EELHAM🌹

28&29

by @rabearhwakili


Episode 28 & 29📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai





______yaushe zamu tafi Abuja Kinga yau meeting sauran kwana uku kuma zuwa yanzu nasan kowa ya hallara suke kira na suna gaya mun gasunan duk sun zo"
  "Kina da gajen haĆ™uri auta inda kin kwantar da kinji! Yanzu sai kije ki haÉ—a kayan naki flight É—in mu 8oclock pm zai tashi yau"
   "Yeeeees bara naje na haÉ—a kaya dan idan na tafi ba dawowan yau ba dan naji ihsan tace anan zatayi hutu! Kinga daga nan sai nayi mata wayau ta biyo ni mu dawo nan idan yaso sai a nima mata transfer ta dawo nan da service É—inta Koh?"
    "Cikin dariya tace kin ko yi mata wayau Allah ya shirya ku"itama dariya tayi tace "su fa basu cika zuwa nan ba sai in mune muka je chan ai gara nayi ta masu wayau suyi ta zuwa"
   "Auta kenan Allah Ć™ara wayau to amma ni dai banga wayau nan ba" tashi tayi tana zumbura baki wai ance mata batada wayau,ganin haka ne sai Ummi tace "zauna kiji albishir" ba musu kuwa ta zauna tana jiran taji
"Ummi ina jii" 
   "Mi kike ci na baka na zuba? Daman Hajiya Mama zata dawo nan da zama ita dasu Hafsah" wani tsalle ta daka tana jin daÉ—i tace habawa shagali ummi kice ba zama grandma zata dawo nan! Toh Ummi yaushe zasu dawo kuma wa zai je dauko su?" 
   "Sai mun dawo daga Abuja shi yasa ana gama meeting washegari gari zamu dawo koda yake kince ke a chan zaki zauna Koh?"
  "Da sauri tace wane niiii ai na fasa tini kowa ya zauna a gidan su" cikin É—an dariya tace "oo se yanzu kikasan haka Koh?" Tashi tayi ta nufa upstairs tana ba haka take nufi bah....


________fitowar su daga office kenan suna jiran Umar ya zo dan yace shi zai maida su,wanda a yanzu soyayya mai karfi ya Ć™ullu a tsakanin sa da Ruqqy,wanda a shekaran jiya iyaye suka zo gaisuwa zuwan da zasu Ć™ara yi na saka rana ne, "Mallama nkfa na gaji da tsayuwa fah?" Cewar eely tana hararan ta "wai ko dai na juya na goya ki ne?" Dukan wasa ta kai mata tana É—an guntun murmushi, kaucewa Ruqqy tayi tana "a'a wallahi karki ragen sadaki ehem" 
   Itama É—in cikin wasa tace "yar is kawaii"  "ke kuma na gaba da is bah" 
   Harara ta kai mata tana dauke kai da kuma É—an motsa lips É—inta alamar akwai abin faÉ—i saidai bakin ya kasa furtawa,É—an wannan maganar da tayi har ya saukar mata da ciwon kai, 
     "Ooo Allah alhamdulillah mungode maka ya Allah da kayi mu masu magana" tsaf eely tasan da ita Ruqqy keyi amma sai ta hita batun ta
Meenal dake ta kallon su tun É—azu sai taji sun burge ta sosai shi yasa ta tsaya ta rinĆ™a kallan su ba tare da sun sani bah gefe É—aya kuma tana mamakin wannan lamarin,  Ć™araso inda suke tayi tana sauke glass É—inta da yi musu sallama, sister ku shigo na rage muku hanya naga wajen shiru babu abin hawa, da yake Ruqqy ta kan haÉ—u da ita idan suka fito salla shi yasa ta É—an waye ta, daukar wayar ta tayi kiran iphone wanda AS ya siya musu,numbern Umar ta kira tace mishi su sun wuce sun jira shi amma shiru,haĆ™uri ya bata sannan yace suje zaije gida su haÉ—u amsawa tayi da ok tana yanke wayar, eely muje Kinga idan muka tsaya anan ba abin hawa zamu samu ba Kinga yamma tayi, ba tare da ta kalle ta ba tace "sai nazo" babu yadda batayi da ita ba amma fir taĆ™i hawa dole ta bawa meenal haĆ™uri ta wuce wanda ita ma bata ji dadin hakan bah.
    "Aiko kowa yaji a jikin ta Allah kuma yasa karmu samu abin hawan inga karshen iyayi" Ć™in tanka mata tayi ta cigaba da tafiya kaman bazata taka Ć™asa ba. Hadari ne sosai a garin wanda ya taso lokaci É—aya machines dasu mota sai gudu suke basu son ruwan ya taÉ“a su. Kinga abinda kika ja mana Koh dan Allah da ace mun bita ai da ba haka bah" "na riĆ™e ki?"
  "Ai da na wuce nan zaki gane cewa kin riĆ™e ni" taÉ“e baki tayi tana É—auke kai,sunyi tafiya ba mai nisa ba suka ji horn daga bayan su,babu wanda ya juya a cikin su, motan Ć™ara matsawa kusa da su yayi ana Ć™ara danna musu horn nan É—in ma babu wacce ta duba, ji tayi ance "Ruqayyah" nan kam Ruqqy ce kawai ta juya dan bata gane muryan ko waye bah, koda ta juyo da driver tayi arba da gani shi yayi kiran nata,eely kuwa bata tsaya ba ta cigaba da tafiyanta tana jin daÉ—in weather É—in
   Kafin Ruqqy ta samu daman cewa komi AS ya sauke glass É—in gefen shi ba tare da ya É—ago ba yace "shiga muje" " yaya ba Ni É—aya bace ni da Elham ne" b tare da wasa a fuska ba ya Ć™ara faÉ—in "shiga" wannan karan kam ba musu ta buÉ—e front sit ta shiga ba da son rai ba dan bazata so ta wuce ta bar ta ita É—aya ba ga magrib ya kawo kai, tana shiga kuwa driver yaja motar suka bar wajen.
    Duk da eely bata juya ba tasan Ruqqy ta shiga motar Ba tare da damuwa ba ta cigaba da tafiya ga hanyan shiru babu abin hawa ko É—aya da ke gittawa sai motocin da suke wucewa da gudu kaman zasu tashi sama, wani mota ne yazo ya wuce ta gaban ta da gudu a hankali kuma taga motan nayin reverse yana yowa baya, "DEJART" tsam tayi tsaye nan gun da take,shi kuma na motan yana ganin haka sai ya fito cikin sauri ya Ć™araso inda take da murmushi a face É—insa, "tabb rai kanga rai daman" cikin É—an murmushi da gani ta saba da wannan É—in tace "taya za'ayi su gani kuwa" "barnan  kin rai na ni da yawa"itama cikin haÉ—in fuska tace toh"ni yaushe na raina ka?"dariya yayi haÉ—i da faÉ—in halin ki na nan ya kwana dubu, sai alkahiri sir"ta Ć™are maganan da son danne dariyan ta "saniya ce ba sir ba" haÉ—i dayin kwafa, "nidai shiga muje kuma sai kin gaya mun yadda akayi kika bar gari babu notice ba irin niman da banyi Miki bah ga wayar ki kashe baya shiga mufeeda ma na kira layinta shima kashe"
     "Wannan bayanin haka sir" 
"Ki raba ni dace mun sir tun kafin a jimu! Kinga eely kizo ki shiga muje Kinga garin nan da hadari kuma idan ruwan nan ya kufce ba tsanewan yanzu ba" ba musu kuwa suka isa wajen motan miĆ™a mata key yayi yace ita zata tuĆ™a yayi missing É—in tuĆ™in ta, "ba wani wayau dai zakayi min"  "haba dai mutuniya kema kinsan ba wannan ki dan tausaya min hannu na ne suka gaji"
   "Toh Allah ya Ć™ara sauĆ™i idan da gaske ne" ta Ć™are maganar da karban key dake hannu shi "karya nake shikenan eely! Badai kin raina ni ba?" "Sharri!Ni yaushe akayi haka"
  "Ban sani ba" cikin taÉ“e baki kaman ba eely mara son surutu ba tace duk hanyan da ka sani su bace ma" pointing É—inta yayi da hannu ita ma ganin haka tayi yadda yayi har haÉ—a baki suke inda eely tace tare da kai shikuma yace tare da ke lokaci É—aya kuma suka kwashe da dariya.
  Har zata bude mazaunin driver yace "mallama wait wait" tun kafin yayi magana dan ta tuna yadda sukeyi sai taje ta gefen shi ta buÉ—e mishi ya shiga sannan ta kulle ita ma zagawa tayi ta ta buÉ—e ta shiga sannan ta kulle daman haka sukeyi inhar dai zasu shiga mota É—aya, É—aya ke budewa É—aya idan an kai wajen da zasu sai wanda ya bude da farko shi za'a budewa, kaman yanzu idan sun isa shi zai budewa eely Ć™ofa
   Driving take slowly kaman bata son yi sai firan su suke sha da gani sun shaĆ™u da juna "eely ban tambaye ki ba?" "Inajin ka"
  "Wai ina mallam É—an ladi ne?" Harara ta sakar mishi tana faÉ—in  "kamanta dai mallam É—an gambo dai"
"Daga tambaya sai masifa Allah ya baki haƙuri to!amma ni dai nasan masoyin ki ne" "Allah ya kiyaye" daidai tanayin parking a ƙofan gidansu, kallan shi, zuwa yanzu ta gaji da surutu ba tare da tayi mishi magana ba ta dai yi mishi alama da ido alaman sun kawo,da yake yasan halin kayanshi ya buɗe kofa ya fita amma bai kulle ba, zagawa yayi gefen ta ya buɗe mata kofan ta fito ta koma side ɗin da ya fito kaman wasu yara suna haɗa baki but slowly sukace 123 suna kaiwa 3 suka buga kofan a tare suna dariya, "na riga ki", "ka dai riga kanka amma nidai nasan nine 1st" "rinto toh na ci girma na bar miki"
"Kaide ka sani muje nidai kafin in barka nan" "ai nasan Ć™aramin aikin ki ne"jerawa sukai a tare suka shiga cikin gidan, tun daga kofa ya fara kiran "goggo! Goggo" amma a hankali wanda ba lailai goggon taji bah.bayan sun shigo ne ta shinfiÉ—a masa tabarma zama yayi yana ya gaji ruwa ta kawo mishi pure water masu sauĆ™in sanyi É—auka yayi ya sha sannan ya dubata "ina goggo nikam?" "Baka da baki?" 
"Da suƙi kam akwai shi! Goggo! Goggo" daga cikin ɗaki goggo tace na'am wake biɗa ta tana fitowa daga ɗakin, a bakin ƙofa ta tsaya sagade tana kallan shi kafin chan tace "Mubarak idanun ka kenan da kyar fa na iya gane ka"ta ƙare maganar da son zolayansa cewa yayi "goggo kiyi shiru kar yarinyan nan ta raina ni" taɓe baki tayi tana shigewa ɗaki tace "idan kun gama ku kira ni"

AS kuwa yana ƙofan gida tun daga zuwan su har rigengen da sukai duk akan idon shi, dauke kai yayi haɗi da faɗin ko ina ruwan shi tada motar yayi ya bar anguwan zuwa gidan Ummi nan ɗin kam ya jima sosai sai da yayi Sallar isha'i ya kama hanya komawa gidan shi.

__________bayan idar da Sallar isha'i suna zaune bayan sun kammala cin abinci wannan karan hadda Ruqqy tazo da ita ake ta fira wanda har lokacin mbk bai wuce ba yana nan, kiran umman shi yayi through video call tambayan shi tayi ina ya tsaya har Yanzu bai dawo bah kuma ga yana yin gari da hadari cikin É—an dariya yace Anty autan ki ce ta riĆ™e ni   "wacce auta na kuma?" 
"Ooh ashe ban shafa miki bah,albishirin ki?"
"Goro fara ƙal"
"Ok tom Anty rufe ido sai nace ki buÉ—e sannan"
 "Nifa iyayi ne bani so tam" ta Ć™are maganar da rufe ido,ya fito eely yayi dake ta jinsu tunda suka fara waya tana jin so da kewar matan na taso mata sanadin haÉ—uwar su da mbk Ammie É—inta da Anty maman mbk suka Ć™ulla abota, tashi tayi tana Ć™arasowa inda yake zaune ta kai daga gefen shi. Juyo da fuskar wayar yayi zuwa gare ta ita kuma ta sunkuyar da kai tana jin kwalla na mata kai koma a cikin idanun, ji tayi mbk nace wa "Anty ki buÉ—e idon slowly" kamar yadda yace kuwa a hankali ta rinĆ™a buÉ—e idon har ta gama buÉ—e su a kan eely da kanta ke duĆ™e,tabbas duk da ta dukar da kanta Ć™asa hakan ba zai hana ta gane wace  anan ba, dan soyayyar da take yiwa eelham ko yarinya ta ce ita sai haka, so take ta tabbatar shi yasa ta ambaci sunan ta "Elham baby" na'am Anty ta amsa muryan ta na rawa sosai alamun tana gab da fara kuka, a ruÉ—e mbk ya fara tambayanta da "Bestie lafiya kuwa mi yasa kike kuka wani abu aka Miki?" Cikin murmushi yaĆ™e ta É—ago ta dube shi tace "qlau fah" zuba mata ido yayi ba dan ya yarda ba dan yasan eely sosai, "daughter mi akayi Miki?" Cikin fake smile ta amsa mata da Lafiyan ta qlau kawai kewan ta tayi ne, ai gani daughter,yasu goggo da Aminiya fatan duk kuna lafiya kwana ki munata niman wayoyin ku Amma duk a kashe munje har chan Minna moĆ™atan ku suka ce kun tashi kun koma Kaduna, itama gidan Aminiya ma haka wai sun tashi ga wayoyin duk basa shiga, miĆ™awa Aminiya mu gaisa kwana da yawa" cikin dauriya tace muna lafiya qlau, ga goggo ta Ć™are maganar muryan ta yana rawa sosai mika wa goggo wayar tayi ta shige É—aki da hanzari dan bata son suga hawayen idanun ta,karÉ“a goggo tayi itama cikin rawan muryan da ya saka Ruqqy da mbk shiga wani hali, cikin dauriya dai ta daure suka gaisa bayan sun gama gaisawa tace "goggo Aminiya fa idan bata nan a bani numbern da zan same ta" anty a lokacin ba abinda take son ji sai muryan Ammie,dan duk cikin su tafi jin kewar ta.
   "Hmmm zulaiha kenan ai aminiyar ki saidai muyi ta musu addu'a dan sun riga mu tafiya" bata samu daman Ć™arasa zancen nata ba taji kuka na zuwar mata kaman yanzu ne abin ya faru, mbk kuwa salati ya sake kamar yadda Anty tayi yace "goggo kina nufin Ammien mu ta rasu?" GaÉ—a mishi kai tayi dan bakin ta bazai iya furta komi anan bah, shina mbk bai san sanda hawaye Masu zafi suka rinĆ™a gangara a fuskar shi bah,ji sukai cikin kuka sosai aunty tace kuyi min kwatancen gidan gani nan zuwa da Alhaji. Ruqqy dai an barta a duhu dan ita sam bata san labarin su bah, ita ta dauÉ—i wayan ta gayawa Anty sunan anguwan da kuma kwatancen gidan, bayan ta yanke wayar ne ta shiga bawa su goggo baki Saida suka É—an lafa da kukan nasu ne sannan ta shiga É—aki wajen eely saidai Ć™ofan rufe yake da key, "eelham dan Allah ki buÉ—e" shiru taji wato ba alamar budewa nan ta hau yi mata magiya akan ta buÉ—e amma taĆ™i, sallamar su aunty da isowan su kenan ita da Alhaji sai É—iyar su Jawaher ya katse mata bugun Ć™ofan da take yiwa eely.
 tabarma ta shifiÉ—a musu tana gaishe su wanda bappa kawai ya amsa aunty sam hankalin ta bai jikin ta, gaisar da goggo bappa yayi yana Ć™ara yi mata ta'aziyya,gaÉ—a kai kawai take haka dai ya samu ya lalashe su dukan su, "banga daughter bah tana ina?" mbk da sai yanzu ya farga babu eely a wajen yayi saurin miĆ™ewa yana tambayan Ruqqy ko ina take, É—aki ta nuna mishi knocking yayi mata a Ć™ofa sau biyu a na ukun ne ta buÉ—e, ba tare da ya kalle ta ba yace "fito su Anty sunzo" ba musu kuwa ta fito tana Ć™arasawa wajen su gaida bappa tayi sannan ta faÉ—a jikin Anty tana sauke ajiyar zuciya shafa bayan ta tahau yi tana lallashin ta, bayan waje ya natsa ne bappa ya tambayi goggo "taya suka dawo nan babu labari? Sannan ina baba?"  Bata ce masa komi ba sai kallan Ruqqy tayi tace "jeki ki kirawo min Abban ku da umman ku kema ki dawo" amsa mata tayi da Toh tana daukan hijab É—inta tayi waje cikin kankanin lokaci sai gata dasu,umma sun shigo bayan sun gama gaisuwa ne sai goggo tayi gyaran murya wanda hakan shi ya Ć™ara natsar da wajen duk da dama ba surutu suke ba, "saminu ka tambaye ni ya akayi muka dawo nan ko?" Ta Ć™are maganar da sigan tambaya "na'am haka ne goggo" toh Masha Allah duk zakuji hadda ku ma" tayi maganar tana kallan su umma da Abba,share fuskanta tayi tas ya zama babu É—igon hawaye ko É—aya ganin haka eely ma ta goge hawayen nata tass tana tuna alwashin da tayi wa kanta na kuka ba nata bane bah.
Goggo duk kallan su tayi kafin ta kwashe komi ta gaya musu tun daga kan auren da sukai wa eely har zuwa sakin da mijin yayi mata cikin bainar jama'a, koran da Abba yayi musu da kuma yadda ya nuna su twince ba yaran shi bane da rasuwan su Ammie da tashin su daga gidan da suke har zuwa dawowan su nan. Baka jin komi sai na shesheĆ™an kukan su umma, Anty,jawaher, Ruqqy,da mbk dan ya kasa daurewa,bappa da Abba ne kawai basuyi kuka ba sai goggo da eely baki su bappa suka rinĆ™a bawa matan su da Ć´aĆ´an nasu, "goggo kuyi hakuri bisa jin mu da kukayi shiru duk bamu san abinda yake faruwa ba kenan dan Allah goggo ina son kiyi mana alfarma mu wanke laifin mu kuzo mu koma chan gidana da zama dan Allah goggo karkice a'a dan Allah" da É—an murmushi a fuskar ta tace "a'a saminu nan É—in ma da muke zaune ya isa dan  uwan ka Kabir gashi nan yana kokari damu, Ni dai bani da bakin gode muku sai dai nace Allah yayi muku albarka daku da zuri'an ku baki É—aya" da Amin suka amsa dukan su suna jin kaunar ta a rai, "goggo amma za'a rinĆ™a aramana Elham Koh?" Cewar Anty ganin goggo dai ba binsu zatayi bah, "gaku ga tanan Ni nawa ido"da sauri kuwa Anty tace "ku shirya mu tafi" É—aki Ruqqy da eelham suka shiga suka haÉ—a kaya shima ba mai yawa ba sannan suka fito tsakar gidan da kayan su cikin É—an madaidaicin bag, cikin zuciyar eelham kuwa tinani take taya zata bar goggo ta kwana ita É—aya a gidan nan, samun waje tayi tayi zaune haÉ—i da faÉ—in ta fasa zuwa tambayan ta dalili sukai inda take gaya musu bazata bar goggo ita É—aya a gida bah, cikin dariya bappa yace "gidan Abban ku zata kwana kafin a samo mai kula da ita" jin haka ne sai ta shiga ta haÉ—awa goggo kaya ta fito dashi,duk waje suka nufa inda suka je sukai wa goggo rakiya har gidan mai anguwa, sannan suka dawo suka shiga mota eely dai na tare da mbk ta É—an ware tunda gashi sai tsokalan juna suke 
    Horn bappa yayi inda da sauri gate man ya taso ya buÉ—e yana miĆ™a musu gaisuwa haka suka Ć™arasa zuwa parking lot fitowa sukai gaba dayan su sukai cikin parlon, parlon ya Ć™awatu sosai da kayan alatu na zamani ga kujeru nan wanda daka kalle su zaka gane ba Ć™aramin Naira yayi kuka bah, "jawaher dauki kayansu ki kaisu É—akin ku kuje ku kwanta ku huta dare yayi sai in Allah ya Kaimu kuma"ba musu duk suka miĆ™e suna sallamar iyayen nasu suka shige É—akin jawaher.
   eely kuwa Saida sukai sallama da Bestien nata sannan ta wuce É—aki tana dariya tsokalan da yayi mata,su Anty suma sun shige É—akin nasu ganin haka ne shima mbk ya fice zuwa nashi part É—in dake a wajen part É—in su Anty.
Bayan sunyi wanka sunzo kwanciya suka fara raba hali an rasa wanda zai  kwanta a tsakiya,gajiya sukai sannan sanan jawaher ta kwanta a tsakiyan tana "gobe Ruqqy ke zaki kwanta jibi eely" "zamu gani toh" cewar Ruqqy, da yake duk a gajiye suke suna kwanciya kuwa sai bacci ya dauke su 


Jirgin su Ummi ya sauka tun tuni inda aka zo aka dauke su zuwa family house ɗinsu dake nan abuja. Sosai ta samu tarbar daga wajen kanne da yayunta da kuma ya'yan ta, tunda suka sauka meenal ta shige cikin yan uwanta suna firan yaushe gamo. Hayaniyar da suka damu kakar tasu dashi ne yasa ta kora su suje suyi bacci dare tayi nisa, da yake suna jin baccin firan ne kawai ya dauke musu hankali aikuwa suna kwantawa sai bacci...............✍🏻