22&23
Episode 22&23📲
***
بسم الله الر رŘمن الر Řىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
_____________su eelham sun fara aiki tuƙuru ba wasa dan ba waje ɗaya suke da ruqqy ba kowa da department ɗinshi saidai idan sun fito salla ne su kan haɗu,yanzu ɗin ma hakan ta kasance sallar la'asar da ake kira ne ya miƙar da ita daga kan kujerar da take ta fice zuwa waje,tana kaiwa bakin ƙofan fita ta haɗu da ruqqy itama ta fito daga nasu ɓangaren gefen ta wata matashiya ce wacce zatayi Sa'a dasu, ganin hakan da eely tayi ne sai ta ɗauke kai tayi kaman bata gansu ba, tayi gaba abinta "yar rainin sence kin ganmu kin dauke kai wato bamu ishe ki kallo ba, ai kin kyauta kuma mu koma gida na faɗawa goggo Saida kika zo har nan kina raba hali ehem" ruqqy ke wannan maganar wa eely,da yake ita miskila ce kuma sarauniyar ƙyaliya ce sai tayi kaman ba da ita Ruqayyah keyi ba dan ko juyowa bata yi bah,
"Sister ke da waye halan kike ta faman zuba?"
"Cikin ƙara haɗe face tace ai koma wane yasan kanshi Allah ya Kaimu gida lafiya mutum zai sani ne ai kuma yau mutum ko yaƙi ko yaso sai yaci tuwo punishment ɗin mutum kenan, eely da take jinta daman ba wani nisa tayi dasu bah, Saida tayi tsamm kafin ta cigaba da tafiya dan itafa bata son tuwo ko kaɗan bataso, kuma tunda taji Ruqayyah tace haka tofa hakan zatayi,Saidai ita ta kudiri aniyar kafin su koma ko a hanya ne zata sama wa kanta abinda zata ci.
"Cikin dariya wannan dayar tace tabb sannu da kokari tsohuwar muguwa wato abinda mutum baiso shi zakici masa punishment dashi Allah dai ya shirya ki"
"Amin" koda suka iso alwalla sukai sannan suka shiga masallacin mata dan su gabatar da tasu sallar.wannan karan sun riga ta fitowa daga cikin masallacin sai suka tsaya jiran ta suna É—an fira kaÉ—an kaÉ—an, "wai sister mi muka tsaya jira ne bamu tafi bah?"
"Kanwata nake jira kinsan bata san waje ba kar ta ɓata"
"Ki jiki da wata magana taya mutum zai ɓace a wannan ma'aikatan?"
"Tsaff kuwa Kinga yana da girma sosai bugu da ƙari ma bata magana"
Wani mugun kallo eely ta watsa mata alamun zaki sani ne ai,Ita kuwa wannan dayar da bata san wainar da ake toyawa ba tace "oooh Allah sarki Allah ya bata lafiya" kamar gaske ta amsa da "Amin"suna masu tafiya inda kowa ya koma wajen aikin ta,
Haka dai sukaje suna ta aikin su har sai lokacin tashi tayi suka fito....
____________cikin miskile kyakyawar fuskar sa mai dauke da hanci zir, lips ɗinsa kuwa pink madaidaita, ga fuskar sa zagaye da kyakyawar ƙasumba da ya zagaye fuskar sa kuma a taje take,anyi mishi shape mai kyau wanda hakan ba ƙaramin ƙara ƙawata kyakyawar fuskar sa hakan tayi bah, da kyar ya ya bude baki ya furta "ina kika kaisu" cikin nuna halin ko inkula tace "ni da yara na kuma zaka zo ka tsare ni da tambaya ina na kaisu? Toh wai ma idan sayar dasu nayi ina ruwan ka? In dai kanason ganin su ne kana iya zuwa ka gansu Saidai ko ka dawo dasu Zan mayar dasu ne dan bazan iya kayan ciwon kai bah ehem" shi kam lamarin Mubeena ya daina bashi mamaki sai tsoro cikin gaɗa kai ya ce "ina gidan" itafa halin miskilan cin shi babu wanda bata sani bah tass saidai ta ba wani labari,shiyasa take shuka rashin mutumcin ta san rai,amma randa ta kai shi bango birkice mata yake sannan take ɗan nutsuwa shima for 2days, "driver ya kai ka dan Ni bansan sunan anguwan ba,dan ko hanya anguwan ban kalla ba so bazan ma iya kai kaina ba dan ba ma komawa zanyi bah" ta ƙare maganar cikin halin ko in kula,bai ce mata komi ba yasa kai ya fice sai baza kamshi yake sosai kayan dake a jikin ƙananu ne haka ya ƙara fiddo da Kirar sa na zaratan maza, faffadan qirjinshi sai ya fito da kyau ga muscles nan masha Allah, har zai fita a haka sai kuma ya fasa yaje ya canza kaya zuwa manya,yadi ya saka kalan indigo wanda ya ƙara fiddo da hasken sa, sosai kayan yayi fitting ɗinsa ga hula zanna ya murza wanda ya hau da kayan sa,sosai yayi kyau sannan ya ƙara bin jikin nasa da tularen sa masu sanyi kamshi,fitowa yayi ya fice wanda a daidai entrance ɗin falon yaga drivern sa na jiran Sa,gaisar dashi yayi ɗaga hannu kawai yayi kafin kaman wanda aka yiwa dole yace "ya faɗa maka inda suka kai yara" in ba dan yana kusa dashi ba da bazai ji mi yace bah, cikin rashi fahimta "sir wani yara? Waye kuma za'a yi wa magana?" Ya ƙare magana cikin girmamawa wa ogan nasa, "Kabiru" iya abinda ya furta kenan, wanda ba dan drivern yasan halin ogan nasa ba da a abinda zai fahimta,dan haka shima ya shiga driver sit da sauri dan ogan nasa ya shige tini,tada mota yayi suka fice har suka iso wajen gate da mai gadi da sauran masu aikin gidan ke zaune,fita yayi zuwa wajen wanda yakai su Mubeena gidan rainon yara, tambayar sa yayi shine yayi masa kwatance tsakanin gidan mai anguna da na mai rainon! gida shida ne, nan yayi masa sallama ya fice zuwa cikin motar,yana gayawa ogan nasa kai kawai ya gaɗa masa alamar suje nan ya banka wa mota wuta suka bar gidan bayan mai gadi ya buɗe gate ɗin...
________________Anam ce take ta kuka goggo sai lallashin ta take amma taƙi tayi shiru ta bata madarar ta taƙi tasha, tunanin ko zafi ne kilan take ji yasa ta kunna abacha Anam na bayanta ta daura ruwan zafi dan tayi mata wanka, ganin ruwan yayi ne yasa ta dauko baho ta juye ruwa tayi mata wanka sannan ta rage wanda zata yiwa Anwar dashi, Anam taji ruwa sai tayi shiru daman zafin take ji da akayi mata wanka sai aka sami salama,cikin kayan da aka kawo musu ta buɗe ta cirowa Anam kayan sha iska da tularenta na yara masu daɗi kamshi, saka mata pampass tayi sannan ta zira nata riga da wando masu sauƙin nauyi, ta ɗa shafa mata tulare kaɗan tana gama shirya ta kuwa Anwar shima ya tashi, goya Anam tayi, tana kama Anwar dan tayi masa wanka, tsaff kuwa tayi masa wankan sannan ta bidar mishi kaya suma ba masu nauyi ba ta saka masa tana kuma gyarawa yaron fuskar nan da take fari saidai ba kal bah.
cikin shagwaɓansu na yara yana zumburo baki yace "danci adinci" da murmushi a fuskarta ta furta "yanzu kuwa bara na kawo maka sai kaci Koh?" Ɗaga mata kai yayi,ita kuma ta tashi taje ta zubo masa, tana basa abinci a baki ne taji sallamar Ruqayya tana shigowa, goggo oyoyo sannu da gida tayi mata ita kuma goggo tayi mata sannu da dawowa ganin bata ga eely ba yasa goggo cewa "halan mutuniyar tana wajen umman ku?" Cikin dariya tace tana chan da yake nan muka fara shiga, kuma nasan ba dawowar yau ba" ta ƙare maganar da dariya "daman Nima ban gaiyace ta nan ba"
"Laaa goggo ina kika samo mana yara haka kyawawa tubarkallah" tayi maganar tana zira hannu dan ta ɗauki Anwar da ya nuna kamar bai san mutum ya shigo bah, ƙin yadda yayi ta ɗauke shi sai ya ƙara haɗe fuska kamar wani babban mutum, "tab ɗi jam, goggo wannan yaron anya ba yaron eelham bane ki duba fah wulakanci da rana tsaka! innalillahi shikenan ƙarami dakai da miskilanci kamar eely ta haife ka?" Shi kuwa ko a jikin shi cigaba yayi da cin abincin sa kamar bai san anayi bah, cikin dariya goggo tace "atoh ashe kin gani kema"
"Nakam gani" cikin jin haushi ta tallaƙe masa ƙeya ta faɗin kar kazo ɗin" ɗagowa yayi ya kalle ta da murmushi kaman wani babba kafin kuma ya dauke kai, itafa tsoron Allah ya fara kamata sak yadda eely take mata idan tayi mata wani abun kuma kamar...... goggo ta katse mata tunanin da ta faɗa ta hanyar faɗin "ki hita batun wannan yara kije ki cire kaya kizo kici abinci idan kin gama sai ku cigaba" amsawa tayi da Toh tana shigewa cikin ɗakin..
___________eely kam tayi gudun bata tsira ba, dan umma tuwo take yi yau faÉ—i take cikin zuciya "yau kam shikenan sai ganyen ta tuwo kota ko ina tab akwai aiki" duk da bata son tuwo saida ta taya umma aiki har suka gama lokacin anata kiran magrib,bayan sunyi alwalla sai duk suka wuce zuwa É—aki dan gabatar da salla basu ne suka fito ba saida sukai isha'i sannan lokacin abbu ma ya dawo gaisar dashi tayi da girmamawa,ya amsa mata da kulawa dan yakan dauke ta kamar shi ya haife ta, a nata bangare itama hakan take a uba take kallansa,
auta zo mu ci abinci, saurin girgiza kai tayi kamar zatayi kuka, cikin dariya umma tace "tabb Abbun su ai eelham bata cin tuwo"
"Ćłata yar gayu ce ai mi kike son a siyo miki kici karki kwanta da yunwa"
"Babu Abbu" da yake yasan halin ta zaman nan da sukai na kwana biyu tare dasu, "tunda baza ki faÉ—a ba Bara na aika a siyo koma mi"
"Da gaske banjin yunwa"
"Ai bance kina jin yunwa ba auta" bata son tana yawan musu wa babba sai tayi shiru kawai daman zuciyar ta na so,kiran waya yayi ya faɗa abinda za'a siyo sannan ya katse, suna a zaune anan ba jimawa akayi sallama a ƙofa, Abbu zai miƙe eely tace ya zauna bara ta dubo, koda ta leka ɗan aiken Abbu ne,miƙa mata ladar hannunsa yayi yace ta bawa Abbu, koda ta dawo gaban Abbu ta ajiye "wai yace a baka"
"Naki ne ai eelham É—auki ki ci"
"Yayi yawa fah ban iyawa" buɗe ledar tayi ta raba shi uku ɗaya nata ɗayar na umma ɗayar na Abbu, da kallo suka bita har ta gama raba naman miƙawa Abbu tayi zuwa gaban shi tana "Abbu ga naka umma kema ga taki" "ni dai bazan ci ba auta" cewar umma,shima Abbu cewa yayi"haɗa da ni, nima haka"bata son tana musu dasu, tasan tunda suka furta hakan ba ci zasuyi ba sai ta maida duka a leda "Umma, Abbu gashi to kusa albarka" dadɗaya suka cire suna shi mata albarka hollandia ta miƙa musu wai shima su sa mata albarka amma fir sunƙi su sha, babu yadda ta iya sai haƙuri tashi tayi tana faɗin "Abbu Umma Saida safe zanje nayi wa Ruqayyah ƙwalele"
"Kunfi kusa ai ni nawa ido, Allah ya tashe mu lafiya" Amin shima Abbu yayi mata addu'a sannan ta fice zuwa gidan goggo.
Shigowar ta kenan cikin gidan taji muryan Anwar yana faɗin shi bazai ci miyan ɗaci bah, da murmushi a face ɗinta ta furta "my boy" da sauri kuwa ya juyo dan yaga wake kiran shi yadda baban nasa ke kiran nashi, koda ya juyo sai ƴa ganta fuskar nan dauke da murmushi gashi ta buɗa mishi hannu alamun yazo,aiko da gudu ya ƙarasa gareta, yana zuwa kuwa tayi sama dashi tana masa wasa,dariya yake kaman bashi ya gama kuka da daudaure musu fuska bah, "my boy! who bit you"nuna mata saitin Ruqayyah yayi,hakuri ta bashi sannan suka shige ɗaki ko kallan su goggo bata yi, koda ta shiga sai taga ƙarin wata yarinya a kwance a katifa wanan din ma kamar su ɗaya da boy ɗinta, taɓa fuskar yarinya tayi aikuwa sai ga yarinya ta tashi, daukan ta tayi tana mata wasa kafin ta cire mata kaya dan tanason tayi mata wanka duk da bata san yaran waye ba amma sun burge ta, daukan ta tayi ta fito ta ajiye ta a gefen su goggo,ɗiban ruwan da ke abacha tayi ta sirka daukar ka tayi tayi mata wanka bayan an gama wanka goyata tayi dan taji ɗumi, da yake Anwar yana wajen shima sai tayi mishi ta jasu zuwa ɗaki,nuna mata box ɗin kayansu yayi buɗewa tayi ta ciro musu kayan bacci pink color iri ɗaya saidai ace kowa da yanayin nasa kwalliyar,shirya su tayi gashi sai tashin kamshi suke, "my boy ka zauna kar ka fita, kayi wasa da sister,nima bara nayi wanka nazo kaji" cikin tsamin bakin shi yace "TOH UMM" Saida ta ɗanji wani iri jin ya kira ta da mama sai ta ƙara jin kaunar yaran a rai,da sauri taje tayi wanka,ɗaki ta koma ta goge jiki sannan kuma tabi shi da lotion ɗinta mai kamshi ta kuma bi jikin da humra masu sanyin kamshi,sannan ta zira kaya ganin hankalin Anwar bai kanta yana wasa da Anam,bayan ta kammala ne ta ƙaraso gare su tana cewa "little an my boy am back" kamar Anam tasan mi tace sai ta fara ɗaga hannu tana mata dariya, daukar ta tayi tana mata wasa,Anwar ne ya matso kusa da ita yana cewa"umm abinci zanci" "ok toh boy ina zuwa" fita tayi ta dauko plate da cup da feedarn Anam ruwan zafi ta zubo a dayar cup ɗin sannan ta koma ciki su goggo dai dake a tsakar gida da kallo suke ta binta.
HaÉ—a ma Anam madarar ta tayi sannan ta saka naman da Abbu ya siya mata cikin plate amman bata juye duka ba ta ragewa su goggo,hollandia É—in shima ta zuba a cup "my boy sauko Kaci kaji?bara na bawa sister abincinta Koh?" Cikin turo baki yace shi ita zata bashi "bara sister ta koshi" ai kuwa ba musu ya zauna har ta gama feeding É—in Anam sannan ta fara bashi naman tana kora mishi da hollandia É—in,
Ganin Anam tayi bacci ne sai ta kwantar da ita a katifa, ci gaba tayi da bawa Anwar Saida ya koshi sannan ta rabu dashi,nan ta fara cin naman itama gani tayi Anwar ya saka hannu ya dauki daya sai ta tsaya tana kallan shi "umm haaaaa" cewar Anwar! ba musu kuwa ta buɗe baki ya daka mata naman sannan ya dauko cup ɗin hollandia haaaaa yace ta kuma yi, ba musu kuwa ta ƙara buɗe masa baki ya kafa mata cup haka dai suke tayi har suka gama, daukan shi tayi tayi mishi brush da wanke hannu sannan itama tayi suka koma ɗaki! Su goggo dai sun zama yan kallo.......
____________"ka juya muje chan anguwan" da yake driver yasan mi yake nufi sai ya juya a kalar motar zuwa can É—in, daman da niyan haka suka fito wani uzuri ne ya tashi mishi shine sai yanzu ya samu kanshi kuma bazai iya zuwa gida yayi bacci bah, bayan bai san inda yaran nashi zasu kwana bah.
A kofan gidan goggo motar yayi parking dake driver ya gane kwatancen da akayi masa,saukin ma gidajen a jere suke amman ba a haÉ—e ba, fitowa yayi ya buÉ—ewa ogan nasa kofa saidai bai fito ba.
A bakin ƙofan gidan drivern yayi sallama, Ruqqy ce ta amsa tana saka hijab dan ta dubo waye anan ɗin! Gaisawa sukai kafin yace mata suna niman mai gidan ne, "ai mune masu gida mallam wa kake biɗa"
"Daman baban su Anwar yake a waje shi ya nimi ai masa iso" "Toh ina zuwa bara na faÉ—a" cikin gida ta koma take gayawa "goggo wai baban su Anwar yazo" Allah sarki ce masa ya shigo,fita tayi ta gayawa drivern sakon goggo sannan ta koma ciki,
komi na gidan a kankance yake luwai ga hasken farin wata ya zagaye ko ina ga iska na ta kadawa, daga kofan gida aka kuma sallama goggo ce ta amsa da faɗin "Bismillah shigo"da wani sallama a bakin nashi ya kutsa kai zuwa tsakar gidan,"sannu da zuwa ɗan nan" cikin rashin son magana da ya riga da ya bi jinin jikin shi yace "yauwa ina wuni mama mun same ku lafiya?" "Alhamdulilla tashi ka ƙaraso ga waje nan zauna" tayi maganar tana nuna masa tabarman da aka shinfiɗa daga gefe! Ba musu kuwa ya ƙarasa ya zauna "Ruqayyah kawo mishi ruwa" daga ciki ruqqy ta amsa da "toh" pure water ta saka a plate ta kawo masa wanda suka siyo babu jimawa da sauran sanyin shi kuwaa, gaida sa tayi a miskile yace "Lafiya" tashi tayi ta bar wajen tana kuma mamakin wannan halin nasu masu kamanceceniya da juna,
"Dauki ruwa kasha mana bara a kawo su" ansawa yayi da toh da É—an guntun murmushi a face É—in sa
"Raqqayya cewa maman su Anwar ga baban su yazo sai ta barsu su fito shima idan ta ga dama kenan" shi dai murmushi ne nashi yadda take magana kamar tana ƙule da wacce za'a anso su Anwar ɗin. Juyowa tayi zuwa garesa tace "kayi haƙuri gasu nan fitowa" "babu komi mama"
Daga cikin ɗaki Ruqayyah ta kwala kiran goggo tana cewa"Goggo wai bazan dauki Anam ba! tana bacci kar ta tashi" kaji halin nata Koh?,ke Ruqayyah ƙarfin ki tafi ne komi ki dauko yarinya ku fito"
"goggo goyata fa tayi taya zan karɓe ta"
"rabu da ita dauko Anwar É—in" a cikin É—akin kuwa eely ce goye da Anam ga Anwar a hannun ta duk ta haÉ—a ta É—auka ita tunanin ko zai tafi dasu ne. "My boy" tayi kiran sunan Anwar a kunni "na'am umm"
"Kanason ka wuce ka barni?" Ciki sauri yace "nooo umm"
"ok toh naji ga daddyn ka yazo amma ko yace zai wuce da kai gida kace Bakaso hear?" Wa ya jeka bye, tana sauke shi kuwa ya fita da sauri da yake akwai hasken farin wata sosai hakan ya bashi daman ganin baban sa da gudu ya shige jikin shi yana cewa "papa i miss you"
"Miss U too my boy ko zaka bine mu koma gida?" Girgiza kai yayi cikin yarinta yace "umm tace karna bika" shi dai yasan ba haka yake kiran sunan maman shi ba cikin taɓe baki yace "ok ina Anam?" "Tana a bayan umm tayi bacci"kafin ya maida masa da magana sai yaji muryan goggo tana cewa "ja'iri ashe kana magana haka" Ruqqy da take a tsaye a wajen tayi dariya haɗi da faɗi ai mu suka raina shi yasa ka suke mana walakanci" kallanta Anwar yayi jin an kira umm ɗinsa "kalle Ni fa kai da maman ka karku bari in riƙe ku a gidan nan ehem" kaman ya gane abinda take nufi sai yayi dariyar su ta yara yana maida hankali ga papan sa inda su goggo suka shige ɗaki dansu barshi ya sake da ɗan nasa.
Cikin yin magana can ciki kamar wanda aka matse yace "mi kaci?"
Nan fa ya ɗinga lissafe-lissafe har zuwa naman da sukaci da umm ɗinsa duk ya faɗa "gud boy" cikin maganar sa da bata gama nuna ba yace "papa! Umm ɗina my boy take kila na irin naka" "wow boy ɗin umm ɗinsa"shifa ya lura da wasu changes a tare da Anwar wanda hakan ya faranta masa rai sosai ga kuma yadda yazo ya samu yaran cikin tsafta da muhalli mai kyau, duk da masu ƙaramin ƙarfi ne su ɗin!amma hakan ya nuna suna da kula sosai,ga shi kuma duk Maganar da Anwar zaiyi sai ya saka umm ɗinsa a ciki wanda ko mahaifiyar da ta haife sa bai cika kira haka bah.
sai wajen 10 ya cewa Anwar "my boy! jeka kira goggo kace mata zan wuce" Anwar irin yaran nan ne da ka gansu kaga yaran dady gashi fari kamar mahaifinsa,daga bakin ƙofan yace "goggo papa zai wuce" fitowa tayi da murmushi a face ɗin ta tana mai bashi haƙurin rashin ganin Anam da baiyi bah "taurin kai ne da ita tunda bata yi niya ba babu wanda zai sa tayi ɗin sai idan ita ta ga dama, shima wannan da ya ya ta bari aka dauko shi"
"sai haƙuri goggo kuma babu komi hakan ma ya nuna yaran suna cikin kulawar uwa" Saida ya gama magana sannan a zuci yace ko wa ya bata yaran bare ta zama uwa, toh "shikenan tunda kace haka Allah ya kyauta mungode" aje mata ledar yayi yana cewa "Goggo ga wannan a sa mana albarka"
"hadda ɗawai niya haka toh angode Allah yayi albarka" da Amin ya amsa yana yiwa Anwar bye bye sannan ya fice daga gidan......................✍🏻