24&25
Episode 24&25📲
***
بسم الله الر رŘمن الر Řىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
______________a can Company kuwa Ruqayyah sai Safa da marwa take ta faman yi bata office ɗinta bata na eelham, yanke shawaran kiran goggo tayi, nan kuwa goggo ta gaya mata yadda aka kwashe cikin dariyar mugunta tace ai nikam sunyi min dai-dai Allah ya ƙara cewar Ruqqy tana dariya tuna abinda Anam tayi mata ɗazun. Yanke wayar goggo tayi tana faɗin karki toshe min dodon kunni in shiga uku.
Yanke shawaran zuwa ta gaya masa tayi tun kafin ya nime ta.
Knocking tayi ya bata izinin shiga,sannu da aiki tayi masa tana kuma faÉ—a masa eely bata dawo ba Anwar ya hanata
"Shikenan u can go"
Miƙewa tayi ta fice,koda ta koma haɗa kayanta tayi da na eely da ta barsu duk ta dauka tana fitowa, direct titi ta nufa dan samun abin hawa cikin Sa'a sai ga napep gayamasa tayi inda zata sannan ta shiga suka wuce.gidan su ta shiga da biyan sai an jima zata leƙa su gogga
_________ "Khadijah tashi a baccin nan haka kije kiyi salla la'asar tayi" bata cika nauyin bacci dan haka sai ta miƙe tana gyarawa Anam kwanciya sannan ta fice zuwa waje, ɗauro alwalla tayi,bayan ta idar da salla ne ta fito dan ta daura masu diner,cikin Sa'a kuwa har ta kammalawa yaran nata basu tashi ba, a nan waje ta zauna wajen goggo suna ɗan fira sama sama ga kuma wayar goggo a hannun ta tanayin game, "goggo baki gaya mana mi ya kawo su boy nan ba"
"Ashe zaki tambaya" ita dai bata kuma cewa komi bah,"raino aka kawo su na ɗan lokaci" a hankali ta ɗan motsa yan ƙaramin lips ɗinta ta furta "zuwa yaushe" goggo tasan ba iya tambaya dake bakinta ba kenan kawai dai wannan ɗin ya fito tunda a cikin su shine gajere "toh nima dai bansani ba! Idan lokaci yayi ai zamu gani ko kuwa?" "Uhm" da abinda ta amsa mata kenan tana cigaba da yin game ɗinta
"Umm! Umm" da sauri ta miƙe jin muryan boy ɗinta,ɗakin ta shiga inda ta same shi a zaune yana ta faman zare ido yaga ta ina zaiga shigowan ta. "My Boy Allah ya tasar da kai?" Da sauri ya shige zuwa jikinta yana ɗaga mata kai alamar eh. "Toh muje kayi alwala kayi sallan la'asar Koh?" Ba musu kuwa ya miƙe, fitowa sukai ta zuba masa ruwa a buta tana nuna masa yadda zai yi haka dai har aka gama,ɗan ƙaramin sallaya ta shinfiɗa masa,hawa yayi yana salla ita kuma ta fice zuwa waje...
______________washe gari da ɗan hanzari saidai nutsuwar sa ya boye haka ɗakin mubeena ya tura ya shiga bakin shi dauke da sallama,saidai mi yana shiga ya ganta saman gado lullube cikin blanket sai sharan bacci take, ganin haka ne sai ya mata short note a ya aje mata a gefen ta wanda tana tashi zata gani sannan ya fice daga ɗakin,abinda bai sani ba! Idanun ta biyu lanbo kawai tayi, jin fitar motar sa daga gidan ne sai ta yaye blanket da tayi rufa dashi, cikin shirin ta na tafiya take wanda tana tashi vail tasa ta buɗe waldrop tana ciro trolley da sauri ta fito daga ɗakin tana tafiya tana latsa waya kiran driver tayi akan ya ƙaraso zata fita, da sauri kuwa ya ƙaraso ƙofan falon,shiga back sit tayi tana faɗa masa inda zai kaita dan ta kusan makara tun ɗazu su zeenat ke ta faman kiranta koda suka isa ba wani ɓata lokaci suka shige ciki kusan su 6 wai zasu hutun karshen wata...
___________"dan Allah Ummi Kiyi ma yaya magana dan Allah ya kaini inga su Anwar nayi missing É—in su sosai"
dan Allah auta ni É—agani!kije ki same sa ki faÉ—a masa inace kinada baki" cikin zumbura baki tace "ummi kinsan bazai saurare ni ba! Ni bansan mi yazo musu ma na kai yara raino ba wai harda Anam maimakon ma a kawo mana su"
"A'a fah bani zaki faɗawa duk wannan ba kije ki same sa ki gaya masa ni ba ruwa na ehem! kuma ki dage ya jiki" cikin dariya wanda hakan ya ƙara baiyana kamannin ta da AS saidai ita ba fara bace,"tace "ummi ai abun bai kai haka ba bara dai na wuce kar nayi late! Kilan in biya gidan Anty Hanan"
"Allah ya tsare hanya ina kuma gaishe su" zasuji bye-bye sai na dawo ta ƙare maganan da ficewa daga danƙararren falon nasu zuwa waje wanda shima ɗin abin kallo ne. Parking lot ta ƙarasa motar ta ta buɗe ta shiga tana bashi wuta sai wajen aikin ta....
_____________shigowan su kenan ita da eelham wanda hakan yayi dai-dai da shigowar motan meenal."sister ni na wuce sai mun haÉ—u zuwa anjima" cewar Ruqqy "ok bye" nan suka rabu kowa ya nufa hanyar department É—inta. A kusan tare suka shiga ita da meenal Saidai basu lura da juna ba,office É—in meenal shine na farko sai na eely da ya zama a tsakiya wato akwai tazara tsakanin su.
________Aiki take saidai hankalin ta ya rabu biyu ɗaya a gida dan ta bar little tana tinanin zatayi kuka idan taga bata ganta ba shi yasaka yau ta karɓi wayar umma dan ta rinƙa kira taji ko Anam tana kuka,dayan kuma a aikin da take haka dai ta cigaba da aikin ta bawai dan tana fahimta ba. Kasa haƙuri tayi dan haka ta ɗauki waya tayi kiran goggo taji yadda ake ciki,
Jin goggo ta dauka amma kafin komi kukan Anam ta fara ji, ai bata san sanda tace "mi ya sameta kardai tunda na wuce take kuka?"sam goggo bata san eely bace ita duk zaton ta ko umma ce,ai da tasan eely ce ba abinda zai kaita ta ɗauki wayar,cikin basarwa tace "yanzu ta fara kukan ina ga ko zafi take ji bara dai nayi mata wanka zatayi shiru! Kuma karki sake inga kin dawo in har ba dauko Anwar kikayi daga makaranta ba na dai faɗa miki" ƙit ta katse kiran,kaman tasan abinda take da shirin yi kenan, Saidai goggo ta katse mata hanzari,babu yadda ta iya haka ta cigaba da aikin shima tanayi tana duba time ba ƙaramin dauriya tayi ba,sai taga kaman time baya gudu, dakyar ta samu taga time yayi, ba wata wata ta miƙe dauke da side bag ɗinta ta fice daga office ɗin zuwa waje har zata fice sai ta fasa ta ƙarasa zuwa office ɗin Ruqqy batare da tayi knocking ba ta shiga.
Ruqqy ce zaune akan kujeran office tana chat a waya dan ta gaji da aikin da take shine ta hau online dan ta ɗan huta,jin anbuɗe mata kofa ne ta juya dan taga waye anan dan eely bata taɓa shigowa ba shi yasa batayi tunanin ita ɗin bace, da mamaki a face ɗinta tace "yau muna da babban ba ƙi kenan sannu da zuwa kece tafe kodai shi yasa na ga garin kaman da hadari hadari" danƙara mata harara tayi wanda ya saka Ruqqy kwashewa da dariya "Ni dai bazan san kina yi ba sai idon ki sun zubo sannan" taɓe baki tayi can ciki tace "zanje na dauko boy" "masu boy manya! Zaki dawo amma?"
"I don't kno"
"Ok sai kin dawo! ko na raka ki?" Sam batayi tinanin zata yadda ba, amma sai kawai taji tana cewa "ok muje" miƙewa tayi tana daukan after dress ɗinta ta saka tana gyara vail ɗin dake a kanta daukan bag ɗinta tayi suka fita daga office ɗin zuwa waje, sun daɗe kafin suka samu napep.
Driver yazo daukan Anwar tuntuni amma teacher É—in sa ta hana wai maman shi tace idan ba ita tazo daukan shi ba karta yadda yabi kowa, shiyasa da driver yazo ta hana ya dauki Anwar.
Koda suka isa har class din su Anwar suka je suka dauko shi kamar yadda tayi jiya yau É—in ma a motar driver suka koma zuwa gida duk suka shige ciki inda driver ya ja motar suka dauki hanya..
____________mubeena sun sauka a ƙasar America Saida suka huta,suka zaga gari,ita ta manta da batun AS Saida suka zo zasu kwanta bacci ne zeenat take tambayan ta ta turawa AS tana America kuwa. "Ke ni wallahi na manta bara na tura masa yaje chan ya ta bala'in sa nidai bana kusa" cikin son ƙara ingiza ta tace "ai daɗi na dake kenan ba sauƙiiiii" suna kashewa. "banda abinki zeenat wani sauƙi za'a yi ai gwara ka nuna masa kaima jan wuya ne ko kuwa?" "Ai kuwa dai daman ai idan kinason Kiyi kima sai kana kama darajan ka kana nuna jan aji amma idan kina naniƙe da miji kai da hoto duk ɗaya" a cikin zuciyar kuwa faɗi take karyanki mubeena kiyi zaman aure, kaman yadda nake yawo a bazawara cikin gari kema very soon Zaki fito tinda ke kince wawiyace baki da wayau,kina fita ni kuma na maye gurbin ki" wannan magana duk cikin zuciya take yinta da murnushi dauke a face ɗinta.
Mubeena kuwa tana tura masa message ta kashe wayar dan kar ya nime bata da abin faɗi, duk abinda ta ke zeenat na lura da ita tana kuma ƙara zigeta.saida ta ga mubeena tayi nisa a bacci sai ta dauko wayarta a hankali ta kunna dan so take AS yayi ta kira idan ya kira bata ɗaga ba yazama laifi biyu kenan dan mugunta ta kuma saka wayar a silent, "mubeena dani kike zance yanzu kuma muka saka ƙafan wando ɗaya dake." Tana tintsirewa da dariya
______________fiwowan shi kenan daga masallaci sai yaji wayar shi tayi ƙara alamun shigowar saƙo fiddo da wayar yayi yana dubawa sai yaga ashe daga matar shi ce,Saida ya koma office sannan ya buɗe sakon wanda lokaci ɗaya yanayin fuskan shi ya canza sosai ɓacin rai ya baiyana akan fuskar shi,numbern da ta turo mishi da message ya kira saidai har ya gama ringing ba'a yi picking ba daurewa yayi ya kira na biyu nan ɗin ma no answer daga karshe ma da ya ƙara kiran na uku sai akace masa wayar a kashe take, ƙarin baƙin cikin abin shine Saida aka katse kiran sannan a ka kashe wayar gaba ɗaya. Wannan abin da tayi shi yaƙara tunzura shi,ganin zai sawa kanshi damuwa sai ya dauki abinda zai ɗauka ya fita zuwa haraban Company.
ganin fitowar sa ne yasa driver ɗinsa ya miƙe da sauri ya buɗewa ogan nasa back sit saidai bai zauna anan ɗin ba sai ya shige front sit, zagawaya yayi shima yayi ya zauna a ma zaunin sa.saida suka hau titi ne yace "sir ina zamuje?",yana da buƙatar ganin yaran shi ko ɗacin da yake ji a rai zai sake shi, ba tare da ya gama yanke shawara ba sai ya faɗa masa inda zasu, koda suka je anguwar su eely gidan umma ya fara shiga bayan anyi masa izini da haka,sun gaisa sosai cikin sakewa da kuma girmamata, ya ɗan jima a nan ɗin kafin ya wuce gidan goggo.
"AHMAD ne sannu da zuwa maraba lale"cikin ɗan murmushi ya gaisar da'ita dayi mata ya aiki ganin sai aiki takeyi, "goggo yaran nan basa nan ne da zasu bar miki aiki" cikin rashin damuwa ta ce "har aikin guda nawa ne Ahmad! Na riga da na gama! Su Ruqayyah kuma suna gidan yayarsu,dawowa kuwa nasan sai dare" fatan dawowa lafiya yayi musu yana son ya tambayi su Anwar amma yana jin kunya dakyar dai yayi ƙundunbalan tambayan ta yana shafa kai ita kam dariya ya bata ganin yadda yayi amma sai ta dake "suna tare da umm ɗinsu dasu taje"shidai bai ce komi ba kuma.
Fira suke ta yi duk da goggo ce ƙarfin yi, kiran sallar magrib ɗin da ake yi shi ya miƙar dashi yace wa goggo zashi masallaci ya dawo, adawo lafiya tayi mishi, yana fita ba jimawa eely suka shigo gidan suna yiwa goggo sannu da gida, aje Anam tayi gurin goggo sannan ta dauki buta tayi alwalla tana shigewa cikin ɗaki, tana cewa Ruqqy Anwar yayi alwalla yazo yayi salla, tana cikin raka'a na karshe Anwar ya shigo ya tsaya gefenta duk abinda tayi shi yake yi da tazo wajen sallama shi sai baiyi ba ya miƙe, wato yaron yasan abinda yake yi duk da ba wani shekaru ne dashi ba,bayan ta kammala addu'oi ne sannan ta dauko ma Anwar qur'ani nan ta dinga koya mishi cikin nutsuwa.da yake yaron akwai kan daukan abu nan da nan ya riƙe komi,suna nan anan suna karatu har isha'i yayi tashi tayi suka gabatar da salla sukai addu'a sannan suka kwashe sallaya, "umm ni Ice cream zan sha ba zanci abinci ba" hararan shi tayi tace "da muke a waje mi yasa baka faɗa bah?" Cikin ɗan zunbura baki gaba yace "umm na manta ne"
"Toh tunda ka nanta ka bari gobe" ba abinda yace mata kuwa sai komawa gefen da yayi ya hau kuka shi Ice cream zai sha, daga waje goggo tace "Khadijah wai mi kika yi masa" kaji fa goggo da son daure mutum nikam mi zan masa kuwa amma a zahiri sai tace "ice cream zai sha" "abun azimun ne! kace yau daÉ—i kake son sha"cewar goggo ita kuma Ruqqy dariya take yi musu da son ganin yadda zata kaya ita da É—an nata.
"Boy!my boy" ansawa yayi da "na'am umm" matsawa tayi kusa dashi tace "ice cream zaka sha" da sauri ya ɗaga mata "ok kayi shiru i promise you tomorrow" no umm I want it now" babu yadda batayi dashi ba amma fir yaƙi kukan da ya cika musu ɗaki dashi shi ya hanasu jin muryan AS.
Shigowar shi kenan ya ci karo da kukan Anwar wanda daga ji kasan na rigima ne kawai,zama yayi akan tabarman da ya tashi ɗazun,yana gaida goggo itama Ruqqy ta gaisar dashi ba tare da ya kalle ta ya amsa haɗi da faɗin "wato baku jira a tashi kuke gudawa Koh?" Cikin sauri tace "a'a yaya yau na bita dauko Anwar ne daga school shine bamu samu mun dawo ba Anwar ya hanata" gaɗa kai kawai yayi kafin a hankali ya tambaye ta "shi wancan mi ya same shi" cikin ɗan dariya tace "wai ice cream zai sha! ba zai ci abinci bah" ɗan guntun murnushi yayi kafin yace "miƙo min little, sai ki kira Anwar yazo"miƙo mishi Anam tayi sannan ta shiga ɗaki dan kiran Anwar, koda taje ta samu eely a kwance ta hita batun shi,shi kuwa sai kuka yake alamun yana kan bakan shi, "Anwar taho papa yazo" jin haka ne sai ya miƙe da sauri ya fita zuwa waje ganin Abban sa da yayi ne cikin sauri ya ƙarasa wajen shi yana sauke ajiyar zuciya, goggo kam tuni ta bar musu wajen tana ɗayar ɗakin da ta koma yanzu wannan ta barna su eely,
Shafa kan shi yake yana lallashin shi "boy ice cream zaka sha Koh" gaɗa kai yayi " tashi kaje ka faɗawa umm ɗinka zaka fita da papa, tashi yayi tunbur-tunbur ya shiga ɗakin "umm zan fita da papa" ba tare da ta kalle sa ba tace "adawo lafiya"kin wucewa yayi ya tsaya a kofa "lafiya Anwar baka wuce bah?" Cewar Ruqqy, nuna mata umm ɗinsa yayi, tsaf eely tasan mi yake nufi amma babu inda zata saidai ya kumbura dan fushi,juyawa tayi ta kwanta tana datse ido, "kayi haƙuri kuje kaga tayi bacci" badan ransa ya so ba ya fito inda ya sami papan sa da goggo wacce ta fito yanzu, "goggo Bara muje mu dawo"a dawo lafiya tayi masa.
Anwar kuwa sai kallo ƙofa ya rinƙa yi goggo ce ta lura da haka ta tambaye shi mi yake so, "umm wai baza ta ba" "affff kaima tunda kaji tace bata zuwa ai ba zuwan zatayi ba dan haka Ahmad kama shi ku wuce karma ku jira wancan ɗin ku tafi"amsawa yay da toh yana kama hannun Anwar suka fito wajen mota, daman tun ɗazu ya sallami drivern sa yanzu kan da kanshi ta ja motar Anwar yana front sit Anam a ƙafan sa, ya kam riƙe ta da kyau kaman wani babba, eatery ya kaisu inda ya buƙaci a basa ice cream dasu gasasshen kaji dan yanason yayi wa su goggo tsaraba, inda duk mi ya siya wa Anwar sai yace na umm ɗinsa fah,a haka dai har ya gama siyan abinda zai saya suka fito.
Sun dawo gidan goggo wuraren ƙarfe 9 ɗaukan Anam yayi daga hannun Anwar suka shige ciki suna yiwa goggo sannu,miƙa mata Anam yayi sannan ya aje mata ledar dake a dayar hannun shi, "kaide Ahmad baka gajiya Allah yayi albarka nagode,da Amin ya amsa yana sallamanta zai wuce,fita yayi daga gidan ba tare da ya ƙara ganin Anwar bah, dan suna shigowa ya shige ɗaki wajen umm ɗinsa yana nuna mata abinda suka siyo,saukowa tayi ta rinƙa bashi Saida ya ƙoshi sannan shima yq fara bata gwanin burgewa Saida suka gama ta ɗauke shi sukai brush sannan ta dauƙo Anam suka kwanta inda goggo da Ruqayyah suke nasu partyn a waje Saida suka gama suma suka shige ɗaki...............✍🏻
f