EELHAM🌹

32&33

by @rabearhwakili




Episode 32 & 33📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai



_________Cikin shiri ta tashi da niyan komawa gida,dan ji tayi duk kewan goggo ya dame ta.
    Tashi tayi ta fito bakin ƙofan Anty tayi knocking izinin shiga ta bata daga ciki,shiga tayi ta nimi ƙasa ta zauna tana duƙar da kai "daughter a kwai abinda ki ke da buƙata ne?".wasa da yan yatsunta take kafin cikin nutsuwar ta murya a kwance tace "ina son na koma wajen goggo yau" ɗan jim Anty tayi kafin tace haba daughter kwanan ku biyu da zuwa shine har zaku wuce? Ɗauka na ko zakuyi mana sati". Ƙasa ta ƙara yi da kai kafin tace "Anty next time zamu dawo" babu yadda ta iya face cewa "shikenan jeku shirya sai driver ya maida ku". Tashi tayi tana yi mata godiya sannan ta fito daga ɗakin zuwa na jawaher.
    Koda ta koma cewa Ruqqy tayi zata koma gida yau, jin haka ne sai Ruqqy tace "haɗa dani nayi kewar su goggo" jawaher na jinsu sai jikin ta yayi lagwab dan zatayi kewar nasu, Kallan su tayi tace "yanzu tafiya zakuyi?" "Sawaaa da gudu ma ai munyi ƙokari ko kuwa eelham?" "Ai ba sai kinyi magana bah" cewar eely tana buɗe waldrop dan ta haɗa musu kayan nasu. Ita dai jawaher shiru tayi tana ta kalan su har suka gama haɗa kayan nasu daman cikin shirin su suke suna gama haɗa kayan suka fito daga ɗakin zuwa falo jawaher biye dasu a baya.
   Anty na falo daman ta gayawa driver akan zai sauke su eelham a gida.
    Ƙarasawa sukai gareta, "yara na har kun gama kenan?" Amsa mata sukai "toh ga wannan ku gaida su goggo ina nan shigowa! Allah ya tsare hanya" godiya sukai mata sosai sannan suka tashi suka fito jawaher tayi musu rakiya har bakin mota suna shiga driver ya ja suka bar gidan,jawaher  na daga musu hannu ganin tafiyar su ne sai ta koma ciki tana jin kaman tayi kuka......

___________ya kamata a kai su Anwar su gaida umm ɗinsu Kinga tunda suka dawo bamu kaisu ba ya kamata a ce anyi haka "cikin rashin damuwa da maganar shi "tace sai sun dawo" "tare zamu zuwa gobe"  "babu inda zani! ba zai yiwu naje geto area na dawo na kasa haɗe yawu ba atoh!kai da su da kuka ga zaku iya ƙofa a buɗe take".da kallo kawai ya bita ita ne da ta gaji da kallon da yake mata sai tace "Ni ka daina kallo na" dan murmushi yayi yana kau da kai gefe, tashi yayi yana cewa "zan je gidan Ummi ki miƙo min su Anwar". Kiran mai aikin ta tayi, gaida su tayi sannan tace "Hajiya gani"
   "Ki shiga ki dauko su Anwar sai ki haɗa musu kaya cikin trolley kiyi sauri yana jiran ki" 
   Amsawa tayi da Toh ta miƙe ta nufi dakin Anwar ta haɗa masa kayan sa, ta shiga na Anam da yake kaman ba ɗakin yara ba, ita ma ɗin kayan nata ta haɗa, fitowa tayi ta nufi wajen motar da driver ya ƙaraso dashi.bot ya buɗe ta saka trolley sai ta rufe ta yanki wani hanya dan tasan Anwar yana can, babba fili ne da aka ƙawata shi da kayan wasan yara na zamani babu abinda babu na wasan yara a wajen, Anwar ta gani yana ta wasan shi ga kuma sabuwar nany da aka kawo musu ɗauke da Anam a hannu.
 Gaisawa sukai sannan tace "Hajiya tace a kawo su Anam zasu fita". Ba musu kuwa ta miƙa mata Anam ta kama hannun Anwar suka fito, wannan karan a waje suka iske AS da mubeena, ganin zuwan nasu ne sai AS ya shiga motan mubeena da ta amshi Anam sai ta miƙo mashi ita Anwar shiga yayi yana yiwa mubeena momyn shi bye bye ita ma ɗin bye tayi mishi ganin sun tafi sai ta koma ciki.....

__________ganin su kawai goggo tayi kwatsam, sake tayi da baki tana cewa "a'a wa nake gani kaman yan kwana?" 
"Mune nan goggo" cewar Ruqqy "ashaaa ai kuwa ku ku ka iya zuwa kwana ina laifin ace kuyi musu koda sati amma kwana biyu ku wani kamo hanya?". "Mun yi kokari ma a haka fa goggo" 
"Kaji ta fa wani ƙokari anan kwana biyu kawai  sannun ku kuraye" cewar umma da fitowar ta kenan taji Maganan "atoh su suka sani sai suzo mu zauna tare ina faɗi suna faɗi daman abinda suke so kenan" "goggo mu ɗin?" Cewar eely tana ƙarasawa wajen umma "a'a ni ɗin"  "tuba muke goggo" nan suka gaida umma da goggo, "ya kuka baro su?" Alhamdulillah suna gaida ku duka tace tana nan shigowa" "muna amsawa kuwa Allah ya bada iko" Amin, kai kayan nasu sukai cikin ɗaki sannan suka fito suna ta shan firan su....

_________"yau an kawo mana su kenan ƴaƴan gold" shi dai dariya yayi da faɗin "za'a gyara Ummi"
  "Allah ya sa haka" da Amin ya amsa 
"Kasan gobe grandma ɗinku zata zo Koh?"
   "Eh ummi bappi ya gaya mun"
Masha Allah daman nayi tinanin ko baka sani bane"
"A'a! Taji sauƙi kenan tunda gashi naga zata dawo nan ɗin?"
   'Toh sai godiya jikin dai sai a hankali daman jikin tsufa"
"Allah ya ƙara mata lafiya" da Amin ta amsa, suna canza fira meenal na gefe suna ta wasa da Anam
    "Yauwa yaya ban faɗa maka ba Yaya" bata jira cewar shi ba ta cigaba da faɗin "a wajen aikin mu akwai mai kama da mu sosai,da muka je Abuja su mufeeda na ganin Anam suka ce tana kama da ELHAM sak"
Ji yayi ƙirjin shi ya motsa tabbas in har maganan eely take duk da bawai yasan sunan ta bane tabba koshi ya shaida kaman nin nasu,amma a zahiri sai ya chuskune fuska yace "meenal ki rage ƙarya" ɗan tura baki tayi tace "yaya wallahi da gaske nake! Idan naje aiki zan dauko ta a hoto ka gani ta ma fi kama da Anam! Tunda anam fuskar ka ta dauko". "Ban aike ki bah"
   Jin yace haka sai tace "Ummi kinason ki ganta Koh?"  "Dole na so naga mai kama da ƴaƴana"
    "Insha Allah zan gwada miki ita kuwa! Saidai Allah yasa ta yadda nayi mata hoto! Kin tuna Ummi labarin dana taɓa gaya miki na wata da naso na ragewa hanya taƙi?" 
    "Na tuna ta auta! Allah yasa ta yadda Toh" "Amin dai" shidai yana jin su baisa musu baki ba,kunnin shi gajiya yayi da jin labarin ta sai ya miƙe ya shiga ɗakin sa da yayi samartaka a ciki, da kallo meenal ta bishi Saida ta ga ɓacewar shi sannan ta matso kusa da Ummi "Ummi! Daman wallahi yaya ya ganta yace yana sonta ba ƙaramin dacewa zasuyi ba" 
    "Auta!Auta ina raba ki da kiwon awaki kina kille ta haihu,ki dage ya ji ki ba ruwa na"
   Zata yi magana kenan sai taji muryan shi a dake yana kiran sunan ta "meenal" ji tayi daram dam dammm haka ƙirjinta taji ya buga, zare ido tayi tana ta shiga uku ƙara kiranta yayi amsawa tayi murya na rawa kallan Ummi tayi amma sai taga ta ɗauke kai,jiki duk a sanyaye ta hau zuwa upstairs da addu'oi a bakin ta, dakyar ta iya knocking a kofan,
    daga ciki taji yace "shigo" tura kofan tayi Sannu a hankali ta shiga ciki wanda sanyin AC da ɗaddaɗan kamshi sukai mata maraba "yaya gani" Kallan ta kawai zakayi kasan cewa bata da gaskiya ko kadan duba da yadda jikin nata ke ɓari. ɗagowa yayi ya kalle ta jin yadda muryan ta ke rawa ba muryan kawai ba hadda jikin nata rawa suke kauda kai yayi kaman zai yi dariya amma sai ya dake yace  "wani time  grandma zasu sauka" eh naji Ummi na cewa 12pm gaɗa kai yayi sannan yace da "/ki shirya keda su Anwar around 4 zamu fita" wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke jin ba akan abinda tayi tinani bane godewa Allah tayi da baiji mi take faɗa ba.
Abinda bata sani ba duk a kunnin shi maganar da tayi ya dai basar ne kawai "je ki" da sauri ta miƙe hadda godiya......


___________tashin hankali kullum a cikin shi yake tun randa ya saki eely ya rasa gane kanshi, a lokacin tabbas shi yasan ba sonta yake ba amma a yanzu soyayyar ta yabi jinin jiki da jijiyoyi,lokacin da yayi sakin abin bai dame sa ba sai daga baya,daka ganshi a yanzu kasan yana cikin damuwa,ƙarin damuwar shi matar shi ce,bai isa yace Zai ɗauki mataki akan haka ba dan momma zata wanke shi tass.
    Kaiwa da komowa yake ta faman yi,faɗin yake cikin zuciyar shi idan ba sata ba mi momma take son yayi bashi da isassun kuɗi itama ta sani,shine zata ce ya siyar wa wata gida har biyu da kuma jari "inaaaaa Allah ya gani saidai suyi haƙuri,Nima manage rayuwa nake"daga bayan shi yaji an kwashe da dariya koda bai juyo ba yasan wace da wannan ɗanyen aikin.
   haɗa fuskar shi yayi tsaff ba wasa a cikin ta ya jiyo da kallan sa kan Aziza dake kallanshi tana dariya kaman ta samu mahaukaci, cikin harzuƙa da kuma cikinta da yake dashi dan yasan babu wanda zai kitsa wanna munafincin idan ba ita bah. Tsawa mai rikitarwa ya sakar mata "Aziza get out" ita da akayi wa ko ajikinta sai manuniyar da ta nuna masa haɗi da faɗin "kul rijiya ba gun wasan makaho bane ka gane!? Ni ba wannan ba zuwa nayi naji an samu gidajen ne kokuwa sai lokacin dana bada ya cika?". Wani malolon takaicinta ne ya tokare masa ƙirji danne zuciyar sa yayi dan kar yayi abinda ba shikenan ba, cikin rashin hayaniyar sa yace na "ƙarfin mutanen da ne sai ki zo ki karɓa"
"A'a dakata bada ni zakayi ba da uwa....." ɗauke ta yayi da Lafiyayyan mari har biyu wanda hakan ya katse mata zancen nata "koda bakin wasa kika ƙara zagin mahaiyata Wallahi sai na lahira yafi ki jin daɗi,nonsense kawai" har ya kai ƙofa ya ji ta ja muguwar ashar tab akwai akwai bala'i har Ni zaka mara akan na zagi wancan matar? Toh na rantse saidai ka kashe zagin nata yanzu kuwa na fara zan gwada maka daga kai har ita banida hankali" bai tsaya ya saurari abinda take ta faɗa ba ya baro mata ɗakin dan in yace zai zauna yana iya yi mata mugun duka a banza a hofi.....



__________dawo wan su eely yasa goggo haɗa yanata yanata ta koma gidan ta wanda umma bataso ba dan taji daɗin zamanta da goggo.
   Elham ce ita da Ruqqy sun saka goggo a tsakiya suna fira eely ce ta dubi goggo haɗi da faɗi "goggo ki siya min waya na gaji da zama hakanan" 
"Ai ko wuta ke fita daga bakin ki bani siyar miki waya, nan Ahmad ya kawo muku waya kikace baki so! Kuma baki ɗauka ba tunda kin aje banki a gida koh" 
    "Toh haka kawai zan tafi in karɓa bayan ba sanin shi mukayi ba"
  "Elham kiji tsoron Allah baki san shi ba amma ai kin san yaran shi! Kice dai baki gadaman karɓa bane" cewar Ruqqy "kaiya mi ya sa kika bata ansa? da hita batun ta kikayi! Waya kuma bani saye idan kina buƙata ga naki can a ɗaki ki dauko kamar yadda yar uwarki ta ke amfani da". "Idan ma bataso sai in haɗa duka biyu in riƙe!ko kuwa goggo?. "Abinki ba" harara take wa Ruqqy tana tashi ta nufi ɗaki Saida ta shiga sannan ta leƙo "karki taɓa min waya na" "daman gulma ne ana so ana kaiwa market"
    Kin kulata tayi tana bugo ƙofan da ƙarfi "yi a hankali ai bashi ya kar zomon ba rataya aka bashi dan haka karki karya min ƙofa atoh" 
  Cikin niman jan faɗa Ruqqy ta ɗaga murya yadda zata ji tace "goggo ratayan ma  ban bashi bah" tashi tayi ta shiga ɗakin goggo ta fiddo da wayar eely tambayan goggo tayi ko eelham tana da sim, amsa mata goggo tayi da faɗin "a'a saidai kuje ayo mata ko zuwa gobe idan kun taso daga aiki"  "insha Allah haka za'ayi kuwa ai dole sai ta riƙe wayar nan" "Allah yasa toh" Amin........



___________𝘸𝘢𝘴𝘩𝘦 𝘨𝘢𝘳𝘪
Hajiya mama sun sauka tun sha biyun rana inda ta samu tarba daga wajen jikokin ta guda biyu da sirikar ta'ta 
   Kyakyawar mata ce tabbas duk da tsufa ya bai yana a jikin nata hakan bai hana kyawunta fitowa ba, gata da open teeth,skin ɗinta ya kasance chocolate,hancin nan zir kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa a zamanin ƙuruciya anyi yar kwalisa da iya wanka.
    Da sauri meenal ta shigo zuwa cikin ɗakin grandma, bappi da Ummi ne a ciki.
  Ummi tana zaune daga gefen ta a ƙasa tana matsa mata kafa dan zama guri dayan da tayi har ƙafan sun ɗan tashi.
 Da sallama ta shigo cikin sauri tace "bappi Ummi grandma sai mun dawo zamu fita da yaya kuma yazo yana jira na kar yace ya fasa" 
    "Ooh ni KHADIJATU yanzu da wannan surutun da kika tsaya ai da wuce wan zai yi da ya wuce" cewar grammar.jin sallamar shi  dauke da Anam, Anwar yace dai bazai shigo ba, gaisar da iyayen nashi yayi da grammar. Ansawa sukai da kulawa duk da dazun yazo tarban kakar su, miƙewa yayi yace "bara muje kar yamma tayi" adawo lafiya sukai musu, fitowa sukai suka nufi mota suka bar gidan....

__________dan Allah eelham kiyi sauri yamma tana yi fa kuma kinsan zuwa 6 suke rufewa! Sabida nasan halin ki yasa nace mu biya daga gurin aiki amma kikace honhon,da yanzu bamu dawo ba! Kuma kinsan daga nan za....." Sallamar meenal shi ya katse mata zancen nata amsawa tayi da mamakin ganin meenal a gidan su, kafin tace komi taji Anwar ya shigo da gudu yana faɗin "umm!umm"
Fitowar ta daga ɗaki kenan kunin ta tayi mata kyakyawar ji da gani,shima ganin ta ne yasa ya a ƙarasa wajen ta yana yi mata oyoyo, "my boy" "na'am umm" nan ta ɗauke shi sama da shafa kanshi cikin nutsuwa tace "boy over miss you" "same too" 
"da gaske?" 
   "Sure umm ask papa"
Shafa kanshi tayi tana ƙara kamƙame shi kaman ance za'a kwace mata shi. 
 "Mallama karki karya wa mutane yaro" Saida Ruqqy tayi magana sannan sannan ta ɗago tana fuskantar Ruqqy sai idanun ta ya sauka akan meenal dauke idon ta tayi daga kanta tana mai dashi ga Ruqqy "idan aka karya basai a biya su bah"
    'Iyeeeeee lailai wuyan ki ta isa yanka toh dami zaki biya su?"
   "Allah ya shirya ki"
"Gaba ɗayan mu ehem!"
"Wa nake gani haka kaman manyan gari?" Goggo ke tambayan da fitowar ta kenan daga banɗaki 
    "Shine fa goggo baki ga yadda aka wani maƙure shi ba?"
    Harara ta kai mata sannan tace "shaƙe shi nayi"
     "Allah ya taro mana ku" cewar goggo tana maida duban ta ga meenal dake zaune akan kujera yar tsugunno tana yiwa dramar su dariya  "yanmata sannu da zuwa" "ina wuni" meenal ta gaishe ta "Alhamdulillah ya mutan gida?"
   "Lfy qlau alhamdulillah suna gaida ku duka"
    Madallah halan ke kika kawo Anwar? 
    "A'a yaya Ahmad ya kawo mu yana waje"
"Ikon Allah wai Ahmad ya rinƙa abu kaman baƙo ke Ruqayyah ce masa ya shigo mana" amsawa tayi da to tana cewa eely "ina dawowa zamu wuce na dai faɗa Miki" 
  Inda ita kuma ta amsa da "toh goggo"
   Da sallama a bakin shi ya shigo yana gaida goggo,bayan sun gama gaisawa ne eely ta gaida shi a daƙile wanda ba lailai yaji ba amma da yake yana da karfin ji ya amsa mata da Lafiya "goggo bamu kuɗin abin hawa"cewar eely tana magana ƙasa ƙasa dan kar aji ta, "kije ki ɗaga pillow ki ɗauka kuyi maza kuje  kunga ga yan uwanku sun zo" 
   Taɓe baki tayi tana maimaita yan uwa kai goggo dai akwai kalan dangi (ba Ni nace ba!kar sister meerah tayi ƙuliƙulin kubra dani). Shiga ɗakin tayi ta da dauki kuɗin a inda ta faɗa mata fitowa tayi tana cewa "Ruqqy muje" 
  Dashi zaki?" Cewar Ruqqy tana tambayan Elham "ya son ranki?" 
 "A'a Allah ya baki na mai bara"
Goggo ce tace "a'a Elham ki aje shi kar suzo zasu tafi baku dawo ba ki saka su jira" duk abinda suke yana jinsu saidai abu ɗaya ya sani bazai iya bari ta fita da wannan guntun vail ɗin ba, ba dan komi ba sai dan ta kasance mai rainon masa yaro so bazai so ta fita a haka ba dan tarbiyan ɗansa (ummm). Ba tare da ya dube su ba yace "goggo ina zasu je?". Da yake goggo ba rufa rufa nan ta gaya mishi "zasuje siyan sim ne dan sai yanzu ta ga daman daukan wayar da ka siya musu shima Saida na haɗa mata da jan ido in ba haka ba ba ɗauka zatayi ba"
    A dan sace ya kalle ta ganin sai harara take banka wa Ruqqy da ba ita tayi magana bah, ɗauke kai yayi da ɗan guntun murmushi a fuskarsa wanda sai ka kallesa da kyau zaka lura da haka "goggo bara na kaita" 
"A kai ni inaaa tab babu kuwa inda zani" haka take faɗi ciki zuciya samun waje tayi ta zauna wai ta fasa zuwa sai gobe  "ƙaryan ki tasha ƙarya tashi kuje kafin na ɓata miki yanzu"
   Ganin goggo da gaske take sai ta dauka Anwar ta wuce fuuuuu zuwa waje su Ruqqy da meenal mi zasu yi in ba dariya bah. Shima sallamanta yayi da faɗin "sai sun dawo" adawo lafiya tayi musu,amsawa yayi da Amin yana ficewa daga gidan.

A gefen mota ya tadda ita Anwar dauke a kafaɗan ta, taso ta dauko Anam amma dizgin da goggo ke shirin yi mata yasa ya fasa tayi fitowar ta. Buɗe motan yayi ya shiga itama ta buɗe front sit ta zaunar da Anwar da niyar ta zauna a back, saide mene ta buɗe ƙofan yaƙi ya buɗu,sosai ta kai wuya tasan shi yayi wannan aiki amma sai ta fisge ta koma front sit tana daura Anwar a kan ƙafafun ta, kauda kai yayi ganin ta shiga yana jan mota suka bar arean.
     Anwar kuwa sai surutu yake zuba mata amma dai bata kula shi ba dan jinta take duk a takure 
     A bakin office ɗin da zasu siya sim suka tsaya kallan ta yayi yaga gyalen da tasa ɗan cikuli ya kuma maida duban shi a waje yaga ga maza je nan ji yayi bazai iya bari ta shiga wajen nan ba, fita yayi saidai baice mata komi ba ya shiga.
   ita kam bata ma yi tunanin bin nasa ba dan baice suje ba Toh wani niman suna zatayi.
   kusan  20 mint sai gashi ya fito dauke kai tayi daga kallon shi. Buɗe motan yayi ya tada suka bar wajen,Anwar kuwa yaji iskan waje bacci yayi gaba da shi. a bazata taji muryan shi yana faɗin "wancan wayar bata Miki bane?" Shiru tayi batace komi ba Saida ya ce "uhmm" amsawa tayi da "yayi"
     "Mi yasa baki amfani da ita?"
Wannan karan ma a daƙile ta amsa da "babu" bai ƙara cewa komi ba har suka iso gida saida ta buɗe kofa zata fita ta tsinkayi muryan shi yana faɗin "karki sake fita da irin wadan nan vail! Ok?" Wane mutum inji mutuwa ai yanzu kuwa ta saka ƙafan wando ɗaya da sanya su ina dalili. Katse mata tinani yayi da miƙa mata sim.hannu ta saka ta karɓa tana yi masa godiya, "kice wa meenal ta fito da Anam mu wuce, zan dawo na dauki Anwar anjima, tunda suka fita bata kalle sa ba sai yanzu da taji za'a wuce dasu juyowa tayi fuska a marairaice a hankali tace "dan Allah ko Anwar ne a barmin ya kwana"
   "bazan dawo anguwan nan a gobe ba dan zanyi tafiya zuwa gobe! idan na barshi wa zai kaishi?"
   "Yaya Umar idan yazo"
"Tare zamu"
      Shiru tayi tana tunani can tace "zamu kai shi nida Ruqayyah"target ɗinshi tana aiki kenan amma sai ya fisge yace "ok zan turo miki da address" gaɗa kai tayi tana fita daga motan Anwar a hannun ta....✍🏻