EELHAM🌹

30&31

by @rabearhwakili



Episode 30 & 31📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai

Da sassafe suka tashi dan suna son suyi abinda zasu yi,Dan yau akwai zuwa gurin aiki, duk da akwai masu aiki a gidan hakan baisa sun zauna ba tashi sukai suka haɗa hannu a kan aikin gidan da kuma breakfast bayan sun gama jera komi a kan dining sai suka shige ɗaki dan yin wanka, cikin shirin su na kayan NYSC suka fito after drees suka daura a kan kayan kamar yadda suka saba,
  Samun su bappa da Anty sukai a dining da gani suna jiran isowar su,miƙa gaisuwa sukai ga iyayen nasu, amsawa sukai da kulawa da tambayan ya suka tashi, Saida suka zauna sai ga mbk shima ya shigo cikin shirin shi na zuwa aiki.
 Duk a gurguje suka kammala yin break ganin suna gab da makara, "dije taso muje" yi tayi kaman bata ji shi ba shima tsokalan faɗa ne kawai irin nashi ya sani sarai ko so dubu zaice mata dije bata amsawa "toh mai sunan yan gayu eelham tashi muje kar ki saka na makara"
   Tashi tayi tana sallamar su Anty ta nufa ƙofa ganin haka ne sai jawaher tace "wato babu ko gaiyata Koh? Da sauƙi tunda muma muna da namu ko kuwa yar uwa" ta ƙare maganar da kallon Ruqqy "inda kika jin nan kuwa" 
    "Gulman ƴa ta zakuyi dan kun ga bata nan Koh?" Cikin zare ido suna haɗa baki wane muu,mun wuce sai mun dawo" adawo lafiya tayi masu tana ƙara jaddada masu dasuyi driving a hankali 
     Elham kam tuni suka wuce dan sun kusa da wajen aikin nata yana driving suna fira, koda suka isa har ciki ya sauke ta sannan ya fito ya buɗe mata ƙofa ta fito da murmushi dauke a kyakyawar fuskar ta,a hankali ta buɗe baki tace "thank you" hararan wasa shi kuma yayi mata yana cewa "barnan da Allah" 
"Idan anƙi?" Kwafa yayi yana kuma hararan nata wanda hakan ya saka ta ɗan saki ƙaramin murmushi,har ta wuce sa kaɗan yace "badan hali ba karfe nawa zaku tashi" cikin taɓe baki ita ma tace "ba dan hali ba ƙarfe 4"  "ok naji a shiga lafiya! Kona raka ki ne?"
"Noo bye" shi ɗin ma hannu ya ɗaga mata Saida yaga shigan ta ne sannan yaja motar yabar wajen zuwa nasa aikin. Tana shiga ciki sai ga su Ruqayyah sun shigo cikin Companyn da take duk department ɗin su daban daban ne sai kowa ya wuce nasa ɓangaren,tunda suka shiga babu abinda ya fidda su sai salla,bayan sun koma ne sai Ruqqy ta bi eely zuwa office jawaher dai bata bisu ba dan tace tana da aiki sosai a table ɗinta da yake ta ɗanyi tafiya na kwana biyu. "eely guess what" ɗan ɗaga kai tayi sama tana tuna mi zata gaya mata da take cewa tayi guessing "na bada gari" "give up da wuri kuma?" Ɗan guntun murmushi tayi tace "I can't" 
"Toh shikenan tunda baki iyawa a bar maganan" 
"Kedai matsala ta dake kenan" cewar eely tana hararan Ruqqy cikin wasa.
Ita ma Ruqqyn taɓe baki tayi sannan tace "Anwar na gani  a hannun yaya Umar da yazo ɗazu" ɗagowa tayi ta dube ta sannan tace "are serious?"
"Yeah seriously" jin hakan ne sai ta duƙar da kanta ƙasa "mi yasa baki kira ni bah?" "cikin sauri ya zo wai yaya AS na jiran shi zasuyi tafiya" 
     "Ok" nan suka canza firan nasu zuwa wata wanda ƙarfin fjran duk Ruqqy ke yin ta....




__________Hamshaƙiyar mata ne zaune a wani katafaren falo ta daura ɗaya kan ɗaya dayar kuwa ta ɗan kishingiɗa,ga masu yi masu hidima a gefe, kallon su tayi tace "kuna iya tashi ku tafi" cikin risunar da kai suka amsa haɗi da miƙewa, Saida ta tabbatar da sun fita Sannan ta miƙe a ɗan fusace tace "yaya mi akayi da waɗan nan uban kuɗin da Company ya fitar a jiya! kuma naga hadda saka hannun ki" ƙara gyara zama tayi kafin tace "Ni zaki zo ki titsiye a gaba da tambaya sai kace kin samu yar ki wai ma tsaya  wace silar shigar ki wannan daular?lokacin da nake ta baki shawara ga abinda za'ayi ba cewa kikayi baki iyawa bah?". 
   Cikin ƙara harzuƙa tace "wannan maganan da ne maganan yanzu muke ina makuɗan kuɗaɗen suka shiga?".
   Yarta cikin nuna isa ta furta "dauka na yi dan nayi nawa buƙatun dasu,tunda ba komi ne zan buƙata inzo wajen ki ba dan ina buƙatan privacy ɗina". 
  "Kin kyauta kuma insha Allah this should be ur first an last wallahi" 
Miƙewa tayi a fusace kaman zata kaiwa Anne bugu tace "bar ganin ina binki ta lalama,banda mutumci akan abinda nake so,sannan ina iya komi a kan haka,so karki duba ciki ɗaya muka fito,idan kunni yajiii?".fuuu ta ɗauki jakan ta tana yin waje.
    Da kallo Anne ta bi bayan ta tana mamakin wannan furucin nata,amma da yake itama zuciyar ta naga kuɗin sai suka ƙyanƙyashe, kwafa tayi tana "ƙaryanki yaya! Dukiya dai nawa ne da ƴaƴa na sai yadda nayi dashi" tashi tayi ta shige ɗaki......


__________AS sun sauka a airport dake a garin Abuja wajajen 3 na rana, da yake ba wanda yasan da zuwan su bare a aika musu da mota. Dole taxi suka samu ya wuce dasu family house ɗin nasu.
    A daidai bakin ƙofan gate driver taxi yayi parking fitowa sukai, AS hannun sa dauke da Anam gefen shi Anwar, mubeena kuwa trolley ɗinsu ta dauka,sallamar mai taxi yayi suna nufan gate knocking yayi, budewa akayi daga ciki mai gadin ya leƙo dan yaga waye anan, ganin su ne yasa ya buɗe kofan yana yi musu barka da zuwa, AS kawai ya amsa suna nufin cikin ɗanƙareren gidan ga part nan kashi kashi.
   Part ɗin kakar shi suka nufa da yake yasan ba kulle ƙofa take son yi ba sai ya tura bakin shi dauke da sallama, mubeena.biye dashi a baya.
   "Wa'alai kumus salam!yan Kano ne sannu ku ya hanya" "mun shawo ta" nan ya gaisar da ita wanda ganin haka ne mubeena ta kai gaisuwa. Amsawa tayi da kulawa haɗi da cewa 
"Bari inkira yaran nan suzo su kawo muku ruwa yau ƙafafun sun ɗan motsa. Allah ya ƙara sauƙi yayi mata, amsaw tayi da Amin,Kiran ihsan tayi tazo ta miƙawa su A'S ruwa amsawa tayi da gata nan, fitowa tayi daga ɗakin ganin AS da matar shi ne ga kuma su Anwar yasa ta ƙarasa tana gaishe su, ciki ciki ya amsa dan bayi sake musu fuska, mubeena daman ko kallan ta batayi ba, miƙewa tayi ta dauko musu  ruwa, aje nusu tayi a gaba, kallan Anwar tayi haɗi da faɗin "Anwar zo" maƙe kafaɗa yayi alamam bashi zuwa, ba ta matsa mishi ba ta rabu dashi, "Anty kawo Anam" miƙa mata tayi daman duk hannun nata sun gaji, tana karbanta ta koma koma ɗaki wajen yan uwanta.
    Tana shiga ciki tayi ihun kiran meenal wacce suka baje sai fira suke "meenal yaya Ahmad sun iso shida Anty mubeena" 
   "Toh Ni ina ruwa na"
"Auuu mancewa nayi! ashe fa babu ruwan ki" ƙarasawa tayi tana miƙawa  meenal ita ganin Anam sai kallon ta take, taro hannu tayi zata karɓe ta, daga bayan ta taji mufeeda na faɗin "Ummi  Sarah Raiha yusrah ƙaraso kuga abinda nake gani" jin hakan da sukai duk suka ƙaraso suna kallan ta da tambayar mi ya faru, ba tare da tayi musu magana ba idon ta na kan Anam da wannan karan take hannun meenal, da hannu tayi musu pointing da Anam wai su kalle ta, kyakyawar gani kuwa idanun su yayi bakin YUSRAH da ba zama yake ba ita tace "EELHAM".
  "Ɗagowa ummi tayi tace a'a mai kama da ita dai ki duba fa babu abinda ta bari na eelham komi nasu hadda skin ɗinsu".
   "Sisters kenan nima akwai wacce na sani kamar su da yaya AS da Anam yayi yawa barin ma idan Anwar yayi murmushi kinsan ai su kama suke da yaya AS".cewar meenal,nan fa suka tuna da rayuwan su tare da eelham wanda har yau har gobe suna sonta da mararin ƙara ganin juna,nan suka hau ba su meenal da ihsan labari da yake duk basu santa ba dan ko lokacin da suke Minna ba'a gidan su eely ta zauna ba, suna tsaka da firan ne saiga Ummi ta shigo tana cewa "meenal da ihsan kuzo maza na aike ku, tashi sukai suna amsawa da toh Sarah ce tayi karab tace "ummi banda mu?" A'a rufan asiri ni ban aike ku ba salon mazajen ku su ganku! Kusha zaman ku,ku kuma taso muje"
   Daukan gyale sukai suna bin bayanta Saida meenal ta kai kofa sannan ta juyo tana yi mata gwalo
Pilon dake kusa da ita  tayi tana wurga mata,ganin haka ne sai ta kauce tana fice daga ɗaki da dariya.


___________𝘌𝘌𝘓𝘏𝘈𝘔
haka ta wuni yau suku suku tunda Ruqayyah ta gaya mata tagan Anwar yau shi kenan kewar yaron da take ta danne wa taji yana ƙara dawo mata sabo.
   koda suka dawo bata shiga harkan kowa bah harda Bestien ta kuwa duk maganan da yake mata ba wani amsawan kirki.
   "Elham Anty tace ki fito muyi diner" ba tare da ta kalli jawaher bah tace ta ƙoshi, bata ce mata komi ba ta wuce ta gaya wa "Anty eely tace ta ƙoshi".
Da kanta ta tashi ta shiga ɗakin "daughter taso muje muyi dinner kinji, zama hakan ai bashi yuwa"
  Shafa cikin ta tayi haɗi da faɗin "Anty am full"   "ok! make sure u eat before u sleep" amsawa tayi da "insha Allah" Fita tayi inda suka yi diner bayan sun kammala suka dawo falon suna ta fira har zuwa goma kafin kowa ya shige ɗaki.
    Koda su Ruqqy suka shiga sun iske eelham har tayi bacci da gani kuma ta daɗe da yinta,Saida sukai wanka sannan suka bi lafiyar gado asuba ta garii......


____________washe gari ya kasance meeting na familyn su mufee wuraren azahar dan Saida sukai salla kowa ya hallara wajen meeting daman haka suke. 
  Tunda ga kan iyaye, jikoki, ƴaƴa, kanne, yayun, da kuma surukai,duk sun hallara dakin taron,sun tautauna sosai akan matsalolin su da kuma sauran abubuwa daga ƙarshe kuma Abba ya nima da a cigaba da sanya su Ammie a addu'a Allah ya baiyana su,
Sosai Abba ya ɗan rame dan tun tafiyar su Ammie ya shiga danasani da yin nadama akan abinda ya faru.
  Amsawa sukai da Amin suna tuno su eelham,Saida suka ƙara tautaunawa sannan aka tashi taro da addu'a.

___________𝘈𝘕𝘕𝘌
"So nake ku saka mun ido akan yaya sosai,dan barazana take mun akan dukiya ta".
   "Hajiya indai zaki sake kuɗi zaki samu yadda kike so! kinsan muna da cikan alƙawari".
    "Ba ku da matsala da wannan idan kuɗi ce". Ta ƙare maganar tana dauƙan jakan ta,ciro rafa rafan yan dubu dubu wajen rafa biyar ije wa tayi bisa table dake gaban su haɗi da faɗin ga wannan a ɗan jajige kafin naga kamun luddayin abun!duk wani motsin ta inasan ya zamana a kunni na ku saka mata ido sosai"godiya suka hau yi mata inda ogan nasu ke cewa "Hajiya aiyanar kawai an gama  za kuma kiga aiki da cikawa! Godiya muke Allah ya bar mana ke".
   Da Amin ta amsa tana sallaman su koda suka fita dariya ta saki kamar wata boss tare da faɗin "yaya mun saka ƙafan wando ɗaya dake kenan".......

__________𝘈𝘡𝘐𝘡𝘈 
    Bayan antashi daga wajen meeting kowa ya nufa sashen shi ya'yan na bin iyayen nasu zuwa part ɗinsu wasu kuwa part ɗin inna suke shiga,
Haka ta kasance ga matan HYDAR Aziza, bin momma tayi zuwa part dinta  har bedroom tana ruho ƙofan
    Dagawo momma tayi babu wasa a fuskar ta. Aziza kuwa bata damu da haka ba sai niman wajen zaman da tayi,tana taunan chewing gum,ta daura ɗaya kan ɗaya.
     "Wani iskan ci ne zaki shigo mun ɗaki kai tsaye babu niman izini"
    Taɓe baki tayi haɗi da hura chewing gum dake bakin ta tayi balan balan dashi sannan ta sace kallan uku saura ta watsa mata sannan tace "na lura wannan ɗan naki bayi jin maganar kowa sai naki!  shi yasa nayi tattaki dan nazo ki isar masa da saƙo na" ba tare da ta jira cewar momma ba ta cigaba da faɗin "kamar yadda yake faranta miki rai Nima haka nake son na farantawa nawa iyayen rai! So nake ya siyan mun gida manya guda biyu da kuma jari mai tsoka wanda zan bawa mahaifiyata dan ta dogara da kanta kamar yadda kike".
     "Munafuka! ƙarya kike baki kai wannan matsayin ba! gida kuma koda ɗaki ɗaya ne bazai siye shi bah sa...... Katse ta tayi da faɗin "Hajiya kenan kin manta wace Aziza ko? Bara na tinasar dake abinda kika manta" daukar wayar ta tayi ta shiga recording ta kunna mata taji. Nan fa zufa ya dinga karyo mata dan batayi tunanin aziza ta naɗi maganar ba. Fisge wayar tayi daga hannun momma tana nufan ƙofa,Saida ta je ƙofa ta juyo tace "kafin nan da 28hours naji alert!ki kuma gaya masa yazo mu koma a yau dan bazan ƙara kwanan gidan nan ba" tana kaiwa nan ta buga ƙofa tana ficewa.
    Sosai momma ta shiga tashin hankali da fargaba tasan wace Aziza,idan tana son rufun asirin ta,tayi yadda take so, daukar waya tayi ta hau kiran yaya Hydar zuwa yanzu ta san dai sun idar da salla, ringing biyu kuwa ya ɗaga,"kazo ka same ni yanzun nan" tana faɗa bata jira cewar shi ba ta yanke kiran
Ba'a dauƙi wani lokaci ba ya iso.bata wani saurari gaisuwar da yake mata ba tace "akwai abinda ya rage da zakayi?" "A'a momma babu"
"Toh ka ɗauki matar ka ku wuce hakanan! sannan ya kamata ace ansiyawa mahaifiyarta gida manya guda biyu a kuma bata jari mai yawa wanda zata iya dogaro da kanta".
  Kallan ta yayi jin lissafin da take ta faman yi,zai yi magana ta katse shi da "umarni nake baka ba Shawara bah kafin nan da 28 hours nake son haka ya faru". Gaɗa kai kawai yayi, dauke idonta daga kanshi tayi tana "zaka iya tafiya" jiki duk a sanyaye ya bar part ɗin,shiga sauran part  yayi yana sallaman su zai wuce wai uzuri ya tasar mishi, haka dai ya dauki matar shi da ta zame masa alaƙaƙai suka bar gidan.....


________mubeena da AS a ranan suka koma Kano jirgin magrib suka bi dan itama tace bata zama.
Wayenda suke kusa ana idar da sallar  isha'i suka bar gidan hadda su ummi duk sun wuce,sai gidan ya koma shiru dan daga meenal sai ihsan da Ummi sukayi saura,Ummi ma taso su tafi a yau ɗin sai meenal tace su bari gobe su bi fligh na safe,shi yasa ma basu tafi bah.

Kamar yadda sukace kuwa karfe goma na safe jirgin su ya sauka a airport na Kano, yaya AS ya turo driver ya dauke su zuwa gida, da yake tafiyar jirgi ba kaman na mota bane yasa suna ɗan hutawa kadan suka shiga part ɗin grand ma suka gyara mata shi ƙal duk da ba wani datti yayi ba dan ana yawan gyara shi akai-akai,bayan sun kammala kulle ƙofan sukai suna fitowa daga sashen........✍🏻
.