46&47
Episode 46 & 47📲
***
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
Sanye take cikin dogon hijab har ƙasa,part ɗin umma ta shiga inda ta samu su Ruqqy suma sun gama shirin fitowa ne kawai ba suyi ba saidai su cikin vail suke wanda duk ya karɓe su sunyi kyau duka,kallon su tayi tana ɗauke kai sannan a hankali tace " za ku zo mu wuce ko sai na bar mutum"
Karab ruqqy tace " in da ace bamu san hanya bane shine abin zai dame mu! Idan kin tashi kifi jirgin sama sauri"
Taɓe baki tayi ta maida duban ta ga meenal tace "zaki tsaya biye mata ko zaki taso mu wuce"
"Toh Ummi duk yadda kika ce haka za'ayi" ai ba shiri ta zuba mata harara tana shiga ɗakin umma wanda sai da tayi knocking aka bata izinin shiga, gaisar da umma tayi cikin girmamawa a gareta,ita kuma ta amsa mata da kulawa da sanya mata albarka,da Amin ta amsa tana tasowa tazo wajen umma tana kwantawa a kan kafaɗun ta tace "umma kicewa yaran nan su zo mu wuce rana na ƙarayi"
"Kar ma ki tsaya a ce mana yara kira mu da jikokin ki kawai" cewar meenal da Allah ya zuba mata son girma,ko ɗagowa ba tayi ba bare su saka rai zata amsa musu,miƙewa tayi tana "umma na wuce"
"A dawo lafiya Allah ya tsare" akan labba ta amsa da Amin tana fita daga ɗakin ganin haka ne yasa suma suka mara mata baya suna sallamar umma
koda suka fita a ƙofan falo suka same ta ganin fitowar su ne yasa ta ƙarasa wajen parking lot,buɗe mazaunin driver tayi ta zauna Ruqqy ta zauna a ɗayar side ita kuma meenal ta zauna back sit haka ta ja motar cikin mutsuwa suka bar gidan.
A dai-dai gate ɗin gidan Anty suka danna horn gate man ya buɗe mata ta shiga suna gaida shi, parking tayi suka fito suna nufan entrance na palo,door bell Ruqayyah ta danna ba jimawa sai ga house help na gidan ta buɗe musu tana gaishe su, amsawa sukai suna shiga cikin falon, zaune suka kai suna tambayan ta aunty na nan "eh tana a sama bara na kirata"
"Yauwa mun gode" cewar Ruqqy.
Kafin ta wuce sai da ta fara kawo musu abu mai sanyi sannan ta haye sama dan isar wa da Anty saƙo
Ba jimawa sai gata ta fito bayan ta Anty. Ganin su eelham ne yasa ta fara washe baki tace "yau muna da babban baƙi sannun ku da zuwa"
Cikin dariyar maganarta suka gaisheta ta ansawa musu da kula, da tambayar su mutane gida, bayan sun gama gaisawan ne ruqqy take cewa "Anty jawaher fah?"
"Ai jawaher tun jiya ta tafi Kaduna bikin cousin sister ɗinta, Nima zuwa gobe i War haka ina can"
"Allah sarki da yake bamu yi waya ba kwana biyu! Allah ya kaiku lafiya" da Amin ta amsa, tana jan su da fira,
Elham kuwa mulmula maganan bakin ta take ta faman yi kafin tayi shahadan cewa "Anty bestie fah?"
"Bestien ki yana nan Kaduna tare suka tafi da jawaher! Yace yana ta kiran wayar ki amma kashe! Muma munyi trying same thing"
"Eh wayar a kashe take har yanzu ban kunna ba"
"Gaskiya kam ya kamata a kunna haka nan" amsawa tayi da "insha Allah" amma cikin zuciyar ta faɗi take "ai ni ban san duniyar da wayar take ciki ba wanda ya siya ya kwace kayan sa".
Bayan sunyi kaman one hour a gidan suka sallameta wai zasu gidan Anty Hanan, "haba daga zuwa sai tafiya kamar wayen da ake kora?"
"Ba haka bane Anty zamu je gidan Anty Hanan ne daman! shine mukace bara mu shigo Mu gaishe ki" cewar Ruqqy.
"Shikenan ko haka din ma am so glad Allah yayi muku albarka" da Amin suka amsa suna miƙewa,
"Ku dan jira ni ina zuwa" cewar Anty, ansawa sukai da toh suna koma suka zauna.
Fitowa tayi hannun ta da ƙatuwar ledar tana miƙa musu "yan mata na ga wannan sai a ƙara a kayan kwalliya! Dan nasan yara na basa ɗaukan last wajen ado" cikin jin daɗi sukai mata godiya sosai sannan suka fito tana yi musu rakiya har wajen parking lot. Wannan karan meenal ta miƙawa key dan duk ɗinsu babu wanda ya taɓa zuwa gidan Anty Hanan saidai ita tazo kuma duk zuwan da zatayi sai tayi musu ƙorafin akan rashin zuwan nasu.
Har suka bar gidan aunty na ɗaga musu hannu.saida gate man ya kulle gate sannan ta koma ciki tana jin kaunar yaran a rai dan duk suna da nutsuwa ga girmama babba.
Gudu take sosai da mota kaman zata tashi sama wanda dan dole eelham tace "nifa karkije ki zubda mu a titi banga ƴaƴana ba atoh"
Cikin dariya tana kuma ƙarawa motan wuta tace "iyeee masu yara yanzu ko kunya idanun mu bakya yi?"
"Ganin ku ne bana yi! ni dai abinda nasani ki bimu a hankali"
"Gaskiya kam tayi a sannu karta rage mana sadaki" cewar Ruqqy.
Dariya tayi tana cewa "insha Allah karku damu zamu je lafiya" amsawa sukai da Amin.
"Wai eely sabida Allah yaushe kika iya shararota ne haka?!" Cewar Ruqqy
Heɗe fuska tayi tana cewa "mi na faɗa da ba dai-dai ba?".
"essy mana madam! Zaki ji mi kike ci na baka na falling down? Kika cewa Anty kin kashe waya? Alhalin ba haka take ba! Kin kashe ko ya kashe?" Ta ƙare maganar cikin shaƙiyanci. Cikin sauri eelham ta dago da kai tana kallon ta alamun tayi shiru amma kaman tace Ruqayya cigaba ne. "Ina jinki ?"
Wata muguwar harara ta sakar mata tana haɗe fuska waje guda dan bata son Ruqqy ta faɗa, ita bama tasan ta yadda akayi Ruqayya ta sani bah.
Menal ne tace "Wai waye ya kashe mata wayar naga tana ta wurga miki harara ne?".
Cikin dariya sosai Ruqqy tace "kedai bari long story ne sai mun zauna na zaiyane miki from A-Z".
"Yau akwai labari da ɗumi ɗumin ta kenan"
"Aikuwa ki kaɗe Kunni da kyau yar uwa"
Cikin hararan su tace "yar uwan munafinci ba! Kije ta koya miki gulma zaki sani ne ai" tayi maganar tana kallan menal.
"Sai fa naji ahem! Yar uwa nima akwai abinda na gani a abuja da mukaje duk zan shafa miki"
"Yauwa ta waje na ai mun san komai"
Nan fa suka dinga tirkan dariya ita kuwa hita batun su tayi.
Horn ta danna inda mai gadi ya taho ya buɗe yana yi musu sannu da zuwa shiga sukai ciki bayan ta tsaya sun gaisa.
Koda tayi parking eelham bata tsaya jiran su ba tasa kai ta fice zuwa entrance ɗin falon.
door bell ta danna wanda aunty Hanan ta buɗe musu da kanta zuwa lokaci su meenal sun ƙaraso, shiga sukai suna gaisheta,amsawa tayi da kulawa tana tambayan su mutanen gida, "kowa na Lafiya qlau sunce a gaida ki".
"Ina amsawa! Ku kuma sai yau Allah yayi zuwan naku gidan nan ba! Ai da baku zo ba mun ɓata kenan"
"Allah sarki Anty tuntuni muke bin meenal ta kawo mu tanayi mana yanga is not our fault sai nata"
"Innalillahi Ruqqy kina rinka jin tsoron Allah, Ni yaushe kukai haka da ni sharri zaki yi min" ta ƙare maganar da wurga mata da pillow, ita kuwa chaɓewa tayi tana dariya haɗi da faɗin ba "gaskiya bane? tun yaushe muke binki ki kaimu amma kina yi mana yanga yau ma fa Saida ummi ta saka baki fah"
"Anty karki yadda da maganan ta kinsan dai bazanyi haka ba" tayi maganan tana marairaice fuska.
"A'a fah meenal na sanki sarai fiye da haka ma za'a samu"
Kicin kicin tayi da fuska ta juyo tana kallon eelham "eely wai kun yi min magana na kai ku nace ban zuwa" tayi maganan da ƙyafta mata ido alamar tace a'a.
Daman Elham jire take dasu ba tare da ta dube ta ba tace "eh mana! Sai da ummi ta saka baki Sannan"
"Shikenan tunda duk kun kware min baya! Babu komi" dariya sukai mata da ganin yadda taƙare maganar kamar wata ƙaramar yarinya..........
_________dan Allan dan Annabi (saw) ki gaya mana inda zamu samu su goggo, lokaci yayi hakanan da zaki dawo daga rakiyan yaya Anne! Wallahi ba sonki take ba dan masoyin ka bazai baka shawara kaci dukiyar gado ba,wanda a cikin dukiyar rabon naki kaɗan ne na tumulin takaba, ko mu goggo zata fi mu samun babban share a dukiyar baba dan uwa ta kori komai! Dama ace iya dukiyar mu kike ci da sauƙi amma wannan fa na goggo ne fah?bayan wannan ku ka ka kori baiwar Allah daga cikin gidan ta, matar da take miki kallan ƴar ta amma ita zaki watsawa ƙasa a idanu! Ke kina nan cikin daula baki da damuwar komi saidai kici ki sha ki kwanta amma itafa? kin taɓa tunanin inda su goggo suke kuwa? Kin taɓa tunanin bayan barinsu gidan nan wani hali suka shiga? Kin taɓa tunanin a inda suke sun samu sunci abinci ko a hannu waye suka faɗa Anne? Ni dan Allah roƙona a gareki ki taimaka ki gaya mana inda zamuje mu samu kakan mu nasan baza ta ƙi gaya miki inda zata koma bah! Plssss Anne" ta ƙare maganar kuka na kufce mata dan gaskiya tana buƙatan da tasan halin da goggo da kuma yar uwarta eelham suke.
"Lailai kam maleeka wuyar ki ta isa yanka! A matsayina na mahaifiyarki zaki na rinƙa gaya min magana haka? Kodan sake muku da nake shine har haka ya fara shiga tsakani na daku? Toh kar ku kama kanku dani kuga, kuma karku ga wai dan kun kasance yarana kuce bazan iya daukan mataki a kanku ba, bazan yi dubi da haka ba ko waye yace zai shiga tsakani na da dukiyata sai na shata masa babban layi koda ya kasance daya daga cikin ku ne! Dan haka Ƙofa a buɗe take kuna iya zuwa niman kakar taku amma duk abinda mutum yaji yayi kuka da kansa! Idan Kunni yaji shima jiki ya tsira,dan haka ku tashi ku barmin gida kar kuma na ƙara ganin ƙafafun ku har sai in nine na buƙaci haka".
Jiki na ɓari suka haɗa yanasu yanasu sukai waje su uku inda suna fitowa ko wacce ta shiga mota escort na bin bayan su da mota wanda ba kowa ya dauƙe su ba sai Anne dan a dinga kulan mata da shiga da ficen da suke.
Bayan fitar nasu ne cikin kaukuaran murya tace "yara kenan wannan abin da kuka ga inayi dan ku nake amma da yake baku gaji arziƙi ba kun koma yi min hassada, wallahi ko wacce ku tace zata shigar min hanya sai nayi watsi da ita tana daukan jakan ta ta fito dan dama fita zatayi......
Tana shigowa ta faɗa kan bed tana rushewa da kuka mai cin rai da zuciya, mijin ta da yake falon ya taso ya bita dan yasan za'a rina, sosai ya dinga bata baki yana tausan ta, ita kuwa abin yana ci mata tuwo a kwarya tun tana iya ɓoye damuwarta dan kar mijin nata yasan halin da suke ciki amma ga shi yanzu zuciyar ta ta kasa cigaba da haka tana buƙatar wanda zata yi shering na damuwar ta yasa ta buɗe baki tana cewa "wai har tsawon wani lokaci Anne zata gane gaskiyar da muke faɗa mata ne? Sai yau.........."
"Shiiii is ok dear, muyi ta saka ta a addu'a! Babu abinda ya gagari Allah,kuma insha Allah muna fatan nan kusa ta gane ta kuma dawo kan hanya"
"Har sai yaushe zata......"
Ok baby komi zai wuce ko yanzu Allah idan ya ga dama zai canza komi, stop bothering ur self! Okay?"
Gaɗa kai tayi tana sauke ajiyar zuciya,shikuma ya goge mata hawayen fuskan ta tass yana janta da fira dan ta sake cikin ikon Allah kuwa ta ware kaman ba ita tasha kuka ba tunda gashi yanzu harda dariya...........
________ "kina abu kamar ba Hajiya Hajara da nasani ba, duk kin wani bari yar ƙaramar alhaki zata birkita miki tunani? kin bi kin saka tsoron yarinya a zuciya har tana iya buɗe baki tayi miki yadda ta so a ko gaban uban kowa,amma ki kasa bada answer, nifa daman tun fill azal haushin yarinya nan nake ji ga ita ba wani kyau ba sai gajarta Allah na tuba kamar wata yar kunkuru! Nifa da kin ma yi shawara da Ni akan maganar sakin yarinya nan da ba'ayi shi ba dan idan kin lura itama Aziza tsoron yarinya take kuma ita zata yi miki maganin ta amma kin ɓata komi! kin sakar mata fuska har ta kai tana yi miki barazana da zatayi miki tonan asiri! To idan tayi kuma sai mi? kan ki farau ko kanki ƙarau? Idan zaki tashi tsaye ki miƙe daman dan ta gan kina yi mata da sanyi ne....." Katse ta momma tayi tare da faɗin "Hajiya Baraka baza ki gane ba ne, bawai ita nake tsoro ba hatsabibancin ta nake gudu kinsan yarinyan nan hatsari ke gareta shi yasa nake bin ta a sannu da na samu na ƙwaci recording dake a hannun ta, Kinga daganan zata gane asalin wace Hajara".
"Shikenan Allah ya shige mana gaba ya shiga tsakanin mu da wannan kunkuru ibliss"
Cikin dariya tace "Hajiya yanzu surikan tawa ce kunkuru ibliss?".
"Eh mana ai yarinyan hatsabibiya ce ta ƙarshe" .
Momma ta buɗi baki zata yi magana kenan sukaji ringing na waya wato akwai mutum a ƙofa yana yi musu laɓe cikin hanzari suka buɗe kofan amma babu kowa fitowa sukai suna dube dube amma basu ga alamar mutun ba, momma ce da ranta ya ƙara ɓaci haɗe da tashin hankali tace "har Ni za'a koma yiwa laɓe a kuma biyo ni har cikin ɗaki na? Lailai kam ai kuwa mutum ya yi ta kansa kafin in juyo zuwa garesa koma waye".
"Haka gidan naku ya zama dauke da munafukai kusfa kusfa? Toh Kinga Hajiya Hajara banga ta zama ba bara nazo na wuce,sai kuma kin ƙara jina"
"Muna tautaunawa zaki wani ce zaki wuce dan Allah mu ƙarƙare maganar'
"Niiiii Baraka rufan asiri ki barni na mutu maza su kai ni ba mata ba, dan haka sai anjima"
Kallon ta momma kawai take har ta bar falon,saida ta ƙara duddubawa amma babu kowa sai ta koma ciki
Hajiya Baraka kuwa koda ta fita sai da ta duba tagan babu momma babu kuma sauran wani waje sai tayi wuff ta faɗa ɗakin mamy tana sauke ajiyar zuciya.
Mamy ke ta faman Safa da marwa cikin tashin hankali.
Tura ƙofan tayi ta shigo tana kallan mamy haɗi da faɗin
"kekuwa Hajiya kubra taya haka ta faru? hmmm sauƙin abin ma da bata gano ki ba, kinsan matan nan ita da muƙarrabanta ba imani ne dasu ba! alhamdulillah da dayar can ne ai sai ta binciko inda kika ɓuya dan tafi ita wanga risk a halin yanzu! ni ba wannan ba je ki duba min na samu na wuce kafin su farga da ni"
Batare da mamy tace komi ba ta fita dan ta dubo dan ta firgita matuƙa, dawowa tayi tace "kiyi sauri ki fita babu kowa" ko sallama basu tsaya yi ba ta fita a gaugauce daga gidan sai da ta fita daga gidan gaba ɗaya sannan ta saki murmushi da cizan lips,kiran waya tayi bai wani yi dogon ringing ba aka ɗauka bayan sun gaisa ne take cewa "Hajiya kina gida ne?" Shiru tayi alamar tana sauraren dayar bangare "ok gani nan tafe! Sai nazo,amma ki sanar da waɗan nan bosawan naki kar inzo suyi ta fama yi mini mazurai da ido! Ok toh". Kashe wayar tayi tana tare taxi shiga tayi tana gaya mashi sunan anguwan da zata.......
_________ zaune take a kan gado na masu jinya ga waye kare a kunnin ta tana trying number, sai da tayi gud 10 call ba'a ɗaga ba cikin rashin damuwa daman tasan za'a rina, aje wayar tayi tana faɗin "idan ka huce zaka biyo call ɗin"
Can dai tagan kaman ba zai biyo ba yasa ta ƙara bashi wasu miss call ɗin wannan karan har yafi na farko.
Cikin sarewa ta ƙara kira wanda a wannan karan tace in har ba'a ɗaga ba bazata kuma kira ba.
Ringing take sai da ta kusa katsewa sannan aka yi picking sai dai ba'a ce komi ba.
Cikin sauke ajiyar zuciya da muryan shagwaɓa wanda tasan yana narkar dashi tace "Hello!"
A bangaren AS kuwa daman bacci yake dan dare ne a can wajen su inda su mubee kuma daren su baiyi nisa ba.
Cikin lumshe oily eyes ɗin sa ya motsa baki cikin murya bacci yace "uhm"
Ƙara narkewa tayi kaman tana gaban shi tace "let turn it to video call".
Cikin shan kamshi dan so yake ya hora ta akan abinda tayi bai jira cewar ta ba yace "gud night" yana kashe wayar gaba ɗaya dan idan ya cigaba da ɗauka zata ci galaba a kan shi, shikuma baison haka har sai ya hora ta.
Sake tayi da baki tana kallon wayar ganin ya datse call ɗin, kwafa tayi tana ƙara trying number saidai is switch off.
Cikin jin haushi tayi wurgi da wayar saman sofa dake a ɗakin sai faman kumbura take tana gun gumi dan hakan da yayi ya mugun ɓata mata wato ga damuwa zata dame shi,shi yasa harda wasu kashe wayar baki ɗaya. Tana a cikin wannan halin ne bacci yayi gaba da ita daman cikin magungunan da suke bata akwai na bacci a ciki.
Jujjuya wayar ya rinƙa yi a hannun shi da murmushi ɗauke a fuskar shi dan yasan yanzu ya kaita iya wuya.
Aje wayar yayi yana komawa baccin shi dan yau yasha zirga zirga a ƙasan mutane,yana kwanciya kuwa ba jimawa wani baccin yayi gaba dashi, dan shima AS yana matuƙar mutunci da bacci sosai........
_______ bayan sunyi sallar isha'i ne sukai shirin tafiya gida wanda da da hali Anty Hanan zata ce su kwana ne dan itakam so dangi ce, ita da mijinta suka fito sukai musu rakiya har parking lot suna musu gargadi da banda rough drive, Saida suka ga tafiyar su ne sannan suka koma ciki inda duk jikin ta yayi wani sanyi kaman tace su dawo shikuwa uncle yana ta tsokalan ta......
Da yake meenal akwai iya driving ɗin gudu nan da nan suka iso gida inda suka fara shiga part ɗin ummi suka gaishe ta sannan suka shiga na umma, anan dai Elham ta fito ta barsu ta shiga part ɗin goggo daman a nan ɗakin ta yake dan bata yarda ta raba jaha da goggon ta ba kuma amanarta.
"Idanun ku kenan? Ai mun zata a chan zaku kwana ashe dai kuna hanya! Toh ya kuka baro namecy ta?".
"Tana gaida ki"
"Ina kuwa amsawa"
Dudduba falon tayi amma bataji motsin su Anwar ba yasa eelham tace "goggo yara na fa ban ji motsin su ba?"
"Masu yara manya".
Taɓe baki tayi tana cewa "pls mana goggo"
"Yaran da kika wuce kika barsu, da Anwar ya dawo ya dinga mana ihu a gida wai shi a kaishi wajen umm ɗin sa dakyar da suɗin goshi yaron nan yayi shiru! Yanzu ma wani kukan yayi kafin yayi bacci yana can ɗaki".
Cikin sauri ta nufi cikin ɗakin nata inda ta same shi yana bacci amma sai sauke ajiyar zuciya yake.
Zama tayi gefen shi tana shafa fuskar haɗi da faɗin "I'm sorry boy" tashi tayi ta ciro mishi Kayan bacci ta canza masa tana gyara mishi kwanciya, sannan ta fito daga ɗakin dan tambayar goggo Anam.
"Goggo little fah?"
Kafin goggo tayi magana sai ga sallamar ummi ta shigo hannun ta dauke da Anam dake ta faman bacci dan itama kuka tasha ta tashi daga bacci bata ga eelham ba sannan kuma bataga Anwar ba, babu kunya kuwa ta ƙarasa wajen ummi tana karban ta, ba musu Ummi ta sakar mata ita, gaida goggo tayi inda ta amsa da kulawa tare da cewa "ai da kin bari tazo ta ɗauke ta da kanta! Daman yanzu take tsare ni da tambayar ina little ɗinta"
Itama cikin dariya tace "a'a goggo ai gwara dana tattaro mata yarinyan ta kafin tazo ni manta"
"Kema an gwada miki fin ƙarfi dasu kenan"
"Cikin murmushi tace kwarai kuwa goggo"
Jin haka ne yasa EElham tana murmushi ta shige cikin ɗaki dauke da Anam.........✍️