EELHAM🌹

19&20

by @rabearhwakili


Episode 19&20📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai



Nan fa ta tasa ta a gaba da tsokala wai tana jin tsoron ta ne shi yasa ta kasa mayar mata da martani, saida ta gaji dan kanta sannan ta barta hakanan, ganin sha biyu tayi ne yasa ta miƙe dan taje ta daura musu girki dan tasan goggo bata wasa da cikin ta sam, umma dai har yanzu tana a gidan bata fice ba, cikin kayan da suka siyo ta buɗe buhun su abaca da tukwane, Saida taje wajen rijiyar ta dauraye sannan ta ajiye su gefe, abacan shima daga chan gefe ta ajiye shi, kallan goggo tayi tace "goggo gawayi"  "toh bara na zira hijab na siyo miki" bata shirya yin murmushi amman Saida tayi "nifa ban san ina ne ba" toh shikenan a barshi! kowa ya huta, can dai tace "kawo" itama goggo Saida ta gama jan ajinta sannan ta miƙa mata kuɗin buhu dan bata son gutsu-gutsu idan suna da bairo sai su ɗaura Miki ki tuƙo, cikin halin ko in kula tace "Toh wa zai raka Ni?" Umma dake jin duk wani draman da suke tana musu dariya dan sun burge ta ta furta "eelham kice Ruqayyah ta fito kuje siyan gawayi" itafa bata son abinda zai haɗata da wannan mai baƙin parrot ɗin! Amman ya ta iya dole tayi,ɗakin ta shige ta dauka hijab Saida tazo kofa sannan tace "tashi" tsaff duk maganar dasu umma ke yi a tsakar gida tana ji sarai kuma tasan ance ta raka eely ɗin amman tayi alwashin inhar dai bazata yi magana mai tsawo ba ta barshi ita kam babu inda zata, yau ko sai ta jata, zuciyar ta fal da dariyar ta, "muje"ta ƙara faɗa shima Saida ta mula sannan, ganin fa ba tashi zatayi ba yasa ta fito wajen umma taje da kyar ta buɗe baki ta firta "taƙi" jinjina miskilancin eely kawai umma take wai ta buɗe baki tayi maga ya zamar mata big work? Lailai kam, Ruqayyah! Umma tayi kiranta, fitowa tayi daga ɗakin dariyar mugunta na cinta "umma gani"   "na ganki ai maza je ki saka mayafi ki zo ki raka eelham ta siyo gawayi kafin ku wuce ku shiga gida ku ɗauka bairo sai a aza muku gawayi a kai amman fa kafin ku wuce ku  Nima yaron da zai tuƙo fah" ba haka taso ba taso ne sai eely ta magantu amman ba komi a kwai anjima,Saida ta shiga ta dauki mayafi sannan suka fice daga gidan,
     Wani yaro suka samu ya dauko musu gawayin har gida ya shigo musu dashi hamsin goggo ta cire ta bama yaro Saidai yace a'a bazai karɓa ba yana fita daga gidan.
    Buɗe gawayin Ruqayyah tayi ta zuba a murhu ta kunna wuta,cikin tukunyar da eely ta wanke ɗazu ta dauka ta ƙara daurayewa sannan ta zuba ruwa ta daura a kan wuta, wajen goggo taje haɗi da cewa "goggo mi za'a dafa?" Cikin farin ciki goggo tace kiyi duk mene zamu ci ai, to goggo bara muyi tuwan shinkafa da miyar better leaf, a firgice eely ta ɗago daga jikin umman da take dan itafa ta ɗauki umma a matsayin ammie ne, ganin haka ne yasa Ruqayyah dagewa da cewa "ai goggo ba'a bawa yaro mai ƙiwa barin ma yaji kifi da ɓomo kuma alhamdulillah duk mun siyo su ɗazun"
 "Da kuwa kin kyauta Ruqayyah dan ni kam na gaji da cin shinkafa hakanan" 
   "Ai kuwa tunda kina son tuwo kullum shi zamu rinƙayi dan ni kam bana gajiya da tuƙa tuwo"
    Firgita kam eely tayi shi gashi za'a musu tuwo bugu da ƙari ma ana maganar miya mai ɗaci ita kam taga Idi cikin marairaice face take kallan goggo,amman sai ta ɗauke kai, da yake ita ma ɗin A ɗince sai ta basar dan ta lura yau tunda Ruqayyah ta baiyana a gidan su goggo ke mata wulakanci, dan haka sai ta maida akalar kallon ta fa umma wacce yanayin eely yaso bata dariya, kamar wacce zatayi kuka haka tayi da fuska tana kuma kallan umma amman bata ce komi bah, ganin haka ne yasa umma cewa "barta karki damu tashi mu wuce chan gida sai ki dafa mana abinda kike so" ba musu kuwa ta a mike tana sallamar goggo shima hannu aka ɗaga mata,umma ma tayi mata sallama sannan suka wuce Saida eely ta kai ƙofa sannan ta juyo ta danƙarawa Ruqayyah ƙatuwar harara ai kuwa karab ruqqy ta gani "oho dai inda zansan kinayi idon naki ya faɗo" ita dai bata ce kanzil bah haka ta bi bayan umma


Koda suka je da yake su da icce suke aiki nan ta hau hura wuta ta daura musu farar shinkafa da wake da mai da yaji, bayan ta kammala umma cewa tayi ta zubo musu a plate guda,haka kuwa akayi a plate daya ta zuba musu, nan suka zauna suka ci Tare harda ƙari bayan sun kammala eelham ta gyara gidan tsaff, sannan tayi alwalla dan lokacin salla tayi dakin ruqqy ta shige,nan tayi salla sannan ta kwanta akan yar madaidaiciya gadon dake a ɗakin, eely tana mutumci da bacci dan haka tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita, ba ita ne ta tash ba sai la'asar shima dan umma ta tashe ta ne, koda tayi sallah sallamar umma tayi akan zata gida, fitowa tayi ta nufa gidan nasu,koda ta shiga ta samu goggo da ruqqy sai fira suke, ko kallan su batayi ba ta dai yi musu sannu da gida sannan ta shige ɗakin su, cikin binta da kallo ruqqy tace "goggo anya kuwa eely zatayi ƙawance dani ki kalla fah bata son tana min magana" duk maganar nan da take a hankali take yinshi wai dan kar eely taji ta raina ta "zata yadda kingan ta nan! ki dai barta da baƙin halinta ba rashin son magana, amman tana da son mutane barin ma ƙananan yara" cikin jin daɗi ruqqy tace"shikenan mun zama ƙawaye kilan ita ma tana so iyayi ne dai"  nan suka hau dariyar ta wai tana so tana kaiwa kasuwa, Saida suka gama dariyar su sannan ruqqy ta bi eely zuwa cikin ɗakin ko sallama batayi mata ba ta buɗe labule,wanda hakan shi yasa ta juyo dan taga waye nan, "Malama wai lafiya? zaki wani tsatsareni da idanu bashi ko tara?" Dauke kai tayi dan da gaske idan ta biye mata toh fah bakinta sai yayi tsine dan tsawo, shi yasaka ta hita batun ta, zuwa tayi ta zauna kusa da ita tace "ya kamata muje kasuwa mu siyo abinda ya kamata sai mu fara zuwa ranar monday, ido kawai ta ɗago ta kalleta kafin kuma ta saukar da kanta ƙasa tana cigaba da karatun hisnul Muslim dake a hannun tah, ita kam ruqqy ta gama yadda lailai eely miskila ce ta ƙarshe, ɗan zaman da tayi da ita na yau kawai ta kan gane abinda ke a baƙin ta kokuma ta ba ta amsa da idanu, duk tana ganewa, yanzu kuma kallo da tayi mata alama ce da akwai magana a bakin ta, "toh mudai Allah mun gode maka da kayi mu masu magana ba kamar wasu ba gasu nan dai su ba kurame ba, ba kuma bebe bah,mudai Saidai muce Alhamdulillah" kin kallan ta tayi wannan karan ta cigaba da a abinda take yi, cikin shammatarta ta warce littafin dake a hannun ta ta yadda bazai yage ba kuma ba wai da karfi ta ansa bah, ita ma eely bakwai ta riƙe littafin gam bane, a ƙule ta ɗago amman saidai kashhhh bakin ta ya kasa furta komi ta dai gama motsa baki sai kuma tayi shiru, cikin wani dariyar da ya kwace ma ruqqy tace tabbb mutum kam yana da aiki jajawur nan ta hau tsokalan ta,ganin haka ne yasa ta fice Saida taje ƙofa da ɗan guntun murmushi a fuskarta cikin murya can ciki kamar wadda aka matse ta furta "parrot"  "tana yin gaba kamar ba ita tayi maganar bah, iyeeeee nice parrot Koh Aida kin tsaya kiga ƙarshen surutu" da ɗan guntun murmushi a face ɗinta ta fice ta bar mata ɗakin dan ruqqy tafi ƙarfin ta, itama ɗin fita tayi daga ɗakin ta fito wajen su,kusa da goggo ta zauna tana   faɗa mata zasu je kasuwa gobe dan zuwa jibi Monday zasu fara service ɗinsu, "ok toh Allah ya kai mana rai lafiya daman akwai sauran siyayyayan da zaku yo min na katifa mai dan faɗi yadda zai ishe mu" "toh goggo da wuri zamuje dan mu samu mu dawo da wuri" cewar ruqqy,hakan ma yayi.


Kamar yadda tace kuwa karfe goma ta biyowa eely akan suzonsu wuce da yake ta shirya sai kawai ta dauka hijab ta zira suka sallami goggo sannan suka fice zuwa kasuwa..............


___________bacci nakeson nayi kun hanani wai wannan wani irin masifa ne haka? Ke lanta kike ko waye ma? Miye amfanin ki cikin gidan nan?" Jiki na rawa wacce aka tambaya tace "kula da yara Hajiya" " oh wato kisan aikin ki shine dan rashin mutunci baza kiyi bah sai kin barsu sunzo sun addabe ni dan bala'i?" " Dan Allah kiyi haƙuri Hajiya hakan bazata ƙara faruwa bah"  "oho wannan kuma ke kika sani dan nikam na gaji da ke, bangan kuma amfanin ki ba da zaki bar yara suna damun mutum da ihu kina kallan su,ga waje nan duk bai ishe su wasa ba sai sun shiga hakƙinna?"Kwala kiran dayar mai aikin nata tayi Asabe!Asabe, jiki na rawa daga chan gefen aka amsa da na'am Hajiya, nan da nan kuwa sai gata,matar kan ba karamar mata bace dan ta manyan ta,hakan kuma bai hanata kaiwa duƙe har ƙasa tana furta "Hajiya gani" Saida ta ƙare mata kallon banza sannan ta amsa da "na ganki daman so nake ki sama min mai rainon yara wacce zata raine su a gidan ta dan bansan takura" zancen zuci baba Asabe ta shiga yi,"wai mutum da yaran shi yake hantaransu kamar ba ita ta haife su ba?yaran ma tsoron ta suke ji dan bata jan su a jiki kullum cikin masifa take musu" daka mata tsawa tayi ta hanyar kiran sunan ta "Asabe wanna wani irin rashin mutunci ne ina Miki magana kinyi kunnin uwar shegu dani. 
    "Kiyi hakuri Hajiya banji bane" 
    "daman ku matsalar ku kenan cewa nayi ba yarinya zaki samo min ba tsohuwa nake buƙata wacce batada yarinya budurwa ko ɗaya, kuma a gidan ta zatayi rainon"
    "insha Allah za'a bincika Hajiya ko yau na fita ba'a rasawa"
"Idan kin gama sai kije ko ma zuwa gobe ne dan kar ihun yaran nan ya ɗaura min hawan jini" (Niko nace tab wai mutum da yaran shi amma kake gwada musu Wagga hali, dan Allah iyaye muna rinƙa jan yaran mu a jiki kodan sanin wani hali suke ciki, amma in har ba kya jan yaran ki a jiki ba abinda zaki sani a kansu dan ko sunyi tunanin su faɗa miki sai su fasa tunanin ko zaki hantare su,da haka har yaro ya faɗa mugun hali ke baki sani ba,shi kuma yana tsoron ya tunkaro ki da magana, iyaye mata ku maida ya'yan ku tamkar ƙawayen ku,ku maida su abokanan shawara, da dai sauran su idan kina haka zakiga baza su na jin yadda zasu tunkaro ki da magana bah, Allah ya bamu ikon gyarawa Amin)................✍🏻