34&35
Episode 34 & 35📲
***
بسم الله الر رØÙ…Ù† الر ØÙ‰Ù…
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
___________"yaya wai ya akayi ka santa? itace fah nake baku labari jiya! Dan Allah yaya baka ga kamannin mu a tare da ita bah?" .
"Ke mi yasa baki gani kiyi shiru ne?"
"Kawai dai yaya tambaya nake, ita ma wajen aikin mu É—aya, saidai kowa da nasa department"
"Ashe wajen aikin ku É—aya ai ban sani bah a wani ma'aikatan?". "Lallai ma yaya wai ni zai yi wa haka sha kurumin ka kaman a kunnin Ummi" duk wannan zancen da take a zuci take yinta.
Koda suka kawo gida har sauri sauri take ta ganta gaban ummi dan ta shafa mata inda suka je. Shi kuwa kallan ta kawai yake yana mamakin son gulma irin na meenal,haka dai harsuka shiga part É—in grandma......
_____________kiran duniya tayi wa momma amma taƙi ta dauka wayar dan ta dau alwashi duk abinda Hydar yayi mata a kanta zata huce ganin dai ta kira ta kira ba'a ɗauka ba, ita kuma bata jin zata iya kyaleta bata baƙan ta mata bah, shi yasa tana tashi daga baccin rana ta zari mayafi ta fita daga gidan tana ƙara ƙiran momma.
Duk kiran da Aziza ta rinƙa yi mata duka akan idanunta tun daga na jiya har na yanzu ɗauka ne kawai bata yi ba dan tasan kiran nata ba alkhairi bane a gunta.
Daga É—akin Abbie ta fito dan kwana biyu bai baiji daÉ—i ba shi yasa baya fita gun aiki.
sauri sauri take ta shiga ɗaki tayi kiran Hydar karya bari matar shi tazo mata gida,dan ga call ɗin ta nan sai shigowa suke.saidai kash zata shiga ɗaki kenan sai ga mamy tana nufo inda take hakan yasa ta dakata daga shiga ciki tana ƙirƙiran dariyar da bai ciki bah, "mamyn yara ne tafe? Sannu da zuwa" cewar momma da fake smile "aikuwa dai kin ganni da tsakar rana daman jikin yaya nazo dubawa" ba tare da tunanin komi ba ta ce "ya samu bacci ai" "Allah ya ƙara sauƙin, tunda yana bacci bara na dan zauna nan can ɗin duk sun fita" harara ta sakar mata a sace amma a zahiri tace "Bismillah mu shiga" koda suka shiga tana ta niman hanyan da zata shiga dan ta kira hydar amma no way.
Kamar wacce a ka hankaÉ—o haka ta faÉ—o cikin parlon ba sallama ba komi, ji momma tayi zuciyarta ta motsa faÉ—i take watan tonon asirin ta ya tsaya nan fa zufa ya fara karyo mata kamar wacce ta haÉ—i kwaÉ—o.
Aziza da tashigo a bala'ence saidai ganin mamy a wajen sai ta wayan ce tana gaida ts.
Ita kuwa da take musu kallan tsaf ta ƙasan ido amsawa tayi kaman bata san halin da suke ciki ba, haɗi da faɗin "yaya na gaishe ki bara naje" tayi maganan tana saka wayar Tata a gefen hannun sofa dake falon ta yadda babu wanda zai lura da waya a gun.
Cikin yaƙe momma ta amsa mata da "na kuwa gode sosai"
Amsa ta bata da babu komi sannan ta fita daga falon tana murmushi.
_________"kina a garin nan kuwa mubee? kin kuwa san mike faruwa ke kina nan zaune cikin gida?". "Kiyi magana mana zeenat duk kin saka hankalina kasa kwanciya"
"Tun kafin kiji ma hankalin ki ya kasa kwanciya inaga ma kinji" ƙallata mubeena tayi haɗi da faɗin "Ni nace ki faɗi kan ki tsaye"
"ai abun ne da nauyi kai kana gida ana can ana ci maka amana, ɗazun na fita wajen dawowa traffic ya tsaida mu ashe napep ɗin mu yana gefen motan AS ni ban sani ba kaman ance in juya naga mace a gaban motan shi ga Anwar a kan ƙafafun ta sai raha suke suna dariya ga......" Katse ta tayi da faɗin "Dakata zee wannan wani irin maganan banzace har ni zaki kalla kice Kinga mijina da wata a mota?". Da kyar ta iya danne zuciyar ta gudun kar ta gwada mata halin ta so take sai ta kore ta daga gidan ta kuma aure AS sannan. Da yake ta iya makirci sai ta fisge haɗi da faɗin"shi yasa tun farko naƙe jin yadda zan gaya miki Ni badan kin matsa ba ma ai baza kiji ba da kaina zan tayaki daukan mataki saidai kiji labari daga baya". Lailai namiji kenan,toh wallahi ya dawo ina nan ina jiran shi, da girma na a gari zai je yana nima mata wa......." Habawa sai kuka ya ƙwace mata kuka take sosai kamar ranta zai fita,ita kuwa zeenat tana kallon ta amma ko lallashin ta batayi ba. Saida taci kuka ta gode Allah sannan tayi shiru dan kanta. Ita kuwa zeenat farin ciki fal zuciyar ta, ganin tayi shiru da kukan da take ne ta taso tana zama a gefenta tana faɗi "kiyi haƙuri tunda kin samu kin rage nauyin da zuciyar ki take, shiyasa na barki kiyi kuka! Tabbas abin da ciwo kana tare da miji amma shi hankalinsa na waje babu daɗi! Shi yasa tun farko na gaya Miki ki daina sakar masa da yawa hakan yakan kawo raini amma da yake wancan gidahumar Shamsiya na baki shawaran banza sai kika yi watsi da nawa, to yanzu Kinga wa gari ya wa ya?".ta ƙare maganar da taɓe baki tana hararan ta.
"Tabbas na gasgata maganar ki zee kuma nayi dana sanin ƙin bin shawaran ki tun farko" ta ƙare maganar da sharan kwallan da suka kasa tsayawa "a Toh yanzu gashi abinda nake ta Miki gudun shi ya faru! Abinda za'ayi ko ya dawo kar kiyi mishi magana ki jira sai na ƙara confirming, saidai kar ki ƙara sakar masa fuska har sai mun gano,kar ki kuma sanar da shamsiya ko ba gaskiya bah?". Cikin gaɗa kai da ganin zeenat mai sonta tace "haka zan yi kedai kiyi kokari ki binciko mana ita da kuwa har gida zan bita naci ubanta! Tunda su sun iya bin mazajen mutane" datse ido zeenat tayi tana ganin kaman habaici mubee ta ke mata.
Bari inje daman akwai inda zani sai nace Bara dai na tsaya! Shiga ki fito min da yan canji kin ganni nan biyar ban ma gani"
"Saidai ko nayi miki transfer banida cash" wani transfer kuma dashi nake son na hau napep gashi ban fito da ATM ba"
"Ya kike son ayi yanzu nidai banda cash?".
"Ki duba mana ko mai gidan naki ya aje"
"A'a Ni bana taɓa masa kuɗi dan yana bani koda ban buƙata ba"
"Tabb ai shi yasa wahala bata ƙare Miki,sabida Allah kice sai kin jira ya miƙa miki? Wasu matan dai suke zub da kansu wajen mazajen nasu, yo to ina dalili! Nidai je ki dauko min ko 20k ne tunda ke baza ki dinga ɗauka kiyi hidiman gaban ki ba kice ke sai abinda ya ɗauka ya mannara Miki,alhalin wata banza tana can tana ci a waje! Wallahi mubeena u better shine ur eyes ehem". Ba dai tace mata komi ba ta shiga ɗaki,fitowa tayi hannun ta riƙe da ATM da ake aikan yan aikin gidan kasuwa dashi "zeenat ga wanga kiyi amfani da shi" tana miƙa mata, ba kunya kuwa ta saka hannu ta karɓe babu sannu bare nagode sai taɓe bakin da tayi tana barin falon.mubeena kuwa kogin tunani ta faɗa dan batayi zatan haka ba amma bazata yi mishi magana ba za dai ta cigaba da saka masa ido ta kuma daina sakar masa kamar yadda zee ta bada shawara....
_________"wai ke sai yaushe zakiyi hankali so nawa zance ki daina shigo min ɗaki kai tsaye, ina ƙara nanata miki kibi a hankali bani da kyau idan kuma kin ce ba haka ba hmmm"
"Hajara kike ko waa?ke kika saka ɗanki ya dake n....." "Dakata ƙaramar mara kunya ba duka kawai ba! Idan ma akwai abinda yafi haka tsaff zan saka shi yayi! Dan haka tun wuri kafin na canza ra'ayi kizo ki barmin gida kafin kiyi kuka da kanki"
"Hehehehe chasss kin zata barazanan da kike wa mutane zai bani tsoro ne? To ko ɗaya barazanan ki bai taɓa bani tsoro ba ko dai-dai da second ɗaya wucewa kuwa zanyi sa ne dan na ga daman badan kince ba dan baki da wannan matsayin da zaki saka ni nayi! Sannan Gobe ranar da na yanke muku ke da ɗanki zai cika idan har yakai gobe ba'a yi min abinda nake so ba sai na tona sirrin da kike boyewa duniya sun shaida ke din mai fuska biyu da zuciya biyu ce,sannan karki fasa Turo min mutane su karɓe recording ɗin dake hannu na, dan ko sun karba akwai wani a wani wajen! wajen mutane 6 fatan kina ganewa!na barki lafiya" karan rufe ƙofan da tayi shi ya maido ta cikin hayyaci, eh lailai ta ƙara tabbatar da cewa Aziza hatsabibiya ce ta ƙarshe ji tayi jikin ta na karkarwa dan gudun abinda zaije yazo cikin karaji ta ce "mi yasa na bar Aziza taji sirri na mi yasa na bata ƙofan yin hakaaaaaaa" ta ƙare da ihu kaman wata sabuwar kamu a hauka......
_________Ruqqy ta dauko wayar eelham ta saka mata sim sannan ta yi mata settings da buÉ—e mata WhatsApp da dai sauran su. "Toh Hajiya eelham ga wayar ki Allah yasa a kashe lafiya duk da dai ba son wayar ake ba"
Hannu ta saka ta karba tana juya wayar a hannun ta,irin wayarta ta da ce saidai color ya banbanta,aje wayar tayi gefen ta tana cigaba da shan gari ta da yasha madara ga gyaÉ—a biji biji a cikin ta ga Anwar shima sai sha yake yana mata surutu.
"Goggo baban shi yace a maida shi gobe zuwa family house É—in su" tayi maganar kamar bata so, "eh ya kira Ni É—azun yayi min bayani bazai samu yazo ba zai yi tafiya gobe yace ku taimaka ku kaishi"
"Bari in fito mana da hijabi na goge mana mu samu na fita"
"Mai ƙafan yawo kawai" cewar eely tana hararan Ruqqy "Ni da ƙafata ace bazanje inda nake so ba kiji min mata"
"Mutun ne za'a ji miki ba mata ba"
"Oho dai"
Fita batun ta tayi tana kallon Anwar haɗi da faɗin "boy ka ƙoshi?" Amsa mata yayi da eh jin haka ne sai ta miƙe riƙe da hannun shi zuwa bakin rijiya dan ta daurayebmasa jiki.
Bayan ta dauko shi daga wajen wanke hannu ne ta kai zaune tana jan numfashi. Duban ta sukai "Ruqqy tace wannan jan numfashin fa na lafiya?". "Normal"
"Allah yasa! dauƙi ɗanki ki kaishi ɗaki naga ya fara jero hamma". Cewar goggo amsawa tayi da Toh tana daukan shi ta shiga ciki..
__________saida ta bari AS ya daÉ—e da barin gidan sannan take gayawa su Ummi "ummi kinsan inda yaya ya Kaimu?" Bata jira cewar su ba dan zumuÉ—in faÉ—i take "gidan girl É—insa ya kaimu ai acan muka baro Anwar! Ummi kiji abin mamaki wannan ne fa da nake ta baki labari jiya, toh gidan su mukaje"
"Iyeee kice kin gano mana ita,ya kika same su fatan duk suna lafiya?".
"Lfy qlau sun ce in gaida ki"
"Masha Allah muna ansawa"
Grandma ce ta dube su tace "maganar wa ake yi haka?"
"Wata ce da take aiki a company yaya shine yau ya kaimu gidansu fitan da kika ga munyi kenan"
"Shi Ahmad da kanshi? Lailai abun babba ne" dariya suka hau yi wa maganar ta ganin yadda take fabbama abun....
__________koda AS yaje gida yasha mamaki ganin mubeena ba tayi ta kanshi ba, sai shine yayi mata sannu da gida da tambayar lafiyar ta kamar yadda ya saba indai ya fita ya dawo.
A daƙile ta amsa da lafiya tana cigaba da dannan wayarta.
Da kallo kawai ya bita ganin changes a tare da ita na babu gaira babu dalili dan shi lafiya qlau ya fita ya barta.
Bai biye mata ba ya tambaye ta ko akwai damuwa ne. Amma ta share shi ta bawa banza ajiyar shi,wanda hakan ya zafe sa dan ya tsani yayi magana anaji ayi masa banza shi yasa shima sai ya hita batun ta,daga karshe ya haye sama ya barta nan.....
________mamy kuwa bata bi ta kan wayar ta ba Saida Aziza ta bar gidan sannan ta dawo da kanta Lokacin momma na cikin É—aki,hakan yayi mata daÉ—i tana É—auka tayi saurin fitowa dan kar momma ta fito.
Dakin ta ta koma tana saving din recording haÉ—i da faÉ—in "Hajiya Hajara kenan gani nan tafe gare ki insha Allahu".......
____________washe gari da misalin karfe 4 su eelham sun shirya tsaff dan zuwa kai Anwar gidan Ummi dan a jiya da dare ya tura mata sms na address É—in gidan.
"Goggo sai mun dawo" adawo lafiya Allah ya tsare hanya ku gaishe su"
"Insha Allahu"
"Anwar babu sallama koh?"
ÆŠaga mata hannu yayi yana"bye bye see u goggo"
Saida na roƙa? Toh banso riƙe abinka
"Mun tuba goggo" cewar eely, "shikenan! Anwar a gaida mutan gida".
Ficewa sukai daga gidan zuwa titi,babu jimawa suka samu napep zuwa anguwan su Ummi wanda eely take jin ƙirjinta yana sama da ƙasa.
A layin anguwan ya sauke su dan ba'a barin napep ya shiga da yake sun san numbern gidan haka suka rinƙa tafiya suna duba numbobin har dai suka iso gidan. Ruqqy kuwa sake tayi da baki galala tana kallan katafaren gidan. eely kuwa tunda ta kalli gidan sau ɗaya bata ƙara masa na biyu ba har suka ƙarasa gate, knocking sukai security na gidan ya fito ganin su da Anwar ga kuma eelham da yaga sai ya buɗe musu ƙofa suna shiga ciki.
Zare ido sukai tayi dan basu san inda zasu shiga ba Anwar É—an gida kuwa nunawa yayi kaman bai san inda suka zo ba.
"Elham yanzu wani part kike ganin zamu shiga?" Dan jimm tayi kafin tace "to Nima tunanin da nake kenan"
Ruqqy ta kalli Anwar tace boy ina ɗaƙin granny?". Ba tare da tunanin komi ba ya gwada musu part ɗin grandma toh shi ance masa part ɗin granny ai haka su papan sa ke ce mata shi yasa da suka tambaya sai yayi musu pointing da hannu.
"Ashe yaro yana da wayau" jin É—adi ya hauyi ance masa mai wayau.
Koda suka isa ƙofan knocking sukai Saida sukayi wajen knocking wajen huɗu sannan a kazo aka buɗe musu, mai aikin grandma ce, gaisawa sukai daga ƙofan, tana musu iso har cikin falon, zama sukai duk a ƙasa dan hakan ba tarbiyan su bane ba,inda mai aiki ta shiga ɗakin dake a gefen falon tayi kiran granny da take zaune tana jan chasbaha. Fitowa tayi daga ɗakin tace musu gata nan zuwa, godiya sukai mata,dawo wa tayi hannun ta ɗauke da ruwa a kan tray aje musu tayi haɗi da faɗin "Bismillah" da murmushi a face ɗinsu suka amsa suna ƙara yi mata godiya ita kuma ta bar wajen.
Grandma ce ta fito fuskarta dauke da fara'a kaman ta san su tayi musu sannu da zuwa sukuma suka gaida ta cikin girmamawa,
"Kallan Anwar tayi tana Anwaru baka ganni bane?" Lafewa yayi a jikin eelham da kanta ke ƙasa bata yadda ta ɗago ba dan jin yadda zuciyar ta ke ɗan bugawa,cikin ƙasa da murya tace "boy jeka ku gaisa" maƙe kafaɗa yayi wai bai zuwa "ɗagani tunda baza ka je ba" ta ƙare maganar da son ɗaga shi daga ƙafafun ta wanda haka yasa ta ɗago da fuskanta da ɗan murmushi ganin yadda take ƙokarin ɗaga shi shikuma yana ƙara kwanto mata.
ÆŠagowar da tayi shi ya bawa grandma daman ganin fuskar ta wanda take ta son tayi haka tun sanda suka shigo amma ta dukar da kai.
A razane grandma tace "KHADIJAH KE CE?". Bata ƙara furta komi ba sai numfashin ta dake sama da ƙasa kaman zai ɗauke. Ai bata san sanda ta dangwarar da Anwar ba tayi kanta Ruqqy ma haka jijigata suke cikin fitan hayyaci daga zuwan su mata zata mutu a gaban su idan haka ta faru sun san babu mai wanke su sai mai sama.
Suna cikin wannan halin ne sai ga sallaman bappi da dawowar shi kenan shine ya nufo wajen mahaifiyar sa "subhanallahi mike faruwa haka" a rufe yayi maganan ganin halin da take ciki ne ya gane asthma ɗinta yake son tashi yasa cikin sauri ya shiga ɗakin nata wanda da kyar ya samo inhearla cikin kayan ta a gaugauce ya fito bai kula su ba ya karɓi kanta daga hannun eely yana shaka mata wajen sau uku, cikin ikon Allah ta fara sauke nunfashi a hankali haɗi da faɗin KHADIJATU! KHADIJATU shima cikin sanyi murya wanda daka ji kasan mutum yana ɗan jin jiki, "MAMA wace Khadijah kuna" bappi ya tambaya jin sai kiran sunan take babu ƙauƙautawa. Da hannu tayi masa pointing da eelham. ɗagowa yayi yana Kallan su aikuwa karab idanun shi sai a fuskar eelham wacce da ka ganta kasan tana cikin ruɗu miƙewa yayi a zabure yace "EELHAM?".nan ya fara jero sallallami yana salati
Ita kuwa ƙasa tayi da kai bata ce komi ba dan batayi tunanin ƙara haɗuwa dasu ba a rayuwa, amma sai gashi kwatsam rana tsaka ta gansu a inda batayi tunani ba, a kuma lokacin da babu Ammien ta sai ga hawaye sharrr dan duk lokacin da zata ga abinda ya shafi Ammien ta bata iya daurewa sai ta zubda kwalla. Ita kuwa Ruqqy ido ta zuba musu tana mamakin to eelham a ina tasan su da suke ta faman kiran sunan ta tunanin ta katsewa yayi jin bappi ya ƙara kiran sunan eelham.
"EELHAM?".
Bata ɗago ba ba kuma ta amsa ba kanta na ƙasa dai ƙara kiran ta yayi a karo na biyu "UMMI NA" ɗagowa tayi ga fuskanta duk hawayeurya na shaking ta amsa da "na'am bappi" jin ta amsa yasa grandma saukowa daga saman sofa tana yin sujudu shukur, kafin ta ɗago tana "Khadijah matso gare ni matso naji ɗumin ki" a lokacin tana bukatan jikin da zata kwanta tayi kuka shi yasa grandma na faɗi ba wata wata ta ƙarasa inda take tana kwantawa a jikin ta kuka na kwace mata ba komi ya saka ta kuka ba sai rashin Ammien ta inama Ammie tana nan taga wannan rana ina ma Ammie tana nan da wani irin farin ciki zatayi,ƙara ƙamƙame grandma tayi tana sakin kuka a yau kewar da take dannewa na mahaifiyarta da mahaifinta taji ya dawo mata sabo, dan a da duk lokacin da zaka ganta wajen grandma Abban ta da Ammien ta suna a wajen amma a yau babu ko ɗayan su basa nan. Grandma she can't help it but to cry, kuka sosai suke,wanda bappi yana gefe idanun shi sun kaɗa da yake namiji yake sai baiyi kukan ba amma daka ganshi kasan yana cikin buƙatan haka duba da yadda idanun shi suka kaɗe tsabar ja, daurewa yayi ya dauki wayar shi yayi kiran Ummi dan itama tazo taga ikon Allah, koda yayi kiranta jin muryan shi da tayi tasa ba lafiya ba, ansa masa tayi da gata nan.
Kukan da grandma da eelham suke shi ya saka Ruqqy kuka ganin kukan nasu na tafiya ne da kewa da marari, wanda idan kaji kukan sai zuciyar ka ya taɓu shi yasa itama bata san sanda ta fara kukan ba. Anwar kuwa shiru yayi yana kallon su ya haɗa fuskar kamar zai yi kukan shima.
Shigowa Ummi tayi jin kukan grandma ga wata a jikin ta tana kuka yasa ta rude tana tambayan bappi "mi ke faruwa mi ya samu mama dan Allah kayi min bayani" baiyi mata magana ba sai nuna mata Elham da yayi dake a jikin grandma. Maida dubanta tayi zuwa ga wajen sannan ta ƙara kallan bappi duk ta ruɗe. Ganin haka ne sai yace mata "Ummi na ce ta dawo gare mu" cikin sauri har tana tauna harshe tace "wani Ummin ka yaya?" "Kije ki ga" ba musu kuwa ta ƙarasa zuwa gare su da sai kuka suke dafa kafaɗan Elham tayi amma inaaa ba ta ji ba dan gaba ɗaya hankalin ta baya tare da mu a wannan duniyan tana duniyar tunani mai zurfi. Ɗan bubbuga kafaɗan ta tayi wanda hakan ya sa cikin nutsuwarta ta ɗago da dara daran idanun ta irin na mahaifinta. "EELHAM?". Ta ambata sunan cikin mamaki al'ajab da kuma farin ciki dan ko shekara dubu tayi baza ta manta da wannan fuskar ba bare kuma ba abinda ya canza daga fuskar nata saidai ko a ce shekarun da da yanzu ba ɗaya ba dole za'a samu ɗan banbanci. Ƙara kiran ta tayi a karo na biyu "Elham baki gane Ummin ki bane?! Zo gare ni" cikin kukan da take ta miƙe daga jikin grandma a hankali ta koma gurin Ummi. Shafa mata kai take tana lallashin ta,amma kaman ƙara ingiza ta take.
Zuwa yanzu grandma tayi shiru ta bar kukan ta dai zubawa eelham ido kamar yadda bappi yayi.
Meenal ce ta shigo dowowar ta daga gidan Anty Hanan kenan shi ne ta biyo wajen grandma, ganin su tayi zugum zugum kaman wasu masu zaman makoki, "ikon Allah mike faruwa?" Bappi ne ya amsa mata da É—an murmushi a face É—in sa yace "yar uwarki ce ta bayyana ba zato babu tsammani".
Wacce yar uwata tayi maganan tana bin mutanen falon da kallo, ganin Ruqqy ta ce "sister kece a gidan namu?" Cikin murmushin yaƙe dan halin da eelham take ciki duk ya saka ta jin wani babu daɗi dan angode yanzu da tsaida kukan. "Eh fah mun kawo Anwar ne" ita sai yanzu ta lura da zaman Anwar a gurin dan yayi shiru baza kace yana a falon ba "ya su goggo da umma?" "Suna lafiya qlau" "Elham fa ko ba tare kuke ba?" "Allah ya haɗa ta da mai surutu abinda ake gwada mata daban abin takeyi daban kai akwai wautar autanci tare da ita"Cewar Ruqqy cikin zuciya. "Gata can" tayi maganan tana nuna mata Elham dake a jikin Ummi. Itafa zata iya cewa sai yanzu ta lura da mutun jikin Ummi, zata fara zuba kenan bappi ya katse ta da "yi wa mutane shiru dan Allah" maida duban shi yayi ga Elham ya ce "Ummi na taho".ba musu kuwa ta miƙa ta isa wajen shi tana zama daga gefen shi a ƙasa.
gaisar dashi tayi ganin haka ne sai Ruqayyah ta gaida su inda suka amsa da kulawa "Khadijahtu ina mamanki da goggon naki fatan duk suna lafiya da ɗan yaƙe ta ce "goggo tana lafiya ta ce a gaida ku"
"Muna amsawa!ina da tambayoyi a baki na da yawa amma yafi dacewa naji shi daga bakin Hajiya bari muyi sallar magrib sai mu tafi can É—in" cewar grandma
GaÉ—a mata kai tayi kawai tana wasa da yan yatsun ta.
Bappi ne yariƙe hannu Anwar suka fita dan shirin salla ummi ma ta koma part ɗinta sai ya rage daga grandma, Ruqqy, Elham, meenal ke a falon su ma salla grandma tace suje suyi aikuwa dukan su suka tashi suka shiga zuwa ɗakin ta dan yin salla.......