutu Amman dai haka suke tayi mata. Ita kuwa nata gaɗa kai dan bata jin daɗi dan tunda ta tashi yau haka ta rinka jin kanta.


2:00pn babban masallacin juma'an cike yake makil da mutane, manya manyan yan kasuwa, duk sun hallarta a masallacin dan daurin auren ƳAƳAN ALHAJI MUHAMMAD.
    Bayan idar da sallah ne aka sanar akwai daurin aure nan mutane suka koma wajen zaman su 
 A cikin masallaci kuwa na'ibi ya miƙowa liman da papper da aka rubuta suna amaren da angunan su.
 
An fara daura auren YUSRAH lawal Adam da angon ta MUZAMMIL Ahmad Adam,SARAH Ahmad Adam da angon ta KHALEEL  lawal Adam, MUFEEDA Muhammad Adam,da angon ta SADEEEQ ahmad Adam,UMMI Muhammad Adam da angon ta ADAM lawal Adam, RAIHANAT Ahmad Adam da angon ta ABDUL SALAM Mubarak. Sai aure na karshe da aka daura inda ladan ke mai mai tawa "AN DAURA AUREN KHADEEJATU USMAN TARE DA ANGON TA HYDAR MUHAMMAD ADAM AKAN SADAKI DUBU DARI"
 Su yaya khaleel angwaye sun shiga ruɗa ni jin sunan da aka ambata sake sukai da baki,amman tina ba mutum daya yake da suna shi ɗaya ba yasa suka basar, amman fah abin na a ransu.
   Su Abbie kuwa sai washe baki suke dan suna cikin farin ciki kwarai dan sun sauke nauyin da ke a kansu sun aurar da duka ya'yan su babu wanda yayi musu saura to mi zasuce da Allah banda Alhamdulillah. A gefe kuwa sai ji da ɓaƙi suke 
   Angunan dai suma fuskan nan kaman gonar auduga sai faman washe baki suke dan zuciyar su tasamu abinda suke so.......


Ɓangaren yar gidan goggo kuwa lokacin da ake daura aure a masallacin ita kuma lokacin ƙirjinta yayi wani mugun faɗiwa da sauri ta kai hannu ta dafe ƙirjin ta tana karanto addu'an da yazo bakin ta.

Yusrah da ta kula da halin da take ciki da sauri da ƙaraso gare ta tana dafa ta "sister lafiya kuwa? Mike damun ki  kika dafe ƙirji ko yana Miki ciwo ne?"  Cikin wannan halin da take ciki ta ɗan datse labbanta cikin juriya da rashin son magana tace "babu komi kawai de na ɗanji yayi min nauyi ne amman nasan insha Allah zai sauka" da kyar ta ƙarƙare maganar dan wannan maganan da tayi ya haddasa mata ciwon kai, daman haka take ba ta da yawan magana, "ooooh Allah sannu sister! Ko zaki je ɗakin inna sai ki ɗan samu ki kwanta Kinga hayaniya yayi yawa a nan"cewar Ummi, ba musu kuwa ta miƙe ta fice dan ita ma hakan zai fi mata 



bayan anguna sun dawo aka hau guɗa ana Allah ya sanya alkhairi,

Mutane sun yi al'ajab da wannan aure na yaya hydar sun shiga mamaki ya haka ta faru dan babu shi a lissafin masu auren 

Wallahi bazan yadda ba Saida ayi uwar watsi ayi duk mi za'ai amman wallahi ba ko wacce yar iskan da zata shigo min gida!har ni za'a muna furta dan ba'a sona an ƙi jini na an tsane ni?  Masifa take tana nufan ƙofan part ɗin momma da take da baƙi birjik yan biki

 Hankaɗe kofa tayi kamar shi yayi mata ba dai-dai ba,babu ko sallama ta faɗa musu ciki,su kuwa yadda a ka hankaɗo kofan ne ya ja hankalin su nan, suna ganin ta kuwa suka fara gulman ta a zuci 

Hajiya daman zuwa nayi naji ke ce kikayi wa miji na aure ko wancan tsohon ne? Ta ƙare magana kaman wacce zatayi faɗa da tsaran ta
     Cikin mamaki momma ke kallon ta, ita ba mamakin hajiyar da ta kira ta dashi take ba a'a daman ai haka take kiran ta, ita abinda ya bata mamaki yadda ta shigo mata part sannan kuma tazo ta titsiye ta da tambaya kamar wata ɗiyar cikin ta abinda ya bata mamaki kenan.
    Magana fa nake Mallama kinyi shiru ki bani amsa dan insan yadda zanci mutumcin mutum tass tass kuwa. In banda ma hassada dan kin zauna da kishiya kice ɗan ki shima sai yayi? Kinci buri  kuma yayi amman ko wace wannan yar iskan bazata kwana da igiyan auren miji na ba na rantse miki 
 
Cikin wani baƙin cikin wannan abu momma ta ɗago ta zuba mata ido kawai dan bakin ta ya gaza furta koda kalmar A ce.

Ita kuwa wannan matar haka ta cigaba da tijara da Saida hali,ita tana ganin kamar burge wace ko wayewa, kokuma ma ace kishi, dan ta tunzura momma tace "nace wani she..........tass tasss tasss tasss saukar marin da taji a kan fuskan ta shi ya katse mata tijarar da take wanda kafin ta dawo dai-dai ta kara jin saukar wani haka har aka mata maruka masu kyau guda huɗu wanda yayi sanadiyar dauke war jin ta na wuccin gadi, wanda kafin ta dawo dai-dai taji zazzaƙar murya mai taushi yana faɗi " ke wai a cikin dabbobi wace ke a ciki? Banda aikin jahilci da daƙi kanci ke baki san darajan tsufa bane? Ita ɗin tsaran ki ne? NACE TSARAN KI NE? Ihun da ta sakar mata wannan karan ya ɗan sa ta zabura, ci gaba tayi da faɗin "idan a gidan ku ba'a sanar dake yadda akewa babba ladabi da bashi girma da kuma iya magana a garesu ba to ki je ki koya dan nasan ba komi ke ɗawai niya da ke ba sai jahilci, dan haka sai a koma a je a nimo sani mtsswwwww. Ta ƙarashe maganar da jan tsuka tana ƙarasa wa gurin momma da wannan karan babu damuwar komi a rai dan EELHAM ta ɗauke mata haka da izinin Allah, mikar da ita tsaye tayi ta hanyar ɗago da hannayen ta, bedroom ta karasa suka shiga, suna shiga kuwa ta dauko mata ruwa mai sanyi ta buɗe bakin goran tana tsiyaya shi a cup "momma ga ruwa ki sha"tayi maganar cikin taushin Muryar ta amman duk da haka zaka gane a fusace take kwarai da gaske
      Bayan momma ta sha ruwan ne ta hau sanya mata albarka haɗi da faɗi "daughter mi yasa kika mare ta kin san dai ba tsaran ki bane ita ba ko?" Cikin yin ƙasa da kai tace "momma ke ba tsaran ta bane kin haifi wayenda suka fi ta nisa ba kusa ba, shine har zata iya tsayawa a gaban ki tana yi miki rashi ɗa'a kuma ina kallo momma in kasa yin komi? Wallahi bazan iya ba, balle momma wani girma ke gare ta ni banga wannan girman ba dan bana ganin girman wanda ya nima ya raina ko ya taka min uwa"  "toh naji masu uwa sai a kiyaye ba kyau marin wanda ya girme maka kinji daughter?" Gaɗa kai kawai tayi bawai dan ta ɗauki maganan bane dan ko a yanzu tayi ma ta koda Kallan banza ne sai ta nakaɗa mata mugun duka,ihu da kururuwar da sukaji an sake ne yasa momma miƙe wa da sauri tayi hanyan ƙofa ganin haka ne yasa ita ma ta bita, 

Ihu take tana fashe fashe ga ƙasa yayi ratsa ratsa da glass ɗin,Amman da yake ido ta ya rufe da kishi da masifa haka ta dinga taka glasses din nan amman ko a jikin ta

 da sauri momma ta ƙarasa gare ta ganin zata lahanta kanta a banza, ki nutsu mana MUBEENA! fashewa tayi da kuka tace bazan nutsuba a cuce ni sannan a hana ni kuka? Inaaaaaaaaa bazai yu baaaaaaaaaa, sai ga wani kukan ya kufce mata 

Jin an saka ta a jiki kuma ga kamshin tularen mijin ta nan ta ƙara lafewa sanin cewa tabbas shine, cikin kunni ta ya rinƙa lallashin ta haɗi dayi mata alƙawarin insha Allah yanzu zai rabu da wannan matar da aka aura masa, Shi ko kunyan idon mutanen da ke a falon baiyi bah.

Daga wajen daurin auren ne bayan sun dawo Abbie yayi kiran yaya hydar  falon shi suma su Abba da Daddy suna a nan ɗin 

Miƙa gaisuwa yayi ga iyayen nashi cikin girmamawa, suma ɗin ansawa sukai da kulawa, kafin Abbie yace munyi maka katsalanda hydar munyi maka aure ba tare da izinin ka ba saboda haka muke baka haƙuri dan mun san munyi ba dai-dai ba, duk da ba wai yana son auren bane kuma bayida ra'ayin auren mata biyu haka dai ya danne zuciyar shi " babu komi Abbie ku ai masu zartar da hukunci a kanmu ne koda da sanin mu ko akasin haka" duk ajiyar zuciya suka sauke daman sun san ba za'a sami matsala daga garesa ba 

Nan Abbie ya faɗa masa dalilin da akayi haka "daman uncle din EELHAM ne zai yi mata aure kuma ba'a san daga inda mutumin ya fito ba shi dai kawai ya bi kuɗi yace zai aura masa ita zuwa gobe,toh da labarin haka ya zo mana daga majiya mai karfi sai muka yanke wannan shawaran Muda iyayen ta da kuma inna, munyi haka ne dan kar ya aura mata wannan mutunin kuma alhamdulillah labarin auren naku ya isa gare sa tunda wancan din ya karɓi kuɗin shi" cikin zuciyar shi kuwa  cewa yake "kuce dai kuna niman kai da ita,ai saidai kuyi haƙuri aman bazan zauna da ita ba"

Kaman gaske yace ɗiyar wace ita dan bai gane ta ba 
  Wannan karan Abba ne yace yarinyan wajen Ammien ku ne ai, cikin gamsuwa ya gaɗa kai dayi musu godiya sosai 
    Tashi ka je Allah yayi maka albarka amsawa yayi da Amin fitar da yayi daga falon,shine ya shigo wajen momma dan shi baiyi tunanin labarin ya kai wajen matar tashi ba.

EELHAM dauko first aid box ɗin nan kiyi mata treatment amsawa tayi da toh, 

EELHAM din da momma ta ƙira shi ya tina masa da sunan matar da aka ƙaƙaba masa,kuma yana da tabbacin ita ce ɗin dai duk da a fuske ya kalle ta ya ga kaman nin ammie tattare da ita...

Baiwar Allah ta juya kenan zata wuce taji ance dakata,batayi tunanin da ita ake ba sam dan haka ta cigaba da tafiya, cikin dakaa tsawa yace "ke wacce irin daƙiƙiya ce bada ke nake magana bah?" Juyo wa tayi da mamaki a fuskan ta dan ita idan ba yanzu ba tana iya cewa bata taɓa ganin shi fuska da fuska ba saidai a hoto amman sai ta fiske tuna labarin da taji na wai an aura mata yaya hydar,dalilin shigowar ta nan kenan dan taji haka ne ɗin da gaske, shine ta tadda rashin kunyan da matar shi ke zubawa momma.

Shi bai kula da mutanen da suke a dakin ba burin shi kawai ya baƙanta mata dan kallo ɗayar da yayi mata yaji bai taɓa tsanar mutum ba sai a kanta, "kina tuna nin zan iya bacci da igiyoyin aure na akan ki? Ki san da sani na tsane ki na tsaneki with passion,Dan haka bazan iya zama da ke ba na"........... Kul kul hydar kar inji kar in gani wannan wani irin tijara ne da cin fuska saboda Allah wannan abin da kake yi tozar ci ne fa, cikin halin ko in kula yace " momma inhar na zauna da ita zan cutu ba ƙarami ba dan bani da ra'ayin auren mata biyu wannan da nake da ita ta ishe ni" ya ƙare maganar da nuna mata matar shi da yanzu ta dawo ta gefen shi sai wani yatsine fuska take,

Toh shikenan kayi abinda kake ganin shi ne daidai a gare ka, amman ina gudun maka ranar da nasani.

Momma babu abinda zai faru sai alkhairi insha Allahu. Maida duban sa yayi ga EELHAM dake daskare a wajen dan ta shiga shock ɗin maganar shi na ya tsane ta.Ganin kaman bata jin abinda yake faɗa ne yasa ya daka mata tsawa KEH DABBA, ai babu shiri ta ɗago a sittin har ita za'a kira dabba akan auren da Bama tasan da zaman shi bah? Sai taji wani abu mai ɗumi yana bin fuskan ta sai tayi sauri ta share dan kar mutane su gani, 

Ƙara kiran ta yayi da KEH KIJE NAAAAAAA............................✍🏻



DIDIDIDI DIMMMMMMM  har naji ƙirjina ta buga! Koya abin nan zai kasance? Mi yaya hydar yake shirin yi ne??????????
{🌹 EELHAM🌹}