EELHAM🌹

26&27

by @rabearhwakili

Episode 26&27📲





***







Jumma'at Kareem to all Muslim ummah🕋📿 may Almighty Allah accept our silent prayers🤲






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai



        Satin su mubeena 1 kenan a America wanda ita har cikin rai bataso su kai haka ba saidai zugin da Ć™awayenta keyi mata yasa ta mance da batun dawowa kodan taga yadda yaĆ´an nata suke amma deep down tana jin kewan su fiye da tunani. Yau de tunda ta tashi take marmarin Nigeria aiko bata biÉ—a shawaran kowa cikin Ć™awayen nata ba sai shamsiya inda take gaya mata tana son ta koma Nigeria hakanan, gashi tunda suka zo kota kira AS bai É—auka "banda abin ki mubee taya ma za'ai ya dauka bayan kin fito ba tare da izinin shi ba! Yanzu ba fata nake miĆ™i ba idan wani abun ya same ki ko kuwa kika mutu mi zaki cewa Allah? Wallahi ya kamata ki dawo daga rakiyar su zee, nidai shawara nake baki idan kin É—auka daidai ne in akasin haka shima daidai, wallahi ki aje mugun huÉ—uban dasu zee ke yi miki ki koma ga Allah ki riĆ™e mijinki da Ć´aĆ´an ki! Yanzu yadda kikeyi inda ace mijin ki mai niman mata ne mi kike tunani?" Hmmmm ta sauke ajiyar zuciya wani zuciyar na Ć™okarin karban maganar shamsiya saidai hakan ya kasa yiwa "Ni dai ba wannan ba yaushe zamu tafi" "daman ai ke ba gaskiya kike so bah sai mu shirya gobe mu tafi shawara karki sake ki faÉ—awa su zee  ehem" ita da kanta tasan idan ta faÉ—awa su zee tofa ita da gida sai baba ya gani amma sai ta amsa mata da "toh mama" duk dariya sukai, shirya kayansu sukai suka saka cikin waldrop dake a É—akin dan kar sauran Ć™awayensu suyi tunanin wani abin.
   sosai take son Shamsiya saboda idan tana Ć™okarin kaucewa ita ke taro ta idan anyi Sa'a bata yi nisa bah,nan dai suka zauna suna ta fira  wanda a ciki shamsiya ke dan bata shawarwari wanda zata bille shima cikin hikima take yinshi. Shamsiya dai ka barta da halinta amma tsaf tasan abu mai kyau da akasin haka, haka dai ta cigaba da bata shawarwari cikin hikima wanda a lokaci da ka kalle su zaka gane Ć™awance ne na tsakani da Allah ba kaman su zee dake mata hassada bah...

_____________tunda AS yake zuwa bai taÉ“a zuwa ya haÉ—uwa da eely a waje ba dan kullum tana cikin É—aki lunĆ™ume, ko a wajen aiki bai taÉ“a ganin ta ba, haka kuma bai taÉ“a jin muryan ta ba gashi yanzu satin su Anwar daya da kwana biyar sun shaĆ™u da eely sosai kallan uwa suke mata, hakan da suke gwada mata bai hana ta nuna musu darajan mahaifiyar da ta haife su ba,kullum Ć™ara chusa musu kaunar mahaifiyar su take,a yanzu kam su kan barta ta tafi aiki haka idan ta dauko Anwar shima yana barinta ta koma sun Ć™ara wayau bata kuma barin shi yana fita waje, saboda gudun haka ta siyar mishi Kayan wasa. 
    Yau ta kasance weekend wuraren magrib zaune suke a tsakar gida su duka harda umma wanda zuwan ta kenan ba jimawa,eely kwance take ta daura kanta a kan Ć™afafun umma tana game da wayar goggo, Anwar kuwa yana a ta gefe yana buga ball,su goggo da umma sai fira suke inda Ruqayyah take wasa da Anam ta kan É—an saka baki a firar tasu. "eely ki shirya muje gidan su Anty Maryam mu karÉ“o tsara ban mu tun kafin ta gama rabar dashi kin dai san halinta" 
"Da zata wuce na wa kika bata"
"Iyeee lailai ma aiko saidai kar tayi tsaraban! Ai idan batayi dan Allah ba zatayi na dole dan tana hana Ni zan jido ne na bar gidan" 
    "Sata" amsar da eely ta bata kenan wanda hakan ya tunzura Ruqqy tace dillaliyar ce Ni karshen sata" É—an guntun murmushi tayi tana É—an tabe baki haÉ—i da faÉ—in "kayan mu dai É—aci ne dasu eh......ai bata Ć™arkare magana ba Ruqqy ta taso a harzuĆ™e tayi kanta ganin haka ne yasa eely miĆ™ewa da sauri ta faÉ—a É—aki hadda su banko kofa, bugbuga Ć™ofa Ruqqy ta rinĆ™a yi tana ta kumfan baki su umma kuwa dake sun san halin su kana shiga tsakani zasu watsa maka Ć™asa a ido shi yasa suka hita batun su, gajiya tayi da buga Ć™ofan ta dawo ta zauna, daga cikin É—aki kuwa jin da tayi Ruqqy ta daina buga Ć™ofan ne sai ta leĆ™o ta window tace "dan Allah dillaliya É—an miĆ™o min wayar umma" ta Ć™are maganar cikin rashin son magana. banza tayi da ita sai Anwar ne ya Ć™araso wajen da kayan kwallon sa a jiki "umma waya in kai wa umm na" ba musu kuwa tace "karÉ“i maza miĆ™a mata" yana nufan Ć™ofan É—akin sai ga sallamar AS bashi izinin shigowa akayi sannan ya Ć™araso har duĆ™e ya kai yana gaisar dasu umma inda suka amsa masa da kulawa da tambayan shi iyali nan É—in ma ya amsa da Alhamdulillah, Ruqqy ma ta gaisar dashi shima ya amsa da kulawa yana kai zaune kan tabarman da ta shimfiÉ—a masa. Ruqayya "tashi ki miĆ™o masa furar sa a É—aki" "Toh goggo" dakin goggo ta shiga ta dauko masa furan cikin kofin silver ajewa tayi a gaban sa, cikin jin daÉ—i dan yanason fura sosai yayi mata godiya.
   "Umm ki buÉ—e kofa nine ba anty bace" cewar Anwar da yake ta faman bugun Ć™ofa dan da farko baiyi magana ba sai yanzu yayi ita kuma bata buÉ—e ba tana tunanin ko Ruqqy ce, "boy kai ne" "Yes umm open the door"  
   Abin mamaki wai Anwar yana ganin shi amma ya nuna kaman bai san shi ba, hankalin shi gaba É—aya yana kan umm É—insa,burin shi ta buÉ—e masa ya samu ya miĆ™a mata wayar. Shi yasa AS ya kafe wajen da ido yana fatan yaga wannan umm É—insa,tunanin shi katsewa yayi ganin an buÉ—e kofan É—akin saidai baiga kowa ba, Anwar kuwa yana shiga ta rufe kofan da key yadda yake, Ruqqy kuwa cikin É—an É—aga murya yadda zata ji tace "mutun ga tsoro ga tsokalan faÉ—a ai yau saidai karki fito daga É—akin" oho eely yi tayi kaman bata jita ba ta share, "umm ga waya na karÉ“o wurin umma" ya Ć™are maganan da miĆ™a mata wayar karba tayi tana shi mishi albarka,kiran sallar magrib É—inda akeyi ne yasa ta canza masa kaya zuwa jallabiya na yara da niyan idan ta idar da salla tayi mishi wanka tunda bai samu tayi mishi na yamma ba, wa ya boy muje ayi alwalla muyi salla "noo yau da papa zani masallaci yazo" "ok jeka Allah ya tsare" Saida ya buÉ—e kofan har ya fita sannan ya amsa da "Amin bye" ganin fitowar shi ne yasa AS nufan Ć™ofa wanda ya riga da yayi alwalla,Saidai da sauri Anwar ya dawo kaman yayi mantuwa a bakin Ć™ofan É—akin ya tsaya yana "umm mi zan dawo miki da tsaraba?" Cikin dariya tace "komi ma inaso boy" bai bata ansa ba ya fice inda ya samu papan sa a inda ya barshi yana jiran shi, duk Maganar da Anwar ya faÉ—a a kunnin sa, kama hannun shi yayi suka fice zuwa Masallaci, bayan an idar da salla ne suka fito "Papa" kyalesa yayi kaman bai ji kiran nashi yake ba, "papa" "mene"
 Babu ko kunya tuna bai gaisar dashi ba sai cewa yayi "papa ka kaini nayiwa umm tsaraban masallaci"  yi yayi kaman ba dashi yake ba "papa pls" "muje" mota suka nufa shiga duk sukayi sannan ya bawa mota wuta suka bar arean,kayan su maĆ™ulashe ya dinga jidar mata shi kuwa AS binsa kawai yake saida ya gama daukan abinda zai É—auka ya juyo yana papa na gama gani yayi duk babu kayan arziĆ™i a ciki sai na kwaÉ—ayi shi kuma haka kawai yaji yana buĆ™atan siyan mata wani abu kodan kula mishi da yara da take, jan hannun Anwar yayi suka nufa wajen Saida wayoyi ya dauka iphone 11 guda biyu sai bangaren tulare ma Saida ya zaÉ“o kamshin da yayi masa,wajen biyan kuÉ—i suka Ć™arasa inda akayi masa calculating ya fidda ATM ya biya nan suka fito da ledoji,
Koda suka isa anguwan su goggo isha'i sukaji ana kira sai basu shiga ba sai da sukai sallar sannan suka shiga gidan sallama dauke a bakin AS Anwar kuwa umm ɗinsa ya hau kira wai tazo ga tsaraban masallaci, da yake duk suna tsakar gida saidai wannan karan umma ta koma gida goggo da Ruqqy ce sai eely da fitowar ta kenan, amsa masa tayi da "na'am boy mu ga" da sauri kuwa ya iso gareta yana zazzage ledar daukar wayar goggo tayi ta kunna haske dan basu da light mi zata gani kuwa kayan su chocolate ne gasu nan kala kala, kallan shi tayi face ɗinta ba wasa tace "wa ya siyar maka duk wannan" ta ƙare maganar da nuna su chocolate ɗin, "papa ne ya kaini shine na siya miki" "awwwn that's my boy Allah yayi maka albarka but don't try it next time here?" "Bazan kuma ba" "yawwa gud boy" "yaya barka da dare" cewar Ruqqy amsawa yayi shima a daƙile, ita eelham sai yanzu taji muryan shi daman takan ji muryan nasa saidai bata taɓa ganin shi ba, ba tare da ta ɗago ta kalleshi ba tace "ina wuni" daman tunda suka shigo idon shi ke akanta, jin tana gaisar dashi ne sai ya dauke kai cikin basarwa yana amsawa da "lafiya" gefen zuciyarsa yana mamakin ta wai itace umm ɗin su Anwar. Ya kice tunanin yayi a rai kafin yace "Ruqayyah gashi" tashi tayi ta saka hannu biyu ta ƙarɓa duk da baiyi mata bayani bah hakan ya nuna nata ne godiya sosai tayi mishi kamar tasan abinda yake ciki,tashi eelham tayi dauke da Anam da tayi bacci tini ta shige ɗaki bata cewa komi bah, da kallon gefen ido ya bita yana mamakin ta,shigan ta ba jima shima yace zai wuce yana sallaman goggo,Saida ya fita sannan Ruqqy ta buɗe ledar da ya bata,farin ciki sosai tashiga yi da ganin abin arzikin da ya kawo masu nuna ma goggo tayi haɗi da faɗin goggo duba kiga yaya ya siyar mana wayar zamani ga kuma tularen nida eelham"
"Masha Allah kun gode kwarai da gaske Allah ya Ć™ara buÉ—i Ahmad dai baya gajiya Allah ya saka nasa da mafificin alkhairi" "Amin ya Allah! eelham fito ga fa abin arziĆ™i da zafin ta ya sauka"cikin nutsuwar ta ta fito daga É—akin "lafiya zaki cikawa mutane kunni" "dole fah in cika abin arziki ne ya same mu! Yaya Ahmad ya siyan mana waya ni É—aya ke É—aya ga kuma tualare" kwarai da gaske tayi murna da haka amma a zahiri sai ta taÉ“e baki irin ba'a burge ta bah. mi wani kika tsayawa mutane a kai kina wani ya mutsa baki kaman Kinga kashi,ganin goggo zata fara wanan faÉ—an nata ne sai ta kai zaune tana kallon wayar miĆ™a mata Ruqayyah tayi wai ta zaÉ“i É—aya ai dan ita aka siyo,dan mĆ™ararren harara ta watsa mata sannan ta É—auke kai "kema dai Ruqayyah Allah ya Ć™ara banda abin ki inace ke ya miĆ™awa wayar, banji yace keda wata can daban bah" cikin fara'an ta tace "goggo haka yake nufi! Kinga ai bazai siyo waya biyu dan mutum É—aya ba" "wannan kuma ku kuka sani É—auki wanda ranki yake so ki zaÉ“a ki darje" "Yanzu kuwa goggo" nan ta zaÉ“a wanda take so shima bawai ta tsaya Ć™are musu kallo bane, miĆ™awa eely tayi tana cewa "ga naki Allah yasa a kashe lafiya" Ć™in karÉ“a tayi tana faÉ—i "ba buĆ™ata ko nace inada buĆ™atar waya ne?" 
    "Toh nidai ba Ni nasiya wayar ba dan haka bani zaki faÉ—awa ba,kijira wanda ya siya idan yazo saiki gaya masa baki buĆ™ata"
   "Ai kuwa dai kin bata amsa dai-dai da ita" cewar goggo,jin suna son suyi mata chaaa a kai yasa ta miĆ™e ta shige É—aki ganin haka ne Anwar ya bita suka shige ciki dan su kwanta su hutawa rayuwar su....
    Ba daÉ—ewa da shigar ta goggo suka suka miĆ™e suka nufi É—aki (asuba tagari)....

___________daga wajen goggo gidan Ummi ya nufa knocking yayi a Ć™ofan parlon yana tsaye ba jimawa aka buÉ—e Ć™ofan wacce ta buÉ—e Ć™ofan ne ta leĆ™o dan ganin waye, ido huÉ—u tayi da Ć´aĆ´an ta cikin sake murmushi tace yaya "ina wuni" "lafiya" ya amsa a daĆ™ile dan shi ba ma'abocin son magana bane, jayewa tayi nan ya samu daman shiga ciki inda ya tadda Ummi a zaune ga mubeena a gefen ta, "Ummi ina wuni?" "Lafiya qlau,ya aikin?"  "Alhamdulillah" 
  "Daman ai yanzu nake shirin nayi kiran ka" gyara zama yayi yana mai cewa "gani Ummi" ba wasa sam a fuskarta tace "mi yasa da mubeena tayi tafiya idan ta kira ka baka É—auka?" Lallai kam wato har mubeena tana da bakin kawo Ć™aran shi wurin mahaifiyar shi, cewa yayi "Ummi hakan bazata Ć™ara faruwa bah insha Allah" "tambayar ka nayi mi yasa take ta Ć™ira ka amma kaĆ™i ka É—auka?" Shiru yayi baice komi bah, ganin haka ne sai Ummi tace "mi ya haÉ—a ku kikace?" Tayi maganar tana kallon mubeena, ita kuwa babu ko kunya ta Ć™ara maimaitawa "wai akan tayi tafiya bada izinin shi bah shiyasa yake fushi da ita amma wallahi ummi nayi nadama" faÉ—i yake lailai ma mubee wato tasan tayi laifi ta kuma san bata da gaskiya shine ta wuto nan gashi babu ko kunya ta faÉ—i abinda tayi,shi dai abinda yasa yake Ć™ara sonta kenan,bata iya karya ba koda ita take da laifi Indai magana ya tashi ta kan faÉ—i gaskiyar abinda ya faru yanzu É—in ma shiyasa yaji zuciyarsa tayi sanyi,jin kuma tayi nadama inda ace batayi ba bazata buÉ—e baki tace tayi bah, "tunda ta gane laifin ta har tasan tayi kuskure kayi haĆ™uri komi ya wuce".   "amsawa yayi da insha Allahu komi ya wuce" cikin sauri mubee tace "ina son a dawo mun da yara zuwa gobe dan Allah Ummi ki saka baki dan zai iya cewa sai ya hora ni! kuma ni ba zan gane gidan ba"  "Toh Ahmad ka daiji idan Allah ya Kaimu sai aje a dauko su" cikin rashin damuwa ya amsa da "Allah ya Kaimu"  'ku tashi kuje dare na daÉ—a yi" miĆ™ewa sukai suna sallamanta, buÉ—e mata front sit yayi sannan ya zaga ya buÉ—e ya shiga yana ta da motar suka bar gidan,da yake da anguwan su dana Ummi ba wani nisa ne dashi bah, a Ć™ofan gate É—insu ya danna horn mai gadi yazo ya bude da sauri Saida ya tsaya suka gaisa da gate man, sannan suka shige ciki da mota, parking yayi, ya fito ya buÉ—ewa mubeena kofa suka nufa cikin gidan key ya ciro ya buÉ—e kofan falon, dan ya bawa masu aikin gidan hutu amma mata, shiga sukai yana kunna wuta ko ina yayi tar da haske ba tare da yayi mata magana ba ya riĆ™o hannun ta suka hau sama zuwa É—akin baccin su...


_____a zabure ta tashi bakin ta da addu'a Kallan su Anwar tayi ganin dai duk suna a gefen ta yasa ta sauke Ć™atuwar ajiyar zuciya tana kuma Ć™ara recalling mafarkin da tayi, gani tayi AS ya zo zai tafi dasu Anwar jin haka da tayi ne sai ta fito a zabure  daga É—akin tana dan Allah karka tafi dasu ina sonsu,dan Allah, har zubewa kasa tayi tana roĆ™an shi amma ina kama hannun Anwar yayi ga Anam a kafaÉ—an shi haka yasa kafa ya bar gidan ko tausaya mata baiyi bah, mtwsss tsaki tayi tuna mafarki ne ba gaske bah, addu'a tayi tana kara komawa bacci, 
   Jin ana buga Ć™ofa shi ya tasar da ita daga baccin da ya kwashe ta ji tayi gaban ta ya faÉ—i innalillahi kawai ta shiga nanatawa kafin ta miĆ™e cikin sanyi ta buÉ—e kofan,ganin goggo ne sai taji ta É—an samu natsuwa harda su sauke ajiyar zuciya, "lokacin sallah yayi kiyi maza kizo kiyi alwalla kar lokaci ya Ć™ure, yau duk mun makara"
GaÉ—a mata kai kawai tayi dan bata jin zata iya magana. Fitowa tayi ta dauki buta ban É—aki ta fara shiga sannan da fito ta daura alwalla ta koma É—aki
 Yau bata da karfin fita yin aiki shiyasa ta zauna a nan inda tayi salla, goggo kuwa bata leĆ™ota ba ta dauka ko ta koma bacci ne shiyasa ta kyale ta, tana nan zaune a É—aki tayi zugum har rana ta fara fitowa jin muryan goggo tayi tana "yau Khadijah lafiyan ta kuwa zata tayin bacci har yanzu goma ake biÉ—a fah, Ruqayyah zo ki dubota" tashi Ruqayyah tayi ta shiga dakin ganin ta tayi zaune a kan sallaya ganin haka ne yasa ta koma bata ce mata komi ba dan ita ta dauka wani abin take dake ta bawa Ć™ofan baya, "goggo karatu take bata idar bah" "oo to Allah ya taimaka" da Amin ta amsa

Elham ba ita ta fito ba sai wuraren sha biyu shima dan goggo ta matsa mata ne, daman goggo tini ta É—auki su Anwar tayi musu wanka dan ganin maman nasu sai a hankali, bucket ta dauka taje bakin rijiya ta É—iba ruwa ta nufi ban É—aki dan yin wanka, koda ta fito sama sama ta shafa mai dan garin yau akwai zafi, da niyan ta ta fito tsakar gidan amma ta fasa ta koma tayi zaune kan katifa, 

AS da mubeena ne suka shigo gidan goggo ta barma ta shinfiÉ—a musu tana yi musu sannu da zuwa ruwa ta kawo musu pure water, ba musu kuwa AS ya dauka yasha, mubeena kuwa ko kallo, bayan sun gaisa AS yake faÉ—a mata sunzo É—aukan su Anwar ne.
 Elham da take cikin É—aki saida taji gaban ya faÉ—i kardai mafarkin da tayi shi zai faru "ya Allah kasa ba haka bane" can waje kuwa saida goggo taji wani iri dan duk sun saba da yaran sosai saidai babu yadda suka iya masu Ć´aĆ´a suna bukatar abunsu, "Allah sarki zamu sha kewa kuwa bara na dauko su dan Anwar yayi bacci saidai Anam idanun ta biyu, É—aki ta shiga ta dauko Anwar,miĆ™awa AS shi tayi a hankali dan kar ya tashi, komawa tayi ta dauko Anam dake ta wasan ta na yara tana haÉ—o musu da kayansu,koda ta fito mubeena ce  ta karÉ“i Anam,AS kuwa godiya yayi mata sosai yana aje mata rafan yan dubu dubu guda uku, da sauri goggo ta katse shi da faÉ—in "Ahmad É—auka tun muna sheda juna"  dan Allah goggo karkice a'a" na riga da na faÉ—a ba zan dauka bah" "goggo albarka muke nima" jin haka ne sai ta É—auki rafa É—aya ta cire dubu daya a ciki ta aje masa sauran a gaban shi tana Allah yayi albarka na gode kwarai da gaske, babu yadda baiyi da ita ba akan ta karba amma ta nuna wannan É—in ma ya isa,babu yadda ya iya haka ya dauki kuÉ—in sannan ya miĆ™e, ganin haka ne itama mubeena ta tashi sallamar goggo sukai suna ficewa daga gidan.
    Idanun eely sun kaÉ—e sunyi jawur kaman rushe kuka take son tayi saidai ina hakan yaĆ™i ya faru dan ta riga da tayi hannun riga da wannan hawayen a lokacin, jin wani zafin sa na taso mata tayi dole taji zafin sa taya za'ayi jiya yana gidan amma ya kasa gaya musu zai É—auki su Anwar sai da rana tsakan nan, inda ta dauki albashi ta cire su kenan daga babin rayuwar ta zata manta tayi rayuwa dasu tunda tasan ba Ć™ara haÉ—uwa zasuyi ba, tace koda ta ga su Anwar É—in zata dauke su kaman da, nan ta rinĆ™a lallashin kanta har ta É—an fara sauko wa, lokaci É—aya kuma kewar su mufeeda ya tasar mata tabbas tana son su dan sun dauke ta a matsayin yar uwar su ta jini,cikin wani hawayen da bata san da zuwan su taji yana zubo mata a fuska dan tuna rayuwar da sukai tare su shida cikin so da kaunan juna, bawai ta manta dasu bane cikin babin rayuwar ta ba a'a kullum Allah keda kullum da begen Ć™ara haÉ—uwar su take,da ace tana da numbern su da ta biÉ—e su sai dai yan zu bata da numbern su dan wayar Tata a chan gidan su ta barshi, share hawayen tayi tana Ć™ara jaddada wa kanta kuka ba nata bane zata ci gaba da maida komi ba komi ba insha Allah.Tashi tayi tana zaran hijab dan so take ta je ta gaida umma 
    Goggo ma dai ta shiga kewar su Anwar amma sai ta danne dan kar taĆ™arawa eelham damuwa, saidai mi lokacin da eely ta shigo sallamanta akan zata gidan umma sai taga fuskar nan kamar yadda yake a kullum mamaki tayi dan batayi tunanin haka bah,ita duk a nata tunanin eelhan zata sakawa kanta damuwa sai taga akasin haka, katse mata tunani tayi da faÉ—in "na tafi gidan umma" a dawo lafiya tayi mata ita kuma tana ficewa daga gidan...

__________zanga-zanga Anwar ya hauyi da ya tashi yaga ba gidan goggo yake ba kuma gashi baiga umm É—insa ba,aifa nan ya hau kuka hadda birgima wai sai an maida shi gurin umm É—insa hadda su ihu,saida mubeena ta dauko cable charge tace zata dake shi sannan aka samu salama dan ita ta É—auka ko goggo yake kira umm, AS da yake zaune yana jin su bai ce musu komi ba daman yasan idan Anwar ya tashi akwai daru, a nan da yake kwance wani sabon bacci ya kwashe shi
     A takaice dai Saida Anwar yayi sati É—aya yana kiran a kai shi wurin umm dinsa kafin yazo ya haĆ™ura ganin ba kai shi za'ayi bah.

Elham ma dai kewar Anwar na nan daram babu abinda ya rage daga ciki saidai ta kan danne sosai, a tsakanin ne taje school ɗinsu Anwar ta gayawa antyn shi zata daina zuwa daukan shi.............✍🏻