Episode 13&14
Episode 13&14📲
***
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
_______ HYDAR kar kayi, ina gudar maka ranan da nasani, momma karki damu babu abinda zai faru sai alkahiri, ita inda ace zai bi ta ta'ta ne da tace yayi hakuri kar yayi abinda yake son yi amma inaaaaa
Maida duban shi yayi gare ta wanda hankalinta baya tare da ita sam cikin daka tsawa yace KEH!KIJE NA SAKE KI SAKI ƊAYA NA SAKE KI SAKI BIYU. yana kaiwa nan ya kama hannun matar shi suka fice daga gidan gaba ɗaya.
Innalillahi kawai ke iya fita a bakin ta, kafin ta sulale ta faɗi ji ka ke tum ta zube, ai momma da sauran mutanen falon sukayi kanta ana girgiza ta saide ko motsi batayi ba alamar babu rai. Cikin yan bikin ne wata tayi azanci dauko ruwa ta yarfa mata har sau uku kafin ta sauke wata ƙatuwar a jiyar zuciya tana bin kowa da idanu.
Aunty billy ce ta shigo dan su basu san wainar da ake toyawa ba sam suna ta baya suna aiki, ganin momma na kuka ne yasa ta ƙarasa zuwa gare ta hankali a tashe shi yasa ma bata lura da EELHAM ba dake a kwance a ƙasan hawaye yana bin fuskanta.
Momma lafiya mi ya faru kike kuka tana maganar tana share mata hawaye, cikin hawayen momma ke mata nuni da EELHAM dake a kwance a gefenta tana kuka,cikin ƙara ruɗewa tace miya sameta haka momma? naga sai kuka ku keyi dan Allah kuyi min bayani,
Ita dai bata ce komi bah,ganin haka ne yasa aunty Billy ta kama momma ta shigar da Ita zuwa ɗaki, fita tayi ta shigo da EELHAM nan ɗin saidai zuwa yanzu ta daina hawayen da take.
Labari dai zuwa yanzu ya kai zuwa kunnin masu gida da kuma sauran yan biki cewar yaya Hydar ya saki matar da aka aura masa ya kuma ja matar shi ya wuce.
Ran Abbie idan yayi dubu to fah sun ɓaci, dan mi yaya Hydar zai yi masa haka, yasan kuma bai so mi yasa a gaban su ya nuna musu yana so ɗin daman duk ƙaryace? Su dady dasu ke tare har yanzu suka rinƙa bashi baki har ya dan sauko, yace kuyi kiran kowa su zo su same mu a nan,waya sukai wa matan su da ya'yan su akan su same su a falon su, cikin ƙanƙanin lokacin suka fara isowa, Abba yayi kiran inna yayi mata bayani tace gata nan tafe ita da goggo,su momma sun iso suma da EELHAM, Amare da Anguna ma duk sun iso daman ba wani nisa sukai bah, suna a zaune a nan sai ga inna da goggo sun shigo daman su ake jira, Saida suka yi gaishe gaishe bayan wajen ya natsa ne, inna ta yi magana tace " wani mummunar labari nake ji yana ta yawo cikin gida sannan kuma yanzu kunyi kiran mutane,Allah yasa dai ba abinda ake faɗa ɗin ba ne yaron nan yayi ba?" Datse idanun shi Abbie yayi da karfi dan abin ya zafe shi kafin da kyar ya danne zuciyar shi yace "inna muma haka mukaji bamu da tabbas Saida in munji daga bakin ita EELHAM din ko Hajara wato momma" duk maida duban su sukai ga momma suna jiran suji abinda ke a ciki, Saida ta fara goge hawayen dake ta faman yi mata sintiri a face, daurewa tayi " haka ne duk abinda ku ka ji gaskiya ne ya sake ta" ai kafin ta samu daman yi musu bayani ɗakin ya dauki sallallami dan sun dauka duk jita jitan mutane ne,Amman yanzu sun gasgata naganar, Ammie kuwa duƙar da kai tayi ƙasa zuciyar ta tana tafar fasa kaman tafasashen ruwan zafi saidai bata yadda hakan ya nuna a fuskar ta ba. Su mufee ma dai sun girgiza da wannan lamarin kai abu bai yi daɗi ba, ɓangare goggo ma dai shiru tayi dan idan tace zata yi magana to lailai ba furuci mai daɗi zai fito daga bakin nata bah,
"Muna jinki taya hakan ta faru?" Abbie ke tambaya, cikin dan rawar murya kamar wacce ta ɗan da burce tace am am am sai kawai ta fashe da kuka, wa dan da suke a farlon sun dauka abinda ya faru ne yasa ta kasa magana dan an san soyayyar da take wa EELHAM ba ƙarami ba ne ba, Saidai a ranta ba haka bane dan ita idan akwai abinda ta tsana a duniyar nan to bayan EELHAM DA MAHAIFIYAR TA NE,ganin halin da take ciki ne yasa yaya sadeeeq dauko ruwa mai sanyi ya miƙa mata, ba musu kuwa ta karba ta sha sai ta hau sauke a jiyar zuciya, Saida ta samu nutsuwa ne ta faɗa abinda ya faru a nata salon dan ta mugun chanza maganar, bata faɗi laifin yaron ta ba sai ta daura duka laifin a kan EELHAM, "da kyar na samu na tankwarar da ita shi kuma na kora shi ya wuce dan matar tashi ma jikin ta duk rauni ne da ta ji mata" daskarewa tayi anan da take, ta kasa ko motsi dan kunnin ta sun gaza yarda wanna maganar da take ji daga bakin momman ta ne ya fito, innalillahi wa'inna ilai raji'un kawai take ta mai-mai tawa a zuciya,ga kuma wasu hawaye masu zafi na kwaranya daga ida nun ta, mi yasa momma zata ruguza yardan da tayi mata?mi yasa momma zata yi min haka? Wai kodai kunnin ta ne bai jiyo mata dai-dai bah? Tana cikin wannan tina nin taji muryan momma na cigaba da faɗin " ɗazu ma kafin ayi auren bayan kun kira kun sanar mana da abinda za'a yi na hada auren su, to bayan mun fita ne har na koma ɗaki sai naga ya dace ace an sanar ma daughter tunda ita mace ce sai na shiga part dinta ina ta sallama naji shiru, na juya kenan zan wuce sai naji tana faɗin ita baza ta iya haɗa jini da familyn ga ba, shi yasa bata yadda ta haihu da abban su twice ba dan haka ita ma ɗiyar ta baza ta zauna ɗin ba" sai ga wani kuka ya kufce mata cikin makirci da gani dai anyi sabo a cikin ta, kafin ta cigaba da faɗin "da na juya kenan zan fita naji Muryar ta tana faɗin kin gama abinda ya kawo ki? kin gama jin abinda zaki ji? Dama haka nake so, yanzu sai ki saka ɗan ki ya sakar min ƴa ta, dan kamar yadda kika ji bazan iya haɗa jini da ku ba,babu irin haƙurin da ban ba MARYAM ba amman tayi fir har ma tayi ikrarin idan na ƙara mata magana zanji a jiki na! Jin haka ne nikuma na sa kafa na baro mata part ɗin ta dan tana cikin fushi gaskiya, cikin kukan da take ne tace MARYAM kiyi haƙuri ya zama dole na faɗa musu gaskiya ko dan a fita hakƙin fahad da fahid da kuma shi mijin na ki dan Allah kiyi haƙuri na so na ɓoye haka amman na tina idan na ɓoye hakan komin daren dadewa a siri zai tonu ina kuma yi miki kwaɗayin tuba cikin lokaci ta" tana kaiwa nan tayi shiru sai ɗan sheshekan kukan da take.a yadda a kasan momma da kuma yadda take gwadawa kowa soyayya a gidan yasa babu wanda bai yarda da maganar ta ba, jikkunayen su duk sunyi sanyi dan sunji abinda basu taɓa zata ko tsammani ba kuma sunji haka a bakin da bazai yi musu karya ba to wani tina Ni zasu idan ba tayi hakan bane ba
Goggo kuwa koda duniya gaba ɗayan ta zata yarda cewar ɗiyar ta tayi haka to ita kam bazata taɓa yarda ba dan tasan halin autan ta, EELHAM din ma da tace wai ita ta nima ya sau waƙe mata duk bata yarda ba dan duk tasan halin kayanta.
Babu wanda yaga tashin Abba saidai saukar karan marin da sukaji ba kowa Abba ya kaiwa marin ba sai EELHAM nan fa ya hauta da duka babu ƙauƙautawa kamar daman yana jiraye da ita, duk wannan dukan da yake yi mata babu wanda yayi yun ƙurin zuwa ya tai maka mata har muryan inna da take ji sama sama tana faɗin ka ƙara mata yar banzan yarinya kawai,
Bata iya jure taga a na dakar mata ƴa babu gaira babu dalili ba yasa ta miƙe cikin dakiyar zuciya ta isa garesa, cikin karfin da bata san tana da shi ba taja diyar ta da ke ta kuka kamar ranta zai fita, Ammie dai bata ce mata komi ba taja hannun ta zuwa kofa da niyar fita taji Abba yana faɗin ke kuma Kije na sake ki saki uku, sannan kuma ki haɗa da shegun ƴaƴan ki ki barmin gida.(eh saki yana da ciwo kwarai da gaske koda kuwa ya zamana cewa baki son wannan mijin amman In dai ya furta kalmar nan zaka ji shi har tsakar kai). Tsammm tayi ta kasa gaba balle baya, a bun ya zo mata a bazata amma babu komi Allah yasa haka shine mafi alkhairi ta na jan hannun ɗiyar ta suka wuce, ganin haka ne yasa goggo miƙewa ta bi bayan su zuciya duk a kuntace,daman twice sun bi anne gida dan tace zata ta huta shine suka bi ta.
Ko juyowa su sake Kallan gidan babu wanda yayi cikin su daga nan direct gidan goggo suka wuce da tabon haka a ransu.
Koda suka isa gida kiran baba goggo tayi a waya a kan ya dawo gida zasu koma su da yake shima bai riga ya koma ba ne yasa ya dawo da mamakin jin goggo zasu koma yau
Da sallama ya shigo cikin gidan yana Kallan yanayin su yasan babu lafiya sam ga kuma matar shi cikin damuwa ita ma da gani kasan tambayar su take abinda ya faru
Da yake na miji da dakiya aka san shi shima ɗin cikin tashi dakiyar da son danne ta shi damuwar ya hau tambayar su lafiya amma shiru, da kyar dai ya samu kalla a ammie ta kwashe komi ta gaya masa wanda sai a nan wani kuka mai ciwo ya kufce mata
Cikin bacin rai yace daman sun nima auren yar mu ce dan su tozarta ta da kuma mu duka bakomi Allah yasa haka yafi alkhairi duk da Amin suka amsa nan ya hau yi musu nasiha a kan rayuwa hardai suka ɗan sake ba kaman baya ba,
Goggo taso su wuce a yau, saidai Allah bai nufa ba,
a daren ranan kam sun sha hira sosai kamar ba abinda ya faru,cikin gidan baba ya ke cewa Alhaji Muhammad mutumin kirki ne kwarai da gaske an dai fi karfin sa ne dan haka ku shaida ko bayan babu rai na na yafe ma gaba ɗaya zuri'an gidan Alhaji Muhammad,
Tabbas kuwa yaya mutumin kirki ne da kuma sauran mutanen gidan duka,dan sun gwada mana halacci kwarai da gaske nima na yafe musu duka saidai abban su ban........katse ta goggo tayi da faɗi "kul auta banda yanke hukunci cikin fushi,mukai wa Allah laifi ya yafe mana sai mu ne baza mu zama masu yafiya bah?"
Toh shikenan Allah ya yafe mana duka da Amin suka amsa daga nan suka dauko wani babin abin gwanin burgewa, sun daɗe suna fira har wajen 2 na dare amman babu wanda yaji bacci a cikin su, suma su twice sunyi bacci sun tashi a ka hau firar da su, dan harda EELY da bata da yawan magana kuma kamar ba abinda ke damun ta ta saki jiki ana tayi da ita, ganin 3 na dare tayi ne yasa goggo cewa kowa ya tafi ya kwanta dan dare yayi nisa kuma gashi hanya zamu dauka zuwa goben, badan sun so ba suka miƙe suna yi mata sallama itama ammie ta shige gudan ɗakin EELY ta bita chan inda twince da goggo suma suka shige gudan ɗakin
Bayan sun kammala abinda zasu yi ne sun kwanta Ammie ta kalli eelham dake a gefen ta "KHDIJAH" Ammie tayi kiranta da ai na hin sunan ta wanda ba kasa fai take kiranta da shi ba sai in zata yi mata magana mai muhimmancin, yanzu din ma jin haka ne yasa ta miƙe zaune tana amsawa da na'am Ammie
Matso wa tayi kusa da yarta tana kallan ta fuskarta kawace da murmushi, farkon abinda ya fara fita daga bakin ta shine ƴa ta ki zama Jaruma kamar mahaifinki, ki zama mai dakiya da shanye damuwa a koda yaushe, ki zama mai haƙuri da kauda kai,sannan the was part KHADIJAH ki riƙe martaba da kimar ki na diya mace sannan ki zama mai juriya da yafiya dan Allah karki sake ki kalla momma da abin da ya faru ki ɗauke ta tamkar mahaifiya sannan ki guji saɓawa Allah ki zama mai tsayar da salla a kan lokacin ta, duk wahalar rayuwar da zaki shiga dan Allah KHADIJAH kar ki yarda ki zuba kimar ki ta ɗiya mace DAN ALLAH,duk wanda zai aure ki ki faɗa masa gaskiya kin taɓa aure kinji Allah kuma ya kawo miki abokin zama na kwarai idan kuma kika kiyaye duk abinda na faɗa miki ko bayan raina zanyi alfahari da ke kema kuma zaki ji daɗi zama a duk inda kika tsinci kanki ALLAH YAYI MAKI ALBARKA ƳA TA INA SON KI SOSAI ALLAH YA KULA MIN DAKE, tana kaiwa nan taji hawaye na zubo mata a face sharewa tayi da sauri dan kar eelham ta gani,Saidai ta makaro, "Ammie kuka kuma kike yi? Mi ya faru dan Allah Ammie? Ammie idan dai ta nine karki damu zan ninka yadda kike bukata insha Allahu, kuma muna nan tare da izinin Allah" ta ƙare maganar da sharewa ma haifiyar ta hawaye.
Cikin murmushi wannan karan take duban ta Allah ya baki ikon yin haka kinji Allah ya albarkaci rayuwan ki dana kannan ki, Amin ya Allah Ammie na haɗi da kama hannun ta tana manna mata kiss a kan hannayen ta, ita kuma ta ja ta zuwa jikin ta tana shafa mata kai,
A hakan da take jikin Ammie har barci ya dauke ta inda Ammie ta zuba mata ido tana Kallan ta, EELHAM kama take da mahaifinta babu abinda ta bari nashi hadda skin ɗinsu kala ɗaya ne chocolate,ga ta kuma da tabon salla wanda shima mahaifin ta yana da shi, da open teeth saidai nata yafi na baban ta faɗi,ga kuma yanayin su na rashin son magana,ga kuma haƙura haƙuri Saidai a kwai su da dokin zuciya idan a ka ƙure su,
Tana a zaunen da take taji ana kiran sallar asuba wanda hakan shi ya tasar da eely daga baccin da take, ganin ta tayi a jikin Ammie ya zaro manyan idanun ta "Ammie a jikin ki na kwana shine baki tasar da ni ba dan kema ki samu kiyi bacci bah?" Cikin dariyar ta tace kar ki damu ba bacci nake ji ba maza tashi muje muyi salla kar lokaci ya shige, ita ta fara shiga tayi alwalla bayan ta fito Ammie ta shiga ita ma dai alwalla tayi sannan suka fara gabatar da nafila sannan suka kawo subhi sunyi azkar sannan sun taɓa tilawa abinda ya sauwaƙa, kafin nan fari yayi haske fita sukai Ammie ta shiga kitchen dan daura musu abin break fast, ita kuma eely ta hau gyaran part ɗin tana aiki jikin ta duk a sanyaye ta rasa mike damun ta, Saida Ammie ta kammala haɗa break ɗin ne ta fito dashi falo,zuwa sannan eelham ta kammala nata aikin duk wanka suka shiga koda suka fito da shirin su se suka fito inda suka sami goggo zaune a kujera amman da ka ganta zaka san a kwai abinda ke damun ta,har suka iso gare ta bata lura da su ba Saida Ammie ta riƙo hannayen ta sannan ta ɗago tana Kallan autar ta
"Goggo muna ta magana munji shiru lafiya?"tayi maganar cikin tautausar lafazi, cikin kauda abinda ke damun ta tace babu komi auta inaga chanjin yanayi ne
Cikin gamsuwa ammie tace shikenan goggo na, ina kwana ya jiki jikin, jiki kam alhamdulillah kinsan jikin tsufa Saida lallaɓawa, hakane goggo Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana da Amin suka amsa, maida duban ta tayi ga eelham"KHADIJAH GA GOGGO NAN ITA MA NA BAKI AMANAR TA KI KULA MIN DA ITA DAN ALLAH! Saida gaban eely da goggo ya faɗi amman Tina ai magana ake sai hankalin nasu ya kwanta, cikin dauriya tace Ammie insha Allah zan kula da ita tare da ke duk mu kula da ita, murmushi kawai tayi tana Kallan goggo haɗi da faɗin goggo dan Allah ki yafe Mani duk abinda nayi Miki tun daga yarinya har zuwa anjima, wannan karan kasa jurewa sukai suka ɗago suna Kallan ta, goggo ta buɗe baki kenan zata yi magana sai ga sallamar su baba da anne da kuma twince sun shigo dan su twice da suka fita salla ne shine suka tsaya part ɗin wajen anne.
Goggo ina kwana ya karfin jiki, lafiya qlau ya naki jikin? Jiki yayi sauƙi goggo, Masha Allah Allah ya ƙara sauƙi da Amin ta amsa, shima baba miƙa tashi gaisuwar yayi sannan suka gaisa da Ammie Anne ma sun gaisa da Ammie su twice ma sun gaida goggo da Ammie da kuma eelham, itama din dai ta mika masu baba da anne gaisuwa Saida suka gama gaishe gaishen su ne sannan suka sauko sukai break suna kammala suka kashe komi na part ɗin goggo kowa ya fidda kayan shi sannan suka wuce waje wajen mota, da mota biyu zasu je inda Ammie da baba sai fahad da fahid suka shiga mota ɗaya,da goggo da Anne, da kuma eelham suma suka shiga ɗaya suna fita daga gidan.
Sunyi nisa a tafiyar da suke ne dan sun kusa shiga Kaduna, jin wayarta tana ringing ne yasa ta ciro shi daga jaka,ganin mai gidan ta ne ke kiranta yasa ta dauka, sun ɗan taɓa fira sosai kamar baza su rabu ba, Ammie ma ta ansa sun sha fira kafin suce a bama goggo wayar, nan fa suka sa waya a speaker suka rinƙa fira cikin kaunar junan su, dan su twince ma ba'a barsu a baya ba,eely ma haka, yadda suke fira zakace ba gida ɗaya zasu ba, suna fira suna nishadi har Saida akayi ma wayar baba warning card ɗinshi is low sannan sukai sallama kamar karsu rabu
Shigar su Kaduna kenan motar su baba ya kwace ya je ya daki wani babban icce kafin kace mene wajen ya cika da jama'a,kiran ambulance a kai, nan da nan kuwa suka zo nan aka kwashe su Ammie zuwa motar, babu ciwon komi a tare da su ko kadan
Koda motar ta isa asibiti akayi gaggawar shiga dasu cikin emergency Saidai ba'a ja da wani tsawo ba,dan duk da aka duba su babu mai sauran rayuwa,(kullu nafsin za ikatull maut, ko wani mai rai zan danɗane mutuwa, innalillahi wa'inna alaihi raji'un, muna tafiya ne Amman bamu san ranan mutuwar mu ba, yanzu ne,anjima ne,ko gobe ne babu wanda ya sani yah Ubangiji Allah kajikan duk kan musulman duniya baki ɗaya kasa mu cika da imani Allah kasa muyi kyakyawar tuba kafin mutuwa Allah ya ubangiji Allah kasa muyi kyakyawar karshe yah Allah kasa mu cika da kalmar la'ilaha ilallah Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama Amin dan shugaban mu Annabi Muhammadu Allah kai mana dan hasken fuskan manzan Allah Amin ya arrahman rahimin)
Likitocin fita sukai daga ɗakin bayan sun rufe su, nan suka tadda yan sanda da aka kira lokacin faruwar abin, babban doctor din shi yayi ma yan sandan nan magana akan yana bukatar mutun ɗaya zuwa office ɗinsa.
Koda suka shiga yake gaya masa Saidai fa haƙuri wadan nan patient ɗin da suka kawo rai yayi halin sa, inda ya bukaci wayar su yace ayi kiran family su a sanar musu da halin da ake ciki
Cikin gamsuwa ya miƙawa doctor wayar daman sun ciro dukkan wayoyin su daga motar
Wayar baba suka dauka suna kunnawa wayar ta kawo babu password a wayar haka ya basu damar shiga wajen contact din shi numbern da akayi call dashi karshe ya kira ganin an sa my wife
Su goggo kuwa sun kai gida tuni daman motar su shike a gaba, koda suka isa suna ta zuba idon ganin su amma shiru har yanzu. Amman da sukai tinanin kilan sun tsaya wani gurin ne yasa suka basar.
Suna zaune dai hankalin su ya rabu biyu gashi sun kira wayar tasu duk a kashe jin karan wayarta yasa ta jawo shi da saurin ganin baba ke kira tace "goggo Kinga sai yanzu suke kira ko a ina suka tsaya?" Duk ajiyar zuciya suka sauke kafin Anne ta ɗaga kiran, ko kafin tayi magana taji muryan wani chan daban ba baba ba, ji tayi ance mai wayar sun sami accident suna a asibiti nan ya gaya musu asibitin da su Ammie suke. Salati ta sake sai kuka ya biyo baya,nan su goggo suka taso suna tambayan ko lafiya cikin kuka tayi musu bayani, duk ruɗewa sukai kafin su zari mayafi suka wuce waje,drivern daya kawo su shi sukai kira ya kaisu asibitin da akace musu.
Koda suka isa chan ɗin da kyar suka kawo kansu inda aka kwantar dasu Ammie,Police man ɗin dake a jikin kofan ne yace "doctor yace idan kunzo yana bukatar ganin ku a office ɗinsa" jiki na rawa suka buƙaci da yayi musu rakiya zuwa chan ɗin, shi dai koda ya kaisu kofa ya tsaya, sukuma sukai masa knocking daga ta ciki sukaji ance "Yes come in" da sallama suka shiga, nuna musu kujeran zama,goggo da Anne suka zauna eelham kuma na daga tsaye, Saida ya buƙata yasan ya danganta karsu take da patient ɗin,nan sukayi mishi bayani, ya kuma gamsu da hakan, Saida ya dan ja nunfashi yace "waye mai rayawa?" Ansa suka bashi da "Allah" cigaba yayi da faɗin "waye mai kashewa?" Nan ɗin ma suka amsa masa da "Allah" Masha Allah kuma duk wani mai rai baya tsallake ranar mutuwar sa Koh?" Ya ƙare maganar cikin sigar tambaya, gaɗa kai sukai jikin su yana rawa, saida ya ƙara ƙarfafawa kanshi dan sun bashi tausayi kwarai, "Saidai muyi haƙuri Allah ya karbi abinsa"
Daga kan kujerar da take ta sulale ta zube a ƙasa sumammiya, kiran nurses yayi inda aka daura anne a kan bed ɗin dake a office din, taimakon gaggawa suka bata, koda ta farfaɗo da kuka ta tashi, goggo dai shiru ne dan abin ta ji shi sosai jikin ta gashi har rawa yake, Saidai bakin ta ya kasa furta komi sai dan motsin da yake alamar addu'a take ko kuma salati, eelham ma tana layi ɗaya da goggo dan kuka ya ƙi ya fito mata kuma tanason tayi ɗin amma inaaaaa hawayen ta sun kafe saidai idon nan nata ya kaɗe yayi jaja wur kamar rushin wuta,
Bayan sun cike abinda zasu yi ne aka basu gawar wakin su, ambulance zai kaisu sukuma suka shiga mota driver ya ja suka wuce gida inda ambulance ɗin ke binsu a baya, hardai suka iso gidan har ciki suka kai gawar wakin sannan suka fice, yan anguwan kuwa jin karar motar ambulance yasa suka fito ganin motar ya shiga gidan Alhaji Sama'ila ne yasa suma suka shiga dan suji ko lafiya, sallama suke daga kofan falon Amman babu wanda ya amsa sai sheshekar kukan annen da suke ji, yasa ba wata wata suka shiga falon ga kuma gawar su Ammie yasa suka kafe anan ɗin suna karanto duk abinda ya zo bakin su
Ganin kaman basa a hayyacin su ne yasa wani aminin baba da yazo yanxu karban wayar baba ya hau kiran abokan kasuwancin shi da kuma wayenda ake hulda
Ai kafin a ce mene gidan ya cika da mutane maza da mata, dan baba mutumin jama'a ne
Goggo da kanta tayi wa ammie wanka wanda har sannan babu ɗigon hawaye tare da ita, aminin baba da wani liman su suka wanke baba dasu twince,Saida aka haɗa su sannan su goggo sukayi musu sallama wanda fuskar su yayi Fayau kamar ka kira su amsa, addu'a sosai sun sha shi gurin goggo da eelham, wanda sai a sannan wani hawaye mai zafi ya fitar mata a ido ɗaya, goggo ma Saida taga an dauke su za'a miƙa su gidan su na gaskiya ne da tunanin shi kenan ta rabu da ya'yan ta guda biyu da Allah ya bata kuma gashi Allah ya karbe su a lokaci guda nan fa ta fara hawaye wani na koran wani, Anne kuwa inaaaa kuka yafi ƙarfin ta ganin an ɗaga su za'a wuce dasu, kuka take iya karfin ta ganin har an fitar dasu daga ɗakin,tashi tayi ta fito falon, mutanen da suke anan ɗin ganin kamar tana son ta bi su ne yasa aka rirriƙeta ana bata baki da tausar mata da zuciya haka dai har aka samu ta daina wannan kukan sai kuma na zuci,
Bayan kwana bakwai da rasuwar su anyi addu'an bakwai mutane sun watse sai masu shigowa wanda ba'a rasa haka,cikin kwana ki bakwai ɗin nan duk sun rame sun fita a hayyacin su kamar ba su ba, dan basa cin abinci sai goggo ta tsawatar musu sannan suke dan taɓawa .....................✍🏻
Page ɗin nan naki ne sister Ruqayyah kiyi yadda kika so dashi, ina kuma jin daɗin
ƙarfin gwiwar da kike bani, Allah ubangiji ya bar zumunci much luv 🫶 dear😍😘
{🌹 EELHAM🌹}