EELHAM🌹

36&37

by @rabearhwakili


Episode 36 &  37📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai




__________a dai dai ƙofan gidan su goggo driver yayi parking,shiga sukai cikin gidan Ruqqy tana yi musu jagora,umma tana gidan shigowar ta kenan dan tazo kawo mata abinci.
   Ruqqy ce farkon shigowa bayanta Ummi, grandma, sai eelham da meenal. bappi dai na waje yana jiran ai masa iso.
   Sallamar su shi ya katse su goggo da firar da suke wanda suka juyo su ga wake anan duk da sunji muryan Ruqqy a cikin masu sallamar. Karab idon goggo ya sauka akan grandma da itama ta tsaya tana kallan aminiyar da batada kamanta.
   Cikin ruɗu Goggo tace "Hajiya KHADIJAH kece?".
    Ƙarasawa tayi gare ta tana "Hajiya HAUWA nice" 
   Hawaye na zuba ga kuma dariya s fuskar ta tace "Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar!daman rai kanga rai Hajiya Khadijah?".grandma tana zuwa suka rungume juna da yake sun waye,sosai hakan ya burge su umma da suke tsaye suna kallan su, meenal da ruqqy kuwa hadda dariya.
  Sake juna sukai suna ƙara godewa Allah da ya ƙaddara kara haɗuwar su.
Nan fa suka fara gaishe gaishe umma da kanta ta dauko ta barma ta shinfiɗa musu,suna zama,pure water ta kawo musu tana ƙara yi musu sannu da zuwa Saida waje ya natsa ne sannan goggo ke cewa "ina ɗa na yake ne ba'a zo dashi bah?". Tana nufin bappi". Tare muke dashi bai dai shigo bane yana ƙofan gida"
   a'a amma kam bai kyauta ba! Ke eelham je kice wa babanku ya shigo daga ciki" miƙewa tayi a hankali tana fita, dawowa tayi bayan ta kuma bappi, gaisar da goggo yayi da gani kasan akwai sabo a tsakanin su, 'son zaka tsaya daga waje shine baka shigo ba? Feel free nan gidan goggon ka ne kana da daman shigowa a koda da yaushe"
      "Insha Allah goggo"tashi yayi yana bara yaje masallaci dan anyi kiran sallar isha'i, adawo lafiya sukai yi masa suma suna tashi dan su gabatar da tasu. Bayan sun idar da salla  bappi ma ya dawo goggo ta ce wa umma "ta kirawo Abban su ya taho" 
    "Toh goggo" daukan waya tayi ta kira shi ba jimawa kuwa sai gashi yazo yana mai miƙa gaisuwa gare su. Goggo ta gabatar musu dashi a matsayin ɗanta. 
  Saida waje ya lafa sannan grandma ma tace "Hajiya ya bayan rabuwa? Ina son da daughter?" Tana nufin Ammie da baba. 
   Ɗan jimm goggo tace "Alhamdulillah! abubuwa da yawa sun faru ciki harda rasuwar su Maryam (Ammie) ita da yaranta biyu sai yayan ta (baba) sanadin accident".
Taƙare maganar muryan ta na shaking.
    "Innalillahi wa'inna alaihi raji'un innalillahi wa'inna alaihi raji'un innalillahi wa'inna alaihi raji'un" iya abinda ke iya fita daga bakunan su grandma kenan 
  Ummi kam kuka ta fashe dashi tuna kirki da sanin ya kamata na Ammie duk da zaman da sukai a atere ba mai tsawo bane.
   Grandma abin ya jijiga jinta da ganin ta dauke wuta tayi na wicin gadi wanda bakin ta kawai ke iya motsawa tana karanta addu'ar da tazo mata a baki.
   Bappi ma dai Saida ya share kwalla Tina baiwar Allah mai fara'a gata da addini ga kuma abokin shi baba dan abokan juna ne sosai ashe basu da rabon zasu ƙara haɗuwa sai a darul Salam? addu'a ya dinga kwarara musu dan shine soyayyar da zasu gwada musu a yanzu 
   Elham babu ranar da za'a ambaci Ammie bata zubda kwalla ba uwa uwa uwa uwafa akace duk da tasan ta rasa mahaifinta tun tana ƙarama amma hakan baya wani dukan ta dan ta taso bata san maraicin rashin uba ba Ammie goggo da baba sun dauke mata babu abinda yaro mai uba zai gwada mata suna tsaye akan haka, sun kula da ita fiye da zato bata san zafin rashi ba Saida Ammienta ta rasu, kullum da kewar mahaifiyar take kwana da begen ƙara rayuwa a tare saidai tasan haka ba mai yiwa bane share hawayen ta tayi dan ta tuna da maganar da Ammie ta gaya mata ana sauran wata ɗaya ta rasu lokacin suna school cewa tayi "Elham ina son ko bayan rasuwata banso kiyi min kuka idan kika tina da ni kiyi min addu'a wanda hakan shine babban soyayyar da zaki gwada min sannan karki manta da saka mahaifin ki a addu'a Allah yayi masa Rahama" goge hawaye take wani na koran wani tana kuma gaɗa kai at same time gani take kaman Ammie take ƙara maimaita mata haka a zahiri. 
   Ganin halin da take ciki sai bappi ya danne halin da yake ciki ya jawota gefen jikin shi yana shafa mata kai yana bata baki da tayi musu addu'a ba kuka ba,ya ƙare maganar da goge mata dukkan hawayen da suka ɓata mata fuska. Haka dai har aka samu hawayen ya tsaya Saida kowa ya natsu sannan goggo ita ma da ta gama sharan kwalla ta cigaba da faɗin "tun bayan rasuwan Usman (baban eelham) da ku ka tafi India duba lafiyar jikin ki da wata shida, komi ya fara tafiyar mana sai a hankali ga Maryam (Ammie) kullum ciwo ga komi ya tabarbare mana, ganin haka neyasa muka Saida gidan da muke ciki muka chanza gari gaba ɗaya muka koma Niger da zama gashi kullum kiran numbern ku muke bata shiga  kullum cikin kalla waya muke ko zamu ga call ɗinku saidai shiru hakan bai sa mun bar niman ku ba da cire rai a ƙara haɗuwar mu ba.
   Haka muke zaune cikin faɗi tashi inda yaya (baba)  (bata kiran sunan shi dan ɗan fari ne) yake kula da ni da kuma auta dan ya samu sana'ar Kanikanci da yake ya kware,  gefe guda kuma yana ta raba takardun makarantan shi ko za'a dace a sami aiki amma shiru. Haka dai muke ta rayuwa har auta ta gama takaba muka samu government school muka saka Elham haka muke ta rayuwa 
  Muna cikin shekara na biyar a Niger Allah ya fiddo wa auta da miji akayi auren su sanadin auren nasu ne yayan mijin auta ya buƙaci Abba da ya kawo takaddu shi cikin Sa'a yana kawowa aka bashi aiki da salary mai kyau inda a hankali a hankali Allah ya rinƙa buɗe mishi har ya siya fili  hankali dai aka samu aka ida ginin gidan muka koma baki ɗaya hadda matar shi daga baya kuma samun nasa yafi haka dan an ƙara mishi girma wajen aikin nasu an maida shi Kaduna da aiki shekaran sa ɗaya achan ya gida gidan sa mai kyau, yayi yayi mu koma amma naƙi yaso na bashi eelham nan ɗin ma naƙi nan dai suka koma da matar da yaran shi biyu,ya canzawa eelham school zuwa private Nima ya siyan min gida wanda a ciki nake zaune kafin yanzu". nan ta cigaba da basu labarin har auren da akayi wa Elham da sakinta da akayi da accident ɗinsu Ammie,  ba abinda bata gaya musu ba.
   ran bappi idan sunyi dubu sun ɓaci danne zuciyar shi yayi yana yiwa su Ammie addu'a sannan yace "amma goggo wa yayi wannan auren Kodai sunyi shi ne dan su walakanta mana yarinya? inace ai ke kika riƙe ta batayi agolanci a gidansu ba bare ace suna da ikon yin haka" ya ƙare zuciyar shi na tafarfasa "ɗiyar dan uwan shi za'ayi wa wannan tozarci"
   Itama grandma ta shaka har wuya jira take kawai a kira sunan  familyn taji ta nuna musu eelham yar gata ce gaba da baya, ba kuma sun raina kulawan da goggo ta ba ma eelham bane ba.
  Itama ɗin goggo ba wai ta riƙe su bane a rai amma har yanzu abun yana ranta aikuwa cikin ɗan jin haushi haushin su tace "familyn sananne ne suna a Niger  ALHAJI MUHAMMAD ADAMU"  ummi Saida taji ƙirjinta ya buga dammmmm.
   "Goggo Alhaji Muhammad Adamu fah wanda sukai zama a Niger?".
   "A Niger suke ban sani ba ko sun tashi dan tunda suka mana koran wulaƙanci bamu ƙara waiwayar su ba" Allah Sarki Ummi zufa sai karyo mata yake shikenan dara taci gida, 
   Tunanin ta katsewa yayi jin bappi na cewa "Goggo wa auta take aure a gidan" Saida ta taɓe baki Sannan tace "LAWAL take aure harda yaran su biyu amma mutumin nan dan rashin mutumci ko kunyan idanuna baiyi ba yace fahad da fahid ba yaran shi bane toh ai gashi yanzu sun koma ga mahaliccin mu! Hmm  ko mutuwa na kunya idon mahaifa amma haka bawan Allah nan ya danƙarawa auta har saki uku a gaban idona" 
    "Innalillahi amma wannan mutum anyi ɗan albarka! Ai kece kika kyalesu Aminiya ai da nice wankin ƙatuwar bargo zanyi musu in fito amma ko yanzu sunci bashi".
  Shi dai bappi bai kuma cewa komi ba dan bakin shi ya mutu mururus ganin dangin matan shi sukai wannan ɗanyar aika aikan.
   "Tunda Allah yasa ka sansu idan Allah ya kaimu sai mu shirya muje muji dalilin su nayin haka"
   Shiru yayi sai Ummi ne da kunyan  abinda ɗan uwanta yayi "mama ai gidan mu ne kuma yanzu sun koma Abuja idan Allah ya kai mu  sai nayi muku jagora! Elham ya sunan wanda suka aura miki?" hakan yayi daidai da shigowan AS yaji tambayan da Ummu take yiwa eelham tsamm ya tsaya ya kasa ƙarasowa Allah yasa babu wanda ya lura dashi. Cikin duƙar da kai ƙasa tace "Hydar yaron momma" su goggo kam basu ce komi ba jin wai familyn su Ummi sukai wannan aiki to ai basu da bakin magana kodan darajan Ummi ɗin.
    "Wannan karan bappi ya tambaye ta da saki na wa yayi miki?" Kanta na a ƙasa tace"biyu" 
  "idan munje zai ƙarƙare dayar da ya rage"
"Yauwa kunga zan manta amma a lokacin ce mana sukai sunji labarin ko kawunta ne zai aurar da ita ga wani kuma ba'a san daga inda ya fito ba kawai de an bashi kuɗi masu yawa ne ga yadda zai aura masa ita, su kuma shine da labarin yazo musu sukai gaggawan yanke hukunci dan kar hakan ta faru"
    Cikin ɗan dariya bappi yace wani kawunta kuma ba dai baba bah?" sai da ya gama fadin haka sannan kuma sai yayi shiru yana tinanin inda baba na nan zaice "kai dai dan ka fini son kuɗi" addu'a yayi musu a zuciya yana kauda zancen.


 UMMI dai zance ya mata tsaye a rai ta kasa shanyewa shi yasa ta tambayi goggo da "goggo kikace LAWAL shi ya auri Maryam?".
   "Sosai ma kuwa dan harda yara biyu sannan suka rabu" 
Cikin mamaki take faɗa musu ai yayanta ne.
    daman bappi ya gano hakan tun sanda yaji sunan familyn, bai kuma yi mamakin rashin sanin nata ba dan bata ƙasan suna India jinyan grandma. tunda suka je bata dawo ba dan inna tace tayi zaman ta acan har sai sun dawo gaba ɗaya shi yasa bata dawo Nigeria ba tsawon shekarun siyasa bata san amaryan yayanta ba.
Nan fa suka dinga jinjina lamarin.

   "Wai waye a ƙofa ne?" Cewar grandma dan tafi goggo tsiwa 
Murya a shaƙe yace "mutum" dan rass ya gane muryan grandmaa ce
Jin haka ne yasa tace "sai mutum ya shigo" shigowa yayi sai wani haɗe fuska yake kaman wanda akayi wa wani abun, gaisar da su yayi yana samun waje ya zauna akan ta barman da su eely suke,amma daga gefen su sai wani kallon ta yake ta ƙasan ido.
   Bayan sun ɗan sa ke daga jimami ne suka daura wani fira sai yi suke suna raha suna dariya, Ruqqy da meenal suma tasu fagen firan suka buɗe Elham da AS ba'a jin bakin su dan shiru ne.
   wayar dake a gefen ta ya hau ringing kallan inda wayar yake tayi ganin mai kiran nata ne yasa  ta saka hannu zata dauka wayar taga AS ya ɗauke yana mata mata wani kallo da ta kasa fassara ma'anar ta.
  Dauke ido tayi tana basarwa 
Shi kuwa wayar ya kashe gaba ɗayanta yana sakawa cikin aljihun sa na gaban riga yana ƙara haɗe fuska.
     Ganin sha daya tayi ne yasa bappi cewan bara su zo su wuce dare na daɗayi "da daren nan zaku tafi baku kwana ga ɗakuna nan fah?"
     "Goggo ai kwana cikin gidan nan ya ƙare insha Allah tare zamu koma can duka dan Allah goggo karkice a'a dan lokacin da nayi ginin na ware miki naki sashen na mama haka,dan Allah goggo na karkice a'a".
   Ummi ma ta dauka tare da faɗin "goggo idan kika dawo tare damu zamuji daɗi mun koma kaman da"
 Grandma da meenal sun saka baki wanda dakyar da suɗin goshi ta yadda wai dan dai grandma ta saka baki ne. Su umma dai shiru sukai basu ce komi ba dan ga wayenda suka fisu iko da goggo sun zo to su awa su hanata tafiya? Tinanin ta katsewa yayi jin bappi yana gayawa Abba su shirya dasu za'a ai sun zama family.
Abba kuwa cewa yayi a'a,Saida goggo tasa baki Sannan ya yadda.
    Kowa zuwa yayi dan ya haɗa kayanshi amma banda eely dan tasan Ruqqy zata taya ta haɗawa umma sun wuce gida da Abba dan su haɗa kaya ganin sun wuce su kadai ne ba ɗan tanyo yasa ta miƙe tana bin bayan su daman da hijab a jikinta.
   Cikin kanƙanin lokaci duk suka haɗa kayan su masu amfani amma banda Kayan aikin gida dan bappi yace basai sun dauka ba.
saka kayan a bot sukai.
Goggo grandma Abba sai meenal suka shiga motar da driver ya kawo su inda Abba umma Ruqqy Elham suka shiga motan AS saidai eely bata yadda ta zauna a gaba ba tana baya wajen su umma Abba ne ya shiga front sit nan suka bar anguwan da niyan da safe Abba zai dawo yayi musu bayani sun bar unguwar .

Koda suka dawo gida Abba aka basu nasu part ɗin daban, goggo ma nata daban,suna shiga kuwa sukai shirin yin bacci dan duk a gajiye suke su Abba suna ƙara godewa Allah da ganin karamcin su goggo......


Hajiya KHADIJAH wacce ya'yan ta ke kiranta da Hajiya mama tana da yara guda biyu a duniya YUSUF da USMAN Yusuf shine babba sun taso da son junan su wanda in ba sani kayi ba zakace twince ne dan kansu ɗaya ga kuma kamanni da suke da juna.
    mahaifin su ya rasu lokacin Usman yana da shekara 20 a duniya inda Yusuf yake da shekara 25  sunji rasuwan shi kwarai da gaske tun suna kuka har suka zo suka fawwala wa Allah komi. Lokacin da Yusuf (bappi) yaje haɗa masters ɗinshi a nan ya haɗu da lubna ƴa ta uku cikin ɗakin su tana da yayyi maza uku  gaban ta Muhammad,lawal,Ahmad mahaifin su kuma Mallam Adamu da mahaifiyan ta KHADIJAHTU, soyayya sosai suka kulla wanda har ta kaisu ga aure zuwa lokacin ya gama master ɗinsa.
Bayan auren nasu da shekara biyu Allah ya azurtasu da samun ɗiya mace wacce taci sunan goggo sabida aminta dake tsakanin iyayen su.
     sanadin ƙawancen su ya faro daga school lokacin suna jss1 ƙawance yayi ƙarfi wanda ya zama kaman yan uwan juna iyayen su suna zumunci sosai.
     koda suka rubuta jamb University ɗaya suka saka Allah da ikon shi kuwa suka samu a nan ɗin da yake ba gari sukai karatun ba sai aka kama musu hostel ɗaya, 
   ƙawance su yayi karfi har ana daukan ko yan uwan juna ne. Koda sukayi aure babu abinda ya rage wannan zumunta sai ƙaruwan da yayi dan mazajen nasu suma sun kulle har sukai gini kusa da juna, wanda hakan ya shafi yaran nasu,
    yaron goggo da yaron grandma aminan juna ne sai autan ta Maryam da Usman yaron grandma suka kulla soyayya, hakan yayi wa iyayen daɗi amma ba'ayi auren ba ance sai Maryam ta kammala karatun ta kafin nan.
    Matan Yusuf ta ƙara haihuwa bayan shekara 3 da haihuwar Hauwa wacce suke kira da Hanan, saidai wannan karan zankaɗeɗen namiji kyakyawa dashi gashi ɗan bulbul son kowa ƙin wanda bai samu ba,ranan suna yaro yaci sunan AHMAD,wato baban su Yusuf.
Saida Ahmad yayi shekara 5 sannan akayi auren Maryam da Usman a lokacin anyi auren yayanta tuni.
     Ta dade bata samu rabo ba sai da ta shekara 7 da aure sannan Allah ya kawo rabo a tare suka samu ciki ita da lubna wacce ta uku kenan,haka sukai ta rainon cikin har Allah ya kawo lokacin haihu inda lubna ta fara sauka an samu ɗiya mace, da kwana biyu Maryam ita ma ta santalo  nata yar ranan suna yarinyan lubna taci sunan Amina anayi mata laƙani da meenal ɗiyar maryam kuma aka saka mata KHADIJAH taci sunan Hajiya mama wanda ake mata laƙani da EELHAM.
   Tun daga kan haihuwar su babu wanda ya ƙara samun ciki lokacin da eelham ta cika shekara biyar mahaifinta ya rasu wanda sanadin rasuwan shi ne grandma ta kwanta ciwo haka yaja suka fitar da ita India,  sun kai shekara 1 da wani abu achan.
     Tafiyar da sukai ne da kuma rayuwa da ta sauya yasa su goggo suka bar garin daman ita mijinta ma ya riga mijin grandma rasuwa.sanadin rabuwar su kenan da sai yanzu wajen shekara 19 Allah ya ƙaddara sake haɗuwar tasu,yanzu eelham tana da shekara 24. 
  Allah yasa kun fahimci wannan taƙaitaccen tarihin nasu.

          B̶a̶c̶k̶ t̶o̶ s̶t̶o̶r̶y̶

___________washe gari suka haɗu gaba ɗayan a part ɗin goggo harda grandma sun Jeru a ƙasa suna yin break fast wanda hakan ba ƙaramin burgewa yayi ba. baka jin komi a wajen sai ƙaran plate da spoon kawai kakeji yana tashi.
   Bayan sun kammala su eelham suka kwashi kayan zuwa cikin kitchen suna wanke wa.
   Achan falo kuwa bappi ke cewa "an samu flights da zaije Abuja Ahmad ma ya yankan mana ticket,amma sai 12! zuwa 11:30 ya kamata ace muna can"
"Hakane Allah yayi albarka ai yaron nan ko bayi yiwa Allah sai ya ƙarƙare sakin da ya rage ba sani ba sabo" cewar grandma ta inda take shiga bata nan take fita ba dan ita sai ji take kaman yanzu ake mata fanfan bala'i, goggo kuwa sai haƙuri take bata dan tasan ƙawar ta akwai masifa idan aka taɓo ta.
  Baiwar Allah Ummi kuwa ƙasa tayi da kanta batace komi ba, to mi zata ce bayan yaron brother ɗinta ya ɗibo ƙasa ya watsa musu a ido ai bata da baki.

Da sallama ya shigo dauke a bakin sa, gaida su yayi yana samun waje ya zauna, yana zama kuwa sai ga Anwar sun fito daga kitchen da gudu ya ƙara so wajen papan sa,shi kuwa daukan shi yayi  yana yi masa wasa. Fitowa su eely sukai daga kitchen ɗin tana shigewa ɗakin goggo dan bata son tana haɗuwa da AS,
  Shi kuwa  da kallo ya bita har ta shige ciki, gaisar dashi su Ruqqy sukai wanda hakan yasa ya basar yana ansawa da "lafiya"
Basu zauna a falon ba suka fice zuwa waje dan su sha iska.
   Cikin yin magana ƙasa ƙasa yace "boy je kace umm ɗinka ta kawo min break fast"
     Tashi yayi cikin sauri ya shiga ɗakin goggo yana "umm papa yace ki bashi break" ɗagowa tayi ta danƙara masa ƙatuwar harara tana ɗauke kai, shi kuwa Anwar ƙara maimaita mata yayi yana yi kaman zai yi kuka. bata jure kukan Anwar dan haka tamiƙe tana daukan hijab ta saka ta riƙo hannun sa suka fita, hanyan kitchen ta nufa tana ƙara tamke fuska,
    suna shiga ta dining tagan AS zaune a kan kujeran dining, ɗauke kai tayi tana shigewa cikin kitchen tun daga shigowar ta har wucewar ta zuwa kitchen duk yana kalla.nta Saida ta shige sannan ya dauke ido yana sauke ajiyar zuciya da rintse oily eyes ɗinsa.
   Tray da ta jero masa abinci ta aje a tsakiya daukan plate da ta daura akan tray ta dauka tana zuba mishi abinci wanda tasan zai isheshi aje masa tayi a gaban shi sai a sannan ta buɗe baki a hankali tace "ina kwana" 
Saida ya mula dan kanshi ya amsa da "lafiya". Bata bi ta kanshi ba tana zuba mishi ruwan tea a cup ta bar wajen.
    Jawo abincin yayi ya fara ci.
Cin yake kaman baya so haka dai har ya gama sannan ya bar wajen.

11:30 tayi musu a airport dukan su hadda AS da Anwar, lokaci nayi kuwa suka shiga ciki inda jirgin su ya sauka a Abuja.taxi suka samu ya kaisu har gidan su inna wato gidansu ammie................✍🏻