40&41
Episode 40 & 41📲
***
Jumma'at Kareem to all Muslim ummah around the world may Allah accept our ibada🤲🕋📿
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
____________koda su grandma suka koma gida babu wanda yayi takan eelham dan sunyi tinanin ko bacci take shi yasa suka hana su meenal shiga harda Anwar dake kukan umm ɗinsa.
Suna nan dai zaune a falon inna dan ba batun wucewar tasu ko dan rashin lafiyar Abba. umma kuwa tana part ɗin mamy sun kulle kaman sun san juna tun da can.
Jin sallamar su mufee yasa suka maida hankali a kofan. Masha Allah su mufeeda ne su 5 ko wacce da cikin ta ɗan ɗass dashi ya fito amma ba sosai ba,
"Innalillahi goggo!?".
Da fara'a tace "a'a na'am yan matas"
Cikin farin ciki suka ƙarasa gareta kowacce tana hugging ɗinta
Wato har yanzu dai baku gama wautar taku ba Kodai sai an haifo na ciki?". Cewar goggo.
Cikin kunya duk suka rufe ido wai su a dole sunji kunya.
"Munafincin kawai idan zaku buɗe fuska ku buɗe dan kuka ba su fuska yanzu sai su hana ku sakewa da tsokala". Cewar meenal.
"Ungo naki nan Amina" cewar grandma bata sauke hannun ba inna tace "haɗa da wannan". Dariya tayi musu tana komawa wajen su mufeeda da suma suke tasu dariyar.
"Momies yan biyu daga ina halan?".
Hararanta Yusrah tayi haɗi da faɗin "ba'a sani kina cikin garin nan amma ki gagara zuwa gidan mu".
"Ooooh Allah ku tsaya kuji mana yau muka sauka daman niya ta na je muku a gobe".
"Ni dai ba wannan ba naga goggo banga eelham ba ko ta amarce ne". Cewar mufeeda.
"Ban sani ba ga yar uwata ku gaisa". Tayi maganan tana nuni da Ruqqy.
Nan suka gaisa sosai harda ɗan fira kaman sun saba da chan.
"Wato yanzu kun ƙaro walaƙanci Koh? Ina tambayar ku kun share kanku".
Wannan karan Ruqqy ce tace "sorry maman yan biyu mi kike tambaya?".
"Ya na iya tunda inasan naji!wai eelham fah banganta cikin Ku ba sannan a ina aka gano su goggo".
"Mu dasu muka zo"nan ta kwashe komi ta gaya musu alaƙarta da eelham wato cousin ne su mai ƙarfi.
Sosai suka shiga mamaki da kuma murna kafin mufeeda ta ƙara faɗin "eelham ɗin fa wai dan yanzu nasan wulaƙanci yafi na da"
"Kai sister sharri zaki yi wa eely?". Cewar Ruqqy cikin son ta jaa ta.
Sarah ce tayi saurin faɗin "ba wani sharri sai gaskiya kuna dai rufa mata baya ne".
Nan fa suka fara meenal da ruqqy kuma suna kare eelham idan ka gansu sai sun burge ka.
"Ni fa halin bakin surutun nan naku tsoro yake bani ina dalili daga zuwan ku zaku cikawa mutane Kunni sabida Allah". Cewar inna tana hararan su.
Ganin zata fara ƙorafin nata ne yasa suka tashi suka bar mata falon zuwa cikin dakunan dake part ɗinta
"Kar ku shiga nan Elham tana ciki tana bacci karkuje ku tasar da ita" jin haka ne bama su tsaya sauraran ta ba suka afka ɗakin suna kiran Elham.
Saidai mene wayam babu kowa a ɗakin gadon ma a gyare yake tsaf alamun ba'a ma kwanta a kai ba tunanin su ko tana banɗaki ne yasa suka biɗa waje suka zauna.
Shiru shiru dai haryanzu babu eelham babu labarin ta gashi basu jin ƙaran ruwa a toilet ɗin,tashi Ruqayya tayi tana Bara ta duba cikin toilet ɗin,
Amsawa mata sukai da to.
ita da meenal suka tsaya ƙofan toilet ɗin suna knocking amma shiru,tura ƙofan ruqqy tayi amma wayam babu eelham babu dalilin ta.
Fita sukai suna duba sauran ɗakunan amma babu ita a ciki cikin tashin hankali suke gayawa su goggo cewan eelham bata gidan fah.
Nan suka bazama nimanta harda su goggo,babu inda basu duba ba su mommy sun fito suma cikin masu nima nata ganin haka ne sai Ummi tayi kiran Abbie take gaya masa basu ga eelham ba.
Suma babu shiri suka dawo gidan nan suka farga babu AS Abbu yayi kiran shi dan yaji ko ina yake.
koda ya dauka kuwa ba wani lukuluku yace shi yanzu ma yana Kano komawar shi kenan.
Nan fa hankalin nasu ƙara tashi dan sun san AS bazai wuce da eelham ba dan sun san halin shi.
"Toh mi zai hana a kira hydar aji" cewar ummi dan ita tun farko jikin ta ke bata hydar shi zai wuce da eelham,, kamar yadda ta buƙata kuwa haka Abbie ya fidda waya dan kiran Hydar....
Sun daɗe da sauka a Kano dan da ya tashi babu inda ya hara sai Kano gidan wani abokin shi amma abokin nashi baya ƙasa sai ya barwa hydar key na gidan a lokacin da yazo yin wani aiki.
Gidan dai ba wani mai girma bane dan 3 bedroom plat ne madaidaici a ƙofan gidan yayi parking mota sannan ya shiga ya buɗe gate ɗin yana koma cikin mota ya shigo da shi.
Ganin tana bacci ne har yanzu kuma gashi baiso ya katse mata baccin nata sai bai tashe ta ba sai ma zaman da ya gyara yana kallon ta
Saida ta dauƙi wajen minti 20 sannan ta fara buɗe ido a hankali wanda sun ɗan kunburo amma ba da yawa ba sanadin kukan da tasha.
Kallo ɗaya tayi masa sannan ta ɗauke kai tana maida shi gefe,
"wife kin tashi?".
Ko kallo bai i'sheta ba balle ya samu amsa daga gare ta, ganin dai ba ansa masa zatayi ba sai ya yi unlock na motar,, fita yayi ta buɗe mata side ɗinta babu musu kuwa ta fito babu komi a fuskar ta alamar hakan bai dame ta wanda shikuma yaji daɗin hakan da ta nuna shi ya zata zai sha daga da ita amma sai yaga abin yazo masa da sauƙi.
Ƙofan falon ya buɗe yana kama hannun ta suka shiga ciki bakunan su dauke da sallama.
Zaune ta kai kan kujerun da suke a falon dan kukan da tayi ya haddasa mata ciwon kai.
shikuma ɗakunan duk ya bubbuɗe ya shiga kitchen yaje ya dauko abin shara ya gyara ɗakunan fess sannan ya dawo falon shima ya gyara shi sosai wajen yayi haske kaman ba namiji yayi gyaran ba.
Saida ya kammala komi sannan yace ta zaɓi ɗakin da take so ta shiga ta watsa ruwa kafin ya dawo.
Ba musu kuwa ta gaɗa mishi kai tana tashi shikuma ya fice daga gidan gaba ɗaya dan sama musu abinda zasu ci da kuma kayan sawa tunda haka suka fito babu kaya.
saida yayi nisa da anguwar sosai sannan ya samu wani restaurant shiga yayi ba jimawa sai gashi ya dawo da leda a hannu yana daf da motar shi ne yaji ringing na wayar sa fiddo da wayar yayi ganin Abbie ne sai ya dauka babu ko ɗar ba tare da ya amsa mishi gaisuwar nashi ba yace "ina eelham"
Cikin dake wa yace "muna tare da ita kuyi hakuri Abbie" ƙit ya yanke kiran yana shiga motan a gurguje ya samu mall ya shiga ya siyan musu kaya sannan ya kama hanyan gida.
Abbie kuwa sagade yayi yana bin wayar da kallo
"Lafiya kuwa halan basa tare" cewar bappi
saida ya danne zuciyar shi sannan yake musu baya ni.
"Amman yaron nan anyi isasshe, duk inda yake kuwa sai ya fito da ita komin daren daɗewa!sauƙin abin ma da yace matar shi ce ya maida ta! Toh alhamdulillah ba mu da fargaba".cewar grandma inda su goggo suka gaɗa kai alamar gamsuwa saidai ga Abbie ba haka bane dan shi idon shi idon hydar sai ya shuka masa rashin mutumci, haka dai kowa ya waste jin sallar magrib...
_____________Da dare lokacin da Anwar yake kuka wai shi umm ɗinsa yasa meenal tayi kiran AS a waya tana gaya masa ga Anwar nan sai kuka yake.
"Mi yake buƙata?".
"Wai zaije wajen umm ɗinsa"
"ki kaishi mana! ko ita mi take da bazata duba shi ba ma?"
"Bata nan ne ya hydar ya ɗauke ta sun wuce tun ɗazu"
Ji yayi kaman guduma ta kwaɗa mishi a tsakar kai ga ƙirjin shi sai suya yake Adams apple ɗinsa kuwa sai sama da ƙasa yake cikin ƙanƙanin lokaci idanun shi suka kaɗe sukai jawur kamar rushin wuta mai azabar jaaaa,
Daga ta ɓangaren meenal kuwa yanke wayar tayi jin tana ta magana amma shiru babu ansa bata kawo tunanin komi ba sai matsalar network yasa bata ƙara kira ba ma.
Shi kuwa AS ganin zai hallaka kanshi akan mai rainon ɗansa yasa ya fara karanta duk adduan da ya zo masa baki da yin istigafari
Sai da ya dan samu relief ne yake cewa to shi ina ruwan shi shi daman ba dan komi yaji haushi ba sai dan walaƙatar mishi da yaro da tayi tabi wani ƙato chan daban ita yar daɗi miji. Tsaki yaja yana miƙewa ya faɗa toilet dan ya watsa ruwa ko zai dawo normal.....
______________da dare ne suna zaune a falo yana dan janta da fira sama sama dan ta sake dashi duk da ya san batada yawan magana amma tana maida mishi kaɗan kaɗan
Abinda yasa take amsa masa ma badan komi ba sai dan ya kasance miji a gare ta, ganin kaman tana jin bacci ne yace "tashi kije ki kwanta dare na daɗayi Allah ya bamu alkhairi". Da Amin ta amsa masa tana shiga ɗakin da ta zaɓa da yake tayi wankan ta yasa ta kwanta a gado da addu'oi a bakin ta har barci ya sace ta dan ta gaji matuƙa.
_________koda labari ya kai kunnin momma da muƙarrabanta Hajiya Aziza ji sukai kaman su aza hannu akai suyi ta ihu ba ƙauƙautawa saidai ba hali daukan waya momma tayi tayi kiran sa saidai wayar a kashe. Aziza kuwa da ta ga haka sai ta nima ta ɗaura mata laifi
"Gwara ma ki bar kiran munafincin da kike dan nasan komi yayi da saka hannun ki a ciki ko an ce miki bansan halin makircin ki bane kema kin san saidai na ba wa wasu labarin ki! Kamar yadda baki zauna da kishiya ba nima hakan nake so ta kasance a gida na! Hajara! Hajara hmm basai na rantse Miki ba kinsan kar ta san kar ne! Dan haka duk inda yake kiyi maza kice masa ya dawo sannan kuma ya sake ta! Idan kuma kin ce ba haka ba, ba gidan nan kawai zasu san ke wace ba gaba ɗaya duniya sai sunji kuma bansan hakan ya kulle sati ɗaya. Tana kaiwa nan ta fice haɗi da buga kofa da ƙarfi.
Sauke ajiyar zuciya momma tayi dan ba ƙaramin tsoron Aziza take ba dan duk abinda take mata ƙarfin hali ne kawai....
_________washe gari mubeena ce ta fito cikin shirin tafiya tana jan trolley ɗinta bata ko kalli AS dake a falon zaune ba tasa kai ta wuce
Shi kuwa da yaganta sarai sai bai ce mata komi dan shi bata ita yake ba matsalar da yake gaban shi ma ta ishe shi idan ta ga dama daga nan karta dawo.ganin dai hankalin nasa ba kwanciya zai yi ba sai kawai ya tashi ya haye sama cikin kankanin lokaci ya fito cikin shirin sa, fita daga falon yayi bayan ya kashe wutan gidan.
Kulle kofan falon yayi yana nufin wajen motar shi sannan ya bar gidan bayan gate man ya buɗe masa.
__________tunda ta tashi sallar asuba bata koma bacci ba bayan ta kammala lazimin safe sai ta hau gyaran gidan wanda yayi kal kal dashi,, tana kammalawa ta shiga ɗaki tayi wanka bayan ta fito ne sai ta dauka cikin kayan da ya siya mata Jiya ta saka bata yiwa fuskar ta ko wani kwalliya ba mai kurum ta shafa.
Jin ana knocking ne yasa ta ɗauki hijab ta zira tana nufan ƙofan.
Ba tare da ta dube shi ba ta gaishe shi a daƙile inda shikuma ya amsa da kulawa da tambayar yata tashi, miƙa mata ledar hannun shi yayi haɗi da faɗin "ga taki break fast ni na fita amma bazan jima ba". "Allah ya tsare" cikin jin daɗin addu'an da tayi masa ya amsa da Amin da tambayar ko tana buƙatan a dawo mata da wani abun,,cewa tayi a'a
Toh na wuce gaɗa kai kawai tayi tana komawa cikin ɗakin.....
__________"yanzu daman fligh ɗin mu ta Abuja zai tashi? Nifa na dauka ta nan ne shi yasa na sakankance ban wani damu ba Saida hakima take gaya mun zamu wuce Abuja shine fa nayi saurin yin shiri na fito".
"Jiya da na zo na mance na gaya miki! Nima zuwan nawa kenan Allah yasa ma duk an tanadi ticket" cewar zeenat.
Shiga ciki sukai inda da shigar su babu jimawa Flight ɗinsu ya tashi zuwa Abuja koda suka sauka taxi suka samu ya kaisu hotel.
Ɗaki biyu suka kama inda zeenat da mubee sai hakima da barrah suka dauki dayan dan wannan karan Babu shamsiya tayi tafiya.....
___kiran duniya tayi wa hydar amma wayar a kashe duk bayan mintina sai tayi trying numbern shi amma still a kashe,, ita kam ina zata saka kanta ga Aziza ta saka ta a tsaka mai wuya wanda mafita ta shine ta saka hydar ya saki eely ɗin saidai ta ya? ina zata fara bayan wayar tashi a kashe.
wannan karan ma zaune take sai faman kiran shi take amma dai kamar yadda ake gaya mata yanzu ɗin ma hakan ta kasance "hydar ka buɗe wayar mana ka rufa min asiri ka buɗe wayar dan Allah". Ciro wayar tayi daga Kunni ta wullar dashi bisa kujera.
tunanin ta ina zata same shi? Idan ta ganshi kaman ta raba auren nasu ne.
Jikin Abba da sauƙi sosai dan tun jiya ya farka ba tare da wani ciwo ba sai na hannun shi da yake jin yana yi masa raɗaɗi duk da hakan Saida ya nima sallama haka kuwa suka bashi suka dawo gida inda ya bukaci a kai shi part ɗin inna yanason yaga eelham,, bayan sun shiga yake tambayan ina take sai cewa sukai ai Hydar ya dauke ta sun wuce tun jiya.
Shiru yayi bai ce komi ba yana dai jin firan da suke har su bappi suka shirya dan komawa gida tunda jikin nasa da sauƙi
𝑩𝑨𝒀𝑨𝑵 𝑾𝑨𝑻𝑨 𝑫𝑨𝒀𝑨
Tunda mubeena ta saka ƙafa ta bar gida har yanzu bata dawo ba dan sabuwar rayuwa suka buɗe ita da ƙawayen nata,, bata tunanin ta bar yara har biyu a gida, haka bata tunanin mijin ta da kuma fitar da tayi ba tare da izinin sa ba.
"Mubeena wai dan Allah karfe nawa kike son muje wajen birthday ɗin ne kin san su basa Africa time!dan Allah ki tashi ki shirya!ni ban san wani irin bacci yake damun ki haka ba tunda muka zo kike ta wannan baccin wajen wata guda kenan kamar wata mai ciki".
Dammm taji ƙirjinta ya buga kar dai ace da gaske cikin ne da ita dan sai da zeenat tayi magana sannan ta tuna rabon da taga period ɗinta wata uku kenan,, miƙewa tayi a zabure tana "na shiga uku zee kar dai ace cikin ne da ni dan sai yanzu na farga,rabona da period 3 month kenan".
Ji tayi ƙirjinta ya buga ita ma "koda cikin kike dashi ba ki isa ki ƙara haihuwa ba waɗan nan da kika samu sun isa dan babu wacce zata ƙara haihuwa a gidan AS sai ni ɗaya".
Taɓata da mubee tayi ne ya dawo da ita haiyacin ta, "lafiya kuwa zee ina ta magana kin yi shiru ba ki ce komi bah".
Cikin taɓe baki da son danne kishinta tace "to mi zance nikam mubee! Ciki dai in dai akwai shi sai kiyi haƙuri ki haife shi kaman sauran yan uwan shi mudai a daɗin mu ne".
"Kaman ya ina miki maganar banso kina mun maganar banza da na haifa! Wallahi ko Ahmad da yake uban cikin bai isa ya hana ni zubda wa ba". Tana kaiwa nan ta wuce fuuuu cikin toilet ba addu'a babu komi. Ita kuwa zee da ido ta bita tana dariyar cin nasara "wawiya kawai mara wayau ai sai kinyi danasanin sani na da kikai jaka kawai". Ta ƙarashe maganar da jan doguwar tsuka.
Tana a zaune a nan mubee ta fito wanda ko kallon inda zee take batayi ba dan ta bata haushi taya zata ce ta haifi cikin nan shi yasa ta hita batunta.
Koda ta gama shirin nata fita tayi bata cewa zee komi ba sai itace ta tashi ta bi bayan ta haɗi da wurga mata harara.
Da kanta ta tare taxi take gaya masa hospital zai kai ta.
shiga tayi itama zeeena ta shiga ya ja motar suka nufi chan ɗin,,, koda suka je fitowa tayi tana sallamar shi ta shiga cikin danƙareren hospital ɗin wanda ba dan sunan da yake jikin bangonba zakace gida ne ko wani wajen shaƙatawa, office ɗin doctor suka nufa inda ya basu izinin zama da tambayar complain ɗin su,gayamasa tayi tazo a yi mata test ne ko tana da ciki idan akwai kuma a zubda.
Shi dai ina ruwan shi ita ta kawo kanta koda aka auna aka ga akwai ciki dan wata 3,,, haka ba tsoro Allah tace a zubda shi,
Shi kuwa doctor mai shi tace a zubda to mi nashi na ja in ja shi yasa suka tafi bayan zeeena tayi sign....
Rashin son maganar AS ya ƙaru fiye da zato, ga kullum Anwar sai ya dame shi da kuka wai shi zaije umm ɗinshi dan dai ma yanxu ya rage ba kaman kwanaki ba.
Batun mubee kuwa ba'a magana dan ya tattara ya watsar ya maida hankali ga aikin shi ya hita batun kowa tun grandma tana magana har ta daina danshi ya ma fi ganin laifin ta tunda itace ta fara tado da magana shi yasa ko can gida ba kasafai suke ganin sa ba sai in yaje duba Anam.
A tsakanin ne a ka sanya bikin meenal da ruqqy nan da wata daya masu zuwa, inda Ruqayyah zata auri Umar, meenal kuwa yazeed.
Ruqqy taso ne ace eelham tana nan za'ayi auren nasu Saidai babu yadda ta iya tunda iyayen nasu sun yanke magana
Sosai ran Abbie ya ƙara zafi da abinda Hydar yayi gashi har yanzu idan aka kira wayar shi a kashe shi yasa suka watsar da batun shi suna ƙara godewa Allah da yasa eelham ɗin matar shi ce inda ace ba aure tsakanin su da hankalin su sai ya fi haka tashi
Bangaren momma da Aziza haka ta kasance kullum safe rana dare babu randa basa kiran shi amma a kashe ga gefe ɗaya aziza ta matsa mata dan cikin sati ɗayar da ta sake bata gashi sauran kwanaki biyar ya cika duk ta faɗa saboda takuran Aziza.
Yau ɗin ma zaune suke a bedroom Aziza ta miƙo wa momma wayar ta wanda da ita take tafiya,
Babu wasa a muryan nata tace "maza karɓi kiyi kiran sa kuma karki manta sauran kwanaki biyar ya rage miki na tonan asirin ki".
Momma kuwa da damuwa yayi mata yawa hannu ta saka ta anshi wayar tana danna mishi kira, cikin Sa'a taji wayar tana ɗin ɗin! ɗin ɗin! ɗin ɗin!ɗin ɗin! Da yake Aziza ta saka wayar a speaker tana jin haka ta matso tana ƙara yi mata barazana haka har ta katse ba'a ɗauka ba "ki ƙara kira wa ya". Cewar Aziza cikin zafin zuciya. Haka kuwa ta ƙara kiran......
_________eelham ce zaune a falon jikin nata sanye da hijab wanda yayi mata kyau sosai gashi harda wani glowing take na rashin fita dan tunda suka zo ko ƙofan gida ba ta taɓa fita ba kullum tana nan daga ɗaki sai falo shima sai ta lura hydar baya gidan.
tunda sanda suka zo bai wuci sau uku suka haɗu ba dan idan ya siyo abinci a ƙofa yake aje mata ita kuma ta dauka tayi ciki idan ta gama ta haɗa dattin waje ɗaya idan ta leka bata ga motar shi ba sai ta fito ta zubda dattin ta kuma gyara gidan idan ta gama ta koma ɗaki ta kulle.
Hydar kuwa koda bakin wasa bai taɓa tunkaran ɗakin ba sai ranan da ya miƙa mata abinci shima farkon zuwan su ne kuma daga kofa ya tsaya.
Wayar da ke a gefenta shi taji yana ta faman ringing wanda hakan ya bata tabbacin hydar yana gida kenan dan haka miƙewa tayi zata bar wajen shi kuma ya fito daga tasa ɗakin kenan.
kallon ta ya tsaya yana yi har wayar ya katse dan rabon da ya sanya ta a ido har ya manta ranar,,ita kuwa cikin basarwa ta gsishe shi ta bi gefen shi ta wuce tana dai dai shiga ɗaki taji ya dauka wayar yana hello dan shi bai lura da mai kiran nashi ba ɗauka kawai yayi dan hankalin shi gaba ɗaya na ga Elham wacce bata ma san yana yi ba
"Momma"
Momman ta ji ya kira ne ya katse mata hanzari daga shiga cikin ɗakin ta dakata,
Ba tare da jiran komi ba tace "a yau ba sai gobe ba inasan nagan ka dawo gida kai da wannan yarinyan, kafin na sallamaka kuma kazo da kaddar sakin ta idan kuma kaƙi sai ka zaɓa Ni Ko ita dan ina iya sallama ma duniya kai! nono na da kasha kuma ban yafe ba indai kaƙi ka yi abinda na umarce ka".
Ji yayi juwa na ɗiban sa da kyar ya samu ya haɗa kalaman bakin shi yace "momma dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan iya rabuwa da ita ba! na farkon kinsan nayi miki biyayya nayi mata biyu dan Allah momma karki ce haka wallahi ina sonta ina sonta". Yana kaiwa nan ya fashe da kukan tashin hankali kaman ba namiji bah. Ita kuwa babu tausayi tace "ka zaɓeta kenan akai na bah?". Jijjiga kai yayi alamar a'a kaman tana ganin shi kafin yace "a'a momma" "idan haka ne maza ka rubuta mata takardan ta"
"BAZAN IYA BA MOMMA".............✍🏻
Toh ya kenan hydar zai iya kuwa 🤔dan dan dan dan dammmm dammm dammm hmmmmm
Wannan page ɗin naku ne yan 𝘌𝘌𝘓𝘏𝘈𝘔 𝘍𝘈𝘕𝘚 𝘊𝘓𝘜𝘉 much kauna 🫶