42&43
Episode 42 & 43📲
***
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
_________Elham da ke tsaye daskarewa tayi dan duk da bata ji abinda momma ke faɗi ba daga yanayin amsan da hydar ke bata yasa ta gano momma ce ta bukaci ya hydar ya sauwaƙe mata,,da sauri da shiga daki tana mai cewa "mi nayi wa momma ta tsane Ni lokacin guda? mi na tsare ma ta a rayuwa har haka?".
Tana cikin wannan yanayin ne taji sallamar yaya Hydar wanda sai da taji ƙirjinta ya buga, haka ta tashi ta buɗe masa ƙofa, karo na farko da ya shigo ɗakin nata tun sanda suka zo, bayan ya shigo ne sai ya samu gefen gado ya kai zaune "ƙaraso ki zauna eelham" ba musu kuwa ta zauna daga gefen shi amma a ƙasa jiki duk a sanyaye.
Dubanta yayi da ƙirƙiran fake smile yace "eelham!"
Murya can ƙasa ta amsa da "na'am"
Jin ta amsa yasa yace "kiyi haƙuri eelham! tun farko ba wai bana sonki bane yasa na aikata miki abinda ya faru ba! a'a ina sonki har cikin zuciya ta duk kan nunfashi da nake shaƙa haɗe da soyayyar ki take tafe dan Allah eelham na san na kasance mai laifi a gareki dan Allah ba dan Ni ba ki yafe min".ya ƙare maganar da saukowa yana kaiwa durƙushe a ƙasa haɗi da haɗa hannayen sa alamar roƙo.
Ganin haka ne yasa ta miƙe da sauri tana "haba ya hydar dan Allah ka miƙe! Ni daman ban riƙe ka a rai ba ko da na second ɗaya! na yafe maka tun ba yanzu ba dan bakai min laifin komi ba! dan duk abinda ya faru haka Allah ya tsara mana! dan haka idan kayi min laifi na yafe maka duniya da lahiya Allah kuma ya yafe mana duka".
Cikin shauƙin soyayyarta ya ɗago yana duban ta ga idon shi sai shining take alamar hawaye ke cikin su kwance. murya na shaking yace "eelham duk abinda zai biyo baya daga yanzu har muje gida dan Allah kiyi haƙuri a karo na biyu! babu yadda na iya dole inyi haka Allah yayi miki albarka". Akan labba ta amsa da Amin dan jikin nata ya ƙara sanyi tashi yayi Saida ya kai ƙofa ba tare da ya ƙara duban ta ba yace "ki haɗa kayan ki zamu koma gida yana faɗin haka yasa kai ya fice zuciyar fal ƙuna.
Ƙurr ta zuba masa ido har dai ya fice daga ɗakin,,sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta miƙe a hankali ta nufi waldrop ta haɗa kayan nata wanda duk shi ya siya mata ta jera su a trolley sannan ta canza hijab daman cikin shirin ta take,,fitowa tayi janye da trolley har zuwa cikin falon inda ta iske shi zaune ya zuba tagumi da ka ganshi kasan yayi zurfi cikin ta, ita kuwa bata ce masa komi ba sai nufan ƙofan falon da tayi wanda cire key ɗin da take shi ya fargar dashi.
Tashi yayi shima ya bi bayan nata yana kulle ƙofan daman ya kashe komi na wutan gidan.
a bakin mota ya same ta, buɗe mata kofa yayi ta shiga gate yaje ya buɗe sannan ya dawo ya ja motar waje ya kuma ƙara fita Ya kulle gidan ta waje da padlock yana komawa cikin motan.
Tafiyan nasu ya kasance shiru har dai suka fita daga anguwar ba tare da ya kalle ta ba yace "muna Kano ne in tafi dake Abuja ko na maida ki gidan Ummi?". Ita kam mi zai maida ta Abuja murya can ƙasa tace "gidan ummi" gaɗa kai yayi kawai.
a hankali yake driving har suka iso anguwar su Ummi wanda suna zuwa bakin gate ya danna horn gate man ya buɗe mishi suka shige ciki yana yin parking.
Ta buɗe kofa zata fita kenan ya dakatar da ita haɗi da miƙa mata takardan da yake hannun shi haɗi da faɗin "𝘈𝘓𝘓𝘈𝘏 𝘠𝘈 𝘉𝘈𝘒𝘐 𝘔𝘐𝘑𝘐 𝘕𝘈 𝘎𝘈𝘙𝘐 𝘒𝘈𝘕𝘞𝘈𝘛𝘈! 𝘈𝘓𝘓𝘈𝘏 𝘠𝘈𝘠𝘐 𝘔𝘐𝘒𝘐 𝘈𝘓𝘉𝘈𝘙𝘒𝘈"
Hannun ta rawa yake haka ta karɓi papern idanun ta na cika da kwalla,duk da ba ta taɓa sonshi ba amma taji zafi! cikin son ta danne halin da take ciki tace "Amin ya Allah! Nagode,, Allah yasa haka yafi alkhairi" tana kaiwa nan ta balle kofan ta fita cikin nutsuwa wanda duk bin ƙwaf na mutum bai isa ya gano halin da take a ciki ba, shi kuwa ido ya zuba mata yana kallon ta har ta bace ma ganinsa sannan yaja motar yana barin gidan jiki duk a sanyaye,
Ƙofan falon goggo ta buɗe ta shiga da sallama dauke a bakin ta, saidai babu kowa a ciki dan haka sai ta wuce zuwa ɗakinta ta kwanta dan tana buƙatan tayi bacci ko zata dawo normal..........
___________ successfully aikin da akayiwa mubeena yayi kyau sai dai rashin ƙarfin jiki da bata ji da yake turawa ne sai suka bata bedrest for 2weeks dan suga yanayin jikin nata sannan sun haɗa da magunguna sosai wanda zasu taimaka mata,saidai ba'a sallame ta ba sai gobe suka ce.
Kwance take a gadon majinyata mai kyau wanda ya kasance mai faɗi,fira suke ita da ƙawayen nata kamar ba majinyaciyaba.
Cikin son suji bakin ta sukace "mubeena yaushe zamu koma Nigeria ne wai?".
"Idan zaku wuce ku wuce mana Ni daman ban riƙe kowa ba! Dan Ni da komawa sai next month insha Allah".
"A sheee! Kice likafa tacigaba! Da bakin ki kike cewa sai next month mijin fa da yaran naki?".
"Kefa Matsala ta dake kenan barra kina abu kaman baki san halin da ake ciki ba mtssssw".
"A'a yi haƙuri mana mutuniya ai mun ɗauka ko kin canza shawara ne".
"Ina nan kan baka na".
"Kina wuta babe muna binki da petro". Nan fa suka ƙara samun ƙaimi wajen zigeta Saida suka lura ta zugu iya zuguwa sannan suka rabu da ita. Cikin su babu mai zaune da a ita da zuciya ɗaya sai biyu suke zaune da ita! Sannan kowa da manufan shi a kanta. Baiwar Allah ita kuwa ɗauka take batada wasu masoya bayan su.......
_________tunda eelham ta shigo gidan har yanzu babu wanda ya san da zuwan nata dan tun sanda ta shiga ɗaki bata fito ba.
bacci tasha ma'ishi! koda ta tashi bata fita ba sai ta zauna nan tana tuna nin rayuwa, jin kiran Sallar magrib da ake ne sai ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwalla.
Tana nan zaune har akayi isha'i sannan ta gabatar da sallar tana haɗawa da shafa'i da wuturi bayan ta idar ne sai ta miƙe tana linke sallayan.
Bata cire hijab ɗin ba sai ta fita daga ɗakin dan tanason taje ta gan goggo dan tayi missing ɗinta sosai.
Babu kowa a falon sai ac da ke ta faman aiki bata tsaya nan ba sai ta shige ɗakin goggo da sallama can ciki.
Jin an bude ƙofan ne yasa goggo ɗagowa dan ta zata ko su Ruqqy ne.
Kafe ta da ido tayi babu ko ɗauke wa dan bataayi tunanin ganin nata nan kusa ba, baki na rawa goggo tace "Khadijah! saukan yaushe?". Bata ce mata komi ba sai zuwa da tayi ta lafe a jikinta.
Dago da kanta goggo tayi tana ƙara tambayar nata "Khadijahtu yaushe kika zo ba dai yanzu bah?".
Cikin rashin son maganar ta da ya ƙaru tace "tini"
"kefa Matsala ta dake kenan kaman ya tini? Kifa buɗe baki kiyi min bayani".
"Tun ɗazu"
Ido kawai ta zuba mata tana kallon ta.kafin tace "shi ya kawo ki kenan? Sannan duk tsawon wata dayan nan kuna ina?".
"Shine! Kano"
Tsoron Allah ya fara kama goggo fa, toh dole mana ana tambayar mutum yana bada answer a dunƙule saboda Allah yanzu cewan da zatayi "eh shi ya kawo ni ɗazun nan! Sannan kuma ai muna nan a Kano" shine take gaya mata "shine!Kano".
Cikin nuna kaman bata gane ba tace "waye shine Kano kuma kai amma kanajin suna kala da iri! Kenan shine Kano shi hydar ɗin yace ya kawo ki?".
Ɗagowa tayi ta dube ta da kyau dan ta gano da gaske ɗin ne bata gane ba kokuwa niman magana take! Ganin ta kasa ganowa yasa tace"muna Kano! Shi ya kawo ni"
"Shi waah?"
Wannan karan kam Saida ta shaka shiyasa kafin ta bata ansa Saida ta mulu dan kanta sannan tace "yaya"
"Oooo to to to yanzu na fahimta ina shi yayan yake?". Ta ƙare maganar da son ta kule ta. Bata ko kula da haka ba a takaice tace "Abuja"
"Allah sarki ya tafi gida kenan? Shine baki bishi ba kika wuto nan?". Itafa tambayar da goggo take yi mata ya i'sheta dan haka ta miƙa mata takardan da hydar ya bata ɗazun.cikin sauri kuwa tasa hannu ta karɓe tana buɗawa, kabbara ta saki tana miƙewa harda su taka rawa dan abinda yake a ciki ya faranta mata daman tace ita kam bazata iya haɗa zuri'a da momma ba, ba dan komi ba sai dan kiyayyar da ta gwada musu. Saidai tsoron goggo kar dai ace ciki ne da eelham dan taga yadda tayi wani kiba kiɓa ta murmure ga sai glowing take alamun hutu ya zauna.
Komawa tayi ta zauna tana ƙara godewa Allah sosai kafin ta kalli eelham fuska ba wasa duk da bai dace ace taji ɗin ba amma jin kaman ya zama dole in kuwa abinda take tunani ne sai ta saɓawa eelham "Khadijah" ta kira sunan nata babu wasa jin haka ne sai eelham ta ƙara nutsuwa ta amsa da "na'am"
Ba tare da ta jira cewar ta ba tace "akwai abinda ya taɓa shiga tsakanin ki da Hydar?".
Shiru tayi dan da farko bata gane inda goggo ta nufa ba,sai da ga baya cikin kunya ta duƙar da kai ƙasa murya can ciki wanda lokaci ɗaya kunya ya lullube tace "a'a" wato No.
Wata wawiyar ajiyar zuciya goggo ta sauke hadi da yiwa Allah godiya.
Nan fa ta hau bawa eelham baki kafin tace su tashi suje wajen grandma dan su san da dawowar ta.
Part din grandma suka nufa inda suka samu meenal da ruqqy chan ganin ta da sukai ne sai suka tafi yi mata oyoyo kaman wasu yara cikin farin ciki.
"Ni karku kayar da ni"
Iyeeeee baki gode ba ma anyi Miki oyoyo ba? Laifin mu ne yarinya! Meenal zo mu wuce". Ta ƙare da kama hannun meenal sukayi waje. daman Tun ɗazu grandma ta aike su tashi ne kawai basuyi Saida sukaga eelham. da ɗan gajeren murmushi ta bisu dashi wai su sunyi fushi.
Ƙarasawa tayi kujerar da grandma take,,duƙe ta kai tana gaishe ta kafin ta miƙe tana zama gefen ta da daura kanta a kan kafaɗunta.
Amsawa tayi da lafiya qlau da tambayarta saukan yaushe.
Nan kam goggo ce ta kwashe komi ta gaya mata,, Toh ita ma tayi murna kwarai dan ita abinda yasa taso rabuwan nasu badan komi ba sai dan wulakancin da yayi wa eelham cikin bainin jama'a. Nan fa suka shiga maida zance ita dai bata komi ba.
Anwar ne ya shigo sai cika yake yana batsewa da gani wani abun akayi masa ko kuma yan rigiman suna kai, wanda eelham bata san ya shigo ba dan ƙofa suka ba ma baya.
Jin muryan shi tayi yana cewa "Goggo har yanzu umm bata dawo ba" daga ƙofa yake yin tambayar dan haka yake idan yaji ance bata dawo ba sai ya koma part ɗin Ummi yayi ta mata rigima har sai ta kira yaya AS ya wuce dashi sannan take samun salama.
Muryan boy ɗinta take ji fa amma taƙi ta nuna tana wajen dan tanason taga reaction dinsa.
Duk abinda ake faɗi AS yana jin su a tare suka shigo ciki, amma shi yana bayan shi dan Anwar ɗin ya tare masa hanya, ba abun ya matsar dashi ya wuce ba ya tasa masa kuka, to daman mai niman kuka ne aka jefe shi da kashi awaki shi yasa bai motsa ba yana jira idan aka bashi amsa ya fita shikuma ya shigo.
"Umm ɗin ka tana can babu ranan dawowa"
Kallon ta yake idanun shi na tara kwalla yace "goggo pls call her for mee".
"Auuu ka mance batada phone ne?". Cikin yin kwal-kwal da idanu yace "u should pls take me to her place"
"I don't really know where she's Anwar" cewar goggo tana kuma faɗin "ai dole ka dawo wajen eelham ɗin tunda iyayen ka basa koya maka Hausa sai turanci" amma cikin zuci take complain, dan ɗan hausan da yake bakin shi sun fara guduwa,kun san dai yaro da daukan abu.
Ba wata wata ya wurga da gudu ya shige ɗaya daga cikin ɗakunan dake a part ɗin grandma bai kalli kowa daga cikin su ba.
Ganin haka ne eelham ta tashi cikin nutsuwarta ta shiga ɗakin da ya shiga dan ta lallashi kayanta.
AS da yake ƙofa kuwa kallo ɗaya yayi mata shima a fisge dan baiyi tunanin ita din bace ya zata ko Ruqqy ce. Dan haka ya ƙaraso ya zauna yana gaida su amma a cinkushe sai wani faman shan kanshi yake yana daudauke kai, da yake sun saba yanzu haka yake musu danshi dai har yau daura musu laifi yake.
A can dakin kuwa tana shiga ta tura ƙofan tana ƙarasawa inda yake da sai kuka yake kaman wanda aka kama a ka daka. "Boy!" Shiru yayi dan son ya tabbatar da ita dince kokuwa? Ƙara kiran shi tayi nan kam da sauri ya ɗago kai jin ta ƙara kiran shi.
Da sauri ya taso ya tafi da gudu yana hugging ɗinta da faɗin "umm I really miss U! Don't go an leave me again". Ya ƙare maganar da ƙanƙameta sosai kaman ance za'a kwace masa ita,,daukan shi tayi zuwa kafaɗan ta tana shafa masa kai haɗi da faɗin "miss u too my boy! Is ok Stop crying am now back! an I will not leave u again".Jin haka ne sai ya ɗago yana dubanta.
dan ta ƙara tabbatar masa sai ta gaɗa mishi kai alamar sure.tana manna masa kiss a forehead.
Ƙarasawa gadon tayi suka zauna tana yi masa wasa dan ya sake daga kukan da yasha.
"Idan an aike ku da kyar kuke zuwa haka wajen dawowa kuje ku zauna kaman an aiki Bawa garin su! Kudai ku canza hali wlh".
"Haba grandma Saida aka haɗa fa sannan ta bamu muka taho miki dashi idan karya ne ki kira umma ki tambaye ta".
Taɓe baki tayi tana kauda kai daga kallon su. Shikuwa AS mamaki yake wa ya shiga ɗakin da yaga Anwar ya shiga? Shi fa duk tunanin shi ko Ruqqy ne amma kuma ba ita bace tunda gata anan.
Cewa meenal yayi wai taje ta kirawo Anwar zasu wuce.
Dakin ta shiga inda ta same shi sai dariya yake ta kwasa, taɓe baki tayi tana amaryas ance na dauko Anwar zasu koma gida,ai jin haka Anwar ya kankame ta alamun dai babu inda zai je, jayo shi tayi amma ya saka ƙarfi ya cije shi bayi zuwa,,haka dai ta rabu dashi tana talle mishi ƙeya ta fice.
"Yaya wai yace bazai zo ba ka tafi" ba tare da ya ɗago ba yace "ki dauko shi ko yafi karfin ki ne?".
Ita kam ina ita ina Anwar ga ɗan jawo shin nan da tayi har hannayen ta sun riƙe amma sai ta amsa masa da "toh yaya".
Tana zuwa kuwa ta samu waje ta zauna har Anwar ya sake ganin dai ba tafiya zatayi dashi ba, aikuwa kafin eelham ta ankara taga meenal ta ɗauki Anwar ta gudu daga dakin zuwa falo shi kuwa sai ihu yake bazawa ta sauke shi,shi bazai je ba,amma bata dubi wannan ba ta dire shi gaban AS tana "yaya gashi nan"sai nishi take kaman wacce ta ɗauki buhun doya.
Hannun shi ya kama suna barin falon ba tare da ya sallami su goggo ba dan su masu laifi ne wajen shi da kuma Anwar tunda kullum sai yayi kuka kan zaije wajen umm ɗinsa.
Koda ya isa wajen mota front sit ya buɗe ya saka Anwar yana danna lock dan yasan Anwar da wayau yana iya buɗewa ya gudu, zagawa yayi shima ya shiga mazaunin driver yana barin gidan zuciya duk a dagule.
wajen masu saida ice cream ya tsaya ya siyar wa Anwar,tun a mota ya buɗe mishi ɗaya aikuwa nan su mallam Anwaru akayi shiru kaman ruwa ya cinye shi.
Elham kuwa ranta idan yayi dubu ya ɓaci ai wannan wulaƙanci ne dan ta ɗauki yaron shi shine zai gwada mata iyaka da haka? Toh ita kuwa ta sha alwashin sai ta gwada mishi shima tafi shi iko da Anwar. "(Ni kuwa nace hoooow)?".
Saida ta gama kunbure kumburen ta sannan ta fito falo dan ta danci wani abun kafin ta kwanta.
Koda ta fito tayi niyan ta ɗauke kai kaman bata gamsu ba amma ganin bappi da Abba ne yasa ta ƙarasa nan ɗin ta gaishe su inda suka amsa da kulawa dayi mata fatan samun babban rabo kuma mafi alkhairi a gare ta. kanta na ƙasa ta amsa da "Amin Nagode"
Sannan ta miƙe ta nufi dining.
Bappi ke gayawa su goggo "tafiya ta kamamu!zamu kai 3 month ga shi da Abba da Ahmad zamu! daman maganar auren yaran nan nace za'a dakata dashi har in Allah yayi mana dawowa ne Koh?".
"Daman ai Saida nace dan mi za'a sanya biki wata daya sai kace kun gaji dasu? Idan kun gaji da ganin nasu ne ni ban gaji ba ahem,sannan ko kun dawo sai an kara wata ɗaya a sama wannan kenan! Sai ku sanar da magabatan su mazajen nasu,ko ya kika ce Hajiya hauwa?".
"Atoh nima abinda nagani kenan!ai maganar taki tayi"
Nan su bappi suka tsaida magana zasu tuntuɓi magabatan nasu.
Elham da take dining kuwa tsaff taji komi, kenan an saka ranar auren su Ruqqy shiyasa taga kansu sai rawa yake ashe.
__________ba hydar ne ya isa gida ba sai wajajen karfe 9 inda yana zuwa ya tafi part din momma.
Zaune suke ita da Aziza dan sun san yana kan hanya dan momma tayi kiran nasa kuma ita ta faɗa masa da idan ya shigo ya wuto part ɗinta direct kar ya tsaya ko ina.
Da sallama ya shiga cikin falon yana gaida momma murya a cinkushe ita kuwa bata lura da haka ba sai ta washe baki tana amsawa harda shi masa albarka take.bata ja maganar da tsawo ba tace "ga matar ka nan ka ɗauke ta ku tafi, kamar yadda na saba gaya maka yauma zan ƙara maimaitawa da duk abinda Aziza zatayi maka ka zama mai haƙuri da kauda kai, kar kuma kace zaka dauki mataki a hannun ka idan hakan ta kasance ban yafe maka ba, duk abinda tayi maka ka faɗa min, Ni nasan abinda zanyi!magana ta karshe kar in ƙara ganin ƙafanka a gidan nan har sai in ni na buƙaci ganin ka".
Da sauri ya dago yana duban ta jin maganar ta na karshe dan shi ya bashi mamaki taya zata ce haka bayan tasan Abbie yana fushi dashi?.
"Eh fah kalle ni da kyau haka fa haka nace! idan kuma kace ba haka ba sai muji" saukar da kai yayi haɗi da faɗin "kiyi haƙuri momma za'a kiyaye"
"Amin! My daughter dauko mayafin ki ku tafi koda kallon banza yayi miki kiyi gaggawar sanar min Allah dai yayi Miki albarka"
Tashi tayi ta shiga dakin momma ta dauki vail ɗinta ta fito suka wuce wanda Saida momma ta leƙa ganin babu kowa sai tace su fito da sauri su bar gidan, haka kuwa suka isa mota a gaugauce wanda hakan ba'a son ran hydar ba danshi yaso yaga Abbie duk mi za'ayi masa ayi a yau din komi ya wuce amma momma ta ɓata mishi shiri. Haka dai ya ja motar suka bar gidan wanda Aziza sai iyayi take zuba masa wai ita nan shagwaɓa......
______ ko kafin su koma gida Anwar yayi shiru yana ta bama AS labarin umm dinsa amma bai maida kai ba dan shi ya dauka duk cikin kewan nata da yayi ne.
koda suka koma gida wanka yayi masa sannan ya kwantar dashi shikuma ya hau haɗa kayan shi dan tafiyar nasu gobe ne. Kayan Anwar ma ya haɗa masa dan gidan Ummi zai koma kafin su dawo idan kuma mamanshi taga dama ta dawo to.