EELHAM🌹

17&18

by @rabearhwakili


Episode 17&18📲





***







Jumma'at Kareem to you all






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai








Mama da kin kara yi min bayani ta yadda zanfi fahimta, bayani tayi masa dalla-dalla ta yarda zai fahimta kuma ta fito masa da takardun gidan da sauran abubuwan da zasu zama evidence, "na'am na fahimta kwarai da gaske,daman tace idan an samu wani mabuƙaci a basa ya zauna, kwana biyu ma banji daga gare ta ba"      "cikin dauriya goggo ta furta ai Allah yayi mata rasuwa wata guda kenan da kwanaki"    "innalillahi wa'inna alaihi raji'un rayuwa kenan kai Allah yayi mata rahama mutuniyar kirkice kwarai da gaske Allah yayi mata rahama" amsawa sukai da Amin duk ɗinsu hadda matar mai anguwar.
 "laure ki kawo masu abinci bari nasa a gyaro gidan dan babu kowa a cikin shi ƙura duk sun sauka" " karku damu da hakan yanzu idan muka je ai ma gyara basai an saka yara ba" kiyi haƙuri dai a gyara ɗin mama dan gidan yayi ƙura dan tunda aka sayi gidan babu  wanda ya zauna"  toh shikenan Allah yayi albarka, Amin Amin mama,yana ta yiwa goggo da eelham fira da take kamar bata a gurin, suna a nan ɗin sai ga matar shi ta kawo musu abinci shi kuma ya fice daga gidan,suna jin yunwar dan haka baza suyi wa kansu ba,eely ne dai Saida ta gama iyayinta sannan ita ma ta fara ci, bayan sun kammala ne matar mai unguwa umma laure tayi musu jagora zuwa ɗakin baƙi dan gidan nasu ba'a rabasa da ɓaki shi yasa na suka ware ɗakin daban shiga sukai dan su huta kafin a gama gyara musu nasu gidan, 

Sun sha bacci sosai kafin suka tashi wanda shima kiran sallar nagrib ne ya tasar dasu ba dan haka bah ƙilan su daɗe sunayi fiye da haka ma, sun gabatar da salla suna a zaune a inda sukayi sallar sai ga sallamar umma laure daga bakin kofan, "banda abiki kya tsaya daga waje ki shigo" cewar goggo, da dariya a fuskarta ta ƙara yin wani sallama tana mai kutsa kanta a cikin ɗakin ga kuma hannun ta dauke da kwanukan abinci,ajiye musu tayi tana ƙara musu barka da dare, amsawa goggo tayi wai hidimar ai tayi yawa yarnan Allah ya saka da mafificin alkhairi yayi albarka, da Amin ta amsa kafin ta miƙe tana ficewa daga ɗakin. Saida sukai sallah isha'i sannan suka dan taɓa abincin dan basa jin wani yunwa haka nan, fita da kwanon eely tayi inna biye da ita a baya, a tsakar gidan suka samu masu gida zaune bisa tabarma suna shan iska ganin fitowar goggo ne yasa suka gaisar da ita baba laure kuwa wata tabarma ta ɗauko ta shimfida mata tana ƙara yi mata sannu, bayan sun ƙare gaisuwar ne, mai unguwa yake mata bayani an gama gyaran gidan yanzu ma suke gamawa, madalla abu yayi kyau Allah dai yayi maku albarka dan banida bakin da zani gode maku, yanzu dai Bara mu zo mu koma, cikin sauri umma laure ta furta "goggo dare tayi yanzu da kin bari ko zuwa da rana haka"Allah yana gani tana son matar nan da yar jikanta ɗin nan wanda ba dan ta gaisar dasu ba zata ce ko kurma ce, "a'a laure yanzu dai zamu wuce ai dare baiyi nisa ba kinga karfe tara ma batayi ba dan haka ke Khadijah tashi ki dauko kayan mu mu tafi,babu yadda mai anguwa da umma laure basuyi da goggo ba akan ta kwana ko zuwa da safe ne sai ta wuce, kunsan dai halin mutuniyar tamu fir kuwa taƙi zama, babu yadda suka iya sai tashi sukai dan suyi rakiyar su daman eelham ta kwaso musu kayan nasu itama ɗin ta matsu su koma chan ɗin daga ita sai goggo,

Gidan nasu bashi da wani nisa da gidan mai unguwa dan bai wuce gida 6 tsakani, babu wutar nepa a unguwar shi yasa basu samu sunga wajen da kyau ba,key ya saka ya buɗe masu ƙofar gidan, shiga sukai hadda baba laure inda mai anguwa ya tsaya daga kofa,

Koda suka shiga aje kayan hannun su sukai, zanin gadon dake a hannun baba laure ta shimfiɗa masu shi a ƙasa dan ɗakin babu komi a cikin shi sai in sun siya sunsa,godiya mai yawa kuwa da albarka tasha su gurin goggo, Saida ta ɗan taya su da wani abin sannan tayi musu Saida safe tana ficewa,

Tabarman da baba laure ta haɗo musu dashi ne goggo ta ɗauka taje tayi shimfiɗa dashi daga matsakaici yar tsakar gidan nasu da yasha cement, nan ta kwanta dan tasha iska tana a nan taji shiru eelham bata fito ba ƙwala mata kira ta hauy"Khadijah wai baza ki fito kisha iskar duniya ba, kin wani je kin lumƙume a ɗaki kamar wata sabuwar amarya?" eely dake jinta ƙin tanka mata tayi to kaji goggo fa wai tazo ta sha iskar duniya to ƙilan yanzu na chan take sha, abinda take ta faɗi kenan gyara kwanciya tayi dan duk taji bayan ta na ciwo duk da irin bargon nan masu taushi ne baba laure ta kawo musu amman sai ta jita kamar a ƙasa, nan fa ta fara tariyo rayuwarta ta da da jin daɗin da tayi amman yanzu gashi rayuwar ya ƙara kawo su wani bigiri, wai ita da take kwana a royal bed su Italian bed wai gashi itace a ƙasan cement ba tiles ba,ta saba bacci cikin ac da fanka tayi lullaɓa da bargo mai taushi da laushi wai yau itace cikin zafi babu ko handfan babu kuma abun lulluba ga sauro duk da kuwa ga maganin sauron ansa amman kamar a banza,yah Ubangiji Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawar, yah Allah kasa karshen wahalar kenan,taɓa fuskar ta tayi taji danshin hawaye, sharewa tayi tana kara jaddada wa a rai kuka ba nata bane ba, sai kuma ta tuna da nasihar da mahaifiyar ta tayi mata na ƙarshe akan cewa ta zama mai juriya da haƙuri "insha Allah Ammie zan kasance fiye da yadda kika buƙata!Allah yayi miki rahama" goge hawayen tayi tass sannan ta gyara kwanciya dan ta kuɗiri aniyar mancewa da tayi rayuwar huta zata ɗauki Wannan sabon rayuwar kamar a ciki ta tashi, jin sallamar goggo ne yasa ta ƙara lafewa dan yanzu sai tazo ta cika mata kunni, ita kuwa goggo ganin haka ne yasa ta ɗauka ko baccin tayi, gefenta ta kwanta tana kwanciya kuwa babu daɗewa bacci ya ɗauke ta, itama eely baccin ne ya ɗibe ta wanda bata san da zuwan shi ba asuba tagari.........


_______𝘞𝘈𝘚𝘏𝘌 𝘎𝘈𝘙𝘐
  Zaune suke a ɗaki sunyi zugum zugum, tunda EELHAM ta kammala sharan gidan ta koma ɗaki ta zauna, dan basu da abinda zasu yi break dashi sai insunje kasuwa sannan, kuma goggo tanason ta fara sana'a dan zama haka bashi yuwa, jin ana sallama yasa eelham leƙawa dan taga wake sallamar koda ta fita wata matashiyar yarinya ta gani wanda zasu yi tsara da eelham ɗin da murnushi a fuskar matashiyar tace wa eelham barka da safiya, da alhamdulillah eelham ta amsa daga nan bata ce mata komi ba ta koma ɗaki tayi kiran goggo,nan kam bata biyo ta ba ita ɗaya ta fito, sannu da zuwa yanmata, cikin fara'a ta gaida goggo sannan ta miƙa mata tray ɗin dake a hannun ta tace "goggo gashi nan inji umma na tace a kawo maku tana kuma gaishe ku wai tana nan shigowa anjima. "Daga gidan mai anguwa koh?"    "eh goggo"  "madallah an gode Allah ya bada lada kice ina mata sannu da aiki" tana ansan tray ɗin gefe guda kuma tana ganin kimar matar a idanun ta, nan saman ta barman dake shimfiɗe a wajen ta ajiye tray ɗin ta shiga kwalawa eelham kira, fitowa tayi fuskar nan kicin kicin, "gani" tayi maganar a gajarce "ai na ganki mallama, daman cewa nayi kizo kiyi kari sannan kije mana kasuwa a ɗan sayi abinda babu" "TOH" shima a gajarce ta furta, wannan matashiyar na daga tsaye dai tana kallon su cikin burgewa, "yanmata baki zauna ba?"cewar goggo tana duban wannan matashiyar, cikin fara'an tace "Toh" tana ƙarasawa kan tabarman ta zauna ita ma, wanko hannu tayi sannan ta zauna dansu fara ci ɗin, "yanmata zo muci kema"cewar goggo,zuwa yanzu kam eely ta fara quluwa dan mi goggo zata wani ce tazo taci,amman hakan ko a fuskarta bai nuna bah,ita kam ba musu taje ta wanko hannu tazo ta zauna nan fa inna ta buɗe kwanun masa ke ciki mai yawa wanda ba lailai su iya cinyewa ba, dayar kuma miya ce ga kuma kofin silba shima da kunu cike da shi nan fa suka hau ci duk da eely bata da wani cin abinci amman masan yayi mata daɗi sosai shi yasa ta buɗe ciki ta ci iya ci kafin ta miƙe wai ta ƙoshi,ganin haka ne yasa itama matashiyar ta cire hannu tabi eely wajen wanke hannu, sabida jan magana ruwan da eely ta ɗibo zata zuba a hannun ta kenan sai wannan matashiyar tara hannun ta ta wanke ta fice a gurin, binta da kallo eely tayi tana datse lips ɗinta

Wajen goggo matashiyar ta koma tayi zaune suna fira da goggo kamar sun saba inda goggo ta tambaye ta sunan ta "Ruqayyah" Masha Allah suna mai daɗi rakiya, zaro ido tayi jin wai ance mata rakiya,eely da take doso wajen kaɗan ya rage murmushi ya kwace mata dan yadda ruqqy tayi sai ya bawa mutum dariya, goggo ma dai Saida ta dara, cikin shagwaɓa tace haba goggo nifa cewa nayi Ruqayya" cikin dariya goggo tace "shikenan na bari"

eely kam taɓe lips ɗinta tayi ta nufi ɗaki ganin hakan ne yasa Ruqayyah bin bayanta,a kwance ta ganta a ɗakin kan bargon da suka kwana, ƙarasawa tayi tana kwaciya a gefen nata tana kuma tureta "Ni mallama matsa min" a dan fusace ta juyo daman ta bata baya ne, amman ganin kamar ita ruqqy abin joy yake bata sai ta share tana ƙara cin face, haka dai ta dinga janta da niman magana dayake eely miskila ce ko ci kanki bata ce mata ba, ta ma nuna kamar ba tasan da zaman mutum a cikin ta bah, "Khadijah,Ruqayyah ku fito na ɗan aike ku kasuwa dan wannan kuran ba sani zatai bah" "shikenan yau sai buzu na an haɗani da chewing gum shikenan" haka take ta faɗi a rai dan wannan zaman da sukai da Ruqayyah ta gane tana da mugun surutu uwa wata aku, cikin kayan ta ta ɗauki hijab zata saka kenan Ruqayyah ta anshe tana saka wa ita, datse lips ɗinta kawai tayi ta koma ta ɗauki wani tasa sannan suka fito,kuɗi ta basu a kan su haɗo masu cefane da sauran yan kayayyakin aikin gida irin su tukwane,kwanoni,murhu,da dai sauran su, fita sukai daga gidan zuwa waje dan samun abin hawa,aikuwa basuyi wani nisa ba suka samu nan ya kaisu kasuwa, cefane sosai suka yo dan kayan da suka dawo ya cika napep daman da kuɗi wajen goggo irin wayen da su Ammie ke bata lokacin da suke raye shine take adanar su kaman tasan zai yi mata amfani, da sallama a bakunan su suka shiga da yaran anguna da suka taya su kwaso kayan,inda suka iske matar mai gari wanda yaranta ke cewa umma tazo suna ta fira da goggo kamar ƴa da uwa,gaisar da ita eely tayi tana tsugunnawa har ƙasa dan tana ganin kimar wannan matar,itamavda fara'a ta amsa mata tana kuma yi musu sannu da dawo wah,anan ta bar kayan tayi cikin ɗaki wannan karan ruqqy bata bita ba tana wajen su goggo, cikin firan da suke ne har yazo kan karatun eely inda goggo ke gaya musu ai yanxu NYSC zatayi nan suka turo ta, cikin jin daɗi ruqqy tace " gaskiya abu yayi kyau nima NYSC ɗin zani ni ma kuma anan ɗin nake" iyeeeee kamar sun sani kuwa sun haɗa kawayen guri ɗaya" cewar goggo, ruqqy kuwa tashi tayi ta shige ɗakin "mallama kiyi biyayya in taimaka ina zuwa service dake in kuma ba haka ba mutum ya ɓata a ƙwaryan Kano, wani ƙatuwar harara ta sakar mata kafin ta dan motsa lips kamar zatayi magana sai kuma ta fasa "in ba tsoro ba ai da kin faɗa yarinya"........................✍🏻