EELHAM🌹

Episode 15&16

by @rabearhwakili


Episode 15&16📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai




Not edited 


Haka rayuwa ke ta tafiya zuciyoyin su ɗauke da tabon da baza su taɓa mance wa dashi ba a rayuwa, dan wannan karan rayuwa ta daura su a wani sabon babi, A wannan lokacin idan kaga EELHAM sai ta baka tausayi mayuƙar gaske,dan ta rame ta fice a hayyacin ta ta kuma ƙara zama miskilar wuce misali dan a rana ba ya wuce tayi magana 3 zuwa 4 murmushi ma kuwa ba'a maganar shi bare kuma dariya, ba wai sakin da a kayi mata bane ya dame ta ko kuma sharrin da momma tayi musu ba a'a duk ba kodaya inda ta haka ne ai bata saka kanta a damuwa bah, babban damuwarta shine rashin jigo wato mahaifiya ga kuma rashin mahaifi gana rashin kanne da kuma kawu, idan ta tuna da haka ne sai taji duk duniyar yayi mata zafi.

Anne dai ta ɗan fara dawo wa normal sai ɗan abinda ba'a rasawa dan watan su 1 kenan da rasuwa tana nan dai tana takaba 

Goggo ma dai ta sake ta miƙa wa Allah komi tana dai ta harkokin ta amma bakwai abin bai a ranta bane bah a'a yana nan daram dan wannan ba abinda zasu iya mancewa da shi bane harse ranar da Allah ya karɓi nasu Rayuwar,

Zaune goggo take a compound ɗin gidan tana shan iska, jin knocking daga baƙin gate ne yasa goggo tashi take ta buɗe dan yanzu basuda mai gadi koda sun ajiye shi basu da kuɗin biya.
     Kofar taje ta buɗe hakan ya bama wayenda suke tsaye daga waje daman shigowa, cikin mamaki ta rinƙa binsu da ido.
   Gani tayi suna ta aune sune su basu ce mata komi bah, Saida suka ƙare sannan dayar ya miƙa wa goggo wani paper hadi dayi mata sallama suna fita daga gidan.

Wannan karan bata zauna a waje ba, ciki ta shige da wannan paper da suka miƙa mata,ɗakin da EELHAM take ciki itama nan ta shiga, samun ta tayi a kan sallaya tana karatun qur'ani, ganin goggo ne yasa ta dakatar da karatun tana yi mata barka da shigowa, Saida ta kai zaune sannan ta amsa mata da yawwa eelham, cikin ɗan damuwar dake a fuskar ta miƙa mata wannan paper tace "gashin karanta mana muji" hannu biyu ta saka ta karɓi wannan papern tana warwarewa.

Bayan ta kammala karantawa ne ta ɗago a firgice idanun suna kara girma saidai sun ɗan kaɗa sunyi jaaa shima ba sosai ba 

"Lafiya qlau kike kuwa Khadijah? Kin yi shiru kiyi min baya ni mana! 
    Cikin ƙarfafawa kanta da kuma goggo, "hmmm goggo ba komi bane ba dan haka karki wani damu kanki kinji goggo nah?" Cikin rashin gamsuwa tace Khadijah tabbas akwai wani abu dan haka karki boye min ki gaya mun koma mene ne insha Allah zan karɓe shi da hannu biyu, 
    A dan sace ta share hawayen dake a fuskarta tana ƙara ƙasa da kanta cikin nuna kamar abin bai dame ta bane tace"wai fa cewa sukai gidan nan da muke ciki mu tashi wai karmu dauƙi komi a cikin shi banda Kayan mu! dan gidan nan wai anyi biyan bashi da shi wanda baba yaci shine suka dauka gidan a matsayin dukiyar su"duk maganar nan da take cikin dauriya take yinshi dan a bin yazo masu a bazata,cikin tashin hankali goggo ta hau yin sallallami cikin rawar murya tace "ina suke son muje ne wai fisabilillah,wa muke dashi da zai dube m....... Katse ta eelham tayi da faɗin "ALLAH! ALLAH SHI ZAI DUBE MU GOGGO Kuma shi zai kawo mana yadda zamuyi insha Allah, cikin gamsuwa goggo ta gaɗa kai tana kuma faɗin "insha Allah bazai bari mu tagaiyara bah da izinin sa, Da yardan sa. "Amin ya Allah, "daman goggo a kwai wani takardun gida da Ammie ta taɓa bani na ajiye mata, Kinga lokacin amfanin su yayi sai mu fidda mu koma chan ɗin, Kinga Allah ya rufa asiri" sosai ma kuwa Allah yasa haka shi yafi alkhairi, Amin ya Allah.
    Nufan inda kayan ta yake tayi, fidda duk takardun da ke a cikin box ɗin tayi, kwashe takardun makarantan ta tayi, itafa Saida taga takardun sannan ta tina anyi posting ɗinsu zuwa NYSC saidai ba'a Kaduna a ka barta ba, Kano sukai posting ɗinta, shi yasa ta gagara faɗa ma goggo dan yanzu basu da wani hanyan da zasubi a dawo da ita nan ɗin kuma baza ta iya barin goggo ita ɗaya ba dan amanar ta ce, tun tuni goggo kewa eelham magana amman shiru da gani kasan tayi nisa a tunanin da take Saida goggo ta taɓa ta sannan ta juyo ta kalleta.
    Khadijah na lura cikin kwanakin nan biyu akwai abinda ke damun ki, kuma ki ka gagara gaya min 
Cikin sauke ajiyar zuciya tace babu komi goggo daman anyi posting ɗinmu ne na NYSC saidai basu a jiyar ni ana ba sai Kano.

Madallah abu yayi kyau Allah ya taimaka yayi jagora, ai se ki fara shirye-shiryen zuwa chan ɗin

"Goggo Allah ya gani bazan iya tafiya na barki ana ba"

Dole zakije Khadijah, sannan koda kina nan ko baki a kusa da ni duk abinda zai sami bawa baya tsallake ranar sa dan haka ina mai baki baki da kije Allah ya sanya albarka.

Ƙin kulata tayi dan tasan ita kam babu inda zata ta bar goggo a gidan nan ita ɗaya duk da kuwa Anne tana nan.

Haka ta cigaba da haɗa ta kardun tana sakawa cikin trolley saida ta gama haɗa na makarantar ta sannan ta dauko takardun gidan da Ammie ta bata ajiya buɗe wa tayi dan tana son tasan address din gidan, Saidai abun mamaki abun farin ciki tana dubawa taga ashe gidan a garin Kano yake, nan fa ta hau murna tana gode wa Allah, goggo kiji wani ikon Allah, ashe wannan gidan a Kano yake?  Shikenan kafata kafar ki,
     Goggo tayi murna itama da haka suna kuma daukan niyar tafiya a gobe insha Allah, basuyi bacci ba suka hau harhaɗa kayan su Saida suka kammala sannan suka fito, Anne suka iske a falon ga kuma Charbi a hannun ta, bayan sun gaisa goggo ta hau gayawa Anne duk abinda ake ciki saidai bata gaya mata gidan da suka samu a Kano ba.
 
"Allah sarki daman hakan abun yake, wani hani ga Allah baiw Allah ya sanya albarka" cewar Anne 
   Yanzu dai sai Ki shirya da wuri dan inason muyi sammako,
A'a goggo na gode goggo,ai bana ƙara maku nauyi ba, wanda  kukayi yanzu din ma Allah ya bada lada, babu yadda goggo bata yi ba Amman Anne tayi fir,babu yadda suka iya da ita haka suka kyale ta.
   
Washe gari kamar yadda suka ce haka ta kasance bayan sunyi sallar asuba gari ya sha suka fito da shirin su na tafiya,ita ma Anne ta fito dan zata koma gidan iyayen ta a nan Kadunan, haka dai suka rabu cikin kewan juna yanzu gashi za'a koma kamar ba'ayi rayuwa a tare ba, Allah kuma da ikon shi su goggo basu faɗa wa Anne ina zasu koma ba, haka ita ma bata tambaye su ba duk da tasan an sayar da wanchan gidan goggo dake Minna.

Haka su ka fito daga gidan,maƙota na kusa suka shiga sukai musu sallama akan zasu bar gidan inda wasu sukan miƙa musu wani abun suce su sha ruwa duk da basu faɗa musu inda suka nufa ba.

Saida suka shiga gidan da ake mutumcin dasu sannan suka bar anguwar zuwa gareji suna zuwa suka samu motar Kano wanda sauran mutum uku ya cika suna shiga ba daɗewa aka samu cikon mutum ɗaya, nan fa suka ɗauki hanya sai Kano.

Anne daman bata fito ba dan ita tace sai zuwa anji ma zata wuce dan yau tq tashi da ciwon kai ga kuma kiri tana ji.

________𝘒𝘈𝘕𝘖
Su goggo sun sauka lafiya inda suka samu mai a daidai suka gaya masa anguwar da zasu da kuma gidan mai anguwa, dan Ammie ta rubuta komi hadda hotunan gidan duk suna cikin file ɗin shi yasa abin yazo masu da sauƙi kuma gashi tace su fara sauka gidan mai anguwar shi ta barwa amanar gidan.
   A dai-dai gidan mai anguwar ya sauke su, sallamar shi sukai ya fice,bin anguwar suke da kallo suna ƙara godewa Allah daya kawo su wannnan matsayin, anguwar dai gerto area ce amman a tsaftace take babu wani bola da ake ajewa a hanya kuma gashi babu kwatan dake a buɗe anguwar dai kam akwai tsafta.

Sallama sukai daga baƙin kofar gidan,muryan wata mata sukaji ta amsa da wa'alaikumus Salam jin muryan mata ne yasa wacce ta amsa musu cewa su shigo.

Ba musu kuwa suka shigo bakunan su ɗauke da sabuwar sallama, bayan sun gaisa ta kawo musu ruwa tana kuma ƙara musu sannu da hanya, bayan sun sha ruwan ne sun ɗan huta sannan goggo tace "daman mai anguwa muke nima"  "aiyoooo Allah sarki yanzu kuwa nasan yana kan hanyar sa ta dawowa sannun ku fah" Allah ya dawo dashi lafiya cewar goggo ita dai eely bata ce komi ba, suna zaune anan saiga mai anguwa Ya dawo, sun  gaisa mai ɗakin shine take faɗa masa ai baƙin shi ne, " to to sannun ku da zuwa bayin Allah ina wuni mama"  "lfy qlau alhamdulillah ya muka same ku?" Da godiya, eelham ma ta gaisar dashi, amsawa yayi da sakewa kamar ya sansu.

Eh to daman cewa akayi idan mun sauka mu fara zuwa gidan ka dan kasan da zuwan wayenda zasu zauna a gidan.......................✍