EELHAM🌹

44&45

by @rabearhwakili


Episode 44 & 45📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai





__________washegari ya kama ranan tafiyar su bappi zuwa China dan yin wani aiki.
   Cikin sauri yaƙarasa yiwa Anwar shiri dan ya kusa makara shi yasa yake komi a gaugauce saidai cikin nutsuwar shi yake. Bayan ya gama shirya shi shima ya shiga wanka koda ya fito bai tsaya wani bata lokaci ba,bayan ya tsane jikin shi ya shafa lotion ɗinshi masu sanyin kamshi sannan ya nufi waldrop yana budewa ya shige ciki alamun akwai inda zai saka kaya a ciki.
    Tubarakallahu Masha Allah. Sosai AS yayi kyau cikin shigar sa na suit kirar Tom Ford wacce ta kasance navy blue yar cikin ta kasance fari,takalman ƙafafun shi sun kasance Kirar Jimmy choo wacce take fara convas,ga sumam kanshi da yaji gyara duk da ya kasance mai tara suma a akai amma bai askin banza saidai angyara shi sosai,haka nan sajen sa da ya zagaye kyakyawar fuskar itama anyi mata style ta yadda ya bada shape mai kyau batayi irin buzu buzu ɗin nan ba, a hankali ya tako wajen mirror inda ya ƙara bin jikin shi da designers perfume kirar Calvin klein da kuma Dolce and Gabbana wanda suka haɗu suka bada kamshi mai sanyi da daɗi shaka nan da nan ɗakin ya cike da kamshi. Maida duban shi ga watch ɗin dake hannun sa yayi wacce ta kasance Kiran Company Vacheron constantin. 
  Ganin bayi da isasshen time ne yasa ya dauki wayar sa kirar Samsung yana sakawa cikin pocket ɗinsa,kallan Anwar yayi haɗi da faɗin "boy muje kar nayi late" cikin zumuɗi Anwar yace "papa wajen umm zaka kai ni?" Batare da tinanin komi ba ya gaɗa mishi kai nan Anwar ya hau murna yana jin dadi har suka isa wajen motar da driver ya ƙaraso dashi.
    saida ya fara shigar da Anwar sannan shima ya shiga inda Anwar ke ta yi mishi surutu yana bashi labarin umm ɗinsa wanda a yau kuma AS ya dauka mafarki Anwar ɗin yayi.
   Da yake anguwar su dana Ummi babu wani nisa nan da nan suka iso inda gate man ya buɗe musu suka shiga ciki, ko kafin driver ya gama parking Anwar kokarin buɗe kofa yake danshi burin shi kawai yasa EElham a ido, riƙe shi AS yayi Saida driver yayi parking sannan ya sake shi haɗi da miƙa mishi danƙararriyar iphone 13 wanda cikin wayoyin da yake amfani da shi ne ya miƙa masa haɗi da faɗin "zan dinga kiran ka, ko idan kayi missing dina just give me a call kaji?" Shidai Anwar kai kawai ya gaɗa  masa dan gaba ɗaya hankalin sa na cikin gidan. lura da haka ne sai ya sake mishi hannu yana buɗe mishi ƙofa da kanshi,,aiko ba wata wata ya kwasa a guje,,fitowa shima AS yayi yana nufan sashen grandma.
   Tura ƙofan yayi ya shiga bakin shi dauke da sallama,amsawa sukai,,Saida ya fara gaisar da iyayen shi daman duk suna a nan ɗin isowa nashi kawai suke jira su tafi,,ai kafin ya gaisar da grandma ta dakatar dashi da faɗin "bamu bukata ka riƙe gaisuwar ka! Koke kina so Hajiya hauwa?".
   "Wane ni Hajiya ai inada zuciya!mu ya maida marenan wayan sa shi yasa! dan haka riƙe kayan ka bamu roƙa ba". Dauke kanshi daga kansu yayi yana amsa gaisuwar da su meenal keyi masa saidai babu eelham a cikinsu dan tana ɗaki a chan Anwar ya sameta,,
   Ganin zuwan nasa ne yasaka su bappi miƙewa dayi da yiwa su goggo sallama suna fita inda suka bisu da fatan nasara da kuma sauka lafiya.
   AS miƙewa yayi shima yana sallaman su ummi amma bai ce wa su goggo komi ba yasa kai ya fice daga falon,,inda su meenal suka taso dan suyi musu rakiya zuwa airport.

Elham kuwa baacci take sosai ganin hakan da Anwar yayi ne sai ya rabu da ita shima ya kwanta nan gefenta ya wani kankameta ba jimawa bacci ya ɗauke shi inda suke bacci peaceful. 
Motsa kyakyawan idanunta ta farayi wanda suke cike da eyelashes masu tsawo kaman tayi fix ɗinsu,,buɗewa tayi slowly har ta gama buɗewa idanunta basu sauka a ko ina ba sai a kan Anwar da ya ƙanƙameta.zuba masa idanu tayi tana kallansa wanda hakan ya dauke ta tsawon lokaci.
  Cikin nutsuwa ta janye shi daga jikinta dan kar ya tashi.
Mikewa tayi ta nufi hanyar toilet dan ta wanko fuska,
   "Umm"
Ji tayi muryan Anwar yana kiranta wanda hakan ya dakatar da ita daga shiga toilet ɗin juyowa tayi tana amsawa da "my boy ka tashi?"
  "Eh umm"
"Masha Allah wa ya taso kazo a wanke fuska koh" gaɗa mata kai yayi yana saukowa daga kan bed ɗin,
Kama hannun shi tayi suka shiga cikin toilet inda ta wanke mishi fuska itama ta wanke nata sannan ta kamo hannun shi suka fito, "umm yunwa" 
"Ok muje muyi break"
   Kama hannun shi tayi sannan suka fito zuwa falon inda suka iske su grandma a falo suna fira su Ruqqy suna wajen Ummi, gaishe su tayi tana kamo hannun Anwar suka ƙarasa dining jin muryan goggo tayi tana cewa "mutuniyar ki fa ni sai naga kaman haushin mu take ji mun raba mata aure! Bakiga ta wani canza hali ba?"
    "Saidai tayi ta gama mu dai gata mukayi mata da muka rabata da wannan yaron! Ni fa inda ace a gaban idona ya dauke ta da sai na sharara mishi mari dan yasan jikarmu ba yar tsanar wasan yara bace"  cikin ƙara yin ƙasa da murya wai dan kar eelham taji tace "da yake ita ma ɗin ba zuciya sai ta saka ƙafa ta bishi kamar wata bindi ai ni a lokacin laifin ta na gani bana hydar ba"
   "Affff nima da ta dawo nake tambayan ta inda ace ta bani amsan da ba shikenan ba mai ƙwatan ta hannu na sai ya shirya! Toh sai Allah ya taimake ta"
  "Su suka sani ai Ni yanzu tsoro ma suke bani ita da Ahmad, haka kurum su tsira guntun fushi da gaba da mutane! Nifa na lura gaishe mu da Ahmad yake dan ya zamar mishi kaman dole ne! Atoh kaman dole mana tunda ana gaisheka murya can ƙasa ga kuma hadda kin kallan mu da yake tun sanda mukaje Abuja muka dawo,wanda Ni na rasa dalilin canzawan shi lokaci guda kuma baiyi da iyayen sa sai mu".
   "Nima dai abin nan yana damuna kwarai da fa in zai gaida ni har kasa yake kaiwa amma kamar kar muje Abuja shikenan komi ya ɓaci! Ita kuma namecyn ki tunda miji ya sallameta take wani guntun fushi da mutane sai kace mu mukace ya rabu da ita! Yo to idan munce ai gata mukai mata! Da yake basu san ai musu gwaninta ba".
   "Hmm karma mu damu kanmu mu dauko ido my zuba musu daman halin su ɗaya"
   "Shikenan kuwa Hajiya Khadijah! Wanda yayi damu muyi dashi wanda yace ba haka ba muma ba hakan ba".
  Ƙasa ƙasa suke firan wai dan kar eelham taji,, abinda basu sani ba eelham taji komi da yake Allah ya bata ƙarfin ji, mamaki take ita yaushe tayi baƙin hali dan miji ya rabu da ita,in da ace sonshi take shine abin zai zafeta,amma su ta faɗa daga nan harrr..... Tunanin ta katsewa yayi jin Anwar yana mata magana, nan ta watsar da batun su sannan ta fara feeding Anwar Saida ya koshi sannan ta haɗa nata Golden morn da yaji madara ga ta zanbaɗa mishi sugar har na wuce misali dan kam ita sha zumamu ce wurin shan zaƙi shi yasa idan wata yazo ƙarshe ta ta fama shan wahala kenan,shiyasa goggo take hanata sha in har ta ganta.
  Sai da ta gama tass sannan ta dauki Anwar suka fito daga part din grandma zuwa na ummi, 
   Da sallama ta shiga ciki ga Anwar riƙe a hannun ta, Ummi dake a falo ta amsa da fara'an ta tace "daughter sai yanzu kike tashi baccin kenan?" murmushi tayi ba dai tace komi ba, ta dai gaisar da ita cikin girmamawa,in da ta amsa da "lfy qlau" haɗi da yafito Anwar tana cewa "Anwar yau ba magana ko? tunda ga umm ɗin ka ta dawo bah?" Daga wajen da suke yace "gud afternoon Ummi" taɓe baki tayi tace "su turawa sai Lagos! Riƙe gaisuwar ka tunda sai da na roƙa" kallan eelham yayi inda tayi masa alama da yaje ya bata haƙuri, ba musu kuwa ya tashi ya nufi wajen ta yace "Ummi I'm sorry" 
"to shikenan! Fatan ka tashi lafiya?"
Amsawa yayi da  "Alhamdulillah" yana komawa wajen eelham danshi gani yake kaman wucewa zata ƙara yi shi yasa bai yadda yayi nisa da ita, eelham da take ƙasa tana wasa da Anwar wanda duk maganan da suke da turanci suke yinshi,ganin haka ne sai Ummi tace "daughter haka zata yiwu kuwa?baku gudun yaron nan ya taso bai iya hausa ba?" Ita dai eelham kanta na ƙasa tace "Ummi kiyi hakuri za'a gyara insha Allah" 
     "Allah yasa amma ku rage yi masa akai akai idan ba haka ba ɗan hausan da yake bakin shi sai su gudu, idan ya girma kuma yaga yan uwan shi suna yi zai na rinƙa jin kanshi wani iri tunda bai iya ba"
   "Insha Allah za'a kiyaye! Ummi anam fa?tunda na dawo ban ganta ba" 
   "Tana bacci tayi fushi dake ai tunda kika dawo baki biɗe ta ba sai yanzu".
   "UMMI ina ta tambayan ta wajen su Ruqayyah"
   "ta huce Toh! Tashi ki dubo ta ko ta tashi"
   Tashi tayi ta nufi ɗakin da Ummi ta nuna mata Anam tana ciki.
  Ai kuwa bacci take sha abinta,ganin haka ne sai bata tashe ta ba,ta je wajen waldrop ta kwaso kayan Anam duka babu abinda ta bari ta jera su cikin trolley, 
   Haka kuwa ta dauƙi  Anam a hankali dan kar ta tashi tana cewa "boy muje" fita sukai tana janye da trolley na kayan Anam ga Anam ɗin a kafaɗan ta, sake da baki Ummi ta bita da kallo tana mamakin soyayyar da eelham ke gwadawa yaran, "Ummi sai anjima"
   "Oh da dai yafi kar in ƙara ganin ƙafafun yaran naku tunda daga ke har Ahmad baku da kawaici akan yaran nan, to ku sauka da nauyi" tayi maganan cikin wasa dan taji daɗi yadda eelham ke son yan jikokin nata, cikin dariya tace "ummi zan dawo da ita anjima ta gaishe ki".
   "A'a ban roƙa ba tunda ku rowan yara ke gare ku! Shi yasa ga yaran nan duk ƙiwa yayi musu katutu"
    Haƙuri ta bawa ummi sannan ta jawo hannun Anwar sukai waje tana murmushi. Saida taje part din goggo ta aje wa Anam kayan ta sannan ta goyata suka fito da niyan zuwa gaida umma........

__________ciwon ciki mai tsanani ya kamata cikin dare wanda haka ya kaita har fita daga hayyacin ta, ganin haka da zee tayi ne yasa ta ɗauki telephone ta danna numbern ɗakin doctor nan danan aka dauka ta gaya musu numbern ɗakin, ba jimawa kuwa sai ga doctor har uku sun shigo inda suka bauƙaci  zee tayi waje,bayan fitar nata ne suka rufu akanta dan ganin sun ceto rayuwar ta wanda hakan ya ja su tsawon lokaci kafin su samu numfashin nata ya dai-daita. 
   Fita sukai babban doctor ya buƙaci zee ta biyosa zuwa office, 
  Haka kuwa ta bisa zuwa chan bayan ta shiga ya gabatar mata da kujera ta zauna yake gaya mata "zasu riƙe ta har zuwa wani lokaci dan su ga yanayin jikin nata! aikin da sukai mata yaso ya bata matsala badan Allah ya taimaka ba".cikin gamsuwa ta gaɗa mishi kai da yi masa godiya sannan ta fito bayan ya sallame ta, koda ta fito hannu ta ɗaga sama tana godewa Allah dan bazata so mubee ta mutu bata ga abinda zata yi mata ba. Da wannan zancen zucin da take ta fita daga hospital ɗin dan tana son ta koma gida,ko tsoron bin daren barayi
  
   Allauran da sukai mata na bacci ba sune suka sake ta ba sai da rana wanda lokaci ɗaya ta zabge kaman wacce tayi ciwo na kwana ki.
Tashi tayi daga kwanciyar tana zama sai faman yamutsa fuska take alamun akwai ɗan sauran ciwo a tare da ita ko kwanciyar da tayi shi ya gundire ta.
Ganin ta miƙe ne yasa zee ƙarasowa tana yi mata sannu, taimaka mata tayi ta sauko daga bed ɗin, cikin dafa bango kaman ba mubee ba ta shiga toilet,wanda zee ta bita da dariyar mugunta.
   Daure da towel ta fito alamun Saida tayi wanka sannan, tashi zee tayi ta riƙo mata hannu zuwa bed tana yi mata sannu kaman abun ya dame ta "zee dan Allah miƙo min kaya na saka sanyi nake ji". Ta ƙare maganar da ƙanƙame jiki, kamar gaske harda hanzarinta ta miƙo mata kayan sai faman jera mata sannu take "mubee bara na haɗa miki tea mai zafi hakan zai taimaka ki daina jin sanyin daman doctor yace idan kin tashi a baki tea mai zafi dan zaki tashi kina jin sanyi"
  "Ok amma karkiyi da yawa karkuma ki saka sugar" 
    "Eh daman Shima yace kar a saka sugar! Allah dai ya baki lafiya"
Akan labba ta amsa da Amin, Bayan zeenat ta gama haɗa mata tea ɗin ne sai  ta miƙa mata, karɓa tayi haɗi da faɗin tnx.
A hankali take sipping kafin ta maida duban ta ga zee tace "mi doctor sukace ne" 
   "A'a babu komi sun dai ce aikin da akayi miki yaso ya baki matsala amma dai Allah ya kiyaye"
   Jin haka sai ta sauke ajiyar zuciya da ba wani ƙatuwar matsala bace dan ta firgita da wannan ciwon cikin da ya turniƙe ta jiya "insha Allah inasan da sun sallame ni na wuce Nigeria hutun ya ƙare hakanan ( su mubee anji haza).
   Kadan dariya ya rage ya kwace wa zee dan yadda mubee tayi maganan zaka gane duk a firgice take dan a jiyan  ita ɗaya tasan abinda taji.
Cikin danne dariyar ta tace "haba mubee da sauran lokaci fa kamata yayi ai ace kin ɗan ƙara kwana ki akan wanda kikace! Zuwa lokacin kin maida jikinki kokuwa?".
   ita kanta tasan ta rame sosai ciwon dare ɗaya, without second thought ta  ɗauki shawaran zee, amma tace ending of month zata koma kaman yadda tace babu canji.
  Suna a zaune anan su barra suka iso duba jikin nata inda suka haɗu suna ta fira zaka ce basu da wani ƙyashin juna......


________taya za'ayi daga dawowar ka ka nima ka takura ni! Allah yana gani bazam iya shiga kitchen by this time ba! ka kuwa duba clock kaga ko karfe nawa?".
   Daman ai ta saba hakan bai bashi mamaki ba sai saukar da muryan da yayi alamam lallashi da roƙo yace "dan Allah Aziza ki taimaka ki dafa min koda noodle ne wlh am so hungry! Ga kuma zazzaɓi a jiki na, badan haka ba kinsan bazan saka ki ba Koh?".
     "Haram shan giya gidan liman!na mi na mele,kaga ba baiwar ka nake ba dan haka banga zan iya ba, am not ur maid ka gane? Amma idan ka tashi dafawa kayi da Ni dan nima ina jin yunwa". ta ƙare maganar babu ko kunya.
    "Bani key na mota zan fita na siya"
Shima bazan bayar ba na ƙarfin mutanen da ne ahem". Tana ma tashi ta bar misji wajen dan ba dayan da taga zata iya yi.
   Da kallo ya bita har ta ɓacewa ganin sa kafin ya rufe ido yana jin zuciyar shi na tafarfasa dan baƙin ciki, shifa ba dan momma ba da ya daɗe da rabuwa da wannan azizan.
    Ganin dai yunwa zai masa lahani yasa ya mike a daddafe ya shiga kitchen ya daura noodle haɗe da aziza dan bai isa ya dafa bakin shi kawai ba sai ranshi ya fi haka ɓaci.
   cikin kankanin lokaci ya gama dafawa inda ya saka nashi a plate sauran ya barshi cikin tukunyan dan ya ce bazai kirata ba indai ta fito ta gani da idanun ta, sai dai yana fitowa yayi kicibis da ita zata shiga kitchen ɗin dan kamshi ya kai mata saƙo,shi ya kauce mata ita kuma ta shiga sannan ya samu ya fito.
   Koda ya gama magani yasha sannan yaje ya kwanta dan yana buƙatan hutu stress yayi masa yawa.....


__________ AS sun sauka a ƙasan china dan har sun huta a hotel ɗin da suka kama amma banda AS da ya tafi wani sabgan,bashi ne ya dawo ba sai da dare Saida yayi wanka yayi shafa'i da wuturi ya kwanta, jawo wayar shi yayi yana dialing  dayar numbern shi. Da ya bama Anwar da zasu wuto.

Zaune take ita ɗaya a ɗaki tana karanta Wani littafi sosai ta maida hankalinta a kai gaba ɗaya dan labarin yana yi mata daɗi fiye da zato,wayar dake a ƙarkashin pillow ya fara vibrating wanda hakan ya dakatar da ita, dube dube ta fara dan taga ko wayar wake ringing,jin kaman ta wajen pillow ne yasa ta ɗaga, aikuwa wayace iphone 13 wanda AS ya ba ma Anwar, daukar wayar tayi tana jujjuya shi a hannu tunani take Kodai anyi baƙi ne suka shigo nan har suka mance da wayar su? Kodai ma suke kiran, tunanin haka ne yasa ba wani tinani tayi picking call ɗin cikin sanyin murya tace "Assalamu alaikum!". Daga can bangaren AS kuwa lumshe oily eyes ɗinsa yayi kafin ya kuma buɗe su.
   jin ba'a amsa bane yasa ta ƙara yin wata sallamar,
AS kuwa da bai gane ko muryan wace ba amma muryan yayi masa daɗi kauda tunani haka yayi murya a dake yace "Anwar!" Ji tayi gaban ta ya faɗi ai ba shiri ta datse call ɗinsa tana ma kashe wayar gaba ɗaya da tunani barkatai watsar da haka tayi tana ci gaba da yin karatun ta.
  Ɓangaren AS kuwa tunani yake ko ina Anwar kuma yaje ya jefar da wayar ko dai baƙi sukai ne shine suka ɗauka tunanin haka ne yasa bai ƙara kiran wayar ba koda aka yanke............✍️