EELHAM🌹

38&39

by @rabearhwakili

Episode 38 & 39📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai



Shiga cikin gidan sukai dan basu da shamaki da hakan, part din inna suka nufa dan nan ya kamata suje É—in da sallama a bakin su suka shiga Ummi tana yi musu jagora.
    A zaune take a falo tana kallon TV jin sallamar mutane ne yasa ta juyo da mamakin ta Ummi ta gani ga grandma sai goggo ga kuma eelham, miĆ™ewa tayi a hankali dan Ć™afafun nata sun matsa mata kwana biyu,
   "Takwara kece kokuwa?" 
Dauke kai eelham tayi sai tayi kaman bada ita inna take ba, ganin dai eelham ba tanka mata zatayi ba sai ta komo wajen goggo tana "Hajiya hauwa kune?" Cikin taɓe baki grandma tace "ita ce fa" cikin murna da jin daɗi ta hauyi musu maraba da zuwa tana kallon eelham da ta ɗauke kai kaman bata taɓa sanin ta ba sai wasan da take da Anam dan da ita a kazo.
    Mai aikin inna ce ta kawo musu abu mai sanyi tana komawa zuwa bakin aikin ta,bayan sunyi gaishe gaishe ne grandma tace "sun ne dansu gabatar da eelham matsayin jikarta wanda yaron da ta haifa da cikin ta ya haife ta wato Usman". 
    Tsumuuuu inna tayi ta kasa gasgatar da hakan sai ido da ta zuba tana kallon ta.
  ita kuwa grandma bata damu ba ta cigaba da faÉ—in abu na biyu kuma "muna buĆ™atan ganin mijin da aka aurawa eelham ba tare da sanin ta ba.
    "Haba Hajiya ai zaku bari ku hutu kafin a kai ga wannan" 
   "A'a yau muke son mu koma insha Allah fligh É—in mu na 5 ne ya kamata muyi abinda ya kawo mu mu koma inda mukafi wayau"
    "Haka ne Kuma bara nayi kiran su duk suzo" daukan waya tayi tana miĆ™awa Ruqqy dake kusa da ita tace "kira min Ahmad" karban wayar tayi  "wani suna akayi saving dashi?"
   "Ahmad aka sa" amsawa tayi da Toh tana kiran Abbu jin ya dauka ne sai ta miĆ™awa inna
   "A'a ba gaisuwar ka nake buĆ™ata ba ka kira sauran yan uwan naka su zo maza ga baĆ™i nan na jira"
    Amsawa yayi da "toh inna gamu nan zuwa" yanke wayar tayi tana aje wa gefe, can sai ga sallaman su Abbie, da mamaki suke duban goggo da eelham kafin kuma suka dauke suna gaida iyayen nasu inda sukai musabaha dasu bappi,su eelham ma suka miĆ™a musu gaisuwa inda Abba ke ta duban ta, bayan wajen ya natsa ne inna take musu bayani sun zo ganin hydar ne,haÉ—i da faÉ—a musu eelham jikar Hajiya KHADIJAH ce É—iyar mai rasuwa Usman, babu shiri suka É—ago suna duban ta, barin ma Abba da yake ji kaman Ć™asa ya buÉ—e ya shige dan abinda yayi wa su ammie yake dawo mishi gashi a gaban mahaifiyarta, "Allahu Akbar Allah mai girma  kuma bamu taÉ“a lura da hakan ba Allah yayi masa rahama!Bara na kira shi hydar É—in yazo"  daukan wayar sa yayi ya kira hydar..

    Zaune yake a falo abun duniya yayi masa yawa za Aziza zaune a kujeran dake gefen shi sai magana take yaÉ“a mishi son rai gashi bai da halin ramawa,jin wayar sa na ringing ne yasa da sauri Aziza ta dauka tana duba mai kiran nashi amma ganin baban sa ne sai ta miĆ™a mishi haÉ—i da faÉ—in "baban ka yana kiranka" miĆ™a mishi tayi tana daukan kiran haÉ—i da saka ta a speaker, kallan ta kawai yake bai ce mata komi ba, gaisar da mahaifin sa yayi sannan Abbie yake gaya masa "ga baĆ™i nan nason ganin ka kayi sauri ka Ć™araso"
  "BaĆ™i kuma Abbie? toh gani nan zuwa" nan ya aje wayar yana daukan key É—inshi na mota, har ya kai Ć™ofa ya tsinkayi muryan Aziza tana faÉ—in "sai ka jirani nima zani naje naji abin da ake kullawa dan da ganin kiran nan kasan babu alkhairi a cikin ta"
Ya kusa yayi wa aziza dukan kawo wuƙa ina dalili zata na rinƙa gaya masa magana kaman ta samu tsaran ta
  yana tsaye a nan sai gata ta fito tare da faÉ—in "muje Koh"
Wani kullutun bakin ciki ya tokare masa wuya wanda dakyar yasamu ya haÉ—e shi.
    Haka dai suka fito driver ya ja suka bar gidan zuwa family house É—inshi.
  Koda sukaje sun iske hadda su momma duk gasunan sun zo jiran nashi kawai ake.
   Aziza kuwa da tayi arba da eelham Saida taji Ć™irjinta ya buga da Ć™arfi dan Allah ya aza mata tsoron ta tun sanda ta sha maruka a wajen ta.
   Hydar kuwa qurrr ya zuba mata ido wanda baya ko É—auke wa.
   hakan ba Ć™ara min É“atawa AS rai yayi ba,dan mi zai zo ya tasa mutane da kallo daman dashi da hydar É—in basu wani shiri jinin bai gamu ba.
   Shikuma hydar da kyar ya ita dauke kanshi daga kallon eelham wacce ita bata san yanayi ba.
Gaida su yayi duka sannan ya biÉ—a waje ya zauna, Aziza ma dai anci Sa'a tayi gaisuwa 
  Grandma ce tace "Hydar kasan wannan" tayi Magana tana pointing eelham da kanta ke a Ć™asa har yanzu ba wani É—ar a tare dashi yace "MATATA CE". jin maganar yayi har cikin Ć™oĆ™on zuciyar shi datse ido yayi yana datse lips É—insa a lokaci É—aya.
   "Ban san hauka taya ta zama matarka bayan kayi mata saki biyu yanzu ma da ka ganmu munzo ne ka Ć™arĆ™are dayar da ya rage duk da hakan ba komi bane amma bama san hakan É—in ne" cewar grandma.
   Ba tsoro yace eh "MATATA CE ITA ĆŠIN" 
   "Wai kana hauka me ana maka magana kana matar ka ce! bayan sakin da kayi mata! wallahi hydar zan bata maka rai better mind" cewar Abbie cikin jin zafin abinda yayi wancan lokacin.
   "Eh Abbie ni nariga da na maida ita dakin ta tun bayan   barin su nan da kwana uku".
 "Innalillahi wa'inna alaihi raji'un hydar kasan mi kake faÉ—a kuwa waye ka maida mahauka ta?".
    Babu wanda yaga tashin Aziza sai ganin ta da sukai a gaban hydar.
   "Tabb akwai bala'i da tashin hankali a gidan nan na rantse maka idan ma ka maida auren nan kayi gaggawan kwance shi kafin asirin uban kowa ya  tonu, Ni zaku munafinta kai da uwar ka? Sannan  ku zaga ku maida aure dan buĆ™atan ku ya biya! Hhhhhh to Ć™aryane". 
   Cikin momma ya É—uri ruwa har karkarwa take dan tashin hankali.
  "Kai hydar buÉ—e baki kayi mana bayani ta yadda zamu fahimta" cewar abbu cikin sanyin halin sa.
   A masifance inna tace "wani fahimtar damu zai yi ai daman na gaya masa tunda ya sake eelham koda sun haÉ—u ban yadda yayi mata kallon arziĆ™i  balle na banza ba dan haka miĆ™o mana sauran sakin da ya rage". Tayi Maganan da tara hannun ta alamun ya bata.
    Duk zubama masa ido sukai suna kallon Ć™arfin hali irin na sa, "kasan babu tsaran ka cikin mu ko dan haka tun muna shaida juna ka cike sauran sakin da yarage idan ba haka ba uwarka zata bar gidan". Cewar Abbie 
  A zabure momma ta É—ago wanda jikin nata sai rawan mazari yake,idanun nan kuwa sunyi jawur,
   "Shikenan kuwa tunda yace bayi saki sai a sallami uwar tashi sannan mu dangana da court dan wallahi ko shure shuren mutuwa yake sai ya Ć™arĆ™are wannan sakin, ga kuma ya zo da wata magana ta banza wai ya maida ta dakin ta dan ya maida mu wayenda basu san mi suke ba". Grandma ta Ć™are maganar da danĆ™ara masa muguwar kallo. Da yake shima yasan bawai yana da gaskiya bane sai ya duĆ™ar da kansa Ć™asa bai É—ago ba.
   Ga AS É—inma haka ta kasance tunda ya sauke kai Ć™asa bai É—ago ba duk bin Ć™waĆ™wafin ka baka isa ka hango halin da yake a ciki ba.

        Chaaaa sukai wa hydar akai amma ya Ć™i,ran Abbie ba Ć™aramin É“aci yayi ba cewa yayi "Hydar ba da kai ake magana ba? Wai ma zaka sake ta kokuwa sai ranka dana uwarka gatanan ya É“aci,idan ma baka sake ta ba Ni zan sauwaĆ™e wa mahaifiyarka".
   Idan bangon dake dakin ya motsa shima hydar ya motsa. Tinanin shi katsewa yayi jin Abbie na cewa "Hajara na sake ki saki É—aya"
A bazata abin yazo mishi, yanzu dan yaĆ™i ya saki eely shine za'a sakar mishi mama cikin bainar jama'a 
    Inna kuwa cewa tayi "hakan yayi daidai kunga kuwa abin ko a jikin shi da yake ba son zaman ku tare yake bah"
   sakin da Abbie yayi  wa momma babu wanda yace dan mi sai yazama kaman an daure musu baki ne.
   Tashin sence momma ta shige shi Wanda makircin ta ya kasa hana ayi mata sakin dan basirar ta kuwa toshewa tayi in ba haka ba tasan da tayi mishi magana zai yi abinda suke buĆ™ata daman ita ma ba son haka take bah, sai faman sharan kwalla take tana jin É—acin abin fiye da yadda ake ta faÉ—a.
    "Zaka sake ta kokuws?" Abbie ya Ć™ara tambayar sa, Toh Hydar dai an zama kurma nan É—in ma shiru yayi,ganin haka ne sai Abbie ya maida duban shi ga momma a bazata sukaji ya Ć™ara faÉ—in "na sake ki saki É—aya" jin haka ne Hydar yace "Abbie saidai kuyi haĆ™uri Allah ya gani bazan iya rabuwa da ita ba" yana kaiwa nan ya miĆ™e yanufa Ć™ofa, wata muguwar ashar Aziza ta saki wanda hakan ya dakatar dashi daga fita ita momma daman tuni ta miĆ™e zuciyarta tafasa take so take ta danne zuciyar ta amma ta kasa, jin Aziza na ta faman kiran sunan ta tana kuma zaginta yasa momma Ć™arasawa ta wanke aziza da wawan mari ji kake tasssss, a zabure ta juyo zata rama marin ta amma jin anriĆ™e mata hannu hakan ya dagatar da ita, a zabure ta juyo dan taga wani isasshen ne ya dagatar da ita, ba kowa bane face eelham,cikin yi wa aziza kallan haushi ta yarfar da hannun,ta juya da niyan wuce wa ita ma taji nata kyakyawar mari har biyu wanda ba daga kowa ya fito ba sai daga momma da take jin tsanar Elham na daÉ—a huruwa a ranta dan ita ta mance ba su kadai bane a falon faÉ—i take "ke waye da zaki zo ki dauki mataki akan abinda babu ruwan ki idan ta mare Ni uwarki ta mara nace uwarki ta mara?". Datse ido eelham tayi jin taja wa mahaifiyar ta zagi tana cikin Ć™asa bata ja mata addu'a ba gashi ta jaa mata zagi, tunanin ta katsewa yayi jin murya momma na cigaba da aibanta ta "ki guji shiga lamari na ki guje wa haka" 
   Al'ajabi mamaki,É—imuwa duk ya dirar wa mutanen falon wanda suka tsaya suna kallon ta har basu san sanda Hydar ya kama hannun Elham suka bar falon ba da yake itama ba cikin hayyacin ta take ba bata san ta bi sa ba,AS É—in ma baiga fitar tasu ba dan kanshi na Ć™asa kuma ya datse ido su grandma duk kallon momma shi ya dauke musu hankali toh abinda baka yi tinani ba, ai dole idan ka gani ya É—agawa mutum hankali.
   Idan akace maka mutum makiri ne to sai abinda Allah yayi,
    Jin idanun sunyi mata yawa yasa ta gano zata yiwa kanta É“aramÉ“arama yasa ta saki ihu mai firgitarwa tana buga kanta a bango faÉ—i take "mun tsaneki mun tsaneki kuma sai mun rabaki da Hajara dan idan tana tare dake kece ke hana mu cimma manufan mu a kanta" haka dai ta cigaba da surutai ganin kaman da gaske ne yasa sukayi kanta amma banda goggo da kuma mamy dan sun san wannan wani sabon makircinta ne.
   Sosai suka dukufa suna yi mata tofi ciki kuwa har inna da grandma sai da suka dauki mintina wajen 30 ana abu É—aya daga baya kuma sai ta bingire da bacci a wajen wanda a zahiri duk ta na jin abinda yake faruwa. Aziza kuwa gaÉ—a kai tayi tasan Ć™aryace kawai zata rabu da ita ne har sai ta saka momma ta tilasta hydar ya saki wannan yarinyan ita kuma ta tona mata asiri daga baya.
   Saida sukaga ta samu bacci ne sannan grandma take cewa "Allah sarki baiwar Allah,Allah ya baki lafiya ya shiga tsakanin ki dasu". da Amin duk suka amsa kafin hankalin nasu ya dawo ga eelham É—in saidai wayam babu eelham babu hydar.
    "Ina Khadijah take kar dai nace wannan yaron ya wuce da ita". Cewar grandma, "kila tana cikin É—aki kinsan halin ta" cewar inna 
   "atoh naga babu shi babu ita ne har hankali na ya tashi" 
   Duk dariya suka sanya mata inda goggo ke Ć™ara faÉ—in "in dai itace sai ta kai har 1hour bata fito ba ko wani bugun Ć™ofa za'ai mata kuwa" 
    "Daman masu sunan mu haka suke ga haĆ™uri ga zuciya! Sai a barta kar a takura mata duk lokacin da ta fito shikenan" su meenal da su umma suka amsa mata da Toh.
    Sun É—an Ć™ara tautaunawa cikin firan ne inna ke tambayan "ina Maryam ko tayi wani aure ne?".
   Maryam ai sai dai muyi musu addu'a dan sun riga mu gidan gaskiya nan grandma ta gaya musu duk abinda goggo ta faÉ—a mata kan rasuwan su Ammie.
    Tashin hankalin da ba'a saka mata date, a firgice ya miĆ™e yana faÉ—in "ba dai matata da yarana ba" daman grandma tana cike da shi, "toh kai wace mata ka ke da ita bayan kun rabu? Ni tausayin ka nake walle! Ka saki mata har saki uku sannan ka sheganta Ć´aĆ´an da ka haifa, sabida haĆ™uri irin nata bata É—ago tace dan mi ba haka tabar gidan nan ba tare da tayi wa kowa rashin da'a ba! Abin ta kaicin da baka ni mi ya fiyarta ba, washe garin da kayi sakin nata suka kama hanyan zuwa Kaduna sukai accident anan Allah ya dauki kayan sa,shi yanason su, lawal ka koma ga Allah dan hakkin yaran nan kawai ya ishe ka! idan ka gadama ka É—auka dan kanka shawara ce".
     Duk abinda take faÉ—i ya ji su ji yayi duniya na jujjuya masa kafin su ankara sai ji sukai yayi mugun faÉ—iwa timmm da karfi, 
     Innalillahi wa'inna alaihi raji'un, nan sukayi kansa suna jijjiga shi amma ina baya ko motsi alamar ba sauran rai,ganin haka ne da sauri su Abba suka kama shi suka fito cikin mota suka saka shi wanda AS shi zai yi driving, da gudu ya figi Mota ya bar gidan daman mai gadi ya buÉ—e gate tuni.
     Driver kuma ya kwashi su goggo zuwa asibitin gaba É—ayan su hadda su meenal da Anwar mota biyu suka cike, momma da Aziza kawai aka bari a gidan.

Koda suka isa hospital cikin gaggawa aka shigar dashi zuwa emergency unit, sosai likitoci suka duƙufa a kanshi suna bashi taimakon gaggawa wanda haka ya jaaa su tsawon lokaci kafin suka shawo numfashin nasa.

Fitowa sukai babban doctor yace yana buƙatar ganin su a office Abbie,Abbu da Abba (baban Ruqqy) suka shiga cikin office ɗin.
Wajen zama ya gabatar musu dashi haɗi da faɗin "sun samu shawo matsalar numfashin nasa da ya dauke saidai a dalilin faduwar da yayi ya samu kariya a hannun sa har waje biyu an gode Allah ma a iya haka abin ya tsaya Allah ya ƙara kiyaye wa! Ga wannan sai a nimo su muna buƙatan su yanzu". Jikin su yayi sanyi ƙarau amma da yake maza ne sai suka danne sunayi wa doctor godiya suka fito.
    Bayan sun fito ne suke gayawa su inna "ba wani matsala kariya ya samu a hannu sanadin faÉ—iwan da yayi abin yazo da sauĆ™i". Fatan samun sauki sukai masa hankalin su yana É—an kwanciya jin komi da sauki 
    "AHMAD ka maida iyayen naku gida tunda jikin nasa da sauki dan doctor ma yace a koda yaushe yana iya tashi" amsawa yayi da To cikin rashin son magana, 
   Kamar yadda Abbu yace mishi kuwa ya maida su grandma gida su umma kuma suka bi driver ya maida su. Inda a ka bar Abba Abbu Abbie kawai suke jinyan nasa........


____________tunda suka shiga mota take kuka kamar ranta zai fita kukan da ta daɗe bata yi irin shi ba kuka take mai haɗe da ciwo da kuma zafi a cikinta. Halin da take ciki tana buƙatan jikin da zata kwanta tayi kuka a kuma lallashe ta. Hydar kuwa jin kukan nata yake har cikin zuciyar sa wanda yaso ya barta tayi ko zata rage abinda take ji saidai bazai iya jure wa ba.
   Parking mota yayi a gefen titi juyowa yayi yana kallon ta haÉ—i da fadin "eelham" shiru ba ta amsa ba.
    ganin haka ne sai ya riko hannun ta yana murzawa, alamar lallashi ita kuwa kaman Ć™ara zigata yake sai ma Ć™ara volume kukan da tayi, without second thought ya jawo ta zuwa jikin shi yana bubbuga bayan ta haka dai har tayi shiru ta daina kuka har bacci ya sace ta.
    Saida ya ji tayi shiru ya leĆ™a fuskar ta ganin tayi bacci ne yasa da murmushi yace "uwar daru kawai". kwantar da sit É—in da take kai yayi sannan ya gyara mata kwanciya ya ta da motar ya na barin garin.
  
___________AS kuwa yana sauke su gida bai shiga ba yaje ya kama hotel dan yana buĆ™atan kadaici a wanna lokaci. 
   Tunda ya shiga É—akin da ya kama babu abinda ke fidda shi sai salla, tun daga sallar la'asar bai koma cikin hotel É—in ba ya nufi airport dan yace bayi Ć™ara kwana cikin Abuja bai kuma gayawa su Ummi ya wuce ba dan shi ganin laifin su yake in ba so suke daman su maida ta gida shi hydar ba mi zai sa su matsa sai sunje sun karÉ“o sakin da ya rage?.
  Karfe biyar jirgin su ya tashi zuwa Kano safe (trip ALHAJI AS)


_________"wai banjin motsin yaran naki ba ko suna islamiyya ne?".cewar zeenat tana kallo mubee.taÉ“e baki tayi sannan tace "ai tun sanda ya kaisu gidan kakan nasu basu dawo ba"  
  "Tab kina da haĆ™uri mubee dan mi zaki na rinĆ™a bari ana kai miki yara family house ai wannan bayi bane dan cusa wa yara tsanar iyayen su suke ta Ć™arfi da yaji! Dan haka ki karbo Ć´aĆ´an ki tun kan dare ya miki"
    Ta buÉ—e baki zata bata ansa kenan sai ga sallamar AS wanda daka lalle sa kasan bai cikin walwala, zee kuwa harda su gyara zama ake cikin lankwashe murya ta amsa sannan ta gaisar da shi cikin yanga da ladabin munafinci, ita kuwa soloÉ“iyon bata gane ba sai ma dauke kai da tayi tana danna waya, bayan shigar shi ne mubeena ta kalli zee 
   "kinsan bamu shiri shine kike gaishe sa gashi nan shi da yasan bama shiri Kinga koda kika gaishe shi ai bai amsa ba".
   "Wallahi duk mancewa nayi amma kuwa na daina gaisar da shi kenan idan kunyi faÉ—a"
   Cikin gamsuwa tace "shikenan kuwa  hakan kuma ba Ć™aramin  yi masa zafi zai yi ba a zuciya"
   Sosaima kuwa ai wallahi tsarin nan naki yayi kuma koda da bakin wasa karki kuskura kice zaki raga masa. Sannan tafiyar nan tamu tana nan zuwa jibin fa".
   Ke kuwa mi zai kai ni! Yanzu fa da nake daure masa baki ga har wani tsoro tsoro na yake ba! Ba  komi Allah ya kai mu ai dani za'aje"
   Cikin taÉ“e baki tace "ya barki ne?"
   "Kiji zeeena dan Allah dai na maida ni baya an wuci wannan stage É—in! Dan yanzu fita ta nake duk inda nake so in Kuma dawo a duk sanda na ga dama  so am now free".
   Ta Ć™are maganar da É—aga kafaÉ—u alamar she don't care 
    Cikin farin cikin ganin tana dab da koranta daga gidan tace "yi abinki son rai wayewar kenan ai" kashewa sukai sannan zee ta mike tana sallamar ta,koda zee ta wuce bata ko kalli É—akin AS ba ta shige nata......✍🏻